Showing 66001 words to 69000 words out of 184554 words

Chapter 23 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1881

FAA” tashi Baba yayi cikeda hikima yace “bari na karbi sako wajen mai keke” Dasauri Ammi ta tashi tace “muje na bika nafadamai abinda zai fadama Ramla” kawai suka fice.

Itama Noor dasauri tasaki Hawwa ta sauko daga gadon tai wajen Khaleel dake kallonta tace “Dady I forgot my second teddy in car I brought it for FAA” ahankali yace “meet Salman to take you” dasauri tai wajen kofa tajuyo takalli Hawwa dake binta da kallo tace “FAA I’m coming” Gyadamata kai Hawwa tayi tawuce tafita dakin yarage daga Hawwa sai shi, kafa daya yadaga yadaura kan daya yayi shiru yana kallonta, yanda Hawwa taji ajikinta ana kallonta yasa tadan juyo ta kalleshi hada ido sukayi zata ballamai harara komi daya mata nadawo mata arai, da yanda yayi attempting tabata but yanda taji shiya ceceta, plus dazu Baba nata cewa Ibrahima yakawota asibiti yabiya kudin komi da motocin data bata yasa softly da dan kyar tace “thanks” tadanyi shiru ta dai daure tasaki muryanta tace “thank you for saving my life” tasakeyin shiru ahankali tace “once nakoma aiki i will find a way to pay you back every penny daka kashe” tasakeyin shiru chan tace “all this daka kawo kasa atafi dasu banso, i hate favors barinma na mutane like you! So I will pay back everything” Murmushi kadan yayi batare dayayi magana ba wato tana sick bed still masifa take, Noor tadawo dakin ta tafi wajenta da sauri tabata teddy tace “FAA take, Dady said you will soon move to our house kikazo i will give you more and more teddy kinji” dan murmushi kadan Hawwa tamata tace “thank you beautiful Noor” tana mamaki uban me zai sake kaita gidansu dayake gayama yarsa zata” kusan 10mins yayi sannan yakalli Noor daketa zuba yace “let’s go” kiss ta manna ma Hawea tace “bye FAA” murmushi sosai Hawwa tayi tace “bye Noori” wucewa tayi wajen Khaleel yarike mata hannu sukai wajen kofa hakanan Hawwa samin kanta da kallonshi tayi, the way he walks, he way he held Noor’s hand, everything looks soo….ta tsaida tunanin, saida yakai daidai kofa ya tsaya Noor ta fita dan juyo da kanshi yayi karaf suka hada ido dasauri Hawwa ta dauke kanta, cikin dan iskan murya Khaleel yace “see you soon cry cry Kulu” dawani irin sauri Hawwa tajuyo ta kalleshi kaman zakanya, gira daya yadaga mata yace “see you very very soon Kululu” kawai yasa kai yafice daga dakin Hawwa tawani yunkuro tace “sunana Hawwa not Kulu or kulul whatever” Khaleel na jinta yayi murmushi yawuce abinsa.

