Showing 102001 words to 105000 words out of 184554 words

Chapter 35 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1896

basuyi university ba amman Hawwa ce ta aurar dasu Baba baida ko sisi kudaden Hawwa ne akayan dakinsu, banda haka akai akai take turamanakudi takirasu ta tambayesu yaransu, Mama kinga makarantan masu kudi da Miemie keyi Hawwa ce Umma menene wannan abun wannan wani irin tsana ne eh Umma” ahankali Hafsa tace “Umma dukanmu yaranki mun hadu yau muna miki fada muna nuna miki gaskiya bazaki dauka ba?” Khadija da duk tafisu zuciya tace “kai wlh Umma Allah karya bani bakar zuciya irin taki” dasauri Umma ta kalleta saikuma tafashe da kuka tace “ohh nice mai bakar zuciya ba Mahaufitae Hawwa data rabani da baban ku ba, nakasa auruwa sai bayan tarasu yadawo yawani aureni kuna cemin kaza kaza, ina mahaifiyarku baku sona kin fison Hawwa shikenan na barkı da Hawwa gaku ga ita kufitarmini daga daki” shiru Aminu yayi saikuma yace “shikenan Umma bazamu tursasaki kiyi abinda bakiso ba, kituna Allah yana tareda masu hakuri, sannan Allah baya kama laifin wani da wani, banda haka Umma shi Allah yanada adalci” yawuce yafita, su Hafasat suka bishi abaya dakin Aminu duk suka shiga.

