Showing 99001 words to 102000 words out of 190952 words
Chapter 34 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
yabashi katin next appointment din Rahima ya kwalama Asabe kira da sauri ta shigo, yace "bring all Rahima's things, and come along with the Rahima" gyadamai kai tayi yajuya tafita Dr kuma yacigaba da hira da Sameer dake amsa shi dai dai dan jiyayi ranshi yawani yi masifan baci, almost 8 minutes suka bata sai aka turo kofan dakin Asabe ne rikeda katuwar jakar Sameer na sojoji da kayan Rahima ke ciki sai Rahima dake bayanta ganin Sameer zaune kan kujera a office din yana magana da Dr dawani mai kama da Sameer din saidai ba sosai ba yasa taji gabanta yafadi da sauri ta saukar da kanta kasa, hannu Sameer yamikama Dr tareda tashi yace "thank you Dr saimunzo" sanan ya kalli Asabe yace "where is her hijab?" yamata pointing Rahima da yatsa batare daya kalletaba, hannun Rahima Asabe takama tace "wanan ko anbata hijabin bata yarda tasaka hakama hula duk suna cikin jakan nan" dagokai ahankali Sameer yayi ya kalleta kaman tasan kallonta yake itama tadan dago kai ta kallai hada ido sukayi da sauri ta sunnar da kanta, ahankali ta tsugunna tabude jakan hijabin dake saman kayan ta dauka ta zage zip din tareda zura hijabin, hannu Mu'az yasa yadau jakan ahankali yace "let's go" juyawa tayi tafita tareda Mu'az shikuma Sameer biyeda su, hakanan gabanta ke faduwa ganin a dawo ansake daukan ta again ina za'a kaita, bayan motan Mu'az yabude nata yana kallon fuskarta yace "shiga" shiga tayi ahankali tazauna batare data kalleshi ba ya maida kofan yarufe shikuma ya shiga ciki yazauna already Ya Sameer harya tada motan Mu'az narufo door dinshi yaja motar, tafiya sukai sosai sai kallon hanya take tai shiru har zuwa wani anguwa dabama tasan anguwanba duk zaman ta a Abuja, anguwan na yan gayune gidajen hadaddu, agaban wani gida Sameer yay horn mai gadi yabude musu ya shiga gidan, awajen parking taga sunyi parking, Mu'az yafito yabude mata baya ganin batada niyyan fita yace "fito Rahima" ahankali tafito su Nabila dake jikin window itada Fadila suna leke atare sukace "woww, Baby zokaga matar Ya Sameer she is so beautiful wlh"
Fitowa Rahima tayi ta kalli Mu'az cikin siriruwan muryanta tace "inane nan?" murmushi ya sakin mata yace "gidan Ya Noor ne nan" da sauri tace "Ya Noor? Wayeshi" ahankali yace "muje ki ganshi kanin Ya Sameer ne" ganin Sameer haryay flat yabarsu wajen yasa yace "muje kigani" ahankali take binshi duk tajita wani iri a daidai bakin kofan taga wasu kyawawan mata sun fito da saurinsu sukayo kanta. "Oyoyo Rahima" saiga wasu maza guda biyu suma su fito dataga suna kama da Sameer sosai saidai yafisu kyau da tsayi da cikan jiki duk antsaya ana kallonta ganin yanda ake kallonta yasa da sauri ta matsa wajen Sameer batai wata wataba takama hannunshi tarike gam idanunta nataruwa dahawaye, wani mahaukacin shewa suka shigayi ganin yanda takire Sameer shiko wani kunya yaji da sauri ya karbe hannunshi ya shiga ciki itakuma su Fadila sukai bedroom dinta da ita inda makeup artist kezuwa, karasawa wajen fridge Sameer yayi yabude yadau ruwa yabude bottle din yadan kurba sanan ya maida marfin yarufe ya kalli kannin nashi dake wani kallonshi yace "lemme go back to the office" da sauri Noor yarikemai hannu yace "wlh baxaka tafiba, boys oya" to his biggest surprise gani yayi ganinshi drag him to Noors bedroom sanan suka rufe kofa wani kallo Sameer yamusu Noor yadan sosa kai yace "Yaya munsanar da friends dinka kai aure munmayi inviting some to dinner damuka hada muku by 5 anjima sai bayan magrib mutafi gidanku, yanzu su Nabila za'a fara gyara amaryan ka" shiru kawai yayi yana kallonsu baice musu komi ba, yanaji yana gani suka hanashi fita.
