Showing 33001 words to 36000 words out of 190952 words
Chapter 12 - Bin Abinda Zuciya Ke So Book 1 Hausa Novel Complete
kama da jaririn kunkuru shine ya fesamin goshi" wani mugun kallo Mummy tamai batason tai magana dan tasan yariga yasan few things gameda Rahima batason ya tona musu asiri hakan Yasa tace "barshi yama kanshi, let's go" security ne suka tare musu kofa bazasu barsu su wuce ba, Sameer dake gaban stairs a sama yana kallon komine cikin husky voice dinshi yace "let them pass" da sauri Mummy ta dagokai tareda juyowa hada ido sukayi da Sameer wani wawan faduwa gabanta yayi, chak ta tsaya tana kallonshi harsaida Rahima ta kalleta cikin muryan kuka tace "Mummy mutafi" ajiyan zuciya ta sauke takalleta tace "okay Auta muje" fita sukayi daga wurin security zasu maida kofan su rufe takara juyowa ta kalli Sameer daya fara tafiyan shi nan dai dai yay office din Chairman.
💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
1️⃣9️⃣
Mota suka shiga Mummy taja motar suka tafi, saida suka shiga titi Mummy tace "what kind of matsala kika sani Rahima yanzu? Yanzu wani irin karya zan shiryama baban ki dazai yarda eh? Mezan cemai, kai! Innalillahi wa innailaihi raji'un, wanan Chris anyi dibabben yaro mai bakin jini da badluck mtsww" taja tsaki tana gudu ahanya, Rahima ba tace mata komiba gabanta faduwa kawai yake babu abinda take tsoro aduniya yanzu haka kaman haduwanta da Abban ta ahaka suka kai gida, su Siddiqa duk suna daki, dakin Mummy suka tafi direct wanka Mummy tasa tayi tabata abinci, kasaci tayi tace "Mummy bazan iya ciba, in Abba yadawo gobe kasheni zaiyi ko Mummy?" zama Mummy gefenta kanta takama ta daura akan kirjinta ta rungume ta tace "Hey am ur Mum ko, so kibar komi a hannuna, now eat ko kadan ne saiki sha paracetamol dinan karkiyi zazzabi kije ki kwanta kinji" gyadama Mummy kai tayi tasa chokali cikin abincin zata kai baki ta yatsine fuska tadago kanta ta kalli mummy, murmushi Mummy tayi tace "ina zuwa" tashi tayi tai wurin safe ta bude kara daya na wiwi ta dauko tazo ta juyemata a abincin juyawa tayi ta shiga ci da sauri dan yunwa takeji rabon ta da abinci tun rana, tana gamaci Mummy tabata paracetamol tasha ta kwanta ba'a wani dau lokacin ba bacci yay awon gaba da ita, tsayawa Mummy tayi tana kallonta barinma goshinta dake sanye da bandeji har lokacin da kafadarta dayadan kumbura sabida kulkin da matarnan tabuga mata sai wrist din kafarta, wani irin murmushi tayi ta tashi daga inda take tadau kulan tajuya tafita daga dakin.
Sai wuraren 10 yakoma gida sabida tsareshi Chairman yayi sai hira yakemai, shidai chairman arayuwanshi starting from rana na farko daya fara ganin Sameer yake bala'in sonshi, gabaki daya yama maida Sameer din wani abokinshi dudda ya girmeshi amma yana son yaron, jan Sameer din yayi har zuwa gidan shi sukai dinner mai rai da lafiya sanan wuraren 10 Sameer yamai sallama yarakoshi waje saida ya shiga motarshi yafita daga gidan sanan yakoma cikin gida yana murmushi.
