Showing 3001 words to 6000 words out of 190952 words

Chapter 2 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

390

idanunta sunyi ja kaman wacce akama shegen duka, karban goran ruwan Mummy tayi ganin tana neman shanye duka ta ijiye tace "ya isa kekuma zaki fasa cikinki da ruwane? Karbi yogurt dinan kisha yajin zai tafi duka I promise" karban yogurt din tayi tana sauke ajiyan zuciyan kuka ta shiga sha itakuma Mummy ta juya ta ijiye ruwan kan side drawer gadon sanan tadawo ta zauna gefenta akan gadon, ahankali Rahima ta janye Yogurt din daga bakinta ta ijiye tawani matso jikin Mummy tadaura fuskarta kan kafadan Mummy tai lamo jikinta nadan bari, cikin wani irin murya na mugun shagwaba tace "Mummy kibani abun please, yau baki baniba at all, am feeling hungry" daga kanta Mummy tayi da sauri daga kan kafadarta tana kallon yanda tayi kaman mara lapiya tace "kindai san babanku na garin nan ko, kuma kinsan baya bacci batare daya ganku dukaba, ki rufamin asiri kibari yay tafiya yacemin kwana uku zaiyi, gobe ko jibi zai tafi kibari inya tafi saina baki kinji" fashewa da kuka tayi sosai tana makema Mummy kafada tana goge hawaye da bayan hannunta, dan tsaki Mummy tayi cikeda gajiya da shegen rigiman banzan Rahima tace "ohh My God, Ke wlh kincika matsala Auta, nace kibari babanki yatafi ko kin wagemin baki kina kuka" kara kara karfin kukan nata tayi tana kallon Mummy tana ihu da sauri Mummy tace "to naji yishiru, yishiru lemme think, ki bari nai tunani to" shiru tayi tana sauke ajiyan zuciya tana kallon Mummy nata, hannu Mummy ta daura kan goshi tana tunani, kafin chan tabude ido ta kalleta murmushi ta sakinmata tace "shikenan to naji zan baki but saida daddare, kinga anama kiran sallan la'asar yanzu any moment from now babanku zai shigo, kibari idan zamu kwanta saina baki, yanzu tashi jeki cire towel dinan kisaka kaya babanku yahanaki zama da towel haka" dan turo baki tayi ta tashi tafita daga dakin tana tafiya ahankali Mummy tabita da kallo harta bace mata, dakinta tawuce ta tsallake barin shinkafan datayi tahau kan gado abinta, jakan makarantan ta tabude taciro wayarta Samsung mai kyau ta bude data tana dube duben message, fita tayi ta shiga game tafara bugawa, shima fita tayi ta jefar da wayan kan gado babu abinda kemata dadi, littafan ta taciro na school ta shiga dubawa suma babu wanda ke mata dadi hakan yasa ta watsar dasu akasa ta kifa kanta kan gadon tana nishi sama sama kaman mai asma tana bubbuga kafafun ta akan gado kanta nawani irin sarawa sai lashe bakinta take tana bubbude wa kaman wacce kejin kishi, bude kofanta da akayi yasa tabude idanuwanta dasuka kankance Lubabatu ce ta tsaya daga bakin kofa tana kallonta babu alamun wasa kan fuskarta tace "Malama kitashi kije ankira sallan la'asar nasan ma kona azahar bakiyiba kiwuce kije kiyi, kin daisan Abba yace mudinga kiranki idan zamuyi salla ko to kitashi" harara tawani irin