Rahima kawai binsu take da dara daran idanunta tana gani aka shiga gyara mata kai wani gyara dabatama san kanshi ba, mai lalle namata hadadden gaske, aka kunna fanka banda AC dakin sabida lallen yay yabushe da wuri, duk wani shirin Amarya da ba'a rasaba saida suka mata harda wankan turare sanan akasa tai salla duk sukai salla, wuraren 5 makeup artist tataho aka shiga yi mata makeup nafitina aka gama tsaf wani irin kyan datayi kaman balarabiya sanan akasa tasaka wani white gown sky blue dayasha stones yana jamata kasa sosai sanan aka mata dauri, Fadila ta jawota takai ta gaban madubi tana murmushi tace "kinga yanda kikai kyau kaman fatalwa kuwa" kallon kanta Rahima tayi kafin ahankali takalli Fadila tace "mesa kuketa min kwalliya haka?" dariya dukansu suka kwashe da sauri Nabila tazo wajen rikeda Princess tace "ki tambayi Ya Sameer, bari kiga mu shirya Fadila" shiryawa suka hau yi cikin wani hadadden kaya dasukai anko itada Fadila, sunacikin shiryawa Noor yay knocking yace "baby all set fa" da sauri tace "we are coming out yanzun nan Baby" music sukaji yana tashi daga compound shiryawa sukai tsaf sanan suka fitoda Rahima dasuka rufemata fuska da net suka fito tsakar gida da ita Ya Sameer suka gani zaune kan wani royal chair yana sanye da wata bugaggiyar shadda sky blue anko shida Rahima, ga wasu friends dinshi da su Noor sukai inviting saikuma su kannenshi da sukasha white shadda da some few friends da matayen su, basu da yawa but gwanin tsari zaunar da Rahima kusada Sameer sukayi, aka shiga party ga abinci dan masu girki aka bama kwangilan girki ga drinks, Rahima dai kallonsu take ganin anamata abu kaman wasu ango da Amarya, Sameer yariga yafadi musu baya rawa so basu damai ba su suka dinga shirmen su daga baya suka dauko Rahima dataki tai rawan, kallonsu kawai Sameer yake ganin yanda family dinshi are so happy da auren shi dudda ga yanda auren yazo zaiyaji inama Ummi was here yasan da abin yafi haka haduwa......
Wuraren Magrib aka gama sanan yasa aka dakatar da wakan suka fita masallaci, SU fadila sukai ciki da Rahima suka chanza mata kaya zuwa wani fine lapaya bayan sunsa tai salla sanan suka hada mata wani nagani tasha da kyar yana dawowa ya shiga mota yace afito da ita zasu tafi Abban ta na hanya, fitowa da ita sukayi, sukasha ta shiga gaba Sameer yaja motar zuwa gidanshi, gidane nagani nafada danya tsaru sosai, horn yayi wasu sojoji guda biyu taga sun budemusu Gate Sameer ya shiga da motan ya kashe yafito, ahankali tabude itama tafito tana kallon ko'ina saida ta zagayo sanan yafara tafiya binshi ta shiga yi har zuwa cikin gidan, innalillahi heaven shine furnitures din da aka zuba mata, duplex ne gidan hadadden gaske komi yahadu tsayawa bada labarin gidan bata bakine, horn dasuka ji yasa yace "sit Abban ki ne yazo" fita daga dakin yayi hakan yasa ta zauna ahankali tana tunani dakuma fargaban haduwa da Abban nata, sallaman Abban ta dataji yasa ta dago kanta da sauri suka hada ido da Abban dake kallonta, bakinta nadan rawa rawa tace "in...ina wuni Abba" zama yayi kan daya daga kan kujeran Sameer yazauna akasa ganin Sameer yazauna akasa yasa ta kallai sai itama ta zauna ahankali akasa, gyaran murya Abba yayi anatse kafin yafara da salatin Annabi ya kalli Sameer yace "Sameer kai d'a ne dakowani mahaifi inhar Allah yabashi irinka to ya godema Allah, you are a treasure dat personally I cherish, And Alhamdulillah for knowing in this life