Showing 6001 words to 9000 words out of 190952 words

Chapter 3 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

392

himself down, ajiyan zuciya zuciya yasauke yace "jeki dauro alwala kizo nan kiyi salla agabana inkinga dama ki kara dawomin nan da towel, tashi daga nan, will you get out of my sight ko saina saba miki!" ya daka mata tsawa da gudu ta tashi tai ciki tana kuka sosai, cike da kunan rai Mummy tace "Alhaji dan Allah kadinga yimata ahankali...." "don't tell me rubbish Maryam!" Abba yadaka mata tsawan da saida yasa tai shiru da sauri, cikin fushi yace "I said don't tell me rubbish Maryam! while kullum ina fita nema dan na wadataku keda yayan mu, nabarmiki duka yaran nan namu amana, ke kina nan kina lalata Rahima, babu wanda Rahima ke gani da daraja aduniyan nan, bata ganin kowa da gashi, could you imagine saidai mai gadine zai kwaso mata kayan data shanya which am sure bama ita ta wanke suba, kina gidan nan tareda dukansu kin kasa sata tai salla me amfanin kito eh amatsayin ki na mahaifiyarta? An gayamiki Rahima yarinya ce har yanzu? Allah zai tambayeni dagani harke kan yanda muka bama wayan nan yaran tarbiyah" yanuna mata duka su Siddiqa da kansu ke kasa ganin ran Abba yau yabaci yanama Mummy fada which of course sunsan she deserves it, Abba yacigaba yace "yaran nan matane, idan bamuba Rahima tarbiyah ba intai aure me zata bama nata yayan iyye? Wani irin hali kikeso taje tana nunawa agidan mijinta, angayamiki zata dawwama tana rayuwa damune? Dazu da rana awurin aiki Aminina yasamen da magana dayamin zafi yamin ciwo amma nasan alkhairi yake nufi dani da bazaizo yamin maganan ba" yadanyi shiru yana sauke ajiyan zuciya sanan yace "yau zai taho aiki yabiya ta school dan ijiye su Aisha da Hafsat a school yaga driver ya sauke Rahima tana sanye da Jean fa da t-shirt sai dan ficicin gyale akanta rabin gashinta awaje agabanki yarinyar nan tai shiga kaman yarinyar arna ta tafi makaranta haka baki hanata ba, idan kinsan bazaki iya bama yarana tarbiyah ba zanje na auro wacce zata basu, this children are my life, gift din da Allah yabani ne inhar zan fita nema nabarki dazu bazaki koyamusu abinda yakamata ba wlh zan iyasaka konawane na auro wata matan inhar ta yarda tai na'am zata bama yarana tarbiyah nagayamiki" faduwa gaban Mummy ya shiga yi, tasan halin mijinta tsaf kaifi dayane wlh kuma zai iya aikata hakan, babu abinda ta tana aduniyan nan kaman kishiya, ahankali ta tsugunna tareda kama hannunshi tashi Siddiqa tayi daga wurin hakan yasa sauran yaran ma duk suka tashi sukai dakinsu, cikin damuwa sosai Mummy ta damke hannun Abba ahankali tana kallon fuskarshi tace "nai kuskure baban Siddiqa, amma kayakuri, ka gafarce ni zan gyara, ka gafarce ni dan girman Allah karkace zaka karo aure sabida tarbiyah yara, bagasu Siddiqa ba banine nabasu tarbiyah ba duk nice ko, to kayakuri dan Allah" tai shiru tana kallonshi ganin yaki kallonta har lokacin bala'ine bayyane karara akan fuskarshi yasa ta fashe da kuka mara kara sosai ta yanda yaran bazasu jisuba irin kukan nan mai karya zuciyan miji, cikin kuka tace "nayi kuskure, na yarda nai kuskure, Alhaji inason Rahima dayawa ne, ina son yarinyar nan sama da tunanin ka, saisa bana iya mata fada, burina aduniyan nan shine kome yarinyar nan keso tasameshi