Showing 84001 words to 87000 words out of 190952 words

Chapter 29 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

468

hakan yasa towel din kanta yakarasa warwarewa yafadi akan gadon tace "dan Allah kar amin allura" dan dariya Dr yayi yace "opisa wanan kanwar takane ko Hajiyar ka zance anyi raguwa anan" yay maganan yana dan rage tsawonshi a gabanta, yamika hannu zai kamo hannunta takase komawa chan karshen gadon da sauri, wani mugun kallo Sameer yamata yace "give him your hand right away" gyadamai kai tayi kirjinta na bugawa sosai tana goge hawaye da dayan hannunta, tadawo inda take zaune ahankali ta zauna, hakan yasa Dr yakarbi hannun yana murmushi ganin yanda take kuka yace "yauwa muga hannun ahankali zan miki" sake bare baki tayi tace "to kabani magani wlh zansha Allah amma karka samin alluran nan ajikina" ta karbe hannunta ta boye hannun abayanta tafashe da kuka sosai tace "dan Allah kabarshi kabani magani zansha wlh wlh please" hada ido sukayi da Sameer wani mugun kallon dayamata yasa ta bashi hannunta tareda runtse idanunta da karfi, daure hannun Dr yayi da igiya sabida yasami vein sanan ya soka allura ahankali dudda hannunshi babu wani zafin kirki amma saida ta kurma ihu tace "Mummy, wayyo Mummy zafiii" dan dariya Dr yayi yace "a'a kace yar Mummy ce, saisa kikeda wanan uban rakin, to angama" bude idanunta tayi tana kallon hannun da Dr yamata fixing drip.
Duk wacce ta karanta batare data biyaba Allah ya isa
How to subscribe
Zaki turo 300 ta account number na 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to watsapp number na 07012181461
48.....






Dr yadauko prescription sheet na hospital nashi yarubutamai magungunan sanan ya hada jakan yarufe yatashi yana gyara zaman eye glasses din idanunshi hakan yasa Sameer yatashi yamikamai hannu yace "thank you Dr" murmushi Dr yayi yace "bakomi saina dawo dubata anjima da night, makesure taci abinci yanzu dan saitaci abinci zata iyashan drugs dinan dazaka bata" ahankali Sameer yace "in sha Allah" sanan Dr yamusu sallama yawuce yafita tareda mayar musu da kofa yarufe, komawa Sameer yayi yazauna kan kujeran dayake kai yadaga land line din yakira hotel kitchen din dan kusa da landline din an rubuta various number places a hotel din kaman su reception, kitchen da bar, da sauransu, ringing daya kitchen din suka daga yace "I want fruit salad, anddd" yay shiru yadaga kai ya kalleta har lokacin hawaye take sharewa tana kallon hannun da aka makala mata drip din sai kawai ya dauke kai yace "fried rice with water, the one that's not cold" ya maida wayan ya ijiye, wayarshi ne dake kan jikinshi ya shiga ringing da sauri yadaga wayan ganin Ummi ne yasa yatuna bai sanar da ita bazai dawo gidaba kuma inba tafiya ba koyaje wani assignment a outside Abuja ba, baya taba fashin kwana agida, dudda Ummi na bacci da wuri amma yarasa ya akayi duk in bayanan take notising koda baidawo gida da wuri bane tasani, ajiye landline din yayi yadaga wayan yana kallo, answering call din yayi ahankali yace "Ummi na" yanda yafadi Ummi na saida Rahima tadago kai ta kallai cikeda mamaki dama wanan masifaffen sojan na ragema wani murya haka haladai mamanshi ne.


