Showing 93001 words to 96000 words out of 190952 words
Chapter 32 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
lau" sanin Mu'az cikashi zaiyida surutu yasa yace "Baffa na falo ko, let's go"
Suka wuce, sallama yayi suka shiga hadadden falonsu inda Baffa da Ummi kadaine ka falon Ummi kan dogon kujera Baffa kuma sanye da manyan kaya kan 1siter suna hira saisu Noor da Muhammad dake dining dukansu suna sanye da suits sunacin abinci alamun daga aiki suke, shigowa falon yayi anatse yakarasa inda Baffa yake cikeda girmamawa yadan duka yace "ina yini Baffa" murmushi Baffa yayi yace "lpy lau Sameer, kadawo lpy yanzu mahaifiyar ka ke cemin kaje gombe wani aiki aiko naga news din ashe kaine behind it, you are good my son haka akeso mutane kuma irinsu Wadugaga Allah yakara kara tona musu asiri aduk inda suke adoron kasan nan, sukuma yaran Allah ya saukesu lpy Allah yabasu lpy" atare kowa na dakin yace "Ameen" tashi yayi yajuyo ya kalli Ummi data zubamai ido kaman tana kallon TV ganin dukya rame mata kusada ita yazo ya zauna ahankali yace "ina yini Ummi na" murmushi tamai tace "andawo lpy soja" gyadamata kai yayi, Noor da Muhammad ne suka shigo falon har inda Sameer din yake kusada Ummi sukazo, Noor yace "sannu da zuwa Ya Sameer ina yini" murmushi yamai yace "lpy lau Noor, ya office" fine yace yana zama kusada shi Muhammad dake tsaye dan kujeran tacika yace "ina yini Ya Sameer kadawo lpy, harkadan rame wlh, ni saisa bazan iya aikin soja ba" murmushi Sameer yayi Ummi ta harareshi tace "lazy kawai" dariya yayi yakoma kan kujeran Mu'az yake zaune ya zauna. Ummi ta dubi Sameer tace "go and freshen up Baffan ka wajen ka yazo" girgixa kai yayi yace "nima akwai maganan danake so naida Baffa, anjima I will freshen up" ganin haka yasa Baffa yatashi yana gyara babban riganshi yace "okay bismillah muje sama" tashi Sameer yayi yabishi sukai sama, dakin marigayi mahaifinsu suka shiga Baffa yazauna kan kujera shikuma Sameer yazauna akasa, zama Baffa ya gyara yace "I hope magana zakamin kan zancen da I am sure kasan shine yakawo ni gidan nan this evening" dagokai Sameer yayi jin anbude kofa Ummi ce ta shigo dan takasa hakura so take taji koyasamo matarne, waje tasamu tazauna tareda gyara zama, Baffa ya kalli Sameer dayasake maida kanshi kasa yace "go on Son gani ga mahaifiyar ka we are listening" ajiyan zuciya ya sauke tareda fuzar da iska gabanshi nafaduwa ahankali yace "Baffa nasami wacce zan aura!" babu wanda yay expecting wanan maganan daga bakin Sameer, wani irin murmushi Ummi harshi Baffa sukayi, kafin suce wani yace "Baffa ina neman alfarma daya" da sauri Baffa yace "mecece alfarman Son?" kanshi akasa yace "inaso yau dinan zamuje kudauramin aure da ita I've already promised babban ta from now zuwa lokacin isha'i zamuzo" shiru duk akai a dakin kafin Ummi tace "wanan wace irin magana ce haka? Bikin ka damuke muyi nagani nafada, babban d'ana my first son is getting married kazaci karamin biki zanyi ne eh Sameer" ahankali Sameer yace "that will all come later Ummi, dan Allah Baffa yau dinan nakeso a daura auren" Baffa ne ya wurgomai tabaya yace "why are you so in a rush to get married kaida ba auren kakeso ba, why are you pressuring us muje a daura auren this night?" Baffa ya wurgomai tambayan yana kallonshi, faduwa gaban Sameer yayi yay dan shiru yakasa magana Ummi tace "badakai ake magana ba Soja" dan dagokai yayi ya kalleta kafin yamaida kanshi kasa ahankali, Murya chan kasa yace "sabida inaso na taimaki