shikenan burina, banson naga tana cikin damuwa ko cikin bakin ciki, yayyunta kyaranta sukeyi taita kuka, kaima fada kake mata kullum taita kuka, ni inban jata jiki ba abin zaimata yawa she is too small, kowa Rahima, kowa Rahima, komi Rahima, Rahima tai kaza tai kaza, ni kadai Mummy ta ke lallabata najata jiki, na sanyata murmushi amma kayakuri bazan karaba nai kuskure mijina kayafe mini" tafashe da kuka sosai, ba karamin sosa zuciyan Abba kalaman ta sukayi ba kasa daurewa yayi yajuyo ya kalleta ganin yanda take kuka yasa yasa hannu yadago ta yace "tashi kiga bar kukan hakanan, yi shiru" ya zaunar da ita gefenshi, hannunshi yasa akan fuskarta ya share mata hawayen tasa kafin yakama hannayenta yahade su waje daya, cikin wani yanayi na damu yace "you are getting me wrong Maryam, baki fahimce magana taba, listen I appreciate irin son gaskiya na tsakani ga Allah dakike ma autan mu, nima inason Rahima sama da tunanin ki fadan danake mata danta gyara dabi'un tane, yaro bazai dinga kuskure ba kadinga mai dariya kana nunamai yay daidai ba, inkai hakan cutar da yaron kake, I know daman u as the mother yakamata tadinga samin kwanciyan hankali da happiness a wajenki wanan bakiyi karyaba, abinda nake kokarin nunamiki anan shine ki dinga sata tanayin the right thing, Rahima tadena fita babu hijabi, babu mayafi, haramun ne a musulunci tana bayyana surarta, idan wani abu yasameta fa? Idan surarta ya burge wani da baida niyya mai kyau yay mata fiyade fa? Kinyi wanan tunanin? Ki hanata rashin kunya, sanan kidinga sata tana salla akan lokaci, aduk lokacin dasu Siddiqa zasuyi girki kidinga sasu dukansu ba ita taje ta kwanta ba suje suyi girkin tare, gyaran gida tare, wanki tare, su dinga all house chores tare, yarinyar nan babu abinda ta iya kinga hakan bai daceba kin gane nufina yanzu?" yay maganan yana shafa kumatun ta yanadan murmushi, gyadamai kai tayi itama tana murmushi tace "hakane zan gyara i promise you dan zinare na zakaga chanji" dan dariya yayi yace "ina sonki sabida kina daukan gaskiya, am sorry namiki ihu gaban yaranmu kinji, kiyakuri I was angry then ne yar Zinariya ta" girgixa mai kai tayi tace "bakomi yawuce" motsi dasuka ji yasa suka waiga Rahima ce tafito sanye da wani dogon pink hijabin ta da dadduma a hannu idanun nan sunyi jajir fuskarta duk ruwan alwala, daure fuska Abba yayi yace "shimfida dadduman kihau kiyi sallan kigama kizo" wasu sababbin hawayen dasuka zubomata ta share tana kallon Abban tace "dan Allah Abba karka dakeni kaji dan Allah, please Abba na" wani bakin kallon dayamata batasan lokacin data shimfida dadduma da guduba tahau kai ta kabbarta salla, ganin bamata da natsuwa yasa Abba yace "ki natsu kiyi sallan nan da kyau" kallon Mummy dake gefenshi yayi duktai wani irin kala tana kallon Rahima dake salla, hannu yasa yajuyo da fuskarta ta kallai dan murmushi yamata yasan ta damune yace "kawomin abinci naci, kiramini yarana sufito muci tare, dazaran naci zanyi wanka natafi study room yau zanyi kusan rabin dare achan akwai wani case danake aiki akai" gyadamai kai Mummy tayi ta shiga tai ciki dan kiran yaran shikuma Abba yamaida hankalinshi kan sallan da Rahiman keyi ganin tanayi komi da kyau yasa yadan sauke ajiyan zuciya ya shiga yimata addu'an shiriya da chanza wa a ranshi.



