Showing 51001 words to 54000 words out of 184554 words

Chapter 18 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1882

Hawwa ta tashi tanason abinci, Ramla dakin Antyn ku zaki ijiye kayanmu” Dasauri Baba yace “dakin nata abude yake, kaita Aliyu akwai kazanta adaki zaki iya dumama mata shi Ramla” hannunshi Baban Yaseer yasa ya karbi jakan dake hannun Ramla yace “muje” binshi tayi suka fice wajen yarage daga Ammi sai Baba.

Aliyu na ijiye Ramla yajuyo cus bazai iya jiranta tayi wani girki ba ayanda yadamu din nan tsayawa yayi yay salla yafito yana ciro wayanshi daga aljihu inda yaga Ni’ima tamai sama da 20 miss calls thank God wayan na silent maida wayan yayi back yashiga mota yatada.

Shigowa reception din Baba yayi dan yafita yaje masallaci sallan azahar yadawo inda Ammi take zaune tana kallon gaban dakin da Hawwa tayi yace “likitan dana bari ya shiga yafito”? Ahankali Ammi tace “a’a baifito ba tukunna Malam gabana sai faduwa yake sunki fadamana komi har yanzu” shima Baba cikeda damuwa yace “karki damu in sha Allahu alkhairi zamuji” suna zaune awajen Dr yafito tareda Nurses yakalli su Baba yace “Alhamdulillah yarku ta farfado” harwani rige rigen tashi tsaye ake tsakanin Baba da Ammi but Ammi tariga Baba tashi dasauri tace “Dr zan iya ganinta”? Gyadamusu kai yayi yace “eh zaku iya ganinta amman kafin nan inaso kubini office inada magana daku” faduwa gaban Baba da Ammi sukayi, gaban Baba nafadi sosai yace “to Allah yasa lafiya, muje Zainabu” itama Ammi gabanta na faduwa ta gyadamai kai tabi Baba sukabi bayan Dr. Office din suka shiga suka zazzauna Dr ma ya zauna ganin yanda suke zazzaro idanu yasa yace “ku kwantar da hankalinku bawai wani abu bane dalili yasa nakiraku, na farko dai banda ciwukan data samu daga accident din nan yarku batada lafiya, mun gano tanada Hypertension wato hawan jini” daga Baba har Ammi atare sukace “hawan jini!”? Gyadamusu kai Dr yayi yace “yes BP yayi high sosai shinema dalilin dayasa na kiraku tunda nasan kune iyayenta in tambayeku ko akwai wani tunani da yarku keyi ko akwai takamaiman abinda ke damunta?” Shiru daga Baba har Ammi sukayi cus they know amsan tambayan Dr, abinda ke damun Hawwa is rashin aure da yawan tunanin dalilin, Ammi kuma tasan harda fadanta da Ni’ima yahadun mata but bata taba sanin Hawwa nada hawan jini ba, and she’s sure Hawwa ma batasan tanada shi ba danda zata gayamata, ganin sunki magana yasa Dr yace “I guess kunsan abinda kesa yarku damuwa dakuma tunanin datakeyi, banson na shiga family issue dinku dan haka bazan tambaya ba, amman dai kusani hakkin iyaye ne su kauda duk wata matsala da damuwa daga jikin yaran su especially idan damuwan yasoma haifar musu da cuta ajikinsu, arayuwan nan there’s nothing like yarona yayi girma he can take care of kanshi, naga kasa shekaranta 29 da 10months haka karubuta mana, Baba yaro ko shekaransa dari yana bukatan iyayensa su kula dashi, ku kula da ita dan Allah, ku taimakama yarku cus BP ta yayi high sosai, ku bata farin ciki, ku kauda mata damuwan and support her, BP yatashi yasa tai loosing control kanta tana tuki harta hada hatsari, hawan jini muguwan cuta ce da tashi daya takan dauki ran mutum, dan Allah akiyaye, babu maganin dayafi aiki kaman maganin iyaye a rayuwan yaransu, menene maganin nan danake magana akai? Shine support na iyaye da love da mantar da yaransu damuwa da bama yaran farin ciki da natsuwa……” Dr yaciga da advising Ammi da Baba sosai……