Hawwa na zaune kan dadduma tareda Noor sun idar tana koyama Noor azkar yarinyar is 4 amman wai bata zuwa islamiyya sannan babu mai koya mata agida, Baba kuma na hira da Ammi da Dado da Anty Lami Miemie da Ramla basa dakin sallama akayi Aminu ya bude kofan dakin yashigo dawata katuwar kwali na LG washing machine saiga su Hafsat duka biye dashi Hawwa tabisu da kallo Ammi tace “a’ah wannan kuma menene Aminu haka”? Dan murmushi yayi yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Ammi hada kudi mukayi muka saiwa Ya Hawwa washing machine na tambayi Hafsa tace shine kadai baku sayo ba dakukaje sayayyan kayan daki” yadanyi shiru yakalli Hawwa ahankali yace “Ya Hawwa I wish nafara aiki and I wish I can afford more than this wlh Ya Hawwa zan iya baki duka duniyan nan kin chanchanci haka”dakin kowa yayi tsit yana kallonsu, Ahankali Hafsa tashare hawayen daya zubomata tace “Ya Hawwa baki taba kallonmu kaman yaran kishiya ba, ko ki kallemu da abinda Umma take miki, Ya Hawwa da Baby Minal na ciwo bataci abinci ance a asibiti she is under weight Babanta baida kudin soyamata abinci” tai dan shiru saikuma tafashe da kuka sosai tace “Ya Hawwa kadaice tafito da kudi tadinga siyanma Minal abincin yara daban daban, kala kala, wlh babu wanda bata siyamana ba, cerelac su gaber rice babu kalan abincin yara da bata soyama Minal ba har yarinyar tazo tafara ci tanata kumari” ahankali Hawwa ta tashi dagakan dadduma idanunta yayi ja kanninta are making her emotional, Hafsa tace “I wish kowa aduniya zai sami big sister kaman Ya Hawwa, she takes care of dukanmu zuciyan Ya Hawwa daban ne, she’s too good” hannu Hawwa tabude mata dasauri Hafsa ta rungumeta tsamtsam a jikinta su Khadija ma haka, Aminu Hawwa ta kalla tace “come here big head” zuwa yayi tabashi side hug tareda shafa kanshi hawaye na zubowa daga idanunta she wish this was real marraige, all this farin cikin da yan uwanta keyi she wished for mutum better than Khaleel sukemawa, su Ammi kowa saida ya goge kwalla ganin Hawwa dasu Aminu, ahankali Hawwa tace “zan dinga amfani da washing machine din nan kullum kobanda wanki ma” dariya duk sukahau yi su da ke kuka daidai nan akai sallama ana bude kofan dakin duk suka dago Umma ce sanye da Hijabi kowa ya tsaya turus yana kallonta Umma bata taba shigowa dakin ba, Hawwa ta kalla daga bakin kofan tace “nashigo?” Gyadamata kai Hawwa tayi da sauri shigowa Umma tayi tazo gaban Hawwa ga mamakin kowa kawai saitai kasa zata duka dasauri Hawwa tariketa tace “Umma mehaka”? Fashewa tayi da kuka kawai tace “Hawwa ki yafeni ki gafarceni duk abinda na miki na dauramiki tsana akan abinda baki duniya akayi, na dinga miki mugun fata kema ki dade baki aure ba kaman yanda mahaifinki yamini, nayi kuskure amman yarana sun ganar dani, sun nunamin hanyar gaskiya Hawwa kiyakuri dan girman Allah” Dasauri Hawwa tace “Umma wlh bakımın komiba kiyakuri ki yafeba both Babana da Mamana abinda suka miki kinji” Gyadamata kai tayi tace “na yafe musu har abada” ta rungume Hawwa tace “Allah yamiki albarka, Allah ya albarkaci aurenki yabaku zaman lafiya da yara masu albarka” kowa na dakin harda Baba sukace Ameen, Umma tadauko tadauki ledan data taho dashi tabude atampa mai kyau ne ciganvi na gold irin na 15k dinnan tace “ga gudunmawa kinji” cikeda farin ciki Hawwa tace “Umma wayyooo Allah na nagode Umma tayi kyau ina sonta wlh saida salla zan dinga nasaka” Umma ta washe baki she loves yanda Hawwa ta nuna tanaso itadakeda atampopin millions a akwati Hawwa tawuce takaima Baba dasu Ammi tace “Baba Ammi kallo abinda Umma na tabani” Baba da Ammi tace akashe lafiya zuwa wajen dash Baba suke Umma tayi tace “Zainab Malam kuma kuyafemin” Ammi tace “Zainab komi yawuce amanta da baya” Baba yace “nayafe miki Zainabu nima kiyafeni” ahankali tace “nayafe Allah ya yafemana duka yahadamu a Aljanna” kowa yace Ameen, tace “Zainabu meya rage ba’ayiba? Mezanyi?” Ahankali Ammi tace “jere za’aje gobe agidanta inaso ke zaki jagoranci abin Umma, ga Lami kuma” Umma tace “ba matsala Allah yakaimu gobe da rai da lafiya” kawai suka shiga hira ana planning biki gobe dan akwai dinner da daddare karfe takwas Hawwa sai kallon kowa take adakin one big happy family all this farin cikin da planning bikinta hala nan da wata daya, ko sati daya, ko sati biyu yasaketa fa ko? Gashi mashayi, dan party, dazata gayamusu bazasu yarda ba, babu mai daukar bad magana akan Khaleel, lallen hannunta dayayi fitinannen kyau ta kalla wai itane zatai aure yanzu, kiranta Munawwarah tayi hakan yasa ta tashi ta kwantar da Noor datai bacci agado tawuce taje ganin magani zata bata yasa tace “ba Ammi tace adakata ba Anty” Munnawara ta dungure mata kai tace “wannan ba maganin mata bane, maganin cicciko da naman gaba ne taciki, batace kar abaki wannan ba ai, shanye nidai kibani kitafi” kama hanci Hawwa tayi tasha da kyar tanayi kaman satai amai Munawwarah tace “za’asha daga kafin afasa” Dasauri Hawwa tace “meza’a fasa”? Dan bata gane maganan ba Munawwarah tace “tashi kije nidai bacci zanyi” tashi Hawwa tayi tafice abinta taje ta kwanta. ‎

EPISODE

Da asuba Ammi ta tada Hawwa dan ta hada important kayanta datake bukata su Hafsat suka tayata akwati daya tahada na kayan datakeso uniform nata da credentials dinta, Umma ta karba sannan su Ammi da manyan maza suka shiga kai kayan Hawwa zuwa trailer da Khaleel ya aiko musu aka fitar da komi waje, zuwa around 10 mata suka shiga jeep da yazo daukan su, Aminu ma yabisu as namiji aka tafi dasu jere gidan Hawwa.

