Showing 30001 words to 33000 words out of 184554 words
kanta daya ta kama mata kafafu, daya ciki, daya hannu suka sata a kafafa kaman sun dauko rake sukai gaba da ita, dudda ga abokananshi that click nashi na guys about 10 da babes nasu awajen amman ko ajikinsu Party abinsu suke.
Moh dake kusada Khaleel a zaune yace “kaikuma an ina kasamo yar sanda Lee”? Dasauri Sam yace “itace FAA din Noor?” dan tabe baki Khaleel yayi yana kallon yanda take kokawa dasu yana huro hayaki daga bakinshi daidai an kawo ta gabanshi suka sauketa da sauri Hawwa ta tashi tai wajen Khaleel azuciye daidai zatai kanshi matan suka sha gabanta daya tace “common Baby why are you so Feisty? This party is for you, let’s have some fun” kawai suka shiga zagayeta suna rawa shima Khaleel yatashi daga kujera yadaura hannunshi daya asaman gaban wandonshi yadaga hannunshi daya da pipe din shisha ke ciki yana very classy and iskanci dance Hawwa ta tsaya chak tana kallon Khaleel dake huro hayaki yana rawa, kunnuwanta kaman zasu fashe sabida bass da beat na speakers na DJ.
Lumshe idanunta tayi trying to get a grip of her temper before tabude idanunta dasukai ja tace “Khaleeeeel!” Sabida yanda ta zuciya wlh duk karfin speakun wakan muryanta surpassing karan chak ya tsayan da rawan dayakeyi hakanan kawai yaji muryanta har cikin kololuwan kokon ranshi, suma matan chak suka tsayar da rawan su Sam da Moh da sauran mazan ma haka, da sauri DJ ya kashe wakan yana kallon yanda kowa ke kallon Hawwa datai ihu idanunta sunyi jazur tana wani nishi kaman zakanya tana kallon Khaleel kaman zata kashesa shima yana kallonta chak baya ko motsi kawai zuciyansa na bugawa, hannu daya tasa ta watsar da matan dake gabanta tafara tafiya kaman zakanya dake dauke da izza da zuciya tayi gaban Khaleel dab dashi ta tsaya tana kallonshi da wild eyes nata kaman zatai kisan kai tai wani irin ihu da gidan gabaki daya ya dauka. “I don’t work for you nor do I work for your father Ibrahim!” Wlh saida maganan ya amsa agidan sabida yanda muryanta yayi echo, ta daga hannu tai pointing nashi da index finger idanunta na kyalli sunyi jajir tace “don’t ever and ever try to mess with me again cus saina baka tarbiyan da ba’a baka agida ba” tamai wani irin kallo kaman zata katsamai mari sannan azuciye ta juya zata wuce gidan yayi tsit kaman anyi mutuwa tayi kusan 5steps taji an kama left hand nata an rike gam abala’in haukace Hawwa ta juyo tadaga hannunta zata daurama Khaleel mari chak yarike hannun tana kokarin kwace hannun takasa tace “how dare you touch me!” Dan murmushi yayi yay giggling irin dariyan kunyan iskancin nan, kafin yamata wani kallo yace “not just your hand I can’t touch duk inda naga dama ajikinki and nothing will happen” yayi wani dan dariya dayasa yan iskan abokanshi da matayen suka bushe da dariya akahau dariya awajen sunamai tapi, Hawwa tabi kowa da kallo kafin takalleshi tace “Khaleel idan kayi kuskuren taba jikina saina gwada maka nobody touches Hawwa and gets away with it” wani kalan kai hannunta baya yayi ya murde yaturota gabanshi kirjinta yahade da nashi dan kusan tsawonsu daya baifi yafita tsayi da 3 ko 4inches ba, ijiyan zuciya yasauke alalace sabida yanda full chest bata yayi pressing against his, faduwa gaban Hawwa yayi ganin yaron nan fa da gaske dan iska ne bakinta yashiga rawa tafara kiciniya dashi tana komawa baya shikuma yana tahowa, yace “lemme do you a favor and kiss you it will calm this ur anger spirit down” ganin gadan gadan yataho zai manna bakinshi da nata yasa Hawwa ta fizge kanta da karfinta tai baya bata ankara ba tafada pool dan batasan takai pool ba.