Around 1:30 yashigo asibitin parking yayi yasauko yawuce ciki, ganin baiga Baba ko Ammi wajen ba yasa yayi wajen dakin da Hawwa keciki ya leka ta glass na kofan idanunta biyu amman idanun sun kankance sosai irin na mara lafiya tana kallon waje guda tai shiru tana tunani, daga ita sai dogon ringan jikinta ga gyalenta an rataya wajen bag hanger dake gefen wardrobe na dakin gashin gaban goshinta dukya kwanta luplup ansa bandage a goshinta hakama hannuwanta duk bandage wani kalan sonta da bala’in tausayinta ne ya mamayeshi kaman ya shiga ya karbe ciwon daga jikinta, hannunshi yakai yabude kofan gently yana shiga ciki, ahankali Hawwa ke juyo da kanta kadan da kadan dan har yanzu kanta na banging saidai ba kaman dazu ba so da kyar take juya kan kallo kofan dataji an bude tayi tahada idanu da Baban Yaseer daya shigo yana mata kallon tsantsan so kaman zai hadiyeta, faduwa gaban Hawwa yayi kaman taga dodo tashiga mikewa tana tashi daga kwance dasauri ya yunkuro zai taho yace “don’t move Hawwa ina zaki”? Da muryanta da baya fita sosai cikin rashin lafiya tace “karkazo nan!” Chak ya tsaya daidai tana tashi zaune da kyar idanunta har layi suke kanta yafara kwankwatsa sabida yanda ta tashi, dafe kanta tayi da hannunta da drip ke makale tana damtse idanunta cus her head is pounding kaman ana daka a turmi da kyar tace “kafita Baban Yaseer!” Cus bamata kaunan ganinshi arayuwanta, kallonta Baban Yaseer yake kaman yau yafara ganinta ahankali yace “Hawwa nafita kuma why? Nine fa? It’s Aliyu, Kinsan yanda nake cikin damuwa kuwa?” Ganin yanda yake wani irin kallonta zuwa kirjinta dan andan zage zip na bayan dogon rigan, tashin datayi yasa gaban rigan ya zazzago sama saman kirjinta na showing, da sauri tarike gaban rigan da hannu daya dayan hannun takai bayanta taja zip da mugu karfin hali Hawwa ta sauko da kafafunta daga gadon adan tsorace Baban Hawwa yakara yunkuro wa zai taho yace “ina zaki Hawwa sit please you’re not well, me kikeso ki dauka? I can give it to you”hannunta daya akai dayan ta daga ta nunashi tana haki tace “kafita I don’t want to see you! Stay away from me Baban Yaseer” yana kallonta gently and softly yace “har abada bazan taba ita staying away from you ba Hawwa” ganin yacigaba da kallonta yasa Hawwa ta diro daga gadon danta dauki gyalenta datagani a hanger kawai ta zube akasa babu karfi ajikinta ko digi kaman kafafunta basa aiki tai wani kara tana kama kanta da duka hannun biyu tace. “Kainaaa uhnnnnnn”

Dagudu Baban Yaseer yayi wajenta without having a second thought sabida tsabagen yanda yarude kawai yakai hannunshi yadauki Hawwa dake kasa idanunta a kulle takama kanta da duka hannuwa biyun jin an dauketa yasa Hawwa tabude idanunta da kyar dan kadan suka hada ido da Baban Yaseer hawaye masu zafi ne suka fito daga idanunta cikin muryan da baya fita bamata da karfi sosai tace “Baban Yaseer kaji tausayina kafita daga rayuwana! Ka ijiyeni! Stop touching me, ka ijiyeni nace” tai maganan tana lumshe idanu ta rirrike kanta, yanda hawaye ke fita daga idanunta tana magana kasa kasa kaman yar baby ya kashema Baban Yaseer zuciyan he just wants to kiss her and hug her so damn tight, kofa yakalla ganin babu kowa dake tahowa yasa ahankali yashiga sauke fuskanshi zuwa daidai fuskan Hawwa he just love Hawwa and feels like kissing her baimasan meyake ba, fuskanshi na dab da sauka anata akai mahaukacin bugokofan dakin dayasa yadago kanshi da gudu Hawwa tabude jajayen idanunta da kyar suka kalli kofan suna hada idanu da Ni’ima data bugo kofan tana sanye da abaya idanunta sunyi matsiyacin ja tana kallon Baban Yaseer daya dauki Hawwa ajikinshi kaman yanda yake daukan su Yaseer da Yasmeen, adaidai lokacin kuma Baba da Ammi na zuwa wajen duk sukaci tura suka tsaya abayan Ni’ima duk suna kallon Baban Yaseer, yanda gaban Hawwa yahau bugawa ganin Ni’ima ta dauka kirjinta zai fashene da sauri ta shiga kokarin kwace kanta batama da karfin motsi abin gwanin ban tausayi tana kallon Ni’ima Baban Yaseer kuma yariketa gam ajikinshi yana kallon Ni’ima, wani kalan mosti fuskan Ni’ima yafara tana huci tace “ba kiss zakuyi ba”? Tayi mahaukacin ihu tana daukan kujeran datagani adakin tayi kansu tace “ka sumbace ta mana Aliyu…….”