Fitowan su Siddiqa yasa yajuya yana kallonsu kitchen duk sukayi harda Mummy suka shiga fito da kulolin abinci da tray, bajewa sukayi akasan babban falon Mummy tafara serving Abban su kafin ta zubama yaran, sallame sallan Rahima tayi ta jingina da kujera tana kallonsu duktai kalan tausayi, taba Abba Mummy tayi tace "dan Allah kayakuri Abban su aikin tubako Auta bazaki karaba ko?" gyadama Mummy kai tayi tana share hawaye tana turo baki, murmushi Mummy tayi ta kalli Abba tace "kagani bazata karaba, oya bama Abban ki hakuri" ahankali cikin muryan kuka tana kallon Abban tace "kayakuri Abba bazan karaba" murmushi Mummy tayi tana washe hakora tana kallon fuskan Abban daya daure batare dayace mata komiba tace "yauwa Auta na dena kuka Abban ki yahakura, bama yayyin naki hakuri suma" kallonsu tayi kaman yanda suke kallonta hawaye ne yazubo daga idanunta ta share sannan tace "kuyakuri" murmushi Siddiqa tayi tace "yawuce" murmushi Mummy tayi tace "yauwa oya zo wajena" kaman jira take da sauri ta tashi tazo tafada jikin Mummy tana rera kuka ahankali, Abba bai kara cewa komiba yacigaba dacin abincin shi yanajinsu yanda Mummy ke lallashinta, saida yagama sanan yatashi yafita daga dakin motarshi yaje yabude baya wani babban leda yadauko na Teems Pestry shop gabaki daya bacin ran da Rahima tasa shi yasa yama manta da tsaraban daya sayo musu sanan yadawo daki, Mummy yabamawa sanan yay corridor dan zuwa wanka ganin ana gab da kiran magrib, ice creams ne aciki Mummy tabude, murmushi tayi taciro biyu ta mikama Rahima dake jikinta tace "iyye kinga ice cream dinku jekisaka a freezer yay kankara kaman yafara narkewa anjima sai kidauko kisha" ahankali tasa hannu ta amsa ta tashi tai wajen fridge sanan Mummy ta cicciro daya daya ta mikama sauran yaran duk karba sukayi basu cemata komiba dan inda sabo sun saba kome Abba yakawo na Rahima double ne nasu dai dai, sawa a freezer tayi tadawo zama tai kusa da Mummy tai lamo akan hannunta, ahankali Mummy tace "nazuba miki rice kici" girgiza ma Mummy kai tayi tana yatsine fuska ko kadan batason cin abinci, abinci ma baya mata taste abaki yanzu, shiru Mummy tayi tana kallonta sanan tace "ankira magrib yi saikije dakina ki jirani zanje wajen Abban ku" gyadamata kai tayi ta tashi ahankali tai dakin Mummy duktai wani irin yaushi.


