Showing 6001 words to 9000 words out of 184554 words

Chapter 3 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1867

yace “Miss Hawwa tell us” iska ta fuzar ahankali sannan tace “the girl’s Mom! Noor’s Mother is my suspect!” Zumbur Khaleel yamike kaman zaki, hakanan kawai Hawwa taji gabanta yabuga dum! Awani irin zuciye yazo zai wuce Excellency yabiyoshi da sauri yana kiranshi Momy ma haka tace “Khaleel Khaleel ina zaka?” Chak Hawwa ta tsaya wajen kofan batare data matsaba tana kallonshi tace “if you try anything you might jeopardize chances namu na ganin yarka” wani irin waigowa Khaleel yayi saikuma ya taho gaban Hawwa kaman zaki yamata wani irin ihu! “Who do you think you are to tell me wat to do or wat not to do lady?” Yanda yake tsaye dab da ita kaman zai matseta jikin kofan yasa gaban Hawwa ya shiga faduwa dasauri su DIG suka tashi harda su Abraham da Hayatu ma, Excellency yarikemai kafada Mommy takamamai hannu suna janshi amman ko motsi bayayi huci kawai yake yana kallon Hawwa, DIG yakasa magana, cikeda karfin hali batare data nuna tsoro ba Hawwa tasake juyo da fuskanta kar ta kalleshi ido cikin ido batare datace komiba cus yazo gabanta dayawa she felt so uncomfortable but still kallonshi take, Excellency yajashi yace “enough mana Khaleel muje ka zauna” yatsu yanuna Hawwa yace “careful Lady! Dont overstep your boundary” sauke kanta Hawwa tayi takalli DIG daya girgiza mata kai alamun kartai wani abu, yakalli Excellency yamai alamun yacire Khaleel daga gabanta kaman kwai Excellency yashiga janshi tareda Mommy yace “calm down Son please kaji, dan Allah, don’t take it out on this poor woman she’s just trying to help us find Noor that’s her work, calm down Khaleely na” Mommy ta shiga mannamai kiss a hannu tace “calm down yarona, kayakuri, people like this can be so annoying, so mu barsu ayi agama kowama yahuta, calm down she’s not worth your anger” zuciyan Hawwa har wani makyarkyatan baci yake tadai daure batace komiba.

Momy tajuyo takalli Hawwa dake kokarin zama kusada Abraham tace “young lady ban haifo d’ana sabida mata like you su dinga batamai rai ba, next time be very mindful and cautious of kalaman dazaki dinga fadama d’ana, inba hakaba zan….” Dasauri Excellency yace “just let her be please na lallashi Khaleel I don’t want another drama” yakalli Hawwa yace “wat do you suggest now ayi Miss Hawwa”? Sosai Abraham ke kallonta he could see yanda ranta yake abace shima duk sun batamai rai, juyo da kanta tayi takalleshi da sassanyar muryanta tace “wat about last phone dana ce kaduba kagama?” Dasauri yana taba system dake cinyansa yace “give me few seconds” kafin chan yace “done” yatashi yana daukan wasu papers dayayi printing takawo mata yace “so nashiga wayan and this particular contact happens to be most recent calls nata and it’s not saved, so na dauka and track it down” duba takardan Hawwa tayi sannan da sauri takalli Excellency tace “Sir can I know awani waje kukakai kudin?” Dasauri Excellency yace “kwarbai” dawani irin sauri Hawwa tashiga juye juye a office din kaman mai neman abu wani koton calendar dakeda detailed map na Nigeria tagani a bango dasauri takai hannu taciro map din tazo gaban table na dakin ta shimfida map din kowa yataso yazo wajen banda Khaleel tana kallon map din tace “Hayatu pen” dasauri Hayatu yabata pen ta karba tai circling wani waje tace “this is inda kukakai kudin kuka ijiye” sannan ta kalli paper da Abraham yabata tasake circling wani waje a map din tace “this is location na cellphone datake waya dashi” saikuma ta mike da sauri tana kallon map din kowa na kallonta kaman TV, tace “gps location na wayan yana cikin mall ne” saikuma ta sake dukawa tanabin hanyan map din da kallo kawai sai sukaga tai circling wani waje gefe daya dakeda dan distance kadan da location na wayan tace “got them!” Dasauri kowa na dakin yace “uhmm”? Dasauri Hawwa tace “Sir this is wajen da aka kaimusu kudi almost 20km ne to this mall, kidnappers hardly keep victims nasu a wajen mutane sabida fear of being caught, victim can shout, scream or sick for help, so the nearest place I think zasukai little Noor is Dajin Dawa, this place” ta nuna inda tai circling da pen tace “I’m