Kowa saida yayi salati dasukaga gidan Hawwa gate harsun gaji da kirgawa ga yan sanda da sojoji tako’ina, Mommy na tsaye wajen window office nata su Umma suka sauko daga mota tsaki tayi tace “bunch of local people look at them” tawuce ciki Excellency na falo tareda Khaleel daya kwanta yasa kansa akan cinyansa yana chatting abinsa cikeda masifa tace “wai Khaleely akanme zakaje kayi aure from this local family kuma harda biki maisa ba’ayi descreet marraige damuka sabayi ba? Wlh kunyan gayyatan mutanena reception na yau nake sabida kalan yar gidansu wayanda ka auro, batare da Khaleel ya dagoba yace “Pops talk to Mommm oooooo” Dasauri Excellency yadan rufe Mommy da fada yace “wai me haka Madam? How many time will you go forth and back on this matter eh? Kibar yaro yayi abinda yakeso idanma destination wedding yakeso let it be, meruwan mu da family su ko status nasu badai ya auri abinda yakeso ba fakat!”

Tashi zaune Khaleel yayi yakalli Mom cikeda rashin mutunci yace “ko kallon banza kikama family matana you will see the other side of me Mom” yana maganan yawuce hanyan side nashi yace “ask the workers akaimu su abinci da drinks” kaman Mommy zatai kuka cikin masifa tace “PA” zuwa yarinyar tayi da gudu Momy tace “attend to Khaleely Inlaws” ran Mommy abace tawuce fuuu tayi ciki Excellency yabita da kallo yana kadakai kafin ya cigaba da waya abinshi yau da gobe da jibi yadauki off sabida bikin dansa.

Mutane cike gidansu Hawwa kaman zasu zauna akatanga sabida yanda jama’a suka cika ko’ina, Hawwa na daki tayi wanka tasaka atampa mai bala’in kyau dinkin yamata sai addu’a ake ana mata Allah sanya alheri.

Wuraren 5 stylist nata da makeup artist nata suka fara shiryata in white gown around 7:30 aka gama shiryata lokacin duk an tafi da yan gida hall, salla tayi sannan aka mata daurin kai, wani diamond sarka aka samata Hawwa was screaming money ya Allah ita kanta data kalli madubi sai kawai ta tsaya dan she can’t believe itace, bata taba sanın she’s this beautiful ba, she looks like all this instagram brides da ake gani online, dagata sukayi Hafsy dake rike da wayanta tace “mijinki sai kira yake Hawwa” kin magana tayi dan batajin dadin komi fita waje sukayi wani red roll Royce ke pake akofar gidansu da akai arranging da flowers ga motocin security gaba da baya bude mata akayi ta shiga ahankali batare data kalli Khaleel dake zaune yana kallonta ba aka rufe akaja motan hannunshi yakai zai taba bata tadauke dasauri shi kawai kallonta yake gobe tana dakinshi around this time dan tun 5 zai turo atafi da ita tahowa yayi yadaura fuskanshi akan shoulder nata yakawo wayanshi yayi snapping nasu yana murmushi yace “I have the most beautiful girl as my wife” mtswww Hawwa taja gajeren tsaki gaban hall din akai parking aka bude musu suka fito suka tsaya Moh yazo yana sanye da suit yace “you are late” Hawwa ya nuna da kanta ke kasa yace “matana tarikeni” “Welldone Mrs Lee” Sam yafadi yajuya yakoma ciki dan bride da grooom shigowansu su kadaine bayason hayaniyan mutane na binsu, daganan waje sukaji muryan MC yana ladies and gentlemen the moment is here, Momy and addy Uncle and sister the bride and groom gasunan abasu standing ovation DJ DJ” DJ yasaka wakan like my father by Jax wanda Khaleel yace asamai idan zasu shigo sabida Baba yabashi labarin Mahaifiyar Hawwa and he wants to communicate to Hawwa da wakan ya gayamata cewa he will loves her the way Baba loves her Mom,

Shiga Hall din Khaleel yayi da ita ya Allah Hawwa da Khaleel sunyi kyau watttttt

Tana sanye da white gown nata gawani net da aka dauramata akan gashinta da aka gyara yayi kyau kaman tasaka attachment, Khaleel na sanye da suit black yarike musu hannu, yanda ake kallonsu sai Hawwa taji kuka, wakan dake tashi that is so cool na ratsata kallonta Khaleel yayi cikeda so yanuna mata Baba dake sanye cikin kaya exactly irin na Excellency yana tareda excellency yana kallonsu yana murmushi sosai, kawo kanshi yayi saitin kunnenta suna tafiya yace “I will love you Hawwa just like the way Baba keson Maman ki har yau dudda she’s late, I will love you a million times more!” wani irin kallon Khaleel tayi tayi cus she felt his words har cikin heart nata cikeda so ya gyadamata kai yana kallonta.

