Showing 3001 words to 6000 words out of 184554 words

Chapter 2 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1866

DIG dasauri yace “your Excellency kasan a aikinmu anybody can be a suspect sometimes harnaka ma najini, Miss Hawwa can do her job well idan tagama ruling out duka yan gida tagano basu da hannu, kana ganinta haka by mare magana she can fish out kowaye keda hannu in this kidnapping, she has a masters degree in criminologist currently running PHd dinta still on the field, just watch her magic Allah taimaki Excellency” jinjina kai Dady yayi cikeda gamsuwa yace “is that all abinda kike bukata?” Anatse Hawwa tace “for now yes Sir!” Gyadamata kai Abba yayi yadaga wayanshi yace “bari na kira Khaleely na shine Baban Noor da aka sace” yashiga kiran number Khaleely daidai lokacin Momy na shigowa dakin da kawarta Hajiya Daraja.

Ganinta yasa Dady yace “yauwa Madam come, ga special task force danai involving in this matter” yayi pointing Hawwa yace “she needs to talk to Noor’s parents, ko kinada number matar data haifi Noor”? Dan yatsine fuska Momy Noor’s irin na isa dakuma rashin mutunci tace “I don’t have number ta but lemme call Bisola tanada number ta I think a diary dina” dasauri Dady yace “okay kirata muji nima Khaleely nake kira baya daga wayana” itadai Hawwa da har su DIG kallon wired family suke jin yanda suke addressing Mahaifiyar little gurl din da aka sace wai matar data haifi Noor, number ma wai basuda ita that means bamata san an dauke yarinyarta ba. Duk suna ahaka aka bugo kofan office din kaman za’a cire da sauri kowa ya kalli kofan kamshi mai shu’umin dadi na ketowa cikin office din before wani tall black skin guy ya shigo ciki dakeda crazy ass gym body, ko

kallon jama’an dake cikin office din baiyiba yawuce wajen mahaifiyar shi data tashi da sauri ganin yanda yashigo da bacin yanuna mahaifinsa dake kallonshi zaune kan office chair hankalinsa atashe yace “Mommm I told Pops karyayi involving kowa mesa Pops always enjoy doing abinda nace karyayi?” Cikeda damuwa sosai Momy ta tausasa murya takama hannunshi tace “Khaleely calm down kasan babu abinda ke dagamin hankali aduniya irin fushinka, Babanka yasan meyakeyi bawai police yakiraba special Anti Crime and Kidnapping task force yakira, look at them su uku ne DIG shine in charge of the task force shiya kawosu calm down please, kai suke jira they want to talk to you” cikin fushi sosai ya fizge hannunshi yace “Mom if anything happens to Noo…..” taushemai baki Mom tayi da gudu tace “kul babu abinda zai sami jikata don’t even utter dat word, come” Momy taja hannunshi zuwa kujeran dake kusadana Dady ta zaunar dashi kaman wani basarake tace “calm down hasken idanuna and answer them please do it for me and Noor kaji, just talk to them my love, ina zuwa” tayi maganan tana juyawa tama Baban alamu da ido daya lallashesa tafice, gyara zama Dady yayi yakai hannunsa zai kama hannun Khaleel din ya dauke hannunshi yace “don’t touch me Pops” dan dago kai Hawwa tayi zata kalli wajen sai kuma ta fasa, rage murya Dady yayi yace “toka yakuri kaji Khaleely” dauke kai yayi kaman badashi akeba, Dady yajuyo ya kalli Hawwa daketa yan rubuce rubuce abinta yace “ga mahaifin yarinyar nan Miss, ask him abinda zaki tambayeshi” dan dago kanta ahankali Hawwa tayi ta juyo da kwayan idanunta ta saukesu kan Khaleel daya hade rai yana zaune gefen mahaifinshi bamaya kallon inda suke yadaura kafa daya kan daya yana karkada kafansa daya sanye da wasu designers crocs, ijiyan zuciya ta sauke a boye tanamai kallo da kyau reading how bossy and angry he looks tace “Sir how close are you with your daughter”? Batare daya kalli inda takeba yace “I’m her best friend and everything, what else”? Ya amsata annoyingly, da dan damuwa Excellency dake kallon Hawwa yace “he’s very close to her, just like yanda yafadi shine best friend din Noor, itama haka Noor nason Babanta sosai kaman zata cinyeshi” gyadakai tayi tace “shin ta taba sanar dakai koda wasa akwai wani ko wata dake mata mugun kallo? Ko bata tsoro? Ko dai wani abu makamnacin haka maybe ko a school ne”? Kai tsaye yace “no” still tana kallonshi batare data dauke ido ba tace “kaifa? Kanada wani enemy ko wayanda ke jin haushinka and are trying to hurt you and cause you pain at all cost”? Shiru yayi kaman mai tunani yadan dafe goshinshi ahankali yace “I can’t think of anybody” alalace akuma shagwabe yadan kalli Babanshi yace “Pops ko inada shi?”