Cikeda dan bacin rai Ummi tace "I call to ask you one single question, just a question Sameer" dan faduwa gabanshi yayi dagaji yasan Ummi tai fushi dashi sosai, tace "na lura kasoma zama man of your own yanzu Sameer, you feel kai keda kanka you have the right to do duk yanda kaga dama, naji kuma nagane Sameer, tambayata itace incire idanuna ne akanka kawai na zuba maka ido?" shiru yayi yakasa amsata hakan ya mugun tunzurata ta dakamai tsawa. "answer me Sameer, nace in cire idanuna ne akanka na zuba maka idanu, dan I see no reason dazan dinga damuwa akan ka, sabida ka rainani Sameer kaga ka girma saika tashi bazaka kwana agidaba kuma kaki kira ka sanar dani eh Sameer and inama magana you kept mute kaman wanda yahadiyi dalma" cikeda damuwa ahankali yace "am sorry Ummi, please" tashi yayi akan kujeran yadan juyo hada ido sukayi da Rahima da tunda yafara wayan take kallonshi kaman yauta fara ganinshi harara ya balla mata yawuce yafita daga dakin, ya sauka chan kasa, garden din Hotel din yashiga yazauna kanwata kujera mai kyau tashan iska shi kadai awurin yasake dialing number Ummi din danta kashe cikin fushi jin baya amsata, saida wayan ke gabda katsewa ta dauka tai shiru batare datai magana ba hakan yasa cikin kwantacciyan murya irin ta lallashi yace "am sorry Ummi na, dan Allah kiyakuri kinji" cikin fushi tace "ban neman hakurin ka, just tell me kana ina yanzu haka?" dan jim yayi 1st policy din rayuwan shi shine baya karya ko zaka kasheshi baya karya, instead of yay karya to gwara yay shiru kawai yaki baka amsar tambayan ka koda zaka tsinemai ne. "kana jina kai shiru Sameer?" ahankali yace "ina Gombe Ummi, am sorry I was on my way coming back home da magrib jiya issue came up da dole I had to attend, Ummi am sorry karkiyi fushi dani kinji" cikin kakkausan murya Ummi tace "mekaje yi a gombe Sameer?" dan jim yayi kafin yace "aiki ne, anjima kadan zaki gani a news Ummi, news din will be a all kafafun yada labaran duniya" dan ajiyan zuciya tasauke tadamu da situation din Sameer saisa any abu nashi yake tadamata da hankali, jin tai shiru batace komiba yasa yace "I am sorry, rushing to the place nake saisa I couldn't call you nafada miki zanje aiki Ummi, kiyakuri kinji, kinyafe min?" ajiyan zuciya ta sauke tace "naji nayafema Allah maka albarka" murmushi yayi yaji wani sanyi aranshi tace "yaushe zaka dawo?" ahankali yace "tommorow or next tommorow" "okay daman Mu'az yadawo gida dazun nan wai ASUU sunje warning strike na 2weeks" gyadakai yayi yace "eh yafadamin yamini text, tunda yadawo gida tell him nace yaje farm house yataya su ishak aikin dana sasu" ahankali Ummi tace "tom zan gayamasa gamashi nan ya shigo yana jinka tunda yadawo yadaman wlh Sameer danai magana yace wai shine Auta haka autanni keyi, am fed up fa, ni yakoma school yazauna yajira su gama warning strike din tunda just 2weeks ne yafimin" dan murmushi Sameer yayi yace "put him on the phone Ummi" kafin ma Ummi tabashi wayan Mu'az ya fizge jin Sameer yace abashi, cikeda murna yana wani irin murmushi yace "Ya Sameer ina yini" yay maganan yana tashi daga kusada Ummi yay dinning da gudunshi Ummi tabisu da kallo tana murmushi tanason yanda yaranta keson junansu duka saisa ko kadan batama Sameer fada agabansu shima Mu'az shigowan shi kenan yanzun nan duk fadan datama Sameer ba a idanunshi bane.