sure suna wajen, let’s go” dasauri Excellency yace “Alhamdulillah, Alhamdulillah” juyawa Hawwa tayi zuwa wajen datake zaune tadauki wayanta shikuma Abraham yatafi wajen kayanshi yana hadawa a katuwar bag pack dinsa, tashi Khaleel yayi yace “I’m coming along too” Juyowa duk sukayi suna kallonshi banda Hawwa dake duba wayanta data dauka, anatse DIG yace “Yallabai it’s dangerous, su kansu basusan outcome na operation din ba, kazauna my team will bring yarku safe” tsawa Khaleel yamai yace “I said I’m coming along, and I’m coming along” wani shegen kallo Hawwa tadago kanta tamai kawai tawuce kofa abinta tabude tafice duk suka juyo jin an fita, su Abraham suka bita suma shima Khaleel din yabiyosu, tsayawa wajen motansu Hawwa tayi taciro rigan bindingansu vest tashiga sawa ko kallon inda yake bataiba tadaiji tafiyansa, tadauki black shade nata tasaka sak ta fito bad ass bitch abinta sannan tadago kai hada idanu sukayi da Khaleel dashima ya hade fuska yana kallonta, dauke kai tayi abinta tabude bayan motan tashiga tai zamanta.

EPISODE

Saka vest dinsu su Abraham sukayi, last vest din Hayatu ya dauka ya mikama Khaleel yace “put this on and stay behind us yallabai don’t try anything” kallon vest din Khaleel yayi yamika hannunshi ahankali ya karba yasaka, Abraham yabudemai bayan motan ta dayan side din yace “here zoka zauna” kallonsa Khaleel yayi sannan yataho ya shiga ahankali ya zauna Abraham yarufe kofan, yakoma gaba ya zauna shima, Hayatu ya shiga mazaunin driver yaja motan, dan gyara zama Khaleel yayi ahankali batare daya kalli Hawwa ba dan wani irin haushinta da tsananta yakeji, Abraham yadan leko da kanshi yakalli Hawwa dake kallon glass na motan ga bakin shade a idanunta cikeda kulawa yace “you good Miss Hawwa”? Juyoda kanta tayi ahankali tadan kalleshi ta gyadamai kai tace “yes thanks, set up the drone” gyadamata kai yayi yace “sure” sannan ya gyara zamanshi yabude jakan jikinshi yana cicciro parts na drone din yana hadawa, har suka soma kaiwa wajajen 7:30 na yamma garin yadan soma duhu, dajine wajen but akwai containers na trailers haka that looks abandon, parking motan sukayi daga nesa but still sun shigar da motan cikin daji sabida bishiyoyi su kare motar kada agansu, Abraham yaciro ear bugs guda uku, yasa daya yabama Hatayu daya, yajuyo yabama Hawwa daya ta karba ahankali tadanja gyalenta baya tafito da kunnenta tasaka duk Khaleel na kallonsu sannan Abraham yabude motan yafito ya ijiye drone din ya kunna yatashi sama yana controlling nashi yadawo cikin motan ya zauna Hayatu ya matso kusada shi suna kallon screen din tare suna neman inda kidnappers din yawanci wajen duhu ne hango haske daga tachan nesa yasa dasauri Hayatu yace “take the drone chan naga haske” dasauri Abraham yashiga controlling Khaleel yadan yunkuro cus yakasa daurewa shima yana leka screen din har zuwa inda kidnappers din suke mutum 4 ne agaban wasu bishiya zazzaune suna shan taba daya ya iza ittace dasuka zagaye da dutse suna gasa nama sun kunna katuwan tocula saiga wani container wanda kofan yake abude dasauri Hayatu yace “can you get the drone zuwa ta bayan container wajen window muga ko yarinyar na ciki” gyadamai kai Abraham yayi yana juyawa har zuwa wajen window drone na lekawa but babu haske sai chan sukaji kukan yarinya da muryanta ya galabaita. “There’s ant on my body kwaro Dady” rawa jikin Khaleel yafara adan rude yace “that’s my daughter, it’s Noor” dan kallonshi Hawwa tayi aranta tace “so you love yarka this much