EPISODE

Yau Hawwa ta tashi da karfinta sosai tun asuba Dr yazo yace “za’a sallameta yau but sai Ogansu Mai asibitin yazo” aka ciremata bandage na goshi da hannuwa ciwukan sun warke tanada jiki mai kyau sosai, wanka tayi tasa wani simple gown da aka kawo mata na atampa red dayamata kyau sosai, ta rame idanunta kana gani zai nuna maka tayi ciwo but takara kyau skin nata sai glowing yake na drip datasha, tun wajajen 7 Aminu yazo dan daga masallaci yazo basai Baba yazo ba daya shigo dakin Ammi bata ciki taje karbo magunguna daga pharmacy sai Hawwa dake zaune ta kishingida hannunta rikeda wayanta tana dannawa tana replying messages na DIG dasu Hayatu, ganinshi yasa ta dago kanta dasauri yayi wajen gadon yana murmushi yace “ya karfin jiki Ya Hawwa?” Murmushi kadan tamai tace “Alhamdulillah I’m fine yaushe zaka koma school why did you even come back”? Zama yayi gefenta yace “yayata that is the strongest person I know a duniyan nan tana rashin lafiya why won’t I come?” Shiru Hawwa tayi tana kallonshi tadan harareshi kadan tace “mutum sai dadin baki” dan dariya yayi yace “Ya Hawwa nasha fruits dinnan”? Gyadamai kai tayi yadauka da sauri yana sha Ammi tashigo tace “Aminu jinya kazo ko cin dadi jiyafa haka komi kuka raba naka yamafi na su Khadija” murmushi yayi yace “Ammi to nine babba” hararanshi Ammi tayi ta ijiye magungunan tace “maza gamaci mu hada komi Dr na zuwa za’a sallamemu wai” tai maganan tana mikawa Hawwa red veil nata Hawwa tasa hannu ta karba tayafa saman kanta daba dankwali, duk suna zaune har wajajen 9 wayan Hawwa dake hannun Aminu yana connecting hotspot nata danashi yahau ringing dasauri yabata wayan yace “Abraham office” hannu tasa ta karba tana kwanciya ta danna wayan tana sawa a speaker daidai lokacin ana knocking tareda turo kofan Abraham yace “Hello Miss Hawwa how are you feeling” magana kasa fita yayi daga bakin Hawwa sabida Khaleel data gani ya shigo yana sanye da labcoat ajikinshi an rubuta Dr Khaleel Mangal, ga stethoscope a wuyanshi hannunshi rike da file na Hawwa dakuma office pad da pen idanunshi kyar akanta ga Dr daya saba duba Hawwan tareda shi sai Nurses guda uku daidai Abraham yasake cewa “Hello Hawwa are you there?” Firgigit Hawwa tadan farga daga kallon Khaleel, adan rude tace “uhn” Aminu yasauka dagakan gadon cikeda murmushi yace “sannunku ina kwnan ku” gyadamai kai Khaleel yayi kanshi akasa yace “good morning Mom” kafin ta amsa yayi wajen gadon daidai lokacin Abraham yace “huhh wat a relief! I’m so glad you’re okay I’ve been so worri……” wayan Khaleel yasa hannu ya dauka tareda katsewa Aminu yadaura hannu a bakinshi yana makale dariya Ammi tadanyi murmushi kadan tace “muje waje Aminu” suka wuce suka fita, wani kalan kallo Hawwa tama Khaleel irin who gave you the authority to end my call amman mutanen data gani wajen yasa tadaure tadauke kai batai magana ba, professionally Khaleel yace “can I have your hand Mrs Lee?” Wani kallo Hawwa tamai shekeke irin is something wrong with this guys head, dayan Dr yace “Dr Khaleel she’s the patient I consulted you for kace nakara mata dosage na wannan medication din nan and BP ya sauka sosai” “hand” Khaleel yafadi fuska ahade har wani daci daci Hawwa keji abakinta yanda zata bama dan iskan nan hannu da kyar kaman ta kurma ihu ta bashi hannun tadauke kai tana kallon gefe, daura mata abun auna BP Khaleel yashiga yi sannan ya makala stethoscope a kunne da gangan yawani zauna abakin gadon yana facing nata arude tajuyo zatai magana yace “shiii idan ana auna BP ba’a magana” hadiye maganan Hawwa tayi wannan wani irin mutum ne, pulse nata da heartbeat ya saurara sannan ya zare stethoscope din yakalli Dr yace “she’s good” yakalli Hawwa yace “any complain Mrs Lee”? Dauke Kai tayi tareda girgiza mai kai bataso ta disgashi gaban abokan aikinshi ganin he’s not jobless ashema yayi school, gyadakai Khaleel yayi yace “in that case I can discharge you” yashiga rubuce rubuce a iPad din da pen sannan yabama Dr yace “zaku iya tafiya” wucewa sukayi suka fice saida Hawwa taji an rufe kofan sannan tajuyo hada idanu sukayi yana mata dan iskan kallo azuciye tace “katashi daga kusadani” cikeda kakkausan murya yace “anki” iyyee wow just wow irin kallon da Hawwa kemai kenan ganin karfin halinshi, rage murya sosai yayi yace “idan kika kara kuka kika sa kanki damuwa BP ki yatashi sabida that mad, crazy, babaric woman of yours mai kama da gumakan Egypt mesuem I will reap your heart off your chest kimutu gabaki daya nayi donating all organs naki to mabukata, starting from heart, liver, kidneys with this eyes etc” wani irin kallo Hawwa kemai baki bude ikon Allah, tadaure tarufe bakin tace “you’re nobody in my life dazakamin detecting what I should do and what I shouldn’t, you’re nobody to me Pops boy!” the way she talks shit! he can’t even explain but he enjoys it, dan matso da fuskanshi dab da nata yayi dasauri takoma baya gabanta na faduwa sanin su Ammi na waje tace “me..me….mehaka?” Ahankali Khaleel yace “I want to actually shows you who I’m in your life” dasauri yakawo fuskanshi kaman zai mata kiss Hawwa batasan sanda ta mika duka hannayenta biyu ta daura a kirjinshi ba hakan yasa ya tsaya chak kirjinshi ya buga dum! Hawwa tace “is this abinda ku kema patient naku a hospital dinnan? I will sue you Allah” dan murmushi yayi cikeda tsokana yace “koni i will sue you for touching my chest, index finger naki on my breast kina tabawa!” Abala’in haukacewan sauri Hawwa ta janye hannunta dagakan kirjinshi jikinta yahau rawa tama kasa magana, she just hates dan iskan yaron nan, did he say breast uban wani breast zata taba ajikinshi? Murya chan chan kasa Khaleel yace “do you have crush on me? Cus you were trying to take advantage of your handsome Dr duk kin gama mammatse mini this” yataba nonuwansa yana mata very cute smile da white hakoranshi ke showing yamata wani irin kyau a idanu.