Ahankali Mu'az yace "good morning Ya Sameer" anatse Sameer yace "morning kiddo, why are you disturbing Ummi?" kaman zaiyi kuka ashagwabe yace "Ya Sameer nifa kudi nakeso tabani waidan nace tabani Atm card dinta shine wai ina damunta bazata bayarba zan emptying account dinta" ahankali Sameer yace "tome zakai da kudi?" ashagwabe yace "aski zanyi fa, sanan da gyaran farce" gyadamai kai Sameer yayi yace "alright will transfer money for you, but kadena damun Ummi at her age bata bukatan damuwa sai kwanciyan hankali daga wajenmu, karka bari takara kawomin irin wanan complain din am I clear" gyadamai kai Mu'az yayi kafin ya saramai ya buga kafa akasa yace "Crystal clear Sir!" da sauri Ummi tace "wlh kafasamin tiles saika kawo kudin gyaran su" daga tachan bangaren Sameer yace "bama Ummu wayan" da sauri ya kaima Ummi wayan ta amsa ta kara a kunne yace "okay Ummi namai magana, inya kara damunki just let me know" hararan Mu'az din daya daura kanshi kan cinyarta tayi yana daddanna waya abinshi tace "balm din kafafu na yakare Soja, na aika su Noor da Muhammad basu samomin ba wlh, duk pharmacy dazasu babu" gyadamata kai yayi yace "idan zan dawo zan tahomiki dashi" murmushi tayi tace "shikenan nagode, Allah yay albarka, kome zakayi kadinga yi tsakani ga Allah kaji, abinda akayi tsakani ga Allah, Allah yafi sanya albarka cikinshi, Allah yay muku albarka gabaki daya, Allah ya tsaremin ku aduk inda kuke yakare min ku" ahankali dagashi har Mu'az dake kwance sukace Ameen sanan yace "saina kira anjima Ummi bye" "bye Son" katse wayan yayi yatashi daga Garden din yawuce cikin hotel din. Dakinsu yabude ya shiga kwance yaganta kan gadon tana bacci hankali kwance ta lulluba da bargo, tray da aka aiko musu abinci kusada gadonta yabi da kallo, tsugunnawa yayi yabude yaga ko kadan bata taba rice dinba sai bowl na fruits wanda yaga gane na fruits ne sabida chunks of pineapples dayagani acikin bowl din da fork kenan shi kawai tasha, maida rice din yay yarufe yatashi yasa hannunshi ahankali yadau kayan shi daya saya a boutique din dake hade da nata yabude bathroom din ya shiga ya maida kofan yarufe, wanka yayi yacire uniform dinshi ya kwashe farin riganshi da jacket dinshi datai hanging abayin yajefa cikin wani dan mini basket sanan yay wankan yadade yana wanka ya gama tsaf ya shirya cikin jean da rigan daya saya da suka mai kyau sosai sanan yafito rikeda basket din, yadau wayanshi, wallet da prescription note din yasaka a aljihu yadau car key yafita, saida yabiya laundry hotel din yabasu uniform din nashi dan su wanke mai sanan yafita ya shiga mota ya kunna wani gidan mai yafara zuwa yasha mai sanan yafito ya shiga gari dudda baiwani san kan gombe sosai ba gaban wani shago ya tsaya dayaga ana dinka hijabi yasai guda daya maroon mai hula da hannu sanan ya koma mota yacigaba da tafiya saida yaga wani babban pharmacy sanan yay parking ya shiga yasa yo duka magunguna ciki harda na wanda zata shafa a inda kuraje ya feso mata da kuma reddish din allergies din sanan yafito ya shiga wani super market another set od cloth yasaima kanshi da takalmi itama yasai mata takalmi sanan yawuce yakoma mota ya ijiye komi sanan ya shiga wani masallaci that is at the road side yay sallan la'asar yafito ya shiga mota yaja awani eatry ya tsaya yaci abinci sanan yaja mota yakoma hotel din, har lokacin tana bacci ajiye komi yayi yadau kayayyakin sawa su yasa a wardrobe din hotel din sanan ya zauna ya cicciro magungunan daya siyo mata yana karanta leaflet dinsu, maganin maleria ne dakuma na allergies din sai multuviate dazai bata apatite yakuma sa taci abinci, aijiyewa yayi yatashi yafita.
Duk wacce takaranta min book dinan bata biyaba ban yafeba.
How to subscribe
Pay 300 to 3107021073 aisha Muhammad first bank saiki turo evidence of payment to my watsapp number 070121814621
49&50