Wuraren 10:30 ya isa gidansu Gate aka budemai yay Parking yafito, flat dinshi yawuce direct dan yasan Ummi tariga ta kwanta, sabida hawan jini dakuma matsalan kafanta yasa Dr yace tadinga kwanciya da wuri, yasan ta kwanta saisa bayason yaje yatadata, part dinshi yawuce ya shiga ya maida kofan ya rufe bathroom ya shiga yayi wanka yafito daure da dan towel a waist sanan yadawo falo agogo ya kalla so yake yakira Mu'az he has been busy da tubda yadawo daga zaria baisamu ya kirashi ba, sanin yay bacci yanzu yaja ya kunna laptop dinshi ya shiga yin some work da yakamata ace yayi, almost 1hr yabata sanan ya kashe ya ijiye agefe yay addu'an bacci ya kwanta.
Aka'ida dama ana kiran sallan asuba yake tashi, tashi yayi yashiga bayi brush yayi yay wanka tareda dauro alwala yafito jallabiya yasaka ya feshe kanshi da turare yafito, mai gadinsu yatada sanan yawuce masallaci.
Wuraren 6 na safe ya shigo gidan flat dinshi yawuce ya shirya cikin wasu sport wears, bubu short ne daya tsayamai iya gwuiwa sai wani riga mai kama da singlet da wani karamin towel a wuya na goge zufa ya saka sport sneakers dinshi na Nike yafita gudu haka daily routine dinshi yake kullum ka'idane saiya motsa jiki da safe na 1hr, da yamma inya dawo daga aiki dawuri saiya shiga gym dinshi yay work out har zuwa gab da magrib sanan yay wanka yatafi masallaci.
Around 8 na safe ya shigo gidan, shashin shi yawuce yay wanka ya shirya cikin uniform tsaf sai uban kamshi yake yafito yay flat din Ummi, tana zaune kan dogon kujera sanye da dogon riga tana lazimi, tana ganinshi ta zuba mai harara hakan yasa yay dan murmushi yakarasa inda take, kusada ita yazauna yace "good morning Ummi" addu'a ta shafa sanan ta kalleshi tace "Sameer dama ido kanga ido" kaman zaiyi kuka yace "Ummi am sorry nowww please kidena magana haka" dan tabe baki Ummi tayi tace "toya kakeso Sameer kanunamin kafi karfina" da sauri yace "Ummi dan Allah kiyakuri please forgive me, I've been busy jiyan nan koda nadawo was late saisa ba shigo ba banso natade ke, am sorry kinji Mamana" yanda yay magana cikin kwantar da murya danko kadan baiso yaga Ummi na fushi dashi yasa tace "to shikenan yawuce, tashi muje kaci abinci".
Tashi yayi sukai dining, kunun gyada Ummi ta zubamai da kosai da aka soya sanan tawuce dakinta, faracin abincin yayi dan he loves all this natural local food, he is not a fan of all this abincin yan gayun, bai wani jima da faraci ba Ummi tafito dawani 5liter jarka dayake cike da ruwan rubutu akan dinning table ta ijiye tadau cup ta bude ta tittila ruwan ta cika ta ijiye a gefe sanan ta rufe jarkan tace "maganin da Baffan ka yakawoma ne, ruwan rubutu ne akama na ayoyin Allah koma menene ajikinka dake hanaka aure zai kone ne da izinin Allah, ungo karba ka shanye" tamikamai cup din, dan murmushi yayi dan baiso yasami matsala this early morning hakan yasan ahankali yamika hannunshi ya karba yay bismillah yakai bakinshi ya shanye yabata cikeda murna tace "yauwa ko kaifa, Allah yamaka albarka soja na, Allah kuma yahadaka da matarka kwanan nan" baice mata komiba yacigaba dacin abinci dan bai wasa da cikinshi yanada ci sosai dama ance dogo nada dogon ciki, sanan duk soja nada ci , saida yagama ci tass sanan yatashi tareda goge bakinshi da tissue yace "thank you Ummi na koshi, natafi" kanshi ta shafa tace "adawo lpy, Allah yabada sa'a Allah ya tsaremun ku duka" ahankali yace "Ameen" sanan yawuce yafita saida ya tsaya yabiya mai gadinsu salary shi dan on 25th of every month yake biyansu sai murna Gate man yake yanamai godiya sanan yawuce ya shiga mota yatada yatafi office.