watsa mata kafin takara gyara kwanciya kan gadon kifa kanta kan gadon tace "Malama kitashin mini agaban kofan daki tunda ba dakinki bane" daga bakin kofan Lubabatu tace "okay bazakiyi sallan bako bari nahadaki da Mummy" tsaki Auta tayi tace "anan dukanku kukafi auki gulmammun babbunan banza kawai" "Mummy, Mummyyy" Lubabatu ta kwalama Maman su kira, fitowa Mummy tayi ta tsaya daga bakin kofanta tana kallon Lubabatun, cikin tsananin jin haushi Mummy tace "wai menene matsalan ku da yarinyar nan eh, Zeenatu tasamata yaji a abinci kekuma mai kika biyota yanzu kimata, kasheta zakiyi?" cikin jin haushi Lubabatu tace "Mummy nifa ko dakin ta banma shigaba fa, kiranta nayi tazo muyi sallan la'asar" cikin fushi Mummy tace "to bazatayi ba kubarta inta gama hutawa zatayi Allahu Gafurur Raheem, wuce kibace daganan wurin munafukan yara sun tasa yar kanwarsu agaba wlh Allah zai saka mata" kallon dakin Luba tayi auta tamata gwalo tana kyalkyacewa da dariyan iskanci da sauri Lubabatu tawuce tana kunkuni tace "kiyita lalata ta yarinya bata salla kona asuba da kyar takeyi" da sauri Mummy tace "dani kike magana ciki ciki?" dakinsu ta shiga batare datace komiba, komawa dakinta Mummy tayi ta shiga bayi alwala ta dauro sanan tai sallan la'asar tafito dakin Autan ta leka ganin ta lumshe ido yasa tadauka bacci take tawuce dakinsu, ahankali tabude dakin dawani irin gudu Zeenatu tai bayinsu ta garkame kofan kwafa Mummy tayi tace "ai wlh saina rama mata, ba yanzu zamu haduba Zeenah" ta kalli Siddiqa dake kan dadduma tana kallonta tace "harya tafi Sadiq din?" gyadamata kai tayi, tabe baki tayi tace "shine bakizo kin fadamin ba, anyway kutashi dukanku kuje ku daura abincin dare, Luba tashi kije dakin auta ki sharo min shinkafan data zubar akasa kifito da komi waje" wani kallo Siddiqa tama maman nasu kafin ahankali tace "Mummy yanzu fisabilillahi ya zaki saka taje ta sharo abincin da kanwarta ta zubar ba dole su dingajin haushin autaba in aka kuma tabata kidinga masifa, ita autan batada hannu ne, bata iya aiki bane? Mummy gaskiya abinda kikeyi baida kyau wlh kina nuna sonk......." yowa kanta da Mummy tayi yasa tai shiru Mummy ta nunata da yatsa tace "ina baki girman ki amatsayin ki na yayansu baki kama kanki ko, wlh duk randa kika karamin magana haka I will not mind muna gaban kanninki ne saina kikkifa miki mari wlh, kitashi kiwuce kitchen kuhada dinner babanku yakusan dawowa" tashi Siddiqa tayi cikin bakin ciki sosai ta zare hijabin jikinta tafice daga dakin kaman zata tashi sama fuu, itama Luba tashi tayi Mummy tabita da harara tace "kindaiji aikin danasaki kiwuce ki dauko tsintsiya kije ki kwashe abincin daya bare inkin gama saiki wuce kitchen kuyi girkin" sanan ta kalli bayin tace "wlh Zeenah inna dawo dakin nan nasame ki abayi baki wuce kitchen kun daura abinci ba saina kakkaryaki dako ubanki inya dawo bazai ganeki ba" tana maganan tawuce tafita daga dakin.