EPISODE
Nutsewa Hawwa tayi cikin pool din, bata iya ruwa ba, batada wani relationship da ruwa banda sha dakuma wanka, pool din Khaleel ya kalla Hawwa na tasowa sama atsorace tana dukan ruwan da hannunta tamikama Khaleel hannunta tana nishi kaman wacce ke freezing dan ruwan sanyi tabude baki tace “Kha….” Ruwa ya shige bakinta tana kara komawa ciki ruwan, folding hannunshi Khaleel yayi a kirji yana kallonta so duk rashin kunyan nan batada any idea yanda ake swimming, sake tasowa tayi tana nishi kaman zata mutu idanunta sunyi ja ruwa duk ya shiga cikinsu ta mikama Khaleel hannunta eyes nata are telling him to save her gwanin ban tausayi ya tsaya chak yana kallonta, he’s enjoying the way she looks scared and terrified, and helpless, chan takara nitsewa cikin ruwan ganin bata tasoba kusan 4min yasa gabanshi yafadi, da sauri yafada ruwan yayi diving ciki, swimming pool din nada zurfi hango Hawwan yayi tanayin kasa tabude hannuwanta gyalen kanta ya cire, bakin kitson shukunta na lilo idanunta a lumshe, in his entire life banda Noor da akai kidnapping today is the second time yakejin mugun urge to save someone in danger, da sauri yacigaba da swimming towards her, ahankali yakai hannunshi yakama hannunta wani irin shocking yaji da sauri yajawota ahankali yasa kanta a kirjinshi yariketa da kyau, yakai hannunshi daya yasa abanta ya mannata da kirjinshi da kyau hannunshi daya kuma yana swimming up dashi yafito sama yafito da ita ya dauketa chak yahau matakala yafito ya kwantar da ita agefen ruwan hannunshi yakai zai danna cikinta yana kallon fuskanta saikuma ya fasa yadanyi smirking na iskanci, ya kalli Sam yace “Sam take some good shots” cizan lips yayi yace “u are the baddest in this game cousin” yadauki wayansa iphone 16 yace “all set” kawai Khaleel yakai bakinshi dab da nata like idanba kana kusa dasuba bazama kasan ba kiss sukeba yakai hannayenta yadaura a waist nashi.
Bude duka baturan riganshi yayi yakama hannuwanta yadaura yakama kaman irin she’s grabbing his shirt dinnan Sam yadau hoton, Khaleel yakai hannu ya daga kanta ya daura kan kirjinshi skin to skin Sam yayi snapping, fuskanta ya kalla saikuma gently yadaura fuskanta kan kumatunshi irin ita tamai kiss din nan akai snapping, kafin yayi murmushi sosai yace “that’s enough ” yatashi hannunshi yadaura kan cikinta dayaji babu komi ya matse kusan sau uku yayi sannan tafara tari yazare hannun nashi kawai yatashi ya tsaya chak yana kallon yanda take tarin da gashin kanta da yanda gashi suka kwanta akan goshinta, kafin tabude idanunta tass tadaurasu cikin nashi, ruwan gashinsa ne ya diga akan fuskanta da sauri ta lumshe idanunta, dan murmushi yayi yace “you can go I will call you tomorrow akan case din” yajuya yawuce abinsa, takai kusan 1min a kwance wajen sannan ta yunkuro ta tashi ahankali tana kallon wajen yanda suka cigaba da party su abinsu DJ yasaki waka, mikewa tsaye tayi ahankali ruwa na diddiga daga jikinta tana kalle kalle kozata gyalenta, hango gyalen tayi acikin ruwa chan tsakiya for the first time taji hawaye na neman zubomata tadaure tahana shi zubowa ta fuzar da iska tajuyo da kanta hangoshi tayi shisha na bakinshi yana rawa ahankali juyawa tayi tafara tafiya ahankali jikinta na rawa rawa ji take kaman akwai ruwa acikinta da wuyanta, ruwa na diddiga daga jikinta har zuwa gate tafito taga su Salman tsaye da blanket a hannunshi da wayanta da sauri yataho wajenta yace “Yallabai yace abaki thi…….” Wani mugun kallo tamai sannan tasa hannunta ta fizge wayanta