yarinyar ne" da sauri Baffa yace "taimako? Taimako? Wani irin taimako kuma, Sameer wacece wanan yarinyar dakake so ka aura?" shiru yayi gabanshi nafaduwa baya karya kuma baima iya karyan ba, and koda family shi will find out anything akan Rahima yafiso su faraji daga bakinshi, but yasan his family bazasu yardaba. "Sameer Simran!" Ummi takira full name nashi dan ayanda yakeyi yafara sa tana tsoro itama tace "ba tambayanka abu Baffan ka yayiba" ahankali ya sauke ajiyan zuciya yace "she is Rahima a drug addict" atare daga Ummi har Baffa suke kallonshi, cikeda kokonto tsabagen son ta gasgata abinda kunnuwanta suka jiyomata tace "yar shaye shaye kake nufi Sameer?" gyadamai ma Ummi kai yayi batare dayabari sun hada idoba yace "yes tana shaye shaye, yanzu haka tana rehabilitation centre, inaso na aureta because I want to help her, inaso na taimaki rayuwanta, change her duk tabar shaye shayen tadawo yarinyar kwarai natsassa, I want to do jiha......." "are you mad Sameer?" Ummi tadakama Sameer wani mahaukacin tsawa tace "Sameer anya maganganun da akeyi akanka ba gaskiya bane kuwan, anya bakada aljanu?" girgixa kai yayi yace "Ummi lafiyata kalau, I know what am doing, taimakon ta zanyi" "kaci uwaka da taimakon" tabugamai uban dakuwa da hannu cikin fushi sosai tace "for good 39yrs yanzu Sameer fama mukeyi dakai kayi aure kaki, kanenka duksunyi aure sun hayayyafa, yanzu da mukai pressuring naka ganin u are not getting any younger, Baffan ka yabaka 30days kafito da wacce zaka aura, dakaga 30 days din sun cika shine kazo kana cemana yar shaye shaye zaka aura Sameer, nice zaka auroma sirika yar shaye shaye, shaye shayen natama haryay worse and dangantata da rehabilitation centre shine zaka auromin?, wasa kake yaro, gwarama kafito da wacce zaka aura kabar maganan wanan yar shaye shayen dakakeyi" Ummi ta shiga masifa shiru yayi yanajin ta harsaida tagama tai shiru sanan ya dago kanshi ya kalli Baffa daya tsareshi da ido dahar yanzu baicemai komiba sanan ya kalli Ummi kafin yace "am sorry Ummi and Baffa, ita nakeso na aura idan kuma bazaku barni ba shikenan bazan iya ja da maganan ku ba amman saidai nahakura da auren har abada" yakara she maganan ahankali, tashi Ummi tayi cikeda fushi tafita daga dakin abakin kofar dakin ta tsaya ta kwalama su Noor dake hiransu akasa kira. "Noor, Muhammad, Mu'az kuzonan, you guys should come and talk sense to kan yayan ku, ni yayanku zai auroma yar shaye shaye, kuzo kumai magana" tashi yaran sukayi duk atsorace this is the first time sukejin fadan Ummi da Sameer karara sukai sama duk dakin suka shiga Ummi tanuna musu Sameer dake zaune akasa kanshi akasa tace "kunga yayanku ko Noor yazo yana cemana yar shaye shaye zai aura da tsabagen shaye shaye ya taba kwakwalwanta har aka kaita rehab dan ai wayanda brain dinsu yatabu ne sabida shaye shaye ake dangantasu da rehab kunga wanku wai itane zai auro, kuma da daddaren nan yake so aje wajen babanta adaura auren" ganin yanda Ummi keyi yasa Noor yace "Ummi calm down ki zauna please" zama tayi kan kujera tana kallon Sameer din, Noor ya zauna akasa kusada yayan nashi sauran ma suka zauna ya kalli Baffa yace "Baffa menene me yake faruwa?" shiru Baffa yayi baice komiba yana kallon Sameer din, gyaran murya yayi yace "Sameer me kake cewa inhar muka hanaka aurenta saidai ka zauna ahaka bazakai aureba?" ahankali Sameer yace "Baffa ita kadai ce wacce raina keso ya aura badan komiba sabida inaso nai jihadi na taimaki rayuwanta, inkuma kun hanani