EPISODE

Kyakkyawan baccin gagaran Khaleel yayi danko 30 minutes baikaiba ahankali yabude idanunshi yana juyowa daga rub da cikin dayayi yana kallon saman dakin baimasan meke damunshi ba, normally yakamata yayi bacci har zuwa 4 na yamma but yakasa baccin tunanin yarinyar chan kawai yake, kaman her sick spirit na kiransa, hannunshi yadaga yakalla da Hawwa ta ciza lumshe idanu kawai yayi yabude sannan yatashi zaune yasauka daga gadon, boxer yacire ya yar awajen yawuce abinsa naked yafada bathroom yayi wanka yafito yawuce walk in closet dinshi dake kama dawani exquisite boutique, shiryawa yayi yazaro Balmain monogram print flowing shirt dakeda kalan black print din kuma white yasaka, yadauko dogon denim wando na Diesel yasaka daya zauna ajikinshi da kyau dasdas, agogonshi yaciro from drawer na designers watch dinshi, yacire Furlan Marri yasaka dayama hannunshi kyau, yadan juya yakalli showglass na takalmansa kaman shago yasa hannu yaciro wani suede flat takalmi na Birkenstock Boston, sannan yadau turarukanshi yashiga fesawa yadauki brush yana taje kansa ya shimfada dadduma yayi sallan azahar sannan yamike yabude kofa yafito yasauka kasa, chan falo yayi yana kallon agogon hannunshi is 1:30 ba kowa afalo probably Mommy ta kwanta ko tana spa nasu ana mata massage, kofa yawuce aka budemai yafita wajen black Mercedes Maybach S class dinshi yayi dake kyalli tsabagen kyau da kudi, da sauri security nashi suka taho wajen yakalli Salman dake budemai motan yace “when did you come back?” Dasauri yace “not quite long Sir everything is sorted babu wani matsala motanta I called auto shop sunzo sun dauka har an fara gyaransa” yatsine fuska yayi kadan baice kome ba ya shiga bayan motan ya zauna, Salman ya maida kofan yarufe yakoma gaba yashiga ya zauna driver shima na shiga mopol dinshi ma haka, anatse yace “hospital” Dasauri driver yace “yes sir” yatada motan suka fita yana kallon hanya chan yace “music” waka aka samai yafarabi yanadan shaking kai yadaga wayanshi yayi selfie yasa a instagram story nashi hankalinshi kwance.