Mommy datai shiga na alfarma tasha zinare sarkan jikinta har cıbiya ta tsaya tana kallon Khaleel da yanda taga yana kallon Hawwa daidai sun shigo tsakiyan hall din aka saki wannan hayakin soyayyan wanda duk aikin Juzzyfabevent ne dan ita tayi handling entire wedding decor din aka samusu wakan soyayya na Christina Perri A thousands years, Khaleel yasaki hannun Hawwa yanuna ta yana waka yana rawa Hawwa na kallonshi Excellency da Mom suka saki baki suna kallon Khaleel tunda suka haifeshi basu taba ganin Khaleel this happy ba ko ranan da aka haifi Noor but look at him, today is the happiest day of his life ahankali Excellency yace “Khaleely this is not fun, you’re inlove” rawan yagama kawai yazo ya rungume Hawwa very tight akahau ihu Hawwa ta boye kanta ajikinshi sabida kunya dan har su DIG tagani dasu Abraham da Hayatu kowa ya gayyacesu oho, DJ yace “our shy shy bride”.

EPISODE

Mommy was really scared yanda taga Khaleel was totally lost in love, baya second biyu cikakku batare daya kalli Hawwa ba, and ita yarinyar no even send her son, zata iya kirga sau nawa taga Hawwa ta kalli Khaleel shiko kaman zai cinyeta, Mom duk zuciyanta ya lalace.

Cewa akayi abada labarin Amarya Khaleel yace shi zai bayar kawai yafito yana kallon Hawwa dake kallonshi asanyaye yace “I have alot to say about matana da zan iyakaiwa gobe so I will make it brief” yayi shiru yana murmushi yace “my wife is a very special person, anytime idan zan tsokaneta i call her Kulu” aka kwashe da dariya a hall din, Khaleel yace “kona cemata Kululu kuluwa yar sanda” zokaga dariya Excellency yace ma Baba “haka kake bari yana tsokanar maka yarinya”?

Baba yayi dariya yace “barsu abinsu duk soyayya ce” murmushi Khaleel yayi yana kallonta sosai yace “my wife is the most intelligent and hardworking young lady dana taba gani a rayuwana the first ever one!”

Yayi shiru yace “the first day damuka hadu something happened I called her Ke” Khaleel yawani zaro idanu dayasa yan hall suka kwashe da dariya sabida reaction nashi tells abinda Hawwa tayi kaman comedy, cikeda tsokana yace “matana ta iya masifa” kai zokaga dariya a hall Hawwa ta sauke kanta kasa ahankali duk kunya yakamata, Momy ta haderai tam, murya chan kasa Khaleel yace “my wife is loyal! Honest, truthful and kind, she’s strict batason nonesense da rawan kai and she’s truly loving, she protected me and Noor, Hawwa means everything to me, and I’m her best friend helloooooo” yawani daga hannu hall akace Hi ana dariya, yabada mic yakoma yazauna Sam yazo yabada labarin Khaleel shi sannan akace first couple dance da iyaye Khaleel yarike Hawwa suka fito Excellency Baba Ammi da Momy duk suka fito Mommy ta rungume Khaleel cikeda so tashiga share mai fuska yamata murmushi yana rikeda hannun Hawwa aka shiga manni aka koma.