Bayan sallan magrib suka shigo Hotel din tareda Dr din sunadan taba hira, knocking Sameer yayi tana zaune kan gado rike da rice din dazu data kasaci mugun yunwa takeji but dukta yanda taso ta chusa abincin acikin tane takasa sai kallonshi take akan kafafunta knocking da akayi yasa ta dago kanta batare datace komiba dan batada karfin magana bata dade da tashi daga baccin bama, bude kofan Sameer yay ahankali suka hada ido ahankali ta saukar da kanta kasa duk in suka hada ido sai gabanta yafadi juyawa yayi ya kalli Dr yace "come in" shigowa Dr yayi yana kallon Rahima yace "iyye patient ke kadai wanan delicacy din ba tayi?" dan murmushi tayi batare data dago kantaba yakaraso gaban gadon yace "to kishi abincin mana" girgixa mai kai tayi tasa hannu ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "nakasa ci" cikeda damuwa Dr yace "ahh sorry bakida apatite ne, don't worry tunda yanzu kin tashi akwai magun gunan dazaki sha zaki sami apatite nan da zuwa gobe zaki warke ok, mezakici yanzu?" murya chan kasa kaman wata marainiya tace "sliced fruits" dan juyowa Dr yayi ya kalli Sameer dayay kaman baya jinsu yace "call the kitchen officer akawo mata fruits, she can't take those drugs on empty belly" landline Sameer yadauka ya shiga kiran su shikuma Dr yajuyo ya kalleta yace "ban hannunki ruwan yakare nacire miki" mikamai hannun tayi ahankali yacire mata sanan ya shiga dubata temperature ta yasauka sosai ba kaman dazu ba, knocking akayi Sameer yabada izinin shigowa fruits din aka kawo mata acikin wani bowl da aka daura akan tray aka rufe takawo har gaban Sameer da hannu yanuna mata Rahima takaimata tareda mata sannu da jiki ganin batada lpy sanan tajuya tafita Dr yace "farasha" farasha tayi ahankali shikuma Dr yajuya yaje wurin Sameer ya karbi magungunan sanan ya ballo wanda zatasha yadau bottle water yace "gashi sha" karba tayi gabanta na faduwa watsawa tayi abaki sanan tadau ruwa tasha tana tabe fuska Dr yace "good gurl, shanye fruits din to" cigaba da sha tayi bata wani bata lokaci ba ta shanye tass, Dr ya karbe plate din yadaura kan tray sanan yadau balm din tube din da Sameer yasayo a pharmacy yace "kinga wanan maganin kije kiyi wanka sanan ki shafe duka jikin ki dashi duk wanan kujeren da kaikayi da tashi da tsigan jikin ki keyi zai dena saikizo kiyi bacci, in sha Allah nan da gobe da safe kin warke tatas saidai cigaba da shan maganin harsai kin shanye dan ba'a wasa da maleria dose", gyadamai kai tayi yajuya yahada kayan shi ya kalli Sameer yace "to officer saikuma idan nazo dasafe inhar babu wani matsala da safen shikenan nagama da ita saidai kuma tacigaba dashan drugs dinta" tashi Sameer yayi suka fita daga dakin tare.