Karfe sha biyu da minti ashirin jirgin su Abba ya sauka a Airport din Abuja, yariga yafada driver yakawo mai mota, key motar kawai ya karba yabama direba kudi yahau taxi yakoma gida shikuma ya shiga mota yatafi kallo daya zakamai kagane yanada damuwa sosai, a parking space din headquarter NDLEA yay parking yafito, ya shiga ciki Chairman yariga ya sanar dasu zuwanshi hakan yasa cikin girmamawa sukamai iso har office din Chairman shiga ciki yayi cikeda girmamawa Chairman yatashi kan kujeran shi tareda bashi hannu yace "barka da zuwa Alhaji" karban hannunshi Abba yayi cikeda murmushi yace "barkan mu dai ya aiki yakuma fama da jama'a" "Alhamdulillah please sit" Chairman yanunamai kujera hakan yasa ya zauna ahankali tareda sauke ajiyan zuciya yace "bakomi yakawo ni nanba nazo namaka godiyan karamcin dakamin ne nagode Allah ya rufa naka kaima haka" girgixa kai Chairman yace "wlh is all thanks to Lieutenant Sameer, konima jiya kaina ya kwance he was the one that advised me akan yanke wanan decision din, Nigeria is just lucky to have that guy" "are you talking about Lieutenant Sameer Simran Sameer dana karanta a news an karamai girma?" da sauri chairman yace "shine, shine ma yagano yaran anan Abuja express road yana dawowa daga zaria shine ya gansu suna shaye shaye awani gida cikin daji suna raye raye yasanar damu, all the children are student babu wani tsayayye mai aikin yi Allah dai yakawo mana karshen shaye shayen nan na yara matasa" shiru Abba yayi kafin ahankali yace "Alhaji Rahima, Rahima na that is just 20 itace aka kama tana shaye shaye?" dan murmushi Chairman yayi ya gyara zama yace "I know yanda kakeji yanzu haka I understand you, Rahima da aka ganta ita tama gama buguwa saida aka kwara mata ruwa sanan ta farka, yaron ma da ya gayyace ta wurin sunanshi Chris birthday dinshi ne anyway is a long story basai kasan komi ba kawai ka kula da yarka Alhaji karabata da abokanen banza dansu ke batama yaranmu tarbiya ayau kadage kanama yaro tarbiya agida wani nachan awaje yana batasu, kawai ka tsaya tsayin daka akanta, karabata da yaron dan yace waishi saurayinta ne soyayya suke dan makarantan sune ajinsu daya, karabata dashi dan Allah dan he will only cause more harm to her life, Allah ya shirya mana iyalinmu gabaki daya" ahankali Abba da jikinshi yay wani irin mugun sanyi yace "Ameen" duk shiru sukayi Chairman na kallon Abba ba karamin tausayi yabashi ba sai zufa yake kana ganinshi kasan yadamu toyama za'ayi bazai damuba yarshi na shaye shaye ga yawo da abokan banza, ahankali Dady yasauke ajiyan zuciya yamikama Chairman hannu yace "I will not forget this, nagode nagode, yau dinan zanje har Barrack na nemo Lieutenant namai godiya duk wanda keson cigaban ka sanan duk wanda yarufa naka asiri a lokacin da u can't do anything mutum ne daba zaka taba manta wa dashi arayuwaba, dan Allah karkace a'a am inviting you for a dinner a gidana gobe dakai da Sameer shima yanzu innaje mai godiya zan gayamai hakan" washe baki Chairman yayi a whole Chief justice na Abuja High Court is inviting over to his house for dinner this call for celebrating, cikeda murna yace "that will be an honour sir, nagode zaka ganmu da izinin Allah, Allah kuma yanuna mana goben, this mark the beginning of amazing friendship anzama daya da izinin Allah, and karka damu komi will be fine kadage da mata addu'a kaida mahaifiyar ta she will change" ahankali Abba yace "Allah ubangiji yasa" atare suka fito har wajen motarshi chairman yarakashi sanan sukai sallama yatada mota yawuce Barrack.
