Showing 51001 words to 54000 words out of 190952 words

Chapter 18 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete

M SHAKUR   

22 Dec 2024

409

kuma nizan karba nai signing cewan na karba, bazan wani dadeba zan dawo" ya shiga bayi ya rufo, tsaki Mummy taja ta kife kanta kan follow tana tunani she is just picturing yanda Sameer is, she can't wait for the day she will grab those his muscles and kiss that his dark thick skin.
27.

Washe gari.

Wuraren 8 ya shigo gidan daga jogging zufa yagama wankeshi tsaf yana gangarawa yana didiga, maybe saisa he looks damn sexy koda yaushe sabida wanan yawan workout din dayake yi, jogging dakuma normal soja training as usual baya wuceshi, dakinshi yayi yana zufa tako ina, tsayawa yayi gaban fridge dinshi yadauko bottle water yabude yakafa abaki, saida yasha iya shanshi sanan ya ijiye yay bedroom, bayi ya shiga yayi wanka kafin yafito atsanake ya shirya tsaf cikin uniform dinshi sanan yafito yay part din Ummi, abinci yaci agurguje dan yau yanada ayyuka dayawa cikin harda supervising wasu sojoji a various post nasu, goge bakinshi yayi yana kallon Ummi yace "anjima Noor zaizo yakaiki Checkup aduba kafafun ki, menene babu agida Ummi?" ya tambayeta yana gyara boturan riganshi, ahankali Ummi tace "just fruits kawai ne babu" gyadamata kai yayi yace "zan aiko wani soja anjima yakawo miki, love you Ummi, bye" dan girgiza kai kawai tayi batare data bashi amsaba, yasan fushi take dashi but wlh baiso yay wanan maganan auren da ita and bazai iya fita yabarta cikin fushiba, zama yayi kusada ita tareda dan fuzar da iska hannunta yakama ya rike ahankali yace "how about namiki alkawari dazaisaki farin ciki Ummi" dan kallonshi tayi saikuma ta tabe baki, ta karbe hannunta tace "kaga sakanni Sameer" kin sakinta yayi ahankali yana kallon fuskarta yace "Ummi I Lieutenant Sameer Simran Sameer promise you kafin kwana ashirin da takwas dasuka rage cikin kwanaki talatin din da Baffa yadeban mini zanyi aure, I promise you Ummi na" da sauri Ummi ta kallai, gyadamata kai yayi tareda sakin mata murmushi yace "in sha Allah, daga yau zan fara neman wacce zan aura kinji, Sojan ki yakusan aure" wani irin murmushi Ummi tayi batasan lokacin datace "Allah ya zabamaka mata tagari Sameer, ubangiji Allah yamaka albarka, am so happy today, oh Allah nagode maka" dan dariya yayi yatashi daga taugunnen dayake yana kallon yanda take farin ciki saiyaji hankalin shi yawani irin kwanta, sallama yamata yawuce office yana driving yana tunani anya yau bazaije gidan Judge da rana ba kuwa, dan wuraren four na yamma zai tafi supervising posts and yawanci baya gamawa da wuri dan wurare daban daban ne a Abuja.
***