tawuce, dasauri Salma yace “yace muyi dropping naki agida ki dauki motan ki” ko kallonshi batayiba tafice daga gidan tashiga tafiya jinta take kaman tsirara ba dankwali ga kayan jikinta na tsiyaya Allah yasa unguwanma babu mutane wajen wani bishiya taje ta tsugunna wayanta ta bude tai dialing number Ni’ima wayan na gab da katsewa tace “Best please I will share my location kizo ki daukeni” muryanta Ni’ima taji yasa atsorace tace “what happen to you Hawwa? Why is your voice sounding like that? Are you sick”? Voice nata nadan rawa tace “I will tell you idan kinzo” cikeda damuwa tace “bazan iya zuwaba yau accreditation akema hospital namu but bari nakira Baban Yaseer yazo ya daukeki yana gida send me the location” tana maganan ta katse wayan Hawwa tai sharing lokacin din, tana duke awajen kusan 11min taji anyi horn dasauri tadago kanta Baban Yaseer tagani yana fitowa daga mota da sauri yazo wajen tana kallon yanda har lokacin take diga yace “wat happened to you like this”? Girgizamai kai tayi tama kasa magana tana kokarin mikewa tsaye bishiyan ta dafa tamike kanta akasa, da damuwa yace “Hawwa” juyodakai tayi zata kalleshi sai kuma tai baya zata fadi cus jikinta ya sandare sanyi takeji kodan sabida yanda ta firgita tajita cikin ruwan da bata taba shigaba dawani irin sauri Baban Yaseer yakai hannunshi yakama hannunta yace “Hawwa” tsayar da ita yayi ganin yanda ta kankame jikinta tana shaking yasa da sauri ya saketa ya shiga cire jacket na jikinshi na suit da sauri ya daura tabayanta itama Hawwa da sauri ta kankame jacket din jikinta na rawa asanyaye yace “let’s go” fara tafiya tayi still taji kaman zata fadi da sauri Baban Yaseer yatareta gently yasa hannunshi akafadanta yana kallonta yashiga tafiya da ita tana takawa ahankali har zuwa inda motan nashi yake yabude gaban motan daidai zai sata motan Khaleel yafito daga gidan idanunshi suka sauka kan Hawwa dayaga an karama jacket wani ya dafe kafadanta yana bude mata mota tana kokarin shiga, tsare motan da mutumin da Hawwan yayi da ido, ta shiga ta zauna ahankali shikuma Baban Yaseer ya maida kofan yarufe mata yawuce yabude booth yana addu’a Allah sa akwai something na Ni’ima abayan motan yabata….
Khaleel na kallon motan yace “slow down” rage gudu driver yayi, hannu ya mika batare daya dauke idanunshi daga kallon motan Baban Yaseer ba yace “give me that veil” Dasauri Salman yabashi wani leda mai kyau da wet gyalenta ke ciki karba Khaleel yayi daidai sunzo saitin motansu yace “break” taka burki driver yayi yasa hannunshi ya sauke glass na bayan motan kasa yace “horn aggressively!” danna horn driver yayi da karfin gaske na rashin mutunci yanda Ogansa yace kaman zai cire musu kunne dayasa Baban Yaseer dake neman abu a booth yadago kanshi ya kallesu itama Hawwa ta dago kanta jikinta na rawan sanyi takallo motan dake musu horn din bala’i, ido ta hada da Khaleel dan motan Baban Yaseer ba tinted bace, wani irin kallon zamu sake haduwa yama Hawwa kafin yasa hannunshi yaciro wet gyalen yajefo saman motansu ranshi amasifan bace sannan yace “let’s go” driver yaja glass na motan sama da gangan yasa aka bade Baban Yaseer da kura suka wuce abinsu, rufe booth din baban Yaseer yayi yadawo gaban motan ya kalli gyalen yasa hannu ahankali yadauka yadawo side na Hawwa yabude yana kallonta yace “ba gyalenki bane wannan ba? Me yaranchan suka miki? Meya hadaki dasu?” Yayi maganan ranshi adan bace, yace “What did they do to you? Sune suka saki a ruwa? Basusan you can’t swim ba?” Dan lumshe idanu tayi