Showing 78001 words to 81000 words out of 184554 words

Chapter 27 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1899

even deny it nasan aikinka ne, why would you do that to my friend?” Hamma taji yayi yace “zan fita I know you don’t have friends so bansan wat you are saying ba bye” Hawwa tace “aikin kenan party giya da mata” murmushi yayi yace “gashi na aureki” zatai magana ya katse wayan jitayi ranta yana kuna yana susa tasan yanzu club zaije maybe Allah kadai yasan time dazai dawo shiru tayi sai chan ta tuna yanda yamata kiss a kumatu a mota dasuri takai hannu tashiga share kumatunta kaman yasamata dafi ahaka tai bacci.

Washegari around 8 suka fito dudda tanajin bakin cikin shiga motan nan haka ta shiga Ammi tafara kaiwa park sannan tawuce office.

Tundaga gate ake mata yajiki ana mata Allah kyauta tana zuwa direct office na DIG tayi tai knocking yabata izinin shigowa yana ganinta yadakatar da rubutun dayake yace “Hawwa are you sure you’re strong enough kidawo aiki?” Murmushi tamai tace “yes Sir thank you” anatse yace “welcome back” gyadamai kai tayi ganin ta tsaya bata wuce ba yasa yace “akwai wani abu ne?”

Gyadamai kai Hawwa tayi cikeda damuwa, seat dake gabanshi ya nuna mata hakan yasa ta zauna akan kujeran ya ijiye pen na hannunshi yace “I’m listening Miss Hawwa” gyadamai kai tayi anatse tace “Sir I have a very serious problem I need your help” gyara zama DIG yayi dan yana bama Hawwa respect da girma dan ijiyan zuciya ta sauke tace “Sir I’ve never been to Senate President house banda time din nan damukaje aiki, I know nothing about them or household nasu” with so much anticipation DIG yace “what’s with Excellency Hawwa?” Ijiyan zuciya ta sauke cikin raunin murya sosai tace “Sir ranan danai accident ina hospital Babana yabasu aurena, sai bayan mun dawo gida anyi discharging dina ake sanardani wai wannan yaron nasa Khaleel aka auramin” tayi maganan hawaye mai zafi na sauko mata DIG kanshi was in shock yazaro idanu yana kallon Hawwa yace “you mean Khaleel Baban Noor”? Gyadama DIG kai tayi bakinta na rawa tace “I have no idea me suka gayama Babana, banso Khaleel yake yakarani acikin sahun matansa sabida yayi using dina and dump me bayan 1 or two weeks” Ko kadan DIGGG baiji dadin news dinba but still cikeda damuwa yace “Hawwa akanme mahaifinki zai bada auren ki batare dayayi bincike ba? I’m not saying that because maybe zasu miki mugunta or something no su basa wannan, kawai dansu baisan menene aure ba, baisan darajan auren ba, mata are like papers zai iya bude this page ya yaga and open another page, so why will your father get your married to such kind of man”? Bayan hannu Hawwa tasa tagoge idanunta tace “sabida he’s tired of me, yagaji da yanda nake zaman mai agida ba miji” DIG ko kadan baiji dadi ba yasakeyin shiru sai chan yace “to wani help kike magana zan miki”? Share fuskanta tayi tass kaman batai kuka ba takalleshi tace “I want you to come with me Sir muje ka gayama Babana the type of Man Khaleel is cus wai on 23RD this month za’ayi biki zan tare, I don’t want this marriage I don’t want to be victim of circumstance na gayama Babana all I know yaki yarda I’m sure ka tayani gayamai zai yarda”.

EPISODE 

Kallonta DIG ya tsaya yana yi kaman mai lissafi na kusan 2min sai chan ya sauke ijiyan zuciya yace “Hawwa listen ki fahimceni keba yarinya bace I will be very raw in whatever I will tell you now” yadan sauke ijiyan zuciya yace “I’m a father inada yara mata babu wanda ya isa yazo yace zai aure yarana nabashi batare danayi bincike ba, for mutanen nan suzo mahaifinki yadauke ki sharp sharp batare daya damu dako kinaso ko bakiso, ko kinsan guy din ko baki sansa ba yabada ke only mean one thing” yadanyi shiru yana kallon Hawwa yace “just like rest of the victims parents kema maybe mahaifinki just did it for money ne so kina gani koda zanzo nace gashi gashi mahaifinki zai yarda akashe auren?” Hawwa tai shiru yace “saikuma second abu, Hawwa you’ve been in this job kinsan yanda aikin gwamnati yake, Baban yaron nan sune Nigeria gabaki daya do you want me to be on the bad side of such kind of people?? Naje nace kaza kaza ko baban ki baice ni ba ne las las zasu gano nine kinsan abubuwan da hakan can cost me?”