Atare duk suka gama breakfast, plate din kowa is empty banda plate din Rahima da he is not sure idan tamaci quarter of the food da aka zubamata, bai wani damuba dan he believe with time inhar duk sunacin abinci atare haka zatazo tadinga cin abincin normal normal, clearing wajen sukayi suka shiga kitchen suka wanke kwanukan tass ita tana dauraya, komi ahankali kawai takeyi so slow to the extend su kansu su Lubabatu sun fara tausayin ta, tai kama da mara lapiya, fitowa sukayi bayan sun gama dayake yau su Zeenatu anbasu mid semester babu makaranta zama duk sukayi akasa suna kallon TV inda Abba yasaka arewa 24, ahankali Rahima ta daura kanta kan kafarta ta rungume kafafun ajikinta, ganin haka yasa Abba yaji wani iri tausayinta, tausayi Rahima take bashi bana wasaba, kallon Mummy dake gefenshi hankalinta nakan TV yayi yace "Wife" da sauri Mum ta kallai tace "na'am Alhaji" kallon yaran yayi yace "children" da sauri suka kallai harda Rahima data kifa kanta kan kafa ta dago kanta ta kalli Abban nasu da idanunta dasuka kode sosai kaman mai typhoid, cikin wani irin murna Dady yace "how about we play basketball 🏀 yau in the compound, Rahima da Zeenatu are team Dady, Siddiqa kuma da Lubabatu are team Mummy, let's see who is going to win, yaaayyy" washe baki duka yaran sukayi harda Rahima dan yanda Abba yayi yabata dariya, kallonsu Abba yayi yace "oya oya, kutashi kuje daki ku shiryo cikin jearsy rigunan ku kufito, lemme go and get the ball" tashi sukayi da sauri harda Rahima sukai ciki, Abba ya kalli Mummy yace "jeki shirya kema harda ke kokyayi loosing some fat" turomai baki tayi tace "nine mai kiba gani very very sexy" dariya Abba yayi yace "hakane, Sexy lady, I mean sexy woman" tashi tayi cikeda rangwada tace "sexy lady dai Alhaji, sabida yan mata na haifa saisa ake ganin girmana dansun tasa amma dududu guda nawa nake, yaushe nafita daga menopause" tai maganan tana wucewa corridor, dariya Abba yayi yana girgiza kai yace "Maryam, Maryam badaison yarinta ba, bataki ace she is 12yrs bama indai itane" tashi yayi shima yabi bayanta dan zuwa nashi dakin ya chanza kaya.


Wardrobe dinta ta bude tana kallo, da idanu take neman inda jearsy nata yake, bata manta ranan da Abba yadawo, lokacin yaje Paris shiya kawo musu tsaraba, nata na Manchester ne ja, na Zeenatu ma haka, na Luba da Ya Siddiqa ne na Chelsea fari da blue, a chan kasan kayanta ta hango shi hakan yasa ta janyo tana murmushi sanan ta dauko wani blue Jean nata 3 quater ya wuce guiwan ta da kadan ta ijiye akan gadonta sanan taciro p cap maroon, da sneakers maroon ta ijiye ta maida wardrobe din ta rufe sanan ta kifa kanta jikin gado jikinta yafara mata rawan daya sabayi ta shiga lashe baki, she is craving to the extend yanzu she is kind of loosing it, tasan kozata mutu Mummy bazata bata ba dan Abba na nan gashi kullum yanzu suna tare bakaman da ba da yana dawowa sai tafi study room dinshi sai tsakar dare, yanzu suna tare 247, tasan she could just walk to Mummy's room tabude safe ta dauko tasha tai satisfying kanta tabama zuciyabta abinda yakeso but she is so scared dan tasan Abba zai iya kasheta, besides ita tai alkawari tace yamata kome yaga daman yi inyasake kamata, kwala mata kira dataji anyi yasa ta tashi daga jikin gadon da sauri tana goge hawayen dasuka zubo mata, ta cire rigan jikinta ta yar tana kokarin shiryawa cikin jearsy din.