kafin tabudesu asanyaye tace “swimming pool na fada by mistake basu suka saniba” Tausasa muryanshi yayi yace “what are you even doing anan area private properties ne nan na manya yawanci anan yaransu ke hada parties” ahankali tace “aiki aka turoni” dan shiru yayi yana kallonta ahankali yace “if anybody hurts you, u can always tell me Hawwa? I would be your protective shield, Are you sure you’re fine babu abinda aka miki”? Gyadamai kai tayi tareda sauke kanta cus batason yanda yake kallonta veil daya gani yabata ta amsa yarufe kofan yadawo yatada motan ya kunna heater sannan yaja motan bini bini yana kallonta chan yace “motan kifa”? “Yana chan gidansu gobe zan tura colleagues dina su daukomin” gyadamata kai yayi agaban wani shago yayi parking ya shiga coffee yasaya mata me zafi da abinci yafito side nata yabude ya ijiye mata yana bata coffee karba tayi tace “thank you” maida kofan yayi yadawo yashiga yatada motan yasake parking awani shago yasai hijabi yadawo yazauna yabata yace “put this on kafin Baba or yan anguwan nan naku afara surutu kin dawo ba hijabi” gyadamai kai tayi ahankali tace “thank you” har gaban gidansu yayi parking yau Baba baya kofar gida bude motan tayi ahankali tace “thank you Baban Yaseer” harta yunkura zata fita softly yace “Hauwa’u” ahankali tajuyo ta kalleshi hada ido sukayi dasauri ta dauke kanta, dan fuzar da ijiyan zuciya yayi kaman abu na damunshi murya chan kasa yace “promise me you will take care of yourself” dan murmushi kadan tayi tace “tom” tasake yunkurawa zata fita asanyaye yace “if something happens to you bansan yaya rayuwana zata kasance ba!” Da bala’in sauri Hawwa ta dago idanunta ta kalleshi, gyadamata kai yayi yace “Ni’ima will be devastated and duk abinda yasami Ni’ima nizai taba ko”? Murmushi tayi tace “hakane, thank you Baban Yaseer a gaida Yaseer and Yasmeen, saida safe” gyadamata kai yayi tafita zata maida kofan tarufe yace “Hawwa” dadan sauri ta kalleshi kaman akwai magana abakinshi ganin kaman tana kokarin gane abu yasa yace “if you need anything tell me or your friend kinji” gyadamai kai tayi tana dauke kai tajuya zata wuce yace “Hawwa” sake juyowa tayi dadan sauri akuma rude murmushi yamata mai kawata fuska yace “hijabin nan yamiki kyau”wani irin bambaram maganan yamata a kunne hakan yasa kawai tajuya da sauri ta shiga gidansu.
EPISODE
Babu kowa a tsakar gidan hakan yasa tawuce dakinta tasa hannunta a aljihu taciro key motarta dake wandonta key dakinta dake jiki tasa tabude dakinta ta shiga ciki ta ciccire kayan jikinta tanemi wasu kaya harda rigan sanyi ta saka ta kwaso kayan tafito tasasu a bucket anjima idan tarage jin sanyi zata wanke su yunwa takeji sosai abincin da Baban Yaseer yasaya mata ta faraci tadauki wayanta tana daddannawa har zuwa magrib tafito tai alwala tashiga tai salla tana zaune tana zikiri kaman daga sama taji muryan Baba na kiranta kaman zai daga gidan ransa abace tafito, cikin fada sosai yace “wato yanzu kin kawo matsayi kin isa sabida kinga kece ke bada abincin da akeci agidan sai yanda kikeso zakiyi, bakiji ina kiranki bane?” Baba fa ya iya masifa sometimes itama takanga kaman zafin Baba ta dauko baki tabude zatai magana yadaga mata hannu alamun tai shiru ya nunata da hannu yace “Hawwa yanzu nizan kawomiki abu sabida tsabagen isa da son nunamini ni ba kowane arayuwanki ba ban isa dake ba tunda bani bakici bani baki sha banda kafafu kece ke nema ki bamu, Hauwa nizan kawo mutumi ki aika amai dukan jina jina”? Masifan da Baba yakeyi yana magana da