*

Kansu Ni’ima tayi da plastic chair data dauka dasauri Baban Yaseer yajuya yana sauke Hawwa agadon yajuyo yasa hannu da zafi zai karbe kujeran ta zame tai gefenshi zata rafkama Hawwa dake kallon Ni’ima completely heart broken Baban Yaseer yabude hannuwanshi ya tsaya agaban Hawwa, Ni’ima tace “kama rungumeta idan zakayi amman saina halakata, saina halakata wlh, Allah ya kasheki ya dauki ranki sai inga wazakaso Aliyu? Inaso naga ko zaka bita kabari kuyi soyayya, ba sumbatar juna kukeso kuyi ba kuka ganni kuka wayance? Ka tashi agabana” hannu daya Baban Yaseer yasa ya fizge kujeran daga hannunta yana kokarin ijiye chair a gefe tabi gefenshi zatayi kan Hawwa taji an riketa gam juyowa tayi daidai Ammi na dauketa da mari jikake tasss! Hawwa ta zabura tana kokarin mikewa ganin yanda Ammi ta zubamata mari but takasa tashi, Ni’ima ta dafe kuncinta tana kallon Ammi da jan idanu, Ammi tace “kika kara maganan banza anan saina sake daukeki da wani marin shashasha” Ammi takalli Baban Yaseer dake tsaye yana kare Hawwa cikeda fushi tace “tashi agaban yarinya na bar wajen nan, tashi nace!” ba musu yatashi ahankali yakoma wajen kofa ya tsaya ranshi in yayi dubu yabaci sabida abinda Ni’ima keyi, Ni’ima takalli Ammi idanunta jajir har lokacin kallon Ammi take tace “kika mareni Ammi? Ko uwata bata taba bari naba saike”?Ammi na kallonta jin maganganun datake rai abace tace “saisa ni nake tayata bawa diyarta tarbiya, kika karamin gara gara anan saina sake daukeki dawani marin, you’re very, very and very stupid Ni’ima hauka kikeso kiyi sabida namiji? Eh?” Shigowa Baba yayi zuwa wajen ya tsaya kusada Ammi babu alamun wasa akan fuskanshi yace “meke faruwa Zainab”? Ni’ima Ammi ta nuna tace “Malam Ni’ima tana daya daga cikin dalilan dayasa Hawwa kenan wajen” azuciye Ni’ima tace “menayi? Nakira yarku na yanke alaka da ita, naja mata layi, bansonta arayuwana dayake mayya ce, bakar mayya mara zuciya ce ita wacce tai kwantai haka ta dinga bina tanajan gwuiwowinta akasa tana rirrikeni tana kuka tana karna rabuda ita, nikuma na tattake hannuwan banzan nawuce nayi tafitata” sosai Baban Yaseer ke kallonta hakama Baba da Ammi yanda take magana kaman ba Ni’ima ba, can a sweet person turn monster over night? Sabida namiji? Ni’ima tace “mijina nawane kadai wlh, ba best friend ba ko kanwata ce saina jamata layi wlh, kugayama yarku tafita daga harkan mijina” nuna Baban Yaseer Ammi tayi tace “ga mijin naki nan ai shiya kawo kanshi nan, dau abinki kubar nan” cikeda rashin kunya tace “eh zan dauki abuna amman saina gama, yar iskan yarku kokarin sumbatan mijina take, mara kamun kai da natsuwa, Hawwa zata iyama maza fyade sabida tsabar bukat……” tsawa Ammi daka mata tace “Ni’ima!” Rai abace sosai tace “nasan waye Y’ata! Jedai ki bincike mijin naki, munsan kalan tarbiyan da muka bata” ganin Ni’ima zatai magana tabi Ammi da chachan baki yasa Baba yakalli Baban Yaseer strictly yace “Aliyu dauki matarka kutafi, mungode Allah saka da alkhairi” cikeda tsantsan rashin kunya Ni’ima tace “ba dole kace ka gode ba anci kudin mijina an koshi, yazo yabiya kudin asibiti da kudin magani, mayu kawai kwadayayyu masu neman kai da yars……” fizgota Baban Yaseer yayi yajuyo da ita tai facing nashi ganin abin nata yazama hauka yadaga hannu zai kwasa mata mari Baba yace “kul!”