****
💫 _*BIN ABINDA ZUCIYA KESO*_💫


_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always💔



✍️ M Shakur


5️⃣ & 6️⃣



Wani babban bedroom ne hadadden da everthing looks absolutely neat dakin sai kamshin turaren wutan yan maiduguri dakin yake. Mata biyu ne sunci gayu sosai wearing wani material iri daya da aka musu irin gown dinan da ake kira da dinner gown mai ruwan gold sun daura head black shima sunyi kyau kowacce na sanye da makeup akan fuskarta. Tsaye suke kan wata magidanciyar mata dake zaune kan kujeran gaban makeken hadadden mirror kwalliyan dake dakin, daya daga cikinsu namata daurin kallabi, murmushi matar tayi tana kallon matan biyun ta madubi yanda suka dage dauri sukemata, daya daga cikinsu ne dake left side din matar tace "Ummi kinyi kyau wlh sosai" murmushi matar da aka kira da Ummi tayi cikin natsassiyar calm voice dinta irin na kamilallun manyan mata tace "nagode Nabila" karasa daurin dayan tayi ta kalli madubin tana kallon fuskan Ummi ta mirror tace "yauwa angama Ummi" murmushi tamata tace "angaida Yusra sarkin iya daura kallabi" dariya Yusra tayi cikeda farin ciki compliment from Ummi kaman kyautan kudi ne dan Ummi bata fiye surutu ba ko kadan, tashi daga kan kujeran Ummi tayi ta kalli kanta a madubi ba karamin kyau tayiba wani mahaukacin lace tasa mai bala'in tsada mai ruwan gold dakeda tiny zanen flower na Black, tasaka wani sarkan zinare daya dace da shape din wuyanta da warwaron shi a right wrist dinta, ta daura fine agogo mai kyau a left wrist dinta, purse dinta tadauka Black tazura takalmi na vinci irin mara takurawan nan mai dadin tafiya tadauko wani hadadden mayafin ta yafa tadaga kai ta kalli babban agogon bangon dakin cikeda dan masifa tace "me suke bata lokaci haka ba 9 za'a faraba this is past nine shine har yanzu basu fitoba, bari naje na tattaro su su fito mutafi" tai hanyar kofa harzata fita saita juyo ta kalli matan guda biyu tace "Nabila kun tabbatar kun fadama Nani komi banson jikokina suyi kuka, makesure you set everything and tell the Nani all she needs to know" gyadamata kai sukayi atare, Nabila tace "to Ummi, ba zasuyi kuka ba matar ta iya kulada su sosai, yanzun nanma na dubosu har sunyi bacci kuma basa tashi cikin dare in sukai bacci sai gab da asuba dinan" gyadamusu kai tayi batare datace komiba tafice, fita daga flat dinta tayi tai wani flat dake bangaren wanda tafito daga ciki, shiga tayi bayan tai sallama babu kowa a falon hakan yasa tai bedroom kai tsaye tun kafin ta shiga takejin hayaniya, muryoyin maza suna surutu, bude kofa tayi ta shiga da sauri, tsit sukayi kaman basu ke uban surutu ba da akejin hayaniyar su har falo, maza hudu ne adakin, uku ne atsaye duk suna sanye da Black suit da bakaken cover shoe sunyi masifan kyau da covers kaman wanda zasuje dai wani babban occasion, sai dayan dake zaune kan gado yana sanye da wani green wando dakeda layi jaa tagefe kafarshi sanye da farin safa sai jikinshi sanye da singlet. Agogon hannunta ta kalla kafin ta kallesu duka one after the other tace a"hiranku kawai kuke tayi daman ba shiryashi kukeyi kuda kuka cemin zakuzo tayashi shiri, kunsan karfe nawa? Oya kuwuce kufita kuje falo matan ku najiranku kufito dasu kuwuce mota gamunan zuwa" ta matsa daga jikin kofan ta nuna musu kofa alamun suzo su fita, sadaf sadaf sukazo suka fice one by one har dukansu ukun suka fita sanan ta maida kofar tarufe tayo inda dayan yake zaune yana kallonta murmushi shimfide kan fuskarshi, karasowa gaban gadon tayi tasa yatsa ta dungure mai kai tareda zubamai harara tace "biyema kannenka kayi kunata surutu instead of kashirya gashi lokaci yayi" murmushi yayi batare dayace komiba hakan yasa tasake watsamai harara taja ledan dake gefenshi wanda rigan sojoji ne keciki, hannu tasa ta zaro rigan tana balle maballin tace "oya stand up" tashi yayi ahankali dogone sosai dan yamafi mahaifiyar tashi tsawo, murdadde ne bana wasaba, ga wasu shati shatin six packs dayafito ta white singlet din dake jikinshi, baki ne shi very dark, yanada wani irin bright white idanu da gashin ido sosai bakake gasu dogaye yanada cikan gira gawani siririn hancin shi dogo dayakara ma fuskar nashi kyau, bottum lips dinshi is so so pinkish sai upper lips dinkuma baki hakan yabama bakin nashi wani irin alluring kyau baida gemu ko daya hakama saje baidashi kodan sabida anhana sojoji ajiyewane saisa oho. Yanada cikan jiki dan ko kadan he is not skinny one element dayasa aka dauke shi a soja shine tsayin shi dake karamai kyau koyana cikin mutum dubu zaka ganeshi sabida cikan haibanshi da kwarjini.
Ahankali yamika hannushi ya zura cikin hannun rigan kaman yanda Ummi tabashi sanan yamika dayan hannun yasaka yana kallon fuskanta yanda take rufemai boturan rigan, Murya chan kasa yace "Ummi yaushe zaki dena treating dina kaman baby wai?" batare data kalleshi ba tana sakanmai boturin tace "inka girma"