Fitowa Dady yayi shi kadai tsakar gida rikeda basket ball din a hannunshi, yana sanye da Manchester jearsy shima da gajeren wandon rigan yasaka canvas akafanshi zai kwalama Mummy kira yace sufito wayanshi dake aljihun wandon yahau ruri, da sauri yaciro wayan ganin Sameer ne yasa ya amsa da sauri yace "Hello Lieutenant" cikeda natsuwa Sameer yace "good afternoon sir, ko dayake is still morning" murmushi Abba yayi yace "morning Sameer, ya aiki" anatse yace "Alhamdulillah Abba, ammm Abba I think da daddare am not going to be available dan zanje supervision na various post damukeda shi nan Abj, so I wanted to ask if it is okay nazo yanzu and see Rahima cus am free now" cikin wani yanayi na nuna rashin jin dadi Abba yace "haba Sameer yanzu zuwan ne saika tambayeni, like I said am your father, come anytime u wish and want ba saika tambayeni permission ba d'ana, kana zuwa ka shigo gidanku ne kaji, besides u are doing me a favour fa, helping my daughter ai bazan taba mantawa da alkhairin nanba, saikazo kaji Son" gyadamai kai Sameer yayi kaman tana gabanshi yace "okay Abba sai nazo" "kana zuwa ka shigo ciki direct duk munama compound saikazo" "OK" yace tareda katse wayan, ganin Mummy tafito itama sanye da jearsy Chelsea da team dinta abayanta Siddiqa da Lubabatu duk sanye da nasu, yasa Abba yace "wowowow, My team my team tunda abin harda yar sonkai an waremu" yakarasa wajen Zeenatu da Rahima dake biye dasu Mummy abaya, tsayawa yayi agabansu yace "let's go team Dady and show team Mummy wat we are capable of, ba'a cinmu saidai mu ci" cikin daga murya Mummy tace "impossible, Team Mummy are record breaker forget ku yan Manchester ne kun ajiye record, yau zamuyi breaking nashi, gurlssss mu nunamusu" Mummy tayo cikin filin da yaran biyeda ita, Dady ma yay cikin filin su Rahima suka bishi da gudu Rahima na dariya tana cheering Abba itada Zeenatun. "Aaabbba! Aaabbba! Aaabbba!" sukuma team Mummy suna cheering Mummy. "Mummy eh! Mummy eh! Mummy eh!" wurga kwallon Abba yay sama kafin kace me Zeenatu tai tsaye ta chabe ta ruga aguje su Mummy da Siddiqa suna binta Abba ma na binsu dudda baya wani iya gudu sosai kaman su, Rahima kuma tai gaba chan wajen board tana jiran Zeenatu dan tamata passing kwallon, wani irin circling Zeenatu su Mummy sukayi dan dama batada gudu sosai dan tanada dan jiki tafi su Siddiqa kiba, ganin suna shirin kwace kwallon yasa tai tsalle tareda wani irin ihu. "Autaaa" chabe kwallon Rahima tayi Abba yace "wurga da sauri, wurga Auta" ganin haka yasa su Mummy suka kwasa da gudu sukai wajen Rahima kafin su karasa Rahima tai wani tsalle ta jefa kwallon cikin raga Abba da Zeenatu sukai ihu tareda rungume juna. "is a goal" wani irin tsallen dadi Rahima tayi tataho da gudu ta rungume team dinta Zeenatu da Abba, kafin ta sakeshi tahau rawa tana dariya Zeenatu ta shiga tayata suna rawa suna tsalle suna tafi, kama waist Abba yayi cikeda jin dadi yana kallonta yanda ta sake sosai tana murna rabon daya ganta haka harya manta, dudda he is super tired amma the whole basket ball idea was worth it look at his Rahima now, da gudu yakarasa wajen inda sukema us Mummy da Siddiqa da Lubabatu dasukai kini kini darai yace "who dares stand to Manchester? Am sorry yan Chelsea but Dady team is unbeatable right girls?" atare Rahima da Zeenatu sukace. "right Abba" suna wani feeling kansu, dariya Abba yayi ya rungumo Rahima a one side Zeenatu a one side of his hand, ya zare p-cap din Rahima yana kallon fuskan Mummy yana dariya yace "haba wifey, team dinku ar......" kaman ance ya juyo, Sameer yagani sanye da kayan sojoji ya tsaya jikin Gate rikeda car keys a hannu yana kallonsu yana murmushi, da sauri Abba yasaki yaran yana maidama Rahima p cap dinta akanta yace "laaaa