ID card dinshi kawai yanuna cikeda girmamawa sojoji suka barshi ya shiga Barrack din tareda hadashi da wanda zai kaishi har office din Sameer, parking yayi bayan sun iso suka fito suka shiga, lift sukahau, sanan suka sauka a 4th floor sukai office din Sameer, knocking sojan yayi daga taciki akace come in, bude kofan soja yayi ya shiga Abba biyedashi Sameer ne zaune kan kujeran shi yanama wasu sojoji guda shida dake tsaye a office dinshi magana, sojan dake tareda Abba ne ya saramai tareda kamewa. "Sir, someone is here to see you" tashi Sameer yayi daga kan kujera dan kallo daya yamai yagane shi yasan chief judge sosai kawai ne wani abu baitaba hadasu bane, karasowa yayi har gaban Abba inda yake tsaye tareda bashi hannu yace "you are welcome sir" sanan yajuya ya kalli sojojin dakin yace "you guys can go" saramai sukai suka fita sanan ya nunama Abba kujera yace "please sit" zama Abba yayi tareda yin murmushi ganin yanda yakemai magana cikeda girmamawa yasa ya zauna, komawa Sameer yayi ya zauna akan kujeran shi, ahankali yace "ina yini Sir" murmushi Abba yamai cikin natsuwa yace "barka da ware haka Lieutenant, daga wajen Chairman nake, I went there to thank him, I came here to thank you as well, thank you so much Lieutenant Sameer" cikin dan kunya dajin nauyin mutumin Sameer yace "but why sir? You don't have to thank me am only doing my job, dan Allah kadena min godiya" wani irin burgeshi Abba yaji yayi ganin yanda yake da hankali ga natsuwa, murmushi yayi yace "I have to, chairman told me everything, duk wanda yamin abin alkhairi koda kankani ne saina mai godiya that is the policy dana dauka tun ina yaro Sameer hakan yasa Allah ya albarkaci rayuwana, kuma darajan hakan nakeci haryau, thank you so much Sameer Allah yamaka albarka" dagokai da sauri Sameer yayi ya kallai yanda yace Allah maka albarka saiya tunamai da baban su kafin yarasu, ahankali yace "Ameen nagode" ahankali Abba yace "am inviting you over to my house for dinner gobe kaida Chairman don't say no please son, ina jiranku gobe," wani kati yaciro ya ijiye mai akan table yace "this is my address, ina jiranku, sai anjima" yajuya yafita binshi da kallo Sameer yayi sunan son da yakira shi dashi namai yawo akai ahankali yadau katin ya kalla kafin ya ijiye agefe yacigaba da aikin dayake yi.
💫 *_BIN ABINDA ZUCIYA KESO_*💫
_CHASING THE HEART CRAVINGS_
Doesn't favor you always 💔
✍️ M Shakur
2️⃣0️⃣
Bayan yabar Barrack office dinshi yaje yay failing 1week leave daga aiki he want to stay at home yasama Rahima ido dakanshi.
Tunda garin Allah ya waye Rahima tarasa natsuwa tayi zuru zuru duk idan anbude Gate sai gabanta yafadi dan tasan Abba zai shigo in any moment, Mummy tayi tayi tai calming dinta down amma abin yaci tura tsoron mahaifinta da Rahima takeji dabanne dan ba yamata wasa ko kadan, kosu Siddiqa sun gani akwai wani abu akasa tunda suka tashi sukaga bandeji a goshinta gashi tana dingishi kuma tai zuru zuru ko kallon banza bata musu ba ma ranan dan ta gaishe dasu duka, tai salla kuma sanan ta shigo kitchen dudda babu wani abun kirki data iya amma saida ta taya Zeena aiki Zeena na wanke wanke ita tana dauraya, bayan sun gama kuma ta kwashe bawon doyan da Siddiqa ta fere ta zuba a bola, duk tanayi ne sabida batason akai karanta koda guda dayane wurin Abba, Mummy tai tai taida ita tazo taje ta kwanta ta huta taki yarda saiyi take.