but karabata da mahaifiyanta” juyowa Abraham yayi hakan yasa Khaleel yakoma ya zauna, controller yabama Hawwa ahankali tasa hannu ta karba yace “code 22028IV” ahankali Hawwa tace “noted” bindigoginsu suka shiga cirowa suna kara shiryawa suna bakin guns din silencer Hayatu yaleko bayan ya kalli Khaleel yace “Yallabai I didn’t mean to disrespect but dan Allah don’t interfere in this operation, you have to trust us, rest assure cewa we will save your daughter, karka fito or try anything kada ka zaman mana liability, the mission is saving Noor, you and Miss Hawwa stays in the car, and guide us with the help of drone nida Abraham go inside and rescue diyarka mufito is going to be quick” baki Khaleel yabude dake rawa sosai ahankali yace “you will rescue Noor ko?” Gyadamai kai Hayatu yayi cus daga gani kasan yanason yarinyar yace “yes safe and sound in sha Allah just trust me” gyadamai kai Khaleel yayi da sauri, Hayatu yakalli Hawwa dake kallonshi yace “stay put” ahankali Hawwa tace “safe” gyadamata kai sukayi sannan suka bude motan without making sound suka maida suka rufe sannan suka wuce, Hawwa ta shiga controlling drone din tana zagaye premises din tana patrol chan tace “Halt!” Da sauri Khaleel ya kalleta, hankalinta nakan screen din gabaki daya tace “I just saw another haske I’m going there right now to check” daidai takai wajen tace “is not just 4 of them akwai 3 more a wajen they’re holding rifles” Dasauri Hayatu yace “wat do we do Miss Hawwa?” Dan lumshe idanu tayi kadan chan ta budesu tana sauke ijiyan zuciya tace “can you take four men at a go Hayatu?” Dasauri yace “Yes Ma’am” gyadamai kai tayi tace “proceed to inda target namu take extract her and bring her to extraction point, Abraham lay low awajen and stay alert incase they move take them down, makesure Hayatu yadauko the little gurl, I repeat karkai komi lay low until I give you signal to” dasauri Abraham da Hayatu sukace “yes Ma’am” ahankali Khaleel ya matso dab da ita dago kanta tayi da sauri ta kalleshi kamshin dayake na ratsa hancnta dan kallonta shima yayi kafin ya dauke kai ya maida kanshi kan screen din hakan yasa itama ta maida idanunta kan screen din, tafiya suka farayi tana kallon screen din Abraham yashige cikin ciyayi yana watching those 3men shikuma Hayatu ya wuce wajen maza hudu, dukawa yayi yadauki dutse ya wurga dayayi kara hakan yasa suka zabura suka tashi suka fara tafiya suna dube dube, ganin daya na tahowa inda yake yasa Hawwa tace “stay on alert a guy is approaching wajen bishiyan dakake ta bangaren dama” da dan sauri Khaleel yasake matsowa dab da ita cus so yake yaga screen din da kyau, ta gefen idanu Hawwa ta kalleshi batare datai motsi ba ko magana dan batason tama kulashi daidai guy din na zuwa Hayatu ya kwasheshi ya bugamai kan bindiga a keya ya sume warwas yafadi, karan dasukaji yasa sauran suka jujuyo daya yadauke katuwar security torchlight ya hasko wajen ganin dayansu a kwance yasa da sauri suka taho wajen suna kokarin daga bindiga Hayatu ya kwashesu ya barar dasu ya sumar dasu duka within a blink of an eye yasa tape ya kulle musu hannu sannan yawuce ciki dasauri sauri gudu gudu shiga cikin container yayi zuwa inda yarinyar take kwance baiyi wata wata ba ya duka zai dauketa yaji an bugamai kai ashe dawani adakin but drone baiyi capturing ba sabida daga window suka leka dakin, dasauri gayen yafito yana kalle kalle ganin they’re under attack, ganin wani yafito daga container ba Hayatu ba yasa Hawwa tace “oh