EPISODE 

Bugawa kirjin Hawwa yayi sabida yanda murmushi taga yamai kyau da sauri ta dauke kanta tayi folding hannuwanta a kirji tace “ewww Allah ya kyauta you don’t even belongs to league na men da Hawwa fancy, babu abinda zanyi da womanizer, drunkard and a playboy like you!” Shiru Khaleel yayi yana kallonta kaman mai nazarin wani abu saikuma yatashi daga bakin gadon jakan daya gani a tsakar dakin yadauka yace “we will see about that if this womanizer, drunkard and what’s even the last one dakika fadi Kulu”? Aharzuke Hawwa tace “nace maka ba sunana Kulu ba” dan murmushi kadan yayi baice komiba yawuce kofa, Hawwa data kara kulewa sabida yanda taga ya maidata mahaukaciya tace “ina zaka da jakana? Zaka kara da sata akan qualities din naka ne”? Tsayawa yayi saikuma ya juyo ya kalleta yabude baki zaiyi wata magana kawai saiya daga mata gira daya yamata dan iskan murmushi yabude kofa yafito dasauri Aminu yazo zai karbi jakan yace “kawo Ya Ibrahim nadauka”girgizamai kai Khaleel yayi yace “no dauko sauran saika sameni a mota awaje” yawuce Ammi tabishi da kallo kawai taji yafara kwanta mata arai itama ta tashi tashiga dakin Aminu ya kwaso sauran kayan yafito, Ammi takalli Hawwa data kirne fuska tace “lafiya naga ranki abace” dasauri ta gyara fuskanta tace “bakomi Ammi” hannu Ammi tamika mata tace “tashi mutafi gida to” ahankali ta sauko daga gadon Ammi narike da hannunta suka fito Khaleel na tsaye tareda Aminu yagansu sun fito duk yanda yaso yadena kallon Hawwa data haderai tadauke kai yakasa daga Ammi har Aminu saida sukaga kalan kallon da yakema Hawwa kaman zai hadiyeta da idanu, har wajen motan sukazo Hawwa tace “ina keken Aminu”? Dan sosakai Aminu yayi zaiyi magana Khaleel yace “I’m taking you home dakaina” yasa hannu yabude musu bayan mota yace “Mom shiga” ahankali Ammi ta shiga shikuma Aminu ya zagaye shiga gaba abinshi Hawwa ta kalli Khaleel da idanunta dahar sunyi ja, Ammi ta leko ta window ganin yanda take hararan Khaleel tace “shigo mana Hawwa” danne komi tayi sabida Ammi ta shiga taki rufo kofan yadanyi murmushi yasa hannu yarufe yashiga gaba ya kunna motan he can’t even remembers d last time dayayi driving haka yaja motan su Salman na binsu abaya cikin wata Lexus.