and Alhamdulillah da mutum kaman kai mai hankali ilimi yazamo miji ga yardana haifa, koma mezan fadama kariga kasani, kuma komame zan fada maka awanan daren you've already done that even more Sameer dan cewa zanyi ga Rahima nan matarka kariketa amana but kariketa amana tun kafin ma tazama matar taka, da ayau zanfadi namutu I will be at peace because nasan mutum kaman natare da y'ata kuma zai riketa amana, Allah yamaka albarka Sameer, Allah yabuda maka kofofin samu, sanan Allah ya azurtaku da zuri'a dayyaba Allah yabiya maka bukatunka na alkhairi Sameer" ahankali Sameer yace "Ameen Abba" juyawa Abba yayi ya kalli Rahima da tunda taji Abba yacema Sameer Rahima matar shi taji kirjinta yamata nauyi, ahankali yace "Rahima! Ayanda kika taso da rawan kai aure kan natsar da yara irinku saisa namiki zabi zabin kuma Sameer ne, na daura miki aure da Sameer jiya misali 9 nadare, ga sadakin ki nan" yaciro wasu kudi dake envelope ya ijiye agefenshi kan kujera, yace "inaso ki natsu Rahima ki tuba, yanzu ke matar aure ce ki zubar da duk wata dabi'unki na banza, nina fadama Sameer makarantan ma yahanaki zuwa at all, yacemin zaki cigaba amma saikin chanza nan da next year, Rahima ni mahaifin kine kuma mahaifi baitaba tsanan abinda ya haifaba saidai ya hukunta abinda ya haifa idan yaron yay badaidai ba, duk wani abu dana aikata akanki sabida halinki ne, wanan auren da namiki shine last chance din danabaki, Rahima inhar baki zauna a auren ki ba kin natsu kin zubar da halayen nan naki na banza ba to ki rubuta ki ijiye saidai ki nemi wani uban da wasu yan uwan dan zanma cireki daga cikin yayana ne, kuma you know what I can do, ga mijinki nan kimai biyayya, yi nayi bari nabari, karnaji sirrin gidanki awaje, ki rike sirrin gidanki ki kare dukiyan mijinki, sanan ki kyautata tsakanin ki da mahallicin ki, ina miki fatan alheri, Allah yamiki albarka, Allah ya shiryar dake Rahima, sanan Allah ya yayemiki duk wanan halayen na banzan, Allah ya ganar dake ya natsar dake, ki kula da kanki kinji" gyadamai kai tayi tana chusa hannunta kan bakinta tana kokarin danne kukan dake taso mata tana kallon Abban, ganin haka yasa Abba yaji tabashi tausayi sosai ahankali yabude mata hannayenshi alamun tazo dawani irin gudu ta tashi tawani fada jikin Abba tafashe dawani mugun kuka dayazo mata daga zuciya, rungumeta back Abba ya bubbuga bayanta tareda yima kunnenta kiss yanajin wani sonta aranshi amma yarasa yanda zaiyi da rashin jinta ahankali yace "is okay kukan ya isa haka" sosai take kuka kaman zata shide cikin kuka tace "Abba am sorry natuba kaji, bazan karaba wlh, please kayafe min dan Allah" dago kanta yayi yasa hannu ya goge mata hawayen dasuka kasa dena zuba yace "naji nayafe miki Rahima, amma promise me kin dena shaye shaye zaki natsu kibi mijinki sauda kafa kinyi alkawari?" cikin kuka ta gyadamai kai Abba yay murmushi yace "then is settled, na yafemiki, zan dinga kiran Sameer ina magana dake kinji" gyadamai kai tayi yadau kudin sadakinta yasa mata a hannu yace "this is your money, sadakin kine keep it with you kinji" gyadamai kai tasakeyi tana kuka sanan yazauna da ita agefe ya kalli Sameer da kanshi ke kasa yamike tsaye tareda gyara babban riganshi yace "bari natafi dare yayi" Rahima tanaji tana gani Abba yatafi yabarta tai kuka kaman zata sume takife kanta akan kujera ba'a wani dau lokaci ba Sameer ya shigo dakin da akwatin da Abba yakawo mata na kayanta ya kalleta