Agaban dakin Autan ta tsaya tana kallon yanda Lubabatu ke tattare shinkafan Auta kuma na wasa da wayanta tana shishila kafa ko lura ma da Mummy batayiba. "Auta na" jin muryan Mummy yasa da sauri ta dago kanta, murmushi tayi ta sauko daga gadon da sauri tana gyara daurin towel din jikinta ashagwabe tace "Mummy na nazo yanzu?" Tsaki Lubabatu dake shara tayi ta cigaba da aikinta, ahankali Mummy tace "a'a anjima, me zakici yanzu dan bakici komiba, su dafa miki Indomie ne?" yatsine fuska tayi tareda girgiza kai dan batada apatite ahankali tace "a'a, banajin yunwa yanzu Mummy" murmushi Mummy tamata tace "to kwanta kicigaba da hutawa abinki" gyadama Mummy kai tayi tana murmushi tai kwanciyan ta tana hararan Lubabatu da gefen ido tana murguda mata baki, kallon Luba Mummy tayi tace "dau sharan kifita me kuma kikeyi?" daukan pakan tayi tafita daga dakin Mummy tarufo kofan tawuce tai dakinta.💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_* 💫

_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favour you always 💔


✍️ M Shakur



3️⃣ & 4️⃣



Ahankali Zeenatu ta lallabo tafito daga bayin tafito tana leke leke ganin babu kowa yasa da gudu ta kwasa tai kitchen dinsu, babban kitchen ne sosai irin family kitchen dinan dake dauke da komi irin na yan gayun nan, Siddiqa da Lubabatu tagani suna aiki, Siddiqa dake wanke kayan miyane agaban tap ta kalleta ganin ta shigo tace "zogashi kiyi blending kayan miyan nan nariga na wanke miki, stew zanyi" da sauri takaraso ta karba ahankali itakuma Siddiqa takoma gaban gas, blender ta dauka ta zuba komi ta nika saida tagama blending din tass sanan ta juye a bowl tazo wajen ta mikama Siddiqa dake zuba rice a pot bowl din, karba tayi ta ijiye agefe tana kallon fuskarta ganin duk tayi wani iri hakan yasa tace "menene Mummy tamiki fadane?" girgiza kai tayi hakan yasa Lubabatu dake yanka su carrot itama ta tsaya tana kallon Zeenah tace "to menene duk kikai wani iri?" hawayen dake kokarin zubo mata tasa hannu ta share cikin wani irin yanayi na bakin ciki tace "Ya Siddiqa wai mesa Mummy batason mu tafison Rahima, kuma muyakamata ta......" hannu Siddiqa tadaga mata tareda girgiza kai tace "Zeenah karma kifadi abinda kikeso kifadi nasan me kikeso kifada, konima nasan banson rashin kunyan Rahima but sometimes nafi putting blame din akan Mummy, Mummy ko kadan bata barinmu mu nunama Auta the difference between right and wrong kuma itama bata nuna matan, sometimes ba iskanci zalla takemana ba she really feels is very okay abinda take mana dan haka Mummy take nunamata, Mummy kullum kallon yarinya take mata, yarinyar da aka haifa jiya batasan ta girma ba yanzu, Allah dai ya shiryata, she will change eventually I know that komujima komu dade, now muci gaba da aiki kar Dady yadawo bamu gamaba" cigaba da aikin sukeyi su uku gwanin ban sha'awa sunadan taba hira.



Babansu bala'in mai kudine amma irin mutanen nanne da bai yarda ya shagalar da iyalinshi ba, dudda Mummy ta dameshi asamo musu mai aiki ki yayi acewarshi gashi da yara mata dasuka tasa tadinga koyamusu komi sunayi da kansu, saisa breakfast kawai Mummy keyi kullum shima dan suna zuwa makaranta da safene but weekend suke hadawa dakansu, gyaran gida ma haka sukeyi, dudda kudinshi bai irin ginin mansion dinan ba, gidanshi daidai daidai na rufin asiri ne 6 bedroom flat ne dakeda babban compound daya wadatu da fulawowi.