bazan muku gardama ba amman ni bazanyi aureba kuma dan banda wata wacce nakeson kuma na aura" cikin wani irin yanayi Baffa yace "haka kace?" shiru yayi Baffa yadakamai tsawa yace "I said haka kace Sameer?" gyadama Baffa kai yayi ahankali batare dayabari sun hada idoba hakan yasa Baffa ya karkada kafa yace "good" ya kalli su Noor yace "kumutashi muje masallaci ankira magrib muyi sallan magrib daganan mu wuce muje mu dauroma yayanku aure" da sauri Ummi ta tashi tsaye tace "Baffa!" hannu Baffa ya daga mata yace "kibarshi Sameer ba yaro bane yanada shekaru arba'in ba daya, Sameer yasan difference tsakanin right and wrong, sanan yasan in yan uwanshi sun yarda da abu dakuma in sunki, duk yasani, da ace shi yarone kaman su Noor da Mu'az da zamu iya hanashi amma yariga yawuce wanan stage din yasan meyake yi, if he choose this path dudda kin nunamai bakiso yace zaiyi ki barshi ba karamin yaro bane shiba, ni waliyinshi ne am only going there na sauke nauyina da hakkokina amatsayina na kanin mahaifinshi kuma mahaifinshi banda haka kuma babu komi, duk yanda yayi daidaine Allah bada sa'a" da sauri Sameer yace "Baff...." hannu Baffa yadagamai yace "I've given you that chance na magana and you've said wat u wanna say dan haka tashi mutafi banson jin wata magana daga gareka" shiru yayi yakasa tashi, "katashi mutafi nace!" ahankali yatashi yakasa daga ido ya kalli Ummi datake binshi da kallo cikin tsantsan bacin rai gaba Baffa yayi yakalli su Noor da duk suka tsaya yace "kumuje" binshi duk sukai abaya suka fita Sameer kaman kwai yafashemai aciki kasa fita yayi ya tsaya awajen kofa kafin ahankali yajuyo ya kalli Ummi suka hada ido baki yabude zaiyi magana Ummi tace "banson ji just go Allah bada sa'a" tai kwafa, zaiyi magana Baffa ya kwalamai kira daga kasa da sauri yafita duk ranshi badadi yasame su, batare da Baffa ya kallai ba yace "kira baban yarinya kace muna hanya" gyadamai kai yayi ahankali kannenshi sai kallonshi suke yaciro waya yay dialing number Abba.
Abba na zaune a dining su Siddiqa sun ijiyemai abinci yakasa shi expecting call din Sameer kawai yake yakira yacemai wasa yake yay hakane dan karya kaita kauye yaji wayanshi na ruri, da sauri ya dauka yakara a kunne, kafin yay magana Sameer yace "Abba Baffana yace nafadamaka we are on our way" Abba couldn't believe abinda kunnuwan shi suka jiyemai yama rasa mezaice da kyar ya tattaro yan kalaman bakinshi yace "Allah yakawo ku lpy" katse wayan Sameer yayi Baffa yace "kumu tafi" fita sukai daga dakin, sukai wajen Gate Baffa yaciro kudi masu yawa yamikama Mu'az yace "kaje tsallaken titi kasayo goro da sweet, kaje da gateman yatayaka dauka, kasamemu a masallaci" gyadamai kai Mu'az yayi yana kallon fuskarshi Baffa yawuce yafita yaran biyeda shi.
Kasa yarda Abba yayi da kyar ya lalubo number babban aminin shi Baban Aisha yakirashi yacemai yazo yanzu dan Allah, sanan yakira Chairman din NDLEA duk sukace mai gasunan zuwa, tashi yayi ciki dan ya shirya.
Akusan tare su Sameer da abokan Abba suka iso, shima Abba daman yashirya yaci gayu yana hango motoci yafito daga gidan ahankali yana kallon kowa yama kasa yarda, gaggaisawa aka shiga yi shi kanshi Sameer saida yay mamakin yanda Baffa bai nunama Abba komiba saima wani gaisuwan mutunci da aka shiga yi kaman ansan juna da dadewa gabaki daya sanan Abba yanuna musu masallaci yace "mu shiga, Bismillan ku yanzun nan aka idar da isha'i nariga na sanar da limamu zuwanku kumuje" atare aka dunguma aka shiga masallaci.