EPISODE

Chak Baban Yaseer ya tsaya sabida yanda Baba yahanashi, Baba na kallonsu yace “ba’a dukan mata barta da halinta kutafi kawai, Ni’ima karki damu babu ko biyar na mijinki a asibitin nan, kutafi Aliyu” kunya ne yakama Baban Yaseer kaman kasa ya tsage yashiga ciki, yajata da karfi yace “let’s go” tutturjewa take tana kallon Hawwa dake zaune abakin gadon gwanin ban tausayi tana goge hawaye dake zubomata da sun kasa daina zubowa, Ni’ima can’t even describe yanda takejin tsanan Hawwa kawai so take ta mutu atleast idan ta mutu zata huta, Baban Yaseer zai natsu, ina jitayi bazata iyaba a haukace ta fizge hannunta kaman mai ciwon hauka ta taho tace “Wlh wlh saina kasheki banga dalilin da mijina zaifi sonki akaina ba, yana kirana dakikiya sabida ke ba, he’s telling me kinfini komi” kawai Ni’ima tai kan Hawwa da sauri Ammi ta zauna tana kama Hawwa zuwa jikinta dake sheshekan kuka ahankali dabai fita irin hurtful cry dinnan dayake fita daga soul naka, azuciye Baba ya tare Hawwa da Ammi yakama karfenshi daya a hammata gamgam yazare daya yarike a hannu yadaga sama, daidai Baban Yaseer na kamata tana ihu da karfin gaske, Baba yace “Idan ban miki karatun Alam nashara da karfen nen ba ba sunana Baba ba, hauka kikeyi ne? Nace hauka kikeyi ne? Ni’ima kin haukace ne? Kinmanta kawarki dakuke zuwa wajena nabaku kwandala kwandala na siyan alawa? Ni’ima Hawwa fa dakike fushi dani idan na bata mata rai? Sabida miji Ni’ima kikema kawarki fatan mutuwa? Ina amintan? Ina kauna da soyayya ina? Ina zumunta? Duniyan nan duka duka guda nawa take? Dudda ina nemawa y’ata miji har ina bada sanarwa a masallaci mesa bantaba mata kwadayin mijinki ba? Kin taba tunanin maisa ban ma Aliyu tayin Hawwa ba? Sabida nasan ayanda y’ata ke sonki bazata taba so ta auri mijinki ba! Nima bazan taba kaunar ku lalata zumuntan ku ba! Ni’ima haukacewa kikeso kiyi ne? Kunfi shekaru ishirin kuna tare meyayi zafi haka? Auren Aliyun tayine menene haka? Bakida lafiya a kwakwalwanki ne”? Tana kallon Baba tana fizge fizge da Baban Yaseer tace “eh hauka nakeyi Baban Hawwa! Akan Aliyu zan iyafin hakama haukacewa, yarka ta kiyayi mijina kawai kagaya mata, ta kiyayeshi!” kallon Aliyu Baba yayi yace “Aliyu dudda bansan ko Ni’ima ko wacece wannan ba amman dauketa kubar wajen nan kar raina yabaci” daidai lokacin some Doctors da Nurses da security na shigowa dakin, senior consultant dinsu yace “what is going on here? This is hospital not arena, why are you all traumatizing my patients? Everyone outside” Fizge hannunta Ni’ima tayi kaman mahaukaciya tana kallonsu tace “sakan mini hannu” takalli likitocin tace “patient dinku tai kwantai batai aure ba, ubanta gabaki daya yagaji da ita har tallanta yake gida gida lungu lungu, shine yanzu suke kokarin a manna ma mijina ita” Dr yakalli Baban Yaseer dake faman riketa yace “Sir I know you are a Muslim and bazaka so nasa security maza su dauki matarka ba, nabaka 30secs idan baka dauketa kun fitaba zansa maza su fitar da ita this is hospital not wrestling arena, munada patients dayawa dakuke tayarma da hankali, we can sue her for this, please kindly take her out” Aliyu da kunyan dubiya yasa jikinshi ma yayi sanyi yakai hannu zai dauketa ta fizge tareda tureshi takalli Hawwa dake kallonta idanunta sunyi jajur sabida kuka tanuna kanta tace “mijina zakibi Hawwa? Mijina? Wlh wlh saidai ki mutu ko nida ke mu mutu tare daki auremin miji” tana maganan tai wajen gadon Dr yama security guys magana sukai kan Ni’ima suna tareta suka rirrike mata hannuwa Ni’ima tafara ihu na boo

mutum tace “jama’a azo aga husband snatcher, wacce bakin halinta yasa for almost 30yrs babu wanda ya aureta, ubanta ma yagaji da ita neman kai yake da ita, infact yar iska ce, amfani take da kanta da daddare sannan take iya bacci, nitake kira ina bata maganin rage sha’awa kullu yaumin, aure takeso idanu rufe, da ace tanada mashinshini da tuni tabi maza sabida yanda takeda bakin jaraba, Hawwa harija ce duk dare saitai kukan neman namiji” wani irin nishi Hawwa tafara jin yanda Ni’ima ke tona mata asiri da karya da gaskiya zuciyanta yafara bugawa da karfi security sukai waje da Ni’ima, Ammi na ihu ganin yanda Hawwa keyi “Dr something is wrong with Hawwa na Innalillahi” akai kan Hawwa ana sa Baba da Ammi su fita waje.

A reception Ni’ima tacigaba da ihu mutane na taruwa patients na fitowa daga daki suna lekowa aga meke faruwa, kaman ba ita ake jaba tana nuna Baba da Ammi dasuka fito suna kallonta tace “wazai taimakama tsohon nan ya auri yarsa datai kwantai ba miji? Bai bama yarsa tarbiya ba sabida ciyar dashi datake yasa maza ke tsoron aurenta, itace komi nashi babu abinda yake tsinanawa sai gulman yan anguwansu, kunsan yarsa har gayu takeci tasa janbaki kowani zai ganta yace yanaso amman shiru babu machinchini” “get this mad woman out of this hospital!” Sukaji muryan Khaleel dayasa kowa yajuyo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login