5:38pm
Horn akayi mai gadi yafito da gudu yabude gate danko a bacci yasan horn din motar Alhaji, shigowa wata babbar mota jeep tayi tai parking awurin da aka tanada dan parking, da sauri Mai gadi yarufe gate yadawo wajen parking din daidai wani magidancin mutum dake sanye da bakaken suit da neck tie ga wasu manyan littafai guda biyu masu kama da textbook a hannunshi idanunshi sanye da fararen glass kana ganinshi zaka gane daga aiki yake sabida yanayin shigan dake jikinshi, akalla mutumin zaiyi 64-65yrs, da sauri Mai gadi yadan russuna yace "barka da dawowa Alhaji ya kotu?" Mai gadi yay maganan yana mikamai hannu danya tayashi karban yan littafan hannun nashi dan murmushi yayi yabashi yace "Sani, barka da warhaka, ya aiki?" murmushi Mai gadi yayi yace "Alhamdulillah Alhaji" "to, to barkan mu" mutumin yay magana yanabin gidan da kallo wanda dabi'an shine kullu yaumin idan yadawo daga aiki saiyabi tsakar gidan da kallo yay inspecting gidanshi tsaf, idanunshine suka sauka kan kayan da aka shanyasu kan flowers yace "menake gani haka? Ban hana adena shanya a tsakar gidaba ga backyard nan inda akwai igiyan shanya kala kala, waye da wanan aikin?" Alhajin yay magana azafafe ayanda yay maganan zaka gane irin iyayen nanne masu fada da masifa sosai, cikeda girmamawa Mai gadi yace "Allah huci zuciyan Alhaji laifinane wlh, kayan Auta ce kuma tariga tafadimani idan suka bushe na shigan mata dasu na shafa'a ne, a yakuri bari na kwashe su yanzu nakaima ta su ciki" da sauri Mai gadi yajuya zaije wurin kayan cikin fada Alhajin yace "zonan, dawonan Sani" da sauri Sani yadawo, yace "this should be the last time da Rahima zata saka aiki irin wanan kayi kanajina ko?" gyadamai kai Mai gadin yayi Alhaji yajuya yay hanyar flat dinsu Mai gadi biye dashi, da sallama mai kara as usual yayi yabude kofa ya shiga ciki yana kallon ko'ina jin sallaman Abban su yasa da gudu har suna yar rige rigen fitowa su Siddiqa suka fito daga kitchen din sukai wurin Mahaifin nasu cikeda murna. "Abba oyoyo, Abba sannu da zuwa, Abba Sannu dazuwa" sosai ya shigo da masifa amma ganin yaranshi duk sun fito daga kitchen da gudu suna mai oyoyo da sannu da zuwa cike da farin ciki yasa yasakin musu murmushin dabai shirya yiba ya tsaya yace "yaran Abban su" karban littafan shi Siddiqa tayi daga hannun mai gadi, itakuma Zeenah tace "Abba nizan cirema neck tie" murmushi yayi yace "to yar albarka gashinan zoki ciremin" itakuma Lubabatu da saurinta ta zaremai jacket din suit din jikinshi har rige rige suke, murmushi mahaifin nasu yayi sosai ganin sun gama cirewa yasa yazauna kan kujera yana sauke ajiyan zuciya yace "to nagode, Allah yamuku albarka yabaku mazaje nagari" duk zama sukai kusada shi sukace Ameen Abba, Siddiqa tace "Abba yaya aiki ya kotu? Mutane nawa kasa akai kai gidan yari yau?" dariya dukansu sukayi harda Abban nasu dan Judge ne shi a federal High Court din Abuja kullum inya dawo sai sunmai wanan tambayan, murmushi yayi sosai yace "yau babu kodaya, case akayi za'a sake zama sanan za'a yanke hukunci, me kukeyi a kitchen dukanku gidan ya dumame da kamshin girkin yan matan Abban su" da sauri Lubabatu dake kusada Abban tace "girki mukeyi Abba mai dadi" waigawa yayi kafin ya kallesu duka, babu alamun wasa kan fuskarshi yace "ina Rahima?" da sauri Zeenah kaman jira take tace "Abba tana daki, Abba kagani Ya Luba saida taje takirata tazo muyi salla taki, tun sallan asuba batayiba, Abba kagayau dazu data dawo daga school tama Ya Siddiqa da Ya Sadiq rashin kunya harda cema Ya Siddiqa mayya, tacema Yaya Sadiq dansa ido, sanan muma tamana rashin kunya, kuma kaga Abba mukadai keta girki bata tayamu komiba wlh Mummy wai mubarta tahuta tagaji tana kwance adaki" shiru Abba yayi yana sauraron ta duk cikin yaran nan nashi hudu baiga wacce take bashi matsala marajin magana irin Rahima ba, gashi harga Allah kusan yafi sonta kan dukansu wanan natural haka Allah yadauramai but bataji saisa ko kadan baya wasa da ita, basa shiri, duk gidan shi kadai take tsoro, horata yake da kyau, sabida Rahima ne yanzu yake kokarin yasan yanda zaiyi yadena tafiye tafiyen nan, babu randa baya mata addu'a kan Allah ya shiryar da ita, koya zaneta taci kukan ta koshi baya hana anjima takara laifin dayadaketa akai saisa yanzu yarage dukanta sosai danta girma baiso yamata illa koyaji mata rauni tana mace, ajiyan zuciya yayi ya kalli Siddiqa babban yarshi ta farko dan dukta fisu hankali ga fadan gaskiya, ahankali yace "hakane Mamana?" gyadamai kai tayi tace "hakane Abba" kwala mata kira yashiga yi. "Rahima! Rahima, Rahima!!!"




A mugun zabure Auta ta tashi daga kan gadon jin muryan Abban su na kiranta, tsoron Abba take sosai bana wasaba, bakinta har rawa yake tsabagen firgita tace "na.....Na'am Abba, ganinan zuwa" gyara daurin towel dinta tayi tsabagen rudewa tama manta yahanata yawo agida da towel tafita daga dakin da sauri sauri gudu gudu tai falon.