Dan turo baki yayi kaman zaiyi kuka yay exclaiming. "Ummi!" irin shine yaro dinan, murmushi tayi batare datacemai komiba har saida takarasa saka boturan rigan sanan tadago kanta ta kallai yanda yay da fuska yasa tadanyi murmushi taja hancin shi tace "inhar namiji baiyi aureba is always considered as yaro wanda bai girma ba bakaga yanda nake baka kaida Mu'az special attention ba why because bakuda mai kula daku, ni idan katambayeni wani zubin gani nake su Muhammad da Nuru sun girmeka dan sunyi auren su harda y'ay'a" tana karashe maganan tawuce abinta, wani clean takalmin sojojin shi dake kan shoe rag tadauko mai tana kallonshi yanda yadan bata rai tace "sa takalmin muje" tsugunnawa yayi yasanya takalman ahankali tareda kulle igiyoyin sanan yatashi yay gaban mirror shi yana takun nan daidai irin tafiyan maza dinan yaje yadau hadaddun turarukan shi ya fesa, sanan yadau wani black beret na sojoji yasaka ya gyara tama fuskarshi bala'in kyau, Ummi na tsaye sai kallonshi take tana murmushi juyowa yayi hakan yasa tai murmushi tace "har angama yaron kirki?" "Ummi!" yakara exclaiming sunan nata sabida baiso Ummi nakiranshi yaro, dariya Ummi tayi tace "to nadena sojana, mutafi" atare suka jera suka fice daga flat din nashi, ganin sauran har sun shiga mota already yasa suma suka shiga dayan motan kirar jeep, jeep din dayake ciki dagashi sai Ummi sun zaune abaya sai wani saurayi da shima ke sanye da suit baki kaman sauran mazan baikaishi girma ba amma sunyi kama yaja motar yana tuki yana tauna cingum. "yarda cingum dinan tunda kaiba mace bane Mu'az" Ummi tafada anatse kaman yanda tasaba magana, turo baki yaron datakira da Mu'az yayi yacire cingum din ya manna kan glass din motar yace "Ummi me cingum dina yayi? yau promotion night din Yayan mu amma am not still allowed to have fun, oh am tired Allah kaimu gobe nakoma wana school nabar muku gidan" bata kara kulashi ba dan rigiman Mu'az daban ce cikin yaranta, kodan yaga baida kani ne shine auta oho, tunda dai yacire shikenan aje ahaka. Hankalin shi nakan tuki yace "Yayan mu, Yayan mu" dagokai sojan yayi ya kallai yace "wat is it Mu'az, u are driving u need to be focus" kaman zaiyi kuka yace "ni dama nasani danabar Ya Muhammad ya tukoku this car is so boring duk kunyi shiru kuma nima sainai shiru, kullum kuyita shiru shiru kaida Ummi magana namuku wuya I don't know why, and magana is fun u know kasan mezan fadama ne" girgixa kai sojan yayi irin whatever dinan yacigaba da amsa sakonnin da aketa turomai na fatan alhairi da congratulations ta waya, agaban tangamemen checking point din Sani Abacha Barrack dake Asokoro Mu'az yay slowing down dan akwai motoci dayawa dake gabansu da ake dubawa kafin abarsu su shiga ciki, har aka kawo kansu, saukar da glass din motar kasa Mu'az yayi harda na baya ya kunna wutar motar hakan yasa motar tai haske wanda suka gani zaune abayane yasa suka wani irin kame mai tareda saramai. "Sir" gyada musu kai yayi yamusu alamu da hannu cewa su biyu ne da wanan motar data bayan su, da sauri sukama Mu'az alamu da yatafi motarsu Ya Muhammad ma haka tabiyosu abaya, agaban wani tangamemen Hall sukai parking inda aka tanada dan parking motoci sanan suka fiffito daga motar, da sauri Ummi ta shiga gyaramai kwallan riganshi kafin tai murmushi ta kalli sauran yaran nata tace "kumuje" Allah kadai yasan iya farin cikin datake yi yau, Ummi da shi sai Mu'az ne agaba, sai sauran yaran nata maza biyu da suma ke sanye da suit ko wanen su yarike hannun matar shi sunadan hira kasa kasa gwanin ban sha'awa suna biyeda su abaya, Ya Muhammad matar shi Nabila, sai Ya Nura dasuke cema Ya Nuru shine nabiyu agidan matarshi Nabila sai Ya Muhammad

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login