Lieutenant, barka da zuwa" Lieutenant da Abba yakira yasa kowa yakalli Gate din, karasawa gaban gate din Abba yayi shima Sameer yakaraso Abba yamikamai hannu yace "welcome Sameer barka da zuwa, sorry fa, we were actually playing basket ball, halama ka kirani banji kiranba wlh" gyadamai kai Sameer yayi yace "I actually called twice" cikeda rashin jin dadi Abba yace "so sorry, yaran nan ne wlh muke basket ball, yau sunada mid semester ba school shine suka tasani agaba" murmushi Sameer yayi yace "what a nice family, hakan yakamata" dan dariya Abba yayi ya shafa bayanshi yace "tafi study room din bari naturo maka ita, kaganta chan" yanunamai Rahima dake sanye da p-cap itada Zeenatu suna rawa, kallo daya yamata ya dauke kai ya gyadamai Abba kai yafara tafiya, da sauri Mummy ta dunfaro su tace "a'a su soja ne agidan namu haka, yau munada manya manyan baki, aiko gashi ansha kayan sojoji an wanko kyau, and you know you look good da kayan fa, so handsome and se.....xy" tafadi ahankali ganin Abba yawuce zai kira Rahima dake raye raye, dan sunnar dakai Sameer yayi ganin ta babu mayafi yajuya yadan kalli Rahima dake rawa Zeenatu tagaji takama gwuiwa tabarta ita kadai tanata tikawa yace "good morning Mama" dan juyawa Mummy tayi ta kalli inda yake kallo ganin Rahima ne yasa taji gabanta yafadi tace "wanan kallo haka Sameer bazafa mubama soja ba, banda hakama Rahima yarinya ce, tuzuru irinka yakama min y'a ai saidai akirani ace ga gawarta abu ba kadan ba, irinka sai mata nunannu kaman su mu" tai maganan tana murmushi tareda dan lashe lips tana kallon fuskarshi, juyowa yayi ya kalleta ido cikin ido kaman maison karanta wani abu atattare da ita, Mummy jitake abu na tsayayo mata, tanason namiji dakakke jarumi haka, yanda Sameer ya kalleta cikin ido babu wani alamun darr ko tsoro yasa taji organs din jikinta sun mike, Lord! She is crushing on this sexy giant guy, dauke kai yayi yafara tafiya yace "excuse me Mama" da sauri Mummy tabishi tace "haba Sameer da shekaru nawa na girmeka duka duka yar yarinya dani eh Sameer kake cemin Mama?" dan kallon Mummy yayi kaman yanda ta zubamai idanu itama ta tsaya chak tana wani irin murmushi jitake kaman tajawo shi ta rungume shi. "Wifey" Abba ya kwala mata kira da sauri ta juya yana tsaye tareda su Zeenatu ga Rahima kuma ta taho tana tafiya ahankali tana tahowa, da hannu yamata alamu datazo yace "zomu cigaba wifey" dan batarai tayi tadan harari Rahima dake tahowa tana kallonta sanan tawuce batare dataima Sameer sallama ba dan ko kadan bata so Abba yakirata ba, tsayawa Sameer yayi yana kallon Rahima dake tahowa tana kallon Mummy tana murmushi sosai duka white hakoranta awaje, fadawa jikin Mummy tayi ta kyalkyace da dariya sosai ganin Mummy ta daure fuska tace "Mummy na are you sad we won?" dan tureta Mummy tayi tace "common leave me alone, go and hug your team leader tunda har kun iya cinmu" fashewa da dariya Rahima tayi data dade batai irin shi ba ta kankame Mummy ashagwabe tace "kai Mummy na, inda kunefa kuma da kunci mu muyita jin haushi, kai Mummy wayau ko" takara kyalkyace wa da dariya tana chusa fuskarta kan kirjin Mummy kaman wata yarinya maishan nonno tana dariya, juyawa da Sauri Sameer yayi yadauke kanshi yawuce study room this is the first time yake ganinta so happy like this, kwala mata kira Abba yayi ganin shirmen dasukeyi da mamanta. "Rahima bazaki wuce kitafi ana jiranki ba" da sauri tasaki Mummy tai hanyar study room dinta da gudu, hannu tasa tabude kofan da sauri ta shiga, hada ido sukayi da Sameer din dake zaune kan kujera yadago kai yana kallonta, ahankali tace "good morning" dauke kai yayi daga kallonta hakan yasa ta tabe baki tawuce ta zauna kan kujeran gaban table din Abban tai shiru tana karkada kafafu.28.