Shigowa falon tayi harta karaso gaban Abba jikinta bari yake, sosa keya tayi arude tawani kwantar da murya looking so innocent kaman ta Allah, ahankali tace "sannu da dawowa Abba" tundaga kafa Abba kebinta da kallo daga ita saidan mustard towel din dake daure a kirjinta data daura tun dazu bayan tafito daga wanka ya tsaya mata acinya kanta babu dan kwali tai zuru zuru tana kallonshi, ko jiya saida yamata fada kan wanan daurin towel din gashi yauma same thing still saida ta daura, Zeenah Abba yataba batare daya janye idanunshi daka kan Auta datai zuru zuru tana kallonshi ba yace "je dakina ki dauko min dorinar nan mai baki hudu Zeenatu" dorina dataji Abba ya ambata yasa tafashe da kuka sosai jikinta narawa kaman mazari tace "Abba dan Allah ka yakuri menayi eh? Dan Allah karka dakeni banison dorinar nan please, Ya Siddiqa please kar Abba yadakeni" taja hannun Siddiqa takama tarike tana kuka sosai tana yarfe dayan hannun tana kallon Abba dahar lokacin kallonta yake irin kallon nan dake saka hanjin cikin yara kadawa in fear.




Ganin Zeenatu tadawo rikeda dorinar yasa tawani irin kurma ihu ta kwalama Mummy kira. "Mummy, Mummy kizo, Mummyna wayyo Allah na zan mutu" tawani fada jikin Siddiqa ta chukwikwiyeta tana kuka kaman za'a nikata a injin, Zeenatu da Lubabatu sai gimtse dariyan su suke dadi kaman ya kashesu ganin yanda mara kunyan ta rude haka, har Allah Allah take Abba yafara lallasata, all this haukan kukan tanayi kaman zata koma cikin Siddiqa ko tashi Abba baiyiba yanadai rike da dorinar a hannu yana kallonta cikeda takaici, ganin towel din jikin nata na neman kwancewa yace "saki Siddiqa kitashi kizonan" sakin Siddiqa tayi tana kuka sosai ta sauko daga jikinta tana rike da hannunta tana gyadama Abba kai kaman kadangaruwa, gabanshi Abba yanuna mata da dorinar yace "kneel down here kuma nace kisaki yayan ki ko, saken mata hannu" arude tasaki Siddiqa tana kuka sosai tana yarfe hannu tace "Abba dan Allah karka dakeni kaji dan Allah" tana maganan tana kneeling a gabanshi inda yanuna mata tana gyara daurin towel din jikinta tana kuka sosai, daidai lokacin Mummy tafito arude. "wayatabamin Aut......" kasa karashe maganan tayi sabida mugun kallon da Alhaji yamata ta tsaya chak agaban corridor, Rahima na ganin Mummy takara karfin kukan ta tanama Mummy alamu da hannu datazo ta ceceta tana kallon Abban nasu tana kuka, ajiyan zuciya Abba ya sauke anatse yace "Rahima!" cikin kuka tace "na'am Abba, Abba dan Allah ka yakuri, wlh wlh bazan karaba, Abba in kanawa binta Rasulullahi in kanawa iyayen ka kayakuri Abba, Mummy dan Allah, Mummy kizo" tai maganan tana kuka sosai tana mikama Mummy hannunta kaman mahaukaciya, ahankali Mummy takarasa shigowa cikin falon cikeda damuwa ranta duk abace, takaraso gaban Abba zatamai magana ya daga mata hannu ganin babu alamun wasa akan fuskarshi yasa tai shiru, cikin kakkausar murya yace "Rahima nahanaki yima yayyunki rashin kunya koban hanaki ba?" cikin kuka sosai tace "wlh kahanani Abba" gyadakai Abba yayi yace "bance miki kidinga kifitowa kuna aikin gida tareba" cikin kuka tace "kacemini haka Abba" ahankali Abba yace "good, ban hanaki yawo agida da towel ba?" fashewa dawani irin kuka tayi sosai tace "e....e..h kahanani Abba" "bance kidinga fitowa kuna salla tare da yan uwanki kullum ba?" gyadamai kai tayi hawaye kaman anbude dam tace "kacemini Abba" cikin kakkausar murya Abba yace "laifin ki nawa kenan?" cikin kuka tana kara mikama Mummy dake tsaye gefen Abba hannu tanaso tariketa tace "laifina hudu Abba" shiru Abba yayi ayanda yakejin haushinta inyace yamata hukunci da fushin nan zai iya yimata illa, he is just trying to calm

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login