Bayan Magrib Abba ya shigo gidan da sallama su Siddiqa ne kawai a falo da Mummy dataci gayu sosai suna kallon dan makaho a arewa 24 Mummy tayi tayi da Rahima tazo ta zauna suyi kallo taki, jin sallaman Abba yasa da gudu yaran sukaje suka rungume shi. "oyoyo Abba" tasowa Mummy tayi ta watsama yaran harara tace "sai asakan mini mijina" dan dariya Abba yayi yana kokarin danne bakin cikinshi yace "a'a bazaki koramin yarana ba, zodai tanan" yadan jawota da hannun dakanshi dat is free hakan yasa ta taho ahankali tana murmushi duk ya hadasu duka ya rungume he feels better his family is just his everything, sakinsu yayi ya zauna akan kujera Mummy ta zauna a kusada shi, Lubabatu ya kalla yace "je mota ki daukomin jakan danabari yauma nasake mantawa" duk dariya sukayi dan haka Abba yake kullum saiya kawomusu tsaraba kullum saiya manta dashi a mota, Hulan kanshi Mummy tasa hannu tacire tace "muje kai wanka Alhaji kasha hanya" kai ya girgiza mata yace "anjima inzanyi wanka zanji" gyadamai kai Mummy tayi tace "bari nakawo maka abinci" kai ya girgixa mata tareda yatsine fuska yace "not now kibari anjima" wani iri Mummy taji amma saita basar daidai Lubabatu ta shigo dakin da sallama da jakan Abba tabamawa ya karba yabude snacks ne da ice cream, sai grilled chicken a lejoji guda hudu, daya ya dauka yabama Mummy karba tayi tace "thank you Abban su" yadauko ledaji biyu na chicken din yabama su Siddiqa da ice creams keda uku karba sukayi sukai godiya sanan ya wawwaiga kaman dama chan bai luraba yace "ina Rahima?" Zeenatu ne tace "tana daki Abba" kwala mata kira Abba yayi. "Rahima, Rahima" zabura Rahima tayi ta tashi daga kan gadon gabanta nawani irin mummunan faduwa, bakinta har rawa yake tace "na...am, I....n zuwa" hawayen daya zubo mata ta share da sauri tadau hijabinta ta saka pink daya tsayamata a gwuiwa tabude kofa tafito kaman wanda kwai tafashe mawa aciki.
Kafe bakin Corridor Abba yayi da ido jira kawai yake yaga tafito, ahankali tafito sukai ido da ido da Abba hannun haggunta tasa tadafa gabanta tana harde kafa danji tayi fitsari zai zubo, bayan hannun damanta tasa ta goge hawayen daya zubomata takasa karasowa cikin falon daga wurin tace "san.....nu da dawo.....wa Abba" kafeta da ido Abba yayi yana kallonta irin kallon, haushi, takaici, tausayi dakomi ma barinma bandejin dayagani manne a goshinta, wata boyayyen ajiyan zuciya ya sauke ahankali yace "zoki amshi tsaraban ki" girgizamai kai tayi murya chan kasa tace "a'a nina k.....koshi Abba" tafashe da kuka sosai tana kara danne wurin tana rike fitsarin da kawai jira yake yaga Abba yamike ta sakeshi, shiru Abba yayi yana kallonta kaman yanda yayyinta ke kallonta yanzu suka kara tabbatar wa tayi wani laifi ne dabasu sani ba, itadai Mummy ba tace komiba but itama gaban nata faduwa yake sai shirya kalaman dazata fadama Abba take aranta ta wanke kanta.
Da hannu Abba yamata alamun zo yace "zonan Rahima" fashewa da kuka tayi kafin ahankali tadaga kafanta tsir tsir Abba yaga fitsari na diddiga akasa tana tahowa baice mata komi ba hakama na kowa a falon tsayawa tayi a jikin dinning tafashe da kuka sosai tace "Abba dan girman Allah karka daken please, wlh bazan karaba" girgixa mata kai yayi yace "bazan miki komiba, zo nace" yanda yamata maganan so calm yasa ta taho da kyar ta tsaya agabanshi tana bari tana