yace "stand up let's go upstairs" tashi tayi ahankali cikin kuka, stairs yahau tana biyeda shi har sama wani daki yabude dakin ya jarababben hadu ga makeken gado ya ijiye trolley agefe sanan yadan kalleta, idanunta sun kumbura sosai sai kuka take, ahankali yace "stop crying" jeki alwala kifito yay maganan tareda fita daga dakin, bayi ta wuce kaman yanda yacemata ta dauro alwala tafito wardrobe din bangon dakin tabude taga babu komi ciki sai kamshi sabuntaka dayake yi ahankali ta tsugunna tabude akwatin da Abba yakawo mata, hijabin datagani asama tadauka, natane nagida ja tasaka sanan tabude kofa tafito, afalon upstairs din taganshi tsaye kan dadduma tahowa tayi itama tana tafiya kafafunta na hardewa sabida yanda yake kallonta takasa dagokai ta kallai harta karaso wajen, baice mata komiba ya kabbarta salla ya jasu jami sukai isha'i sanan yay raka'a biyu na nafila da Annabi ya koyar yajuyo yakama goshinta yay mata addu'a yagama tass sanan yazare hannun ahankali batare dayamata wata tambaya ba dan yasan batawani je islamiyya ba. Katoton tray dake kan center table din wajen yanuna mata yace "eat" kallon abincin tayi kaji ne sai dayan tray din drinks ne da farm fresh yogurt, girgiza mai kai tayi ahankali tace "am not hungry naci abinci achan gidan" ahankali yace "okay take it to the kitchen then" tashi tayi tazare hijabin tareda ijiyewa kan kujeran wajen tadan kallai tanaso ta tambayeshi inane kitchen amma takasa, hada ido sukayi da sauri ta sunnar da kanta kasa takasa magana sai wasada yatsun ta dasuka sha lalle take, ahankali yace "the kitchen is downstairs" gyadamai kai tayi ta tsugunna tadau tray din kajin sanan tawuce tafara sauka daga stairs din ahankali tana kallon ko'ina na falon, falon yamata kyau kaman me, dinning taje kofan datagani agefe tabude kitchen ne hakan yasa ta shiga, kitchen din babba sosai gawani Island da akayi a middle of it ansaka kujeru guda hudu anzagaye shi dasu, ahankali takarasa ta ijiye tray sanan tafito tahau stairs din har lokacin yana zaune a falon news yake kallo jinta hawo yasa yadago kai ya kalleta tray din drinks tadauka tasake sauka kasa taje kitchen tasaka su a fridge sanan tadawo sama, dakinta tabude ta shiga, kayan jikinta tacire dan duk sunbi sun isheta
59....
Kanta nawani irin ciwo hakama maranta bayi tabude ahankali ta shiga bayin yamata kyau sosai, wanka tayi da ruwan zafi sosai sanan tai brush da sabon brush din dataga an ijiye mata anan wurin, sanan tadau farin sabon towel datagani abayin tadaura tabude kofan bayin ahankali tafito sai kamshi jikinta keyi sabida wankan turaren dasu Nabila suka mata, hawaye daya zubomata tasake sharewa ta tsugunna ta shiga duba kayan akwatin idan akwai kayan baccin dazata iya sawa gashin kanta na warwarewa duk yazube abayanta, tana cikin neman kayan aka bude kofan da sauri tajuyo, hada ido tayi da Sameer da shima taga ya chanza shaddan dake jikinshi zuwa wani milk pyjamas dayadan bayyanar da kirjinshi dake cikeda gashi, kasa jure kallonshi tayi ta saukar da kanta kasa tama kasa cigaba da neman kayan, karasa shigowa dakin yay yamaida kofan yarufe yace "me kike nema?" murya chan kasa mai sanyi sosai tace "kayan bacci na" dan lumshe ido yayi yace "okay, zan kwanta gud night" dan dago idanunta dasuka cikada hawaye tayi ta kallai kaman wata mara lafiya kafin ahankali tace "gud night" bude kofa yayi yafita daga dakin ya kashe wutan falon saman sanan ya wuce dakinshi.