Aminu sai hira yakema Khaleel, adan hankali yace “me kake karantawa a school” Dasauri yace “computer science engineering but nagama project nakeyi” gyadamai kai Khaleel yayi baisan kodan shi baida siblings bane but he kind of love siblings nata barinma yanda yaga suna sonta and suna sonshi ahaka har gida parking yayi Hawwa tabude tafito azuciye Baba yace “oyoyo oyoyo” kawai ya rungumeta yace “mara lafiya yaya jikin eh patient” dan murmushi tama Baba yace “naji sauki” da gudu Ramlat tafito tana zuwa tai wajen Khaleel tace “Ya Khaleel oyoyooo sannu da zuwa good morning” kallon Ramla yayi kowama na wajen yayi saikuma yayi murmushi, sosai Hawwa ta tsare shi da idanu he looks so good dayana murmushin, he just loves yanda suka nuna suna sonshi, cikeda wasa yace “Ram……” dasauri tace “Ramla sunana” gyadamata kai yayi yace “nice name” zatai magana Ammi tace “ke kibar mutane su huta” Baba yace “zoka zauna Ibrahima” dasauri Hawwa tasaki hannun Baba tawuce ciki abinta su Ammi da Ramla suka bita sai Baba da Aminu suka zauna awajen, Baba ya kalli Khaleel yace “sannu da kokari Ibrahima Allah yabaka lada nagode da komi” dan sauke kamshi kasa yayı Baba yace “yau zan sanar da Hawwa zancen auren ku” ahankali yace “Ibrahima Hawwa matarka ce yanzu kaine keda iko da ita bani ba, Alhamdulillah tasami lpy an salla mota daga asibiti ko yanzu kace zaka tafi da ita ban isa nace a’a ba” Baba yasake shiru yace “inaso ka sanar dani yaushe kakeso ta tare? Kanaso ayi taro ne? Zanso na gayyaci yan uwan marigayiya mahaifiyarta dake kauye da nawa yan uwan, yanda akai auren mudan sanar da mutane bıkın suzo wannan shine ra’ayi ma amman kai me kakeso?” Shiru Khaleel yayi baitaba biki ba as far as public is concerned haryau anamai kallon mara aure ne dan ba’a taba sanar da bikinshi waje ba, hakanan kuma ya kalli Baba ya kalli siblings nata kawai sai yaji he wants to throw wedding for them, sister su batai aure da wuri ba is only right he lets them celebrate her, and one last final point is kodan ya kular da Hawwan yanuna mata he can actually get duk kalan macen dayakeso yasamu aduniya yanaso yayi biki ayi su dinner yayi kissing nata in public yatabata bayanda zatayi, wani, Kayataccen murmushi yayi yace “Baba inaso ayi biki, nan da 3weeks” Dasauri Baba yace “dubamana date Aminu” calendar Aminu yashiga yana duba date yace “July 24th kenan Baba ranan asabar” ahankali yace “Baba I will handle everything zan kawo katin biki da komi” yakalli Aminu yace “kome akeso kamin message” Dasauri Aminu yace “banda number ka” kiramai number shi Khaleel yayi yayi saving sannan yatashi yace “Baba natafi” Baba yamai murmushi yace “bye my son”.

EPISODE 

Sosai Hawwa ke masifa aranta tana shiga cikin gidan, menene business din yaron nan da gidansu? She don’t understand sun masan wayeshi kuwa, tana shiga gidan Umma tagani a tsakar gida tana gyara hatsi tana ganin Hawwa ta dauke kai Hawwa tawuce dakinta batare datace mata ci kanki ba, dakin kamshi Ramla tasaka turaren wuta, kwanciya tayi akan gado ahankali, Ammi tashigo tace “mezakici nadafa miki Hawwa?”Ahankali tadaura kanta kan cinyan Ammi tai shiru batamasan me bakinta keso ba, Ammi tace “bari zanje kasuwa sainamiki farfesu” gyadama Ammi kai tayi tace “Ammi kidauki ATM card dina akwai kudi” dan gyadamata kai Ammi tayi Ramla na shigowa dakin, Ammi tace “Ramla zauna da yayarki kome takeso kimata, bari natasa Aminu gaba muje kasuwa tare muyi cefane zan taho da flask ma asaka ruwan zafi banso daga yanzu kuna zagawa da ruwan sanyi kinjina baida kyau ma mace” gyadamata kai Hawwa tayi Ammi tadauki jakan Hawwan tazare ATM dan bawani kudin kirki takedashi ba, tanaso tasaima yarinyar abubuwa da yawa tace “natafi” atare sukace “saita dawo” tafice tna fitowa waje taga Baba da Aminu na magana dasauri Baba yadakata yace “Zainabu ina zaki”? Anatse tace “wai kasuwa zani Malam nadanyo cefane Hawwa tace zatasha farfesu kasan har yanzu bata iyacin abinci sosai, Aminu tashi muje ka kaini” dasauri Baba yamike yana rage murya yace “inataso muzauna muyi magana Zainab, to mutanen sun samin miliyan hamsin din sadakin Hawwa a account an bani gwalagwalan kuma amman na adanasu, kece mahaifiyar Hawwa inaso na zauna dake da ita mubata sadakin daganan sai mu karbi abinda ba’a rasaba mu mata kayan daki kekuma kiyi naki shirin kinfini sani dai” gadamai kai Ammi tayi tace “ba matsala Malam yau zamuyi maganan da daddare In sha Allah, Aminu tashi muje” tashi Aminu yayi daidai su Khadija na zuwa sunma Hawwa girki Baba ya dakatar dasu yace “ban kuma ce naji wani ya sanar da Hawwa zancen nan ba”