Tadade zaune awurin tana sauke ajiyan zuciya, sosai taji dadin jikinta dan yan ciwuwwukan datakeji sun ragu, sanan kurjewan datayi sun dena mata zafi kaman an zare zafin, yanzu burinta kawai ta ganta a jikin Mummy ta, tashi ahankali tayi dan fitsari takeji ta rike maganin da Dr yabata ta shiga bayi, brush tayi sanan tasake wanka da ruwan zafi kaman wata mai jego sanan ta goge jikinta duka da towel ta bude balm din ta shiga shafawa, tass ta shafe ko ina na jikinta dashi sanan tadau rigan data cire tasaka tafito daga bayin ta zauna kan gado tana kallon wayan Sameer daya bari kan kujera kaman taje ta dauka takira Mummy but tsoro take yakamata ahaka har gyangyadi yadan soma dibanta, bude kofan da akayi yasa tadan firgita tabude ido hada ido sukayi da Sameer daya shigo, maida kofan yayi yarufe sanan yajuyo babu ko digin wasa kan fuskarshi yace "kinyi salla?" yanda ya tsareta da idanu yasa ta girgiza mai kai ahankali batare datai magana ba yace "tashi kidauro alwala" ahankali ta yaye bargon datadan rufa dashi ta mike tsaye hartakai bakin kofan bathroom din saikuma ta tsaya ta juyo ta kallai hada ido sukayi da sauri ta saukar da kanta tana wasa da yatsunta cikin siriruwan muryanta tace "unnnn ai banda hijabi" batare daya kalleta ba yace "akwai hijab, jeki dauro alwala" bude bathroom din tayi ranta ko kadan ba dadi ta dauro alwalan sanan tafito taga harya shimfida mata dadduman daya dauko daga cikin motanshi ya fuskanci gabas shikuma yana zaune kan kujera daga zaune yanuna mata wardrobe yace "there's hijab inside" ahankali take tafiya kaman wacce kwai yafashe mawa aciki ta wuce shi tabude wardrobe din taga hijab ko sabo fil maroon, dauka tayi taciro daga ledan tazura yay mata kyau sosai gashi har kasa yakai mata yanaso yamata over yawa ma wani abu tahadiye sanan ta maida wardrobe din tarufe tajuyo tazo ta gabanshi zatahau kan dadduma remote yadauka ya kashe TV duka dake kara dan inda TV ke kallo ne gabas baison TV yay distracting nata, ahankali tahau kan dadduman, ahankali yace "turn around" dan juyowa tayi duktai zuru zuru ta kallai yace "daga sallan zuhur zaki fara, ahh kinyi subhi?" ya tambayeta without an atom of joke a magananshi, girgiza mai kai tayi hakan yasa yace "okay dana subhi zaki fara, kiyi zuhur, asir, magrib da isha'i" wasu hawayen bakinciki datake kokarin dannewa ne yazubo da sauri ta share sanan ta juya takabbarta tai subhi sanan ta tashi tai azahar da kyar kaman yasata aikin duniya gabaki daya takeji, sallamewa tayi tajuyo ta kallai hada ido sukayi dan yanabin yanda take sallan ne daki daki sallan ma akwai kuskure ciki sosai, hawayen daya cika idanunta ne ta share da hijabin sanan ta janye hijabin daga kan fuskarta ta kallai cikin irin muryan wanda ya cika yay fam gab take da fashewa dinan tace "nai sallan asuba da azahar dan Allah inbar sauran gobe sainayi? Kaga banda lpy" without any sign of remorse ko alamun yaji tausayinta yace "stand up kicigaba" fashewa tayi da kuka kaman dama jira take ta tashi tsaye ta kabbarta tana salla kuka, haka tai sallolin har isha'i kuka take tana sallame isha'i zata cire hijabi yace "remaining shafa'i da wuturi" jitayi dama wajen Wugugaga yabarta dayafi mata da uban sallolin nan dayake sata haka tai shafa'i da wuturi sanan ta sallame ta tashi tacire hijabin tai wurin wardrobe din tana goge kwalla sanin zai iya magana yasa ta linke hijabin tasa acikin wardrobe din tarufe tana share hawaye tazo tahau gadon takifa kanta kan gadon tana kuka ahankali, yana jinta bai kulata ba takai almost 1hr kuka take sanan yajita shiru bacci yay awon gaba da ita.





Wuraren shadaya yatashi bathroom ya shiga wanka yayi ya chanza kayan jikinshi zuwa wani pyjamas daya sayo yay brush shima dan baya iya bacci batare dayay brush ba sanan yafito yana kallon yanda take bacci, gashin kanta ba dan kwali sai kyalli yake dudda ba gyara, yariga yay shafa'i da wuturi a masallaci hakan yasa ya kwanta kan kujera inda ace yanatare da system dinshi dayay wasu ayyuyyuka da yawa amma babu, kujeran yamai kadan tsawo hakan yasa ya saukar da kafafun shi kasa dan yatsine fuska yayi yaja pillow case din kujeran ya wuwwurga akasa sanan ya sauko kasan ahankali ya kwanta tareda yin addu'an bacci ba'a wani dau lokaci ba bacci yay awon gaba dashi ance jiki da jini dole akwai gajiya.


"ki kasa yayanki yamin duka, yajimin ciwo ko kinga wayan nan burma hancin da kadan garun" ta kalli burma hancin da kadangarun da sunfi guda dariya biyu chakude cikin wani farin botikin tallan bons yace "saina juye mikisu acikin ki su burma cikin ki su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login