Free page

Tana karkada kafafun ta dake sanye cikin sneakers, kafe kafafuwan nata yayi da ido yanda right leg wrist dinta ke sanye dawani hadadden leg chain dayama tiny leg din nata kyau kaman ka sace, batare daya kalli fuskarta ba yace "mesa kike saka leg chain?" kallon kafafun nata tayi kafin tasaki murmushi tace "sabida ina sonsu ne, sunada kyau" zai kara magana wayanshi yadau kara hakan yasa yaciro wayar daga aljihu ya kalli screen din sanan yay picking yakara a kunnenshi batare dayay magana ba but da alamu sauraron maganan dayan bangaren yakeyi, dan dago fuska Rahima tayi ta kallai, kayan sojojin sunmai wani irin shegen kyau, bakin fatanshi na shining yana daukan ido, pink lips dinshi ta kafe da idanu shi kadaine abu dan jajja jajja a fuskarshi aranta tace wai mesa yawanci sojoji bakake ne, ahhh dark men are ugly, dan fari zan aura inna tashi aure sunfi kyau, dago idanunshi yayi karaf suka hada ido, dan zaro fararen eyes dinta tayi cikeda rashin gaskiya gabanta yawani irin fadi, batare daya cire nashi idanun daga kanta ba yay magana yace "Alright ganinan zuwa" zare wayan yayi daga kunnenshi yana kallonta, cikeda rashin wasa yace "why are you looking at me?" dan turo baki tayi tana kallon nashi cike da rashin gaskiya kafin tawani irin washemai baki ta kyalkyace da dariya tareda tashi da gudu tai kofa, da sauri yakirata. "Rahima" juyowa tayi ta kallai tana kokarin bude kofa tana murmushi, dan sakin fuska yayi kadan ganin yanda takemai murmushi yau she seems very happy. "come" makemai kafada tayi tabude kofar da sauri tafita, tashi yayi yafito batawani nisa da study room dinba yakirata. "Rahima" da sauri tajuyo sanin su Abba na iya juyowa and Abba yana ganin yakirata bata amsaba fada zai mata, yaga ana kiranta taki zuwa yasa ta juyo da sauri, alamu yamata da hannu datazo inda yake, takowa tayi ahankali ta taho ta tsaya har gabanshi ta daure fuska, Mummy dake buga basket ball sai satan kallon su zuciyata na bugawa bim bim bim.

Karasowa tayi har inda yake agaban dakin, kaman 5 feet tsakanin su ta tsaya yanda yake kallonta yasa tadan juya ido tareda wani lankwasa kai tace "ni gani me kake kirana?" shiru yayi yana kallonta, ahankali cikin low voice yace "ni kikema dariya? Wats funny about me?" yafada babu wasa, dan juyowa tayi ta kallai kaman yanda shima ke kallonta, wani irin murmushi ta sakinmai duka white kananun hakoranta suka bayyana tace "su Mummy ne suka bani dariya ni ba kaiba, wai dan mu Team Dady Manchester munci shine suke fushi sunata hararan na sabida ninaci ball din, kaga ko na iya basketball tun a school Inna karbe ball din saina wurgashi cikin raga sanan zasu sake iya rike ball din, sabida wai Ya Zeenatu tamin passing ball din aiko su Mummy, da Ya Siddiqa da Ya Lubabatu suka biyoni da gudu, na daka wani high jump and throw the ball sai cikin basket and it was a goal, shine suke fushi hahahahha" takara kyalkyacewa da dariya tasa duka hannayenta kan bakinta tana rufe baki tana dariyan harda hawaye, shiru yayi yana kallonta she looks so innocent, so cute while laughing, yanzu dai wats funny acikin wanan labarin datake bashi tana dariya, this is the first magana datamai batare daya tambayeta ba tana uban dariyan nan kaman zararra, murmushi zaiyi amma yahana kanshi dan smirking yayi yasa hannunshi cikin aljihun gaban riganshi yaciro wani dan karamin card ya mika mata, tsayar da dariyan tayi ta kalli card din dayake mika mata tace "menene wanan?" ahankali yace "is my card, just keep it with you, anytime dakike da any problem, ko u are sad or anything my digits are there just give me call" daure fuska tayi tace "why will I call you kaida baka ma mutane dariya, fuskan ka kini kini kaman wani mala'ikan mutuwa Astagafurullah" wani irin kallonta yayi kaman mai shirin tuhuman ta yace "kintaba ganin mala'ikan mutuwa ne?" girgixa mai kai tayi batare data kalli fuskanshi ba tace "ai Mummy naji tana cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login