Yasake shiru yace “banda haka this is personal matter not work related, maganan aure ake ni as Oganki ko Boss dinki baikamata na shiga ba sai inzo naji kunya nan gaba cus of What If dayawa dana hararo in the case, what if ke bai sakeki like the rest of the matan ba? What if ya zauna dake har abada? Hawwa you have power what if you somehow influence him ya gyara all those hali and changed? Idan ya chanza is a good thing since he’s not a murderer ko wani kidnapper” Ahankali DIG yace “just think it through but I don’t think is proper for me to interfere Hawwa, kiyakuri but I don’t think hurumina ne tunda har Babanki ne yabada ke da kanshi just pray and seek Allah guidance Allah sadaki da alkhairinsa” hawaye Hawwa taji ya zubomata sharrrr tai shiru a office din anatse DIG yace “so sorry Hawwa” tadade ahaka sannan ta share fuskanta tamike tace “is it okay nai resuming gobe Sir I have to be somewhere”? Gyadamata kai yayi yace “sure take your time” wucewa tayi tafita yabita da kallo tawuce tashiga motanta ta tada Maman Noor kawai tafado mata arai, she’s her only second hope.

Sanin tana prison hakan yasa tawuce prison na mata, parking tayi tana zuwa ta nuna ID card nata tawuce office na prison warden din ta zauna bayan sun gaisa da Matar Mrs Adebayo tace “wakikeson gani yau Miss Hawwa”? Anatse Hawwa tace “Hadiza Muntari wacce was convicted sabida kidnapping yarta datayi that senate president case ish” dasauri Mrs Adebayo tace “ohh Hady we call her Hady anan, ai jiya an fitar da ita, wasu yan sanda sukazo da clearance from court they withdrew the case against her wlh she’s so lucky” sosai Hawwa ke kallon Mrs Adebayo Khaleel ne ya yafemata sabida jiya ta gayamai she will find evidence against him? Mrs Adebayo tace “why are you looking for her”? Murmushi kadan Hawwa tayi mai ciwo tace “kinsan nine nai investigating case din but well that aside nace ko kunada home address nata yar wani gari ce kinsani”? Girgiza mata kai tayi tace “no gaskiya yar Bidda ce but bamu da address nata” Shiru Hawwa tayi saikuma chan tamike tabata hannu suka gaisa tace “thank you very much” tawuce tafita.

Tunda tafito tana tafiya zuwa parking space ta hango Khaleel tsaye jikin motarta tsaye yana sanye da dogon wando da shirt dabai saka boturan sama ba, faduwa gabanta yayi akwai tracker a motarshi ne datake ja yanzu? How did he know tana nan? Daurewa tayi ta karasa ko kallo bai isheta ba tazo zata wuceshi tabude motan ya fizgota tadawo baya kaman paper azuciye Hawwa ta buge hannunshi tace “don’t touch me again! Stop touching me!” dan zaro manyan fararen idanunsa Khaleel yayi yace “someone is in a bad mood today wow!” Yadanyi dariya yana kallon yanda tahade fuska tana kallonshi yace “smile it’s Sunna!” Hararanshi tayi jin abinda yace tace “so kasan sunna” tashiga fizge hannunta yaki saki sai kawai yabude bayan motanta dan tariga tai unlocking car din da key hannunta tun dazu datazo wajen, yaturata cikin motan yashigo shima da sauri ta matsa baya tamai ihu. “Wai mehaka? Leave me alone!” Dan cute smile yamata yace “sabida kinga matar nan an saketa is that why you’re in this bad mood?” Ja idanun Hawwa sukayi takalleshi azuciye tace “even if it means me bringing down the whole world searching duk lungu da sako I will do it! I will get Evidence and I will show Baba and my entire family the kind of person you’re! Khaleel just know this and keep it at the back of your mind bazan taba zaman aure dakai ba, you’re a worthless boy da baisan darajan mata ba! You don’t value mata! You treat us like trash! And I refuse to be one of your victim”Khaleel na kallonta yadan rage murya yace “konama wasu kenamawa? Why do you hate me?” Ihu Hawwa tamai tanaji kaman ta shakesa tace “I hate you sabida you’re a piece of thrash! I hate you sabida you’re a f*ck boy! I hate you sabida you’re a playboy! I hate you sabida you think life is just about women, money and parties! Kace nikamawa dazan tsaneka?” Tadanyi shiru kadan takalleshi da masifa eyes nata tace “kasan abinda ake cema ciwon y’a mace na y’a mace ce? I hate you sabida abinda kama all those women daka wulakantar” dan tabe baki yayi yace “I don’t want them why should I keep them?” Hawwa afusace tace “you don’t want them why did you marry them and ruined their life eh Pop boy”?.