Sai around 10 aka gama iyaye suka tafi yara aka tsaya after party su Hafsa sukakai Hawwa wani daki Kaman zatayi kuka tace “wai ba’a gamaba” dük eh sukace kaya aka chanza mata zuwa wani pink gown dayamata kyau aka mata dauri aka fotoda ita Hawwa tayi kyau agaban hall taga Khaleel tasa wani crazy shirt ya bubbude botura yana mata wani irin kallo kaman maye da saida gabanta yafadi aka kirasu hall suka shiga suna kaiwa tsakiyan hall Khaleel yashiga juya Hawwa yana wani irin rawa da ita ana ihu chan kawai yahau kissing nata Hawwa naso ta kwace takasa ihuu ake a hall din na bala’i DJ kanshi saida yayi ihu a speaker yace “ango need a room guysss” dasauri Khaleel yasaketa ya rungumeta tsam ajikinshi cus harya sami erection baiso agani, yahau rawa ahaka da ita Hawwa kaman ta mutu da bakin ciki tawahala Khaleel ya wahalar da ita awajen rawa sai wajajen 2 nadare aka gama mota suka wuce tazauna zai kama hannunta ta dauke batacemai komiba aka fara tafiya lumshe idanu tayi wahalallen bacci yayi gaba da ita ahankali ta sauke kanta kan kafadar Khaleel tarike hannunshi kallonta yayi cikeda so saikawai yaciro wayanshi yamusu video yasaka a insta story, har sukakai gida bacci take, tsayawa motan yayi da gangan yakai hannunshi gaban riganta ya matsa boobs nata afirguce Hawwa ta farka takalleshi tace “mehaka”? Turobaki yayi yace “munzo gıda kona wuce dake gıdana? Hade fuska tayi daidai an bude mata kofa saukowa tayi ahankali tawuce cikin gidansu da kaman gari awaye hatta Noor batai bacci ba daki tawuce tarage kaya Ammi tabata ruwan zafi tafada bayi tai wanka tazo ta kwanta sai bacci tagaji, washe gari yinin biki by one za’ayi walima anan cikin gidansu agama by 4, anything 5 atafi da Amarya tunda Hawwa ta tashi taji kawai bakin ciki takeji

Ta kumbura tai tam Noor kawai tama wanka da kanta tasa mata kaya masu kyau tawuce ta tafi wajen su Miemie abinta, sata akaiyi tai wanka tasaka wani lace from akwatinta mai kyau za’amata makeup tana bataso su Hafsa suka fadama Ammi Ammi tace abarta dan tun safe taga kwayan idanunta, kwanciya tasakeyi agado Munawwarah tashigo tace “Oya tashi muje dakina” kaman Hawwa zatai kuka ta tashi tabita magunguna tabata daban daban Hawwa tasha taci farfesun da aka bata sannan tawuce takoma daki bayan anyi azahar aka shiryata Malama tazo na walima aka fito aka zazzauna wa’azi tayi kaman zamantakewan aure da hakkokan aure da yanda ake kissa dasauransu sai around 4 aka tashi aka hadu akai jam’i kafin ma su Idar Aminu ya shigo gidan yace “anzo daukan Amarya” Hawwa na sallame salla kawai saita fashe da kuka sosai awajen abin gwanin ban tausayi nan aka fara kaita wajen yan uwan Baba suka mata fada, Yan uwan mahaifiyarta suka mata fada, Abokanai arziki makota akama Hawwa fada sannan aka maidata dakinta lokacin around 5:35 Baba da Ammi ne zaune awajen su kasa kowa yafita.

Baba yasauke ijiyan zuciya yace “ina mika godiyana ga Allah subhanahu wata’ala daya nunamin aurenki Hawwarh, Hawwa na baki tarbiya nakuma san waye ke Hawwa kibi mijinki sau da kafa, nasan ayanda aurenku ya kasance amman inamai tabbatar miki Khaleel na sonki baniba kowama yaga soyayyan nan ya shaida, Hawwa kada kiga kusan kanku daya banbancinku shekaru biyune tsakani kice bazaki girmamamsa ba, No ban yardaba kibama mijinki girmansa” Baba yace “yi nayi bari na bari, Dan Adam ajizini duk randa kuka sami sabani ku shirya kanku, nasan agidan iyayen mijinki zaki zauna dudda dai bangarenki daban ayanda Umma suka fada inaso ki kula da iyayensa kaman yanda kike kula da mu, ki girmama su ki daukesu tamkar ni da Ammin ki”.

EPISODE

Baba yayi shiru yace “Ibrahima bai riga yace wani abu kan aikin ki ba koda nan gaba zai nuna ki barsa, ki barsa aure yafi aiki Hawwa, Allah yamiki albarka yabaku zaman lafiya, yabaku yara masu albarka,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login