no, Hayatu, Hayatu, talk to me” tashiga kiranshi but shiru arude Abraham yace “what happened Miss Hawwa? Meya sami Hayatu”? Kafin Hawwa tai magana taji mutumin yayi blowing whistle sannan yadaga kanshi yana kalle kelle kaman ance ya kalli sama, ganin drone yasa yaciro bindigar shi Hawwa na gudu da drone din but yayi shooting drone din yayi crashing suka daina ganin komi a screen na controller Hawwa tace “shit!” Dasauri Abraham yace “what happened? Miss Hawwa gasunan they’re leavin……..” shiru Hawwa taji hakan yasa tace “Abraham, Abraham” adan rude Khaleel yace “wat wat…..wat happened”? Cikeda damuwa Hawwa tace “my team are down” tayi maganan tana tashi tamika hannunta tadauko katuwar jakan Abraham dake front sit tashiga neme neme a jakan luckily taga grenade, da sauri tasaka a pocket na vest nata, ta zaro bindigarta tana kokarin fita, asanyaye Khaleel yace “where are you going?” Dan juyowa tayi takalleshi ba yabo ba fallasa tace “going to rescue your daughter”? Dasauri Khaleel yace “maza ne u can’t go alone sun miki yawa, call for backup mana” tana kallonshi ganin damuwa kan fuskansa sosai tace “I can’t wait for backup kafin suzo an tafi da yarka sun gudu cus they know we are here, before we track them again it will take time, maybe muma sun kashemu before back up yazo, if I leave now I might be able to save your daughter so I have to go” takai hannu zata bude motan karaf taji yarike mata bakin gyale hakan yasa gently Hawwa tajuyo tazubamai mayun idanunta, shi kansa Khaleel baimasan mesa ya riketa ba, cikeda damuwa sosai yace “I can’t let you go alone it’s too risky, you’re just a gurl, zan biki and protect you” duk yanda Hawwa kejin haushinsa saida tai smirking tace “I’m not just a girl, I’m police officer!” Ganin yaki sakinta sai kallonta yake cikeda damuwa yasa ahankali tace “kataba rike bindiga”? Girgiza mata kai yayi alamun no, juya idanu Hawwa tayi irin na raini din nan tace “how can you protect me kenan u can’t shoot? Just stay here I don’t want to be looking after an adult when my mission is your daughter, stay here ina zuwa don’t jeopardize my work” wannan karan bata jira amsanshi ba ta karbe gyalenta tafito da sauri Khaleel ya sauko shima Hawwa ta kalleshi zatai magana saita fasa kawai ta wuce tana tafiya ahankali without making a sound, Khaleel na binta abaya sukai wajen, har zuwa bayan bishiyan da Hayatu ya tsaya dazu ta duka ta leka tana kirgasu tajuyo ta kalli Khaleel dake kallonta looking damn scared cikin whispering tace “if you stay here u might be alive, I’m going to rescue yarka now” cikin yar karaman murya Khaleel yace “kefa?” Sounding like a bad ass bitch tace “uhmm, I don’t think yau zan mutu” sosai Khaleel ke kallonta yanajin wani adrenaline na bin jikinshi ganin suna filin daga and she seems to be having fun, shiko zuciyansa kaman zai fito ta baki, Hawwa tasa hannu taciro grenade daga aljihun vest din dake jikinta, takalli Khaleel dake kallonta tace “wanna see magic Pops Boy”? Sosai Khaleel yamata wani irin kallo jin sunan data kirashi dashi, Hawwa tasake smirking tadauke kai ta cire pin din grenade din sannan ta leka ahankali ta wurga musu grenade din awajen tajuyo takalli Khaleel tace “booom!!” Mahaukacin tashi bomb yayi da Khaleel baisan yayi hugging Hawwa ta gefe ba ya manna fuskanshi a kafadanta jikinshi na rawa ba cus baitaba experiencing something like this ba, ko harbin bindiga baitaba ji ba saidai a movie, he has never experienced crime world so he panicked.