Zazzama akayi limam yafara gabatar da huduba kafin ya daura aure tsakanin Sameer Simran Sameer da Rahima Sambo Rikadawa, inda Baffa yaciro sadaki dubu dari da hamsin wanda sune kudin dake jikinshi yabiya mai Abba yakarba sadakin shafa fatiha. Sanan aka shiga gaishe gaishen farin ciki Sameer kanshi akasa yana zaune kawai shikadai yasan me yakeji, Mu'az yakawo sweet da goro limam yadeba yace za'a rabama jama'a gobe sauran Abba yasa gateman dinshi yay gida dashi, su Siddiqa na zaune a falo sukaga gateman na shigowa dasu goro, Zeena ne tace "na menene?" washe baki yayi yace "Alhaji yace nakawo gida nabarshi masallaci dawasu manyan mutane" yay maganan tareda juyawa yafita daga dakin.
Tattaunawa aka shigayi inda Abba yamasu Baffa introducing kanshi, sosai Baffa ya yaba da hankalin Abba ashe babban mutum ne kawai dai irin iyayen nanne dat are so unfortunate Allah yabasu yara marasa ji, ko kadan bai nunama Abba komiba har wajejen goma suka tashi aka shiga sallama aka tafi, ahankali Sameer ke biye dasu suka tafi Abba nadaga musu hannu, sanan Abba yakoma gida ranshi fess, kaman anmai kyautan aljanna, falonshi ya shiga yana murmushi Luba tace "Abba goron nan da sweet na miye?" murmushi yayi yace "don't worry my daughters I promise kaina sai mamanku tadawo sanan zan baku good news din" duk washe baki sukayi ganin Abba na farin ciki, yace "zan shiga study room dina, inkun gama ku kwanta" yay maganan tareda juyawa yafita yay study room dinshi, bude dakin yayi ya shiga ya zauna tunane tunane yake fall ranshi sanan ya kunna computer dinshi, wani page na italian world ya shiga kafin yadau number wajen da sauri yay dialing number da sauri yakara akunne saiyay magana. "I want full house furniture na royal Italian"...... Washe baki kawai Abba yakeyi yana wasu bayanai da banso kuji😛
56......
Koda suka koma gida kasa shiga falon yayi hakan yasa yawuce flat dinshi ahankali Baffa kuma ya tasa sauran yaran sukai bangaren Ummi, almost 1hr suka bata a flat din Ummi sanan suka fito Baffa da Noor da Muhammad kowannensu ya shiga motarshi dan komawa gida.
Dudda irin gajiyane dake jikinshi kasa bacci yayi, wanka kawai ya iya yowa yadawo bedroom din daure da towel a waist, he is so sad he is not happy he never wish for this to turn up like this, to Yaya zaiyi, agogo ya kalla hakan yasa yabude system dinshi dake kan bed din ahankali ya shiga Skype ya shiga kiran contact mai suna Ayaan, ringing kusan hudu kafin Ayaan yadauka yana zaune a office as usual sanye da pc, yana dauka yace "1 minute buddy" tashi yayi yacire lap coat din jikinshi ya sagale sanan yakarasa gaban wash hand basin din office dinshi ya cire hand glove yasa a trash ya wanke hannu sanan yadauko wani handy yadawo yazauna yana kallon fuskan Sameer ta screen din dayaga yamai wani iri, zama yayi tareda jawo kujeran gaba yace "wats wrong buddy?" wani irin ajiyan zuciya Sameer ya sauke ya fuzar da iska mai zafi yace "I got married an hour ago" da sauri Ayaan yace "y....ou, wait are you saying you got married today ko mekake cewa ban ganeba?" cikin wani irin cool voice yace "I got married Ayaan, dazun nan" yafadi maganan tareda dafe goshin shi, shiru Ayaan yayi yana kallonshi kafin ahankali yace "Sameer you got married, yaushe kasami yarinya, yaushe akaje neman auren har aka daura, when did all of this happen batare danasani ba? So ranan nan damukai waya all you said to me akan bakada wacce kakeso u will want to marry a matured mace soja was all a lie?" girgixa mai kai Sameer yayi ahankali yace "kaima kasan your friend never tell lies" da sauri Ayaan yace "yes I know