EPISODE 

Dan shiru Khaleel yayi yana kallonta ganin yanda zuciyanta ke tafarfasa, she’s really angry today, and as far as he’s concern he didn’t ruin any girls life rather he makes their life even better and colorful, all of them and family nasu are living large yanzu, lumshe idanu yayi yabudesu kadan ya kalleta murya chan kasa yace “I can’t stay 2days without having s*x!” Wani irin yammm kunnen Hawwa yayi jin abinda yafadi tadan dauke kai daga kallonshi da sauri, murya chan kasa yace “I started getting married at 24yrs, call me anything ni ba mazinaci bane Mommy na auramin su ne nayi s*x” runtse idanu Hawwa tayi da kyar tabudesu zuciyanta na radadi yanda yake magana akan mata tace “sannu Moms boy! Mata sun dawo maka toys for your selfish satisfaction eh dan gata”? Kallonta Khaleel yayi asanyaye Hawwa taji kaman zata kama da wuta ganin yanda hankalinshi kwance tace “okay nima so kake na shiga cikinsu tell me I will be your 10th wife ko 20th?” Anatse kai tsaye kuma yace “14th wife actually!” Wani zuciyane ya debi Hawwa batasan sanda tayo kanshi takama gaban riganshi ba fearlessly ta jijjigashi ranta na kuna tace “how dare you marry me Khaleel? Sabida kaga nakai 29yrs banyi aure ba is that why you took advantage of desperate state na Baba na and use the perfect timing ka aure ne eh talk?” Tayi maganan Hawaye na cika idanunta sosai tana kallon fuskanshi ta rike gaban shirt nasa gam gam, Khaleel yayi shiru yaki magana ganin ranta abace yake yau sosai cikeda bakin ciki ganin yaki magana Hawwa tace “how dare you take away the only evidence danake sa ran zan samu na nunama Baba wayekai eh? Khaleel I don’t deserve you, after good 29yrs banyi aure ba clocking 30 I’ve been so patient cus nasan Allah will reward me for imanin danayi, why will I end up with the worst person dana sani aduniya you!? I’m too good to be your wife, you are a bad bad badddd person Khaleel I hate that kai Baba ya auramin!” Tai maganan hawaye na saukowa daga idanunta tana kallon cikin kwayan idanunsa kaman yanda yake kallonta shima, all this while batai kuka ba sabida tanasa ran she will have something to show Baba but yau da Khaleel yayi outsmarting nata sai taji duniya yamata zafi, duka takaimai a robust chest dinshi hawaye na dauka daga idanunta tace “I hate that kai Baba ya auramin! I hate you Khaleel I hate hate hate you na tsaneka! Na tsaneka” tafashe da kuka tana kaimai duka sosai akirjinshi duk yana kallonta asanyaye, cikin kuka tace “I remembered the day daka fadamin one day sainai kuka ina begging naka for mercy agaban that super market” cikin kuka har shesheka take hawaye har gemunta tace “you won! You won! You won Khaleel, I’m sorry for everything Ibrahim! I’m sorry for being rude, for insulting you calling you jobless, I’m sorry for everything dan Allah kasakeni! Please divorce me dan Allah” tashiga kuka sosai bana wasaba, bata taba sanin zata iyama Khaleel kuka hakaba, ahankali Khaleel ya lumshe idanunshi da hannu daya ya fizgota yasata ajikinshi “leave me leave me” Hawwa tai ihu amman saida yasata ya kankameta sosai tun tana hargowa hartai shiru ajikinshi tana kuka ahankali.