EPISODE

Mahaukacin faduwa gaban Hawwa yayi jin yanda Khaleel yariketa fuskanshi manne a kafadanta jikinshi na rawa kana gani kasan this is the first time yataba jin karan ko ganin bomb ma, da dan sauri ta tureshi yakoma baya yana kalle kalle kunnenshi sunmai dummm baiji ko kadan, yana kokarin kunnenshi yadawo daidai yaga Hawwa tai wani irin super tai wajen aguje tana shooting nasu, wow! Dabadan he knows this is real ba and he’s present a live location dinba dayace action movie yake kallo, she’s so fast in harbi, and wayanci he notice ba shoot to kill take ba, cus baiga wanda ta harba akai ko zuciya ko ciki ba, she mostly target legs and hands, da gudu ta shige cikin container yarinyar Hawwa tagani tana kuka sosai tana ihu ta kankame kunnenta sabida karan bomb ga wuta data gani, ahankali Hawwa ta duka gabanta tasa yatsanta akan lips nata tace “shiiiiiiu I’m fairy Angel Anty I come to rescue you from bad guys,, dena kuka” juya mata baya tayi tace “hop on my back, hau baya” takai yatsunta biyu tana taba wuyan Hayatu ganin yana numfashi yasa tashiga kiransa “Hayatu Hayatu, wake up” ahankali Noor tahau bayanta ta kankameta, dasauri Hawwa ta tashi she will come back for Hayatu, Noor first fitowa tayi ahankali goye da Noor ganinsu yasa Khaleel yatashi yataho wajen su da sauri yazo ta bayanta yana murmushi sosai looking and sounding so emotional ganin little baby shi that looks so scared and terrified a bayan Hawwa yace “Noory” dasauri yarinyar tace “Dadyyyyy” karban ta yake shirin yi daya daga cikin criminals din data harba a kafa dake wajen yadauki sandan dake wajen yadaga zai bugama Khaleel dake kokarin karbe Noor daga bayanta, karaf Hawwa tagani dawani irin sauri tai pushing Khaleel yafadi a side nata sandan ya sameta a hannu da karfi ya yagi skin nata sai jini, kafa tasa ta daki kan thug din ya sume dasauri Khaleel yatashi yana kallon hannunta da jini yabata hannun rigan already yace “you are bleeding” ahankali tace “it’s fine, leave Noor help me pick Hayatu” gyadamata kai yayi tawuce dajin goye da Noor neman Abraham taganshi a sume akasa, dagashi tayi sukai mota tasashi abaya tasauke Noor ta sata a baya itama daidai Khaleel na zuwa da Hayatu a sheme ya ijiyesa abaya yasa hannu ya dauki Noor ya kankame ajikinshi yarufe kofan baya yadawo gaba yashiga ya zauna Hawwa taja motan da mugun gudu tana calling DIG office waya for backup. “I repeat my team are down, goons are also down seriously injured calling for backup, code 22028IV” Khaleel ya kankame Noor data kankameshi dukansu suna kallon Hawwa dake tuki around 11 nadare tana magana har saida DIG yadaga wayan dan da farko voicemail ne, ahankali Khaleel yakalli hannunta dudda baya ganin ciwon but hannun riganta was bloody.

Kusan around 1:13AM na tsakar dare sukakai gidan sharp sharp aka bude musu gate cus DIG yarıga ya sanar da zuwansu, tun kafin su karasa tsakar compound din Excellency da Momy da mutanensu ke tsaitsaye suna jiransu, tun kafin tai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login