EPISODE

Calmly Excellency yace “uhnnnn I can’t think of any kaida banda su Sameer ai bakada wasu abokai, to ko maybe matayen ka kasan mata da kananun magana” ahankali Hawwa na kallonshi tace “banda mahaifiyar Noor akwai wasu matan ne?” Kallonta Excellency yayi kai tsaye yace “eh, dana aurenshi tara but you know yanda lamarin aure yake duk ya rarrabu dasu, some at 2months some 4month, wasu 6month, akwai ta 1week ma, inaga to duk sunajin yarona” shi kanshi DIG saida maganan ya daki kanshi but yanda uban ke bada labarin as if is nothing bawani abu bane wai kudi shegen abune wlh, rubutu Hawwa tashigayi professionally batare data nuna anything ba chan tace “can I know me suke fadamaka idan sun kira ko kuma sako?” Kaman bazaiyi magana ba sai kawai ya kishingida ya daura kanshi kan kafadar Babanshi yace “I don’t know! Banda number su they normally call my P.A but I asked him to block them, but if I remember correctly yace suna cewa narabu dasu, naci amanansu bla bla bla” yadanyi tsuki kadan yace “they’re just so bittered narabu dasu, I got tired of them saina cigaba da zama dasu Pops?” Dasauri Excellency yace “inafa ai ba’a aure haka, daka ijiye yarinya ka gaji da ita kaita cusguna mata gwara ka sallameta ka auro wata wacce tamaka, life is not hard some people intentionally make it hard for kansu, aure don’t have to be forever and ever it can always be temporary as long as babu feelings of love” abu Hawwa ta hadiye awuya jin maganan uba da dan tace “I need to interrogate all the 8 ko 9 of them” juyo da kanshi Khaleel yayi ya kalleta for the first time suka hada idanu sparking idanunsu sukayi atare, hade fuska Hawwa tayi tamau ta tashi tana daukan wayanta tace “I need to talk to Nanies din da driver dake tareda Noor suna waje ko?” Ta tambayi security da Dady yacema yakawosu dazu ya gyadamata kai tayi wajen kofan hartasa hannu zata bude kofan awulakance Khaleel da tunda yafara kallonta bai dauke idanunsa akanta ba dawani tsinannen voice yace “ke, why do I need to call them?” Chak Hawwa ta tsaya cus yanda yakare maganan sounding kaman yana magana da wata wulakantacciya mara daraja, da kyar ta danne zuciyanta dan kawai taji ta tsani yaron da iyayenshi sabida dan short halinsu data gani, ta juyo ta zubamai bewitching eyes dinta kaman yanda yake kallonta shima ko kyafta idanu bayayi, tace “you need to call them cus they’re potential suspects duba da whatever transpired between you people, ina bukatan magana dasu dan kauda zargi basu da hannu cikin dauke yarka da akayi before we look outside the box, and be fast” takalli agogon hannunta tace “i need to wrap up this case within 24hrs, 1hr is almost gone” sannan ta juya harta daura hannunta kan handle tasake juyowa tasake zubamai idanu tace “next time address me as Miss Hawwa not Ke” tana maganan tabude kofa tafice.

Afusace Khaleel yamike yanabin kofan data rufo da kallo yace “Pops who d f*ck is she? Why is she even here? Kaji yanda takemin magana kuwa Pops? She’s so rude, fire her! I don’t want her here” Da sauri daga Excellency harsu DIG suka kalleshi yanda ya haderai, su Abraham na kallon ikon Allah aranshi yace “you don’t know Miss Hawwa she also doesn’t give a f*ck about who you are she will put you in your place” rai abace Khaleel yace “I don’t want her to be among the team, dismiss her” yayi magannan yana kallon DIG dasauri Excellency yakama hannunshi yace “calm down Khaleely abun zaimaka yawa ga damuwa ga bacin rai kar zuciyanka ta buga please calm down kaji, idan nasa DIG yayi dismissing nata from team din tayaya zamu ceto Noor? This girl itace ragamar ceto Noor, calm down Son me too I don’t like the way tai magana da d’ana agabana” yakalli DIG yace “talk to her to watch her tongue karta kara magana da d’ana rudely I don’t tolerate such” cikeda girmamawa DIG yace “we are sorry Sir, hakan bazai kara faruwa ba I promise” yayi magana yana tashi dan zuwa magana da Hawwa shikuma Excellency yacigaba da lallashi Khaleel kaman kwai.

EPISODE

Wani office aka bata that is next to wanda Excellency yake ciki, ga table ga chairs ga ruwa a ijiye mata na bottle da drink da sweets, tana tsaka da interrogating mutanen dake tareda Noor sanda aka saceta DIG yabude kofa yashigo, yakalli security datakema magana yace “excuse us” tashi yayi yafita, da dan fushi kan fuskanshi yace “wat was that behavior eh Hawwa?” Sauke kanta kasa tayi tace “Sir I don’t care who he is, he should address me with some respect baya kirani Ke ba” dan jim DIG yayi yana kallonta yace “that guy kina ganinshi kinsan he doesn’t think like me and you, bai taso kaman mu da ke ba” yadan sake rage murya yace “Hawwa yayi magana da mahaifinshi rudely ma balle mu? So please let’s do abinda yakawomu and leave don’t repeat abinda kikayi dazu am I clear”? Ahankali badan ranta yasoba kanta na kasa tace