Lumshe idanu Khaleel yayi yana shakan cool kamshin datakeyi dayamai dadi sosai tana kuka yakai bakinshi saitin kunnenta yana matseta ajikinshi ta yanda bazata iya fitaba murya chan kasa yace “I’m glad kinyi admitting defeat Kulu Khaleel never loose a fight! Mace bazata taba winning dina ba!” Zatai motsi yariketa gam ahankali yace “I will never divorce you Kulu! This Khaleel you hate so much saikinyi rayuwa dashi har abada!” Yadanyi dariya kadan mai sound yace “maybe da baki tsaneni ba danai letting naki go” awani irin hankali yace “and I will sex you just like yanda nakeyi da all the rest of those girl creatures, I will add you to the collection of women I slept with!” Yanda Hawwa ke fizge fizge kaman zata tashi amman yahanata fita daga jikinshi, yakara kai bakinshi wajen kunnenta yace “kinata neman evidence akaina bayan nine keda evidence akanki” yayi wani makirin murmushi yace “imagine Baba yaga video or pictures of when you were trying to rape me kina shamin baki, grabbing my shirt just like yanda kikayi dazun nan, trying to reap off my shirt and strip me naked, how will Baba feel?” Fizgo kanta Hawwa tayi daga jikinshi ta sauka gefe takalleshi da jajayen idanunshi tace “wat are you talking about? Ko zanyi raping maza aduniya trust me i will never go for national cake irinka da karabama all matan garin nan jikinka!” Shiru Khaleel yayi yana kallonta babu macen data taba gwada kalan zagin da Hawwa kemai, she just called him national cake, dan ijiyan zuciya ya sauke, wayanta dake inda take zaune yanuna mata yace “check your phone?” Dasauri Hawwa ta dauki wayan tabude, tana dubawa taga yatura mata hoto ta iMessage guda daya inda take saman kanshi bakinta akan nashi tarikemai gaban riga duka jikinsu ajike hannunta yahau rawa takalli Khaleel da sauri cus she’s confuse, kanshi yadan sosa irin na iskancin nan yace “I have the video inhar u finally took off the shirt kina shamin this” yanuna mata nipples dinshi cikeda iskanci, yadan kalli saman motan kaman mai tunani yadaura yatsa abaki saikuma yacire yakalleta yace “I will just start crying to Baba ince yarshi beat me up ta turani cikin ruwa tafito dani kawai tahau kissing baki na and kikayi threatening dina kan cewa dole saina aureki, nazo nagayama Baba, Baba will easily believe me daman that crazy woman tace zaki iyama maza fyade so I’m your first victim” yakashe mata ido daya a iskance Hawwa na kallonshi hawaye na cika idanunta, Comfortably Khaleel yace “idan bakija bakin nan that talks like parrots kinyi shiru anyi bikinmu an kawomin ke gidana ba I will expose this” yanuna mata wayanta yace “family naki will lose all respect for you and zama dani dole, anyhow u look at it I’m still the winner, ko kinaso ko bakiso saikin zauna dani, don’t forget you started this war with me Kulu!” Glass nashi ya warware ya sanya a idanu sannan ya kalleta yace “see you Kululuwa Yar Sanda bye” yabude kofa yafice abinshi yawuce nashi motar aka budemai brabus dinshi yazauna aka ja motan harsaida Hawwa ta daina ganinshi tafashe da kuka sosai tana kallon hoton tana mamaki what happens to her? How come is this picture photo shop ko sun bata wani abu ranan ne tunda yan kwaya ne how did she kiss this man cus batasan sanda akaiba, takai 20min tana kuka amota sannan ta tada motan tabar wajen.

**''''H

Ijiyan zuciya Momy tasauke cikeda damuwa tana kallon Salman daya gama koramata bayani acikin office dinta hannu tasa ta zare glasses dake kan idanunta tashafa goshinta cikeda damuwa tace “why that police girl in all matan dake duniyan nan dan Allah? Ko yar india Khaleely yake bukata zan iya auromai why that girl? Akanme yake chasing nata up and down tell me the truth Salman sonta yakeyine?” Cikeda girmamawa yace “I can’t say Hajiya gaskiya, but one thing is bantaba ganin Yallabai na bin mutum up and down kaman yanda yakebin yarinyar ba shi kanshi ba lallai yasani ba but he’s giving her all of his attention his time and komi Ma’am” table Mom tabuga tace “that’s wat I don’t want, yarinyar will take my son for granted wlh, zata wahalar min dashi Khaleely baitaba bibiyan any girl aduniyan nan ba saidai su suyita bibiyansa what is so special about tsohuwan yarinyar nan da he’s all over her eh? Hmm, u can go Salman just keep me posted whenever he sees her and wat they discuss about” gyadamata kai yayi yace yes Ma yawuce yafita.

Tashi tayi ta tsaya jikin window ta hango Khaleel din na buga ball da Noor he looks so happy haka Noor ma Mom ta sauke ijiyan zuciya, bude kofan office din nata Mom tayi tashiga another elevator dake wajen tasauka kasa tana tafiya zuwa garden da Khaleel ke buga kwallo Noor dake sanye da jersey na Liverpool looking so cute tace “Granny join us” murmushi Mommy tamata tace “continue playing Princess dina” takalli Khaleel dake wasa da kwallo abinsa kaman bai ganta ba tace “why do you keep chasing that Police girl Khaleely?” Batare daya dagokai ya kalli Mom ba yana bugama Noor kwallo yace “what is your business with my affairs Momy”? Dan shiru Mom tayi taji zafin amsan daya bata inda sabo sun saba haka yake musu magana agantale, ahankali tace “common My Leely I didn’t train you to be going after kowace kalan mace aduniya! You have everything na rayuwa babu wacce kakeso dabazaka iya samuba” daidai lokacin yabuga kwallo araga shida Noor sukahau suna jumping suna ihu yadagata yana ihu suna dariya sannan yasauke ta yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login