Wucewa Ammi sukayi kasuwan, sun sayi kan rago, dadan yan abubuwan datakeso tama Hawwa girki dasu sannan tasiyo mata babban flask na ruwan zafi suna dawowa taga Hawwa ma na bacci tashiga girki Umma sai bambami take yanda yaran ta ke dakin Hawwa wlh suka shareta wajajen 3 Ammi tagama girkin sosai Hawwa taci takoshi sai yau ta iya taci abinci.

Around 9 Hawwa na zaune kan gado tana duba wayanta tareda Ramla da yawanci ke tayata replying chats na yan wajen aikinsu dan kowa yaji tayi accident, Ammi nakan dadduma ta idar da salla but still tanakan dadduma tana jan charbi Baba yayi sallama yashigo dakin, da sauri dukansu suka dago kansu Baba yashigo yanama Hawwa murmushi yace “kinji sauki yarinyana? Wannan dakuka natsu ahaka me kuke da waya? Kinji sauki” Gyadamai kai tayi ahankali tace “eh Baba” kallon Ammi yayi dake shafe addu’a yace “kin idar Zainab”? Gyadamai kai Ammi tayi takalli Ramla tace “tashi Ramla je dakin Umma zamuyi magana da Hawwa” hakanan dan faduwa gaban Hawwa yayi wannan dahar suna kada Ramla waje maganan me zasu mata? Wani ciwo gareta aka fada a asibiti? Daidai lokacin Aminu yashigo dakin dawata yar jaka kaman ghana masgo amman bottega ne mai bala’in kyau Baba yanunamai gabansa yace “zoka ijiye anan” ijiyewa yayi Baba yace “zaka iya tafiya Aminu” sannan yayi gyaran murya yadauki kujeran dressing mirror yazo wajen katifan dab da Hawwa itama Ammi tazo dab da Hawwa tazauna kan katifar, Baba yakalli Ammi data gyadamai kai yayi gyaran murya yaciro wayansa yabude yace “Hawwa na aurar dake, ga sadakin ki nan” yanuna mata alert na wayanshi na 50M yace “miliyan hamsin da dirhamin gwal dari gasunan” ya jijjiga mata jakan gabanshi, bugawa kirjinta yafara tana kallon Ammi takasa magana badai Baba yaji haushin Ni’ima yace ya aura ma Baban Yaseer itaba, Baba na kallonta yace “Ba Baban Yaseer bane mijinki ba Hawwa, na aurar dake ga someone even better, wanda ya fisa, yaro mai kunya, yaro mai natsuwa, ga dattaku ga girmama na gaba dashi, sunan mijinki Ibrahim Khaleel” bugawa kirjin Hawwa yayi sosai Ibrahim Khaleel Ibrahim Khaleel waye kuma Ibrahim Khaleel? Kaman Baba yaji abinda take tambaya anatse yace “Mahaifin Noor! Wanda ya ceto rayuwanki yakaiki asibitinsa sannan yabiya masu motocin dakika bata garin hatsari” Wani irin zabura Hawwa tayi ta yunkuro daga jikin pillow data jingina dashi a bango tana kallon Baba maganganun da Khaleel yamata na dawo mata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login