buddy, the news hit me ne kawai with shock kagane, talk to me Sameer wats happening? Besides you don't look good at all" dan lumshe ido Sameer yayi kafin yabude ahankali yashiga bashi labarin tun ranan da yahadu da Rahima harzuwa yau da aka daura musu aure yanzun nan. Ajiyan zuciya Ayaan yasauke yace "Lord! What a story, buddy in this world akwai evil people, and your worse enemy shine wanda kullum yanama dariya yana nunama yafi kowa sonka nan ko he is killing you, wlh I pity yarinyar like sosai ta mugun bani tausayi, ka burgeni da you know the father nothing akan halin matarshi kaiba munafuki bane koba komi darajan 3 children dinta masu hankali but tasani Allah baya bacci kuma wlh saiya sakama yarinyar da looks at her as mahaifiyar ta, yarinyar dake sonta tsakani ga Allah, yanzu tunda kadauke Rahima daga gidan shikenan sai muga inda zata kara ganinta tadinga bata kayan shaye shayen, and karka damu yanda Ummi ke reacting is normal every parent will act like that, ka lallabata kaita bata hakuri trust me zata sauko, kacire damuwa aranka yanda kaga abun nan yafaru haka Allah ya tsara you can't escape okay" gyadamai kai Sameer yayi taredayin dan murmushi hankalinshi ya kwanta, Ayaan yace "to yanzu wats your plan with Rahima?" dan lumshe ido yayi yabude ahankali yace "I don't have any plans, but inaso dazaran tagama rehabilitation din tadena shaye shaye ta chanza zan rabu da ita, taje ta auri mai sonta kota cigaba da school" wani mugun kallo Ayaan yamata yace "wat do you mean by kasake ta? Baxaka zauna da ita karufa mata asiri ba, kasan inta koma gidansu me Mummy zata cigaba dayine ko daga ina zata bullo" dan jim Sameer yayi saikuma yace "okay, zan nema mata wani mijin inhar tasamu tsayayye saina aurama ta shi" wani irin murmushi Ayaan yayi baicemai komiba yace "ok, yanzu dai ka lallaba Ummi, poor Ummi tagama planning how she's going to celebrate her first son marriage amma yazo ya lalata komi" hararan shi Sameer tayi yace "get back to work bye" ya katse wayan tareda kashe system din ya kwanta yay addu'an bacci yay shiru yana tunane tunane ahaka yay bacci.
Da asubahi yatashi as usual wanka yayi yafito ya shirya cikin farin jallabiya yafito yatada gateman yawuce masallaci dan yasan Ummi zata tada Mu'az.
Wuraren 6:30 shida Mu'az suka shigo gidan, Mu'az dukya wani koma kaman mara lafiya ganin Sameer is not happy, ganin yay falon Ummi yasa Mu'az yace "Ya Sameer yau bazaka fita jogging ba?" gyadamai kai yayi yana shiga dakin, falon babu kowa sai yar aikinsu dake goge goge tagaidasu Sameer bai amsaba yayi hanyar dakin Ummi shikuma Mu'az yasami kujera yay zaman shi a falo baiso yanishi suje gaida Ummi tare dan ko kadan baiso anama Ya Sameer fada agabanshi bashi kadaiba harsu Ya Noor ma, sun tsani suga anama babban yayan su fada agabansu wani iri sukeji he can't explain the feeling, but the feeling is uncomfortable.
Sallama Sameer yayi ahankali yatura kofar dakin, hadadden dakin dake dauke da bban gado da hadaddun labulaye, Ummi na zaune kan wata Royal kujera ja dakenan ita kadai ce adakin one sitter tai relaxing bayanta tana sanye da hijabi hannunta rikeda charbi tana lazimi hada ido datayi da Sameer yasa ta lumshe ido bamatason sashi a idanunta, mugun haushin shi takeji bana wasaba, ahankali Sameer yamaida kofar dakin yarufe ya shigo yana kallonta shi kadai yasan yanda yakwshi fushin mahaifiyar shi agareshi sashi yake yaji kaman zai haukace, baida peace of mind karasowa yayi har inda take zaune ya zauna akasa, Murya chan kasa yace "ina kwana Ummi" kaman ma Ummi batasan wani hallita ya shigo dakinba haka tayi