sauri yasa bama ta gane me Baba ke fadaba hakan yasa tace “Baba maganan wa kake haka?” “Maganan uwaki nake!” Ya zubamata ashar yana kumfan baki, yace “bakida mashinshini shekaranki talatin agidana nayi shiga nayi fita na nemo miki Alai Kabiru kinsa yaran aikinku sunje sunmai jina jina daga asibiti nake yanzu” faduwa gaban Hawwa yayi sosai yanzu su Hayatu dukan Alhaji Kabiru sukayi? No anya? There’s no way zasu dakeshi she knows her team, yanda tai shiru hakan ba karamin batama Baba rai yayi ba yanuna kanshi yace “Hauwa nike miki magana kika tsaya kina kallona ba uppan eh”? Umma tace “to kai waye banda abinka Malam, gaka ga ita kadan kagani ai” kallonta Hawwa tayi saikuma takalli Baba da idanunshi sukai jajir yana kallonta ahankali tace “Baba kayakuri nayi kuskure aika su Hayatu danayi su tsoratasa amman na tabbata basu tabasa ba Baba karya yayimaka” Baba namata wani kallo yace “nafito daga asibiti yanzu ni da Malam Sama’ila kice karya yamini”? Gyadama Baba kai tayi kafin ahankali tace “Baba kayakuri banason na batamaka rai yasa nakasa fadamaka, banason Alhaji Kabiru, ni bazan iya aurenshi ba bazan iya zama dashi ba saisa nasa su tsoratashi sabida yarabu dani”ihu Baba yayi yace “so kike na ninke hannu ina kallonki kikai shekara hamsin agidana baki aure ba? Me kike nema ajikin da namiji da Alhaji Kabiru baidashi? Bakimaji dadi kinsameshi ba keda kikai kwantai agida” lumshe idanu Hawwa tayi maganan Baba na mata zafi azuciya, Baba yayi ihu da kusan duka yan anguwan na jiyosu yace “nagaji da zamanki agidan nan nagaji Hawwa ki tattara ki barmin gıdana idan kinsan baki shirya aure ba gwara nasan eh zaman kanki kike da ki zaunamin agida ahaka” bude idanu Hawwa tayi takalli Baba idanunta sunyi ja ahankali tace “Baba ni kake kora daga gida?” Azuciye Baba yace “Abinda kikeso kenan tuntuni ban barkiba yanzu nabaki dama kije kiyi zaman kanki” hawaye masu dumi suka zubomata dasauri tashare su takalli Baba tace “Baba tunda nataso arayuwana bantaba nayi wani abin kunya dazai jamaka abin magana agariba, nakare mutunci na, nayi karatu nadage nazama wani abu sabida na taimakama mahaifina, na dauke maka duk wani wahala da tunani dazakayi da damuwa, Baba kadauka banson aure ne? Kadauka ban gaji da maganganun dakakemin kullum ba? But ya zanyi banda mai sona banda mai nemana titi kakeso naje natare hanya nace sai anzo an aureni dole eh Baba? Yakakeso nayi da raina Baba? Umma ta tasani agaba, kaima haka, yan anguwa haka ina zansa kaina naji dadi Baba yakakeso nayi da raina? Banda me aurena” Baba yace “karya kike Malam Kabiru dakikasa aka dakeshi fa? Shibamai son aurenki bane”? Hawaye Hawwa ta goge tace “bana sonshi bazan aureshi ba” cikin fushi Baba yace “nikuma idan bazaki aureshi ba ki tattara kibarmin gidana nasan banda y’a Hauwa nahuta” Hauwa zatai magana Baba yace “fita kibarmin gida” kallon Baba Hawwa tayi sai kawai ta share hawaye ta tajuya tana huci sosai takoma dakinta, tanada zuciya fa babban akwatinta ta sauko dashi kasa tabude sip tashiga kwashe kayanta tana zubawa ciki tana goge hawaye masu zafi da bayan hannunta taje gaban madubi ta kwashe kayan shafanta tasa tahade akwatin ta rufe taduki wuyanta tasa ajakan goyon ayanta tafito tanajan jakan da karfi Umma ranta kaman an wanke da ruwan zamzam ta taho da sauri tace “au da gaske Hawwa tafiya zakiyi eh? Bazaki bama Babanki hakuri ba ki yarda zaki auri wanda yakeso ki aura ba? Tafiya zakiyi yanzu da daddaren nan” ihu Hawwa tayi. “Tashin mini daga gaba Umma!” Dasauri Umma ta tashi