Bataga wasu kayan bacci ba sai wani barbie pants dinta dark pink, dan babba ne bai kamata ba adaidai hips dinta ya tsaya yarufe ko ina na bombom dinta, sai wata yar karaman t-shirt dinta plain white dakenan very light baida nauyi na crop dan iya cibiyanta ya tsaya hakan ya bayyanar da fine two lines waist bid dinta nayan gayu dan dakananun bid akayisu combination of silver da gold color bids yama dan tiny waist din nata mugun kyau, itadai anything leg chain da waist tana bala'in sonsu saisa take sawa, and tanada su daban daban dan tana chanzawa every every month, tashi tayi ta mayar da kayan tsaf cikin akwatin sanan tadau wani black ribbon ta kama gashinta dashi sanan takoma kan gadon ahankali ta kwanta tana kallon saman dakin tai shiru, juyawa tayi gefe tareda sauke ajiyan zuciya tana kallon window dakin da hadadden labulenta ya kare, gani taki kaman labulen namata shape din fuskar mutum da sauri tasake tajuyawa ta kalli kofa kafin ta lumshe idanunta da sauri trying to force herself to sleep kasawa tayi, bata iya bacci inhar batajin motsin mutane da maganganun mutane around her, wani irin fear takeji acikin zuciyan ta hakan yasa tafashe da kuka she really can't sleep alone, almost 12:15 takai zaune takasa bacci idanunta sunyija sosai, ahankali ta sauko da kafafunta kasa, ahankali tabude kofar dakinta tafito tana kalle kallen falon dayay duhu, barin kofanta tayi abude tafito tafara tafiya ahankali tana bude kofan dakin dake kusada nata ganin babu kowa adakin another bedroom ne shima yasa tai dayan dakin dake tachan bangaren tana goge hawayen daya zubomata ahankali tabude kofan dakin, dakin duhu bata ganin komi but jin kamshin turaren Sameer dataji yasa ta shigo dakin tana goge hawayen ta trying to locate bed ta kwanta, dan bugewa tayi da jikin gado hakan yasa tai yar kara. "washhh" tana taba babban yatsar kafanta tasaki kuka ahankali sanan ta tashi, jitayi tai karo da mutum sunwani fada kan gado, ihu Rahima tayi tarike hannunshi gam jin zasu fadi jin still tanakan jikinshi suka fada kan gado gadon yay wani bouncing yasa tasake rikeshi gam, hannunshi yamika ahankali yataba bedside lamp dakin yay haske fuskarta yake kallo kaman yanda itama take kallonshi tana kan bare kirjinshi gabaki dayanta dan babu kaya ajikinshi dagashi sai boxer harya fara bacci yaji sautin kukanta shine yatashi sukaci karo danshima baya gani cus d room was dark. Numfashi take saukewa da sauri da sauri tana kallon fuskarshi tadan saki baki abude gabanta nafaduwa, dan lumshe ido yayi dan baiso yana kallon fuskarta yace "wat are you doing in my room?" bakinta narawa sosai tace "ba....cci.." kallonta yayi still yana kwancen batare daya tureta ba yace "does this room look like yours?" girgixa mai kai tayi tace "ni nakasa bacci ni kadai am scared" wani dan gajeren wahalallen tsaki yaja yace "that's the problem with Indomie generation, get off me" yanda yay maganan chan kasa yasa bataji ba ta tsaya tana kallon fuskarshi, cikin dan fushi yace "nace kitashi daga kaina ko naikama da gado" da sauri ta daddafa kan kirjinshi ta tashi wani yarrr yaji yanda ta tattaba nipple dinshi dazata tashi, sauka tayi ahankali ta tsaya tana wasada yatsunta, tashi yayi zaune yabi jikinta da kallo idanunshi suka sauka kan waist bid dinta tsaki yayi ya kauda kai yaji wani masifa yatasomai yace "waike wace irin rigimammiya ce haa? Kin hana mutum bacci, oya come and sleep, zoki kwanta" yanda yay maganan da fada yasa tasaki kuka tajuya da sauri zata fita dakin, cikin fushi yace "come back here" dan juyowa tayi tana goge hawayen da bayan hannunta tazo hargaban shi ta tsaya, tsaki yakaraja yama rasa mezaiyi yanuna mata cikin gadon yace "kwanta" ahankali ta shiga cikin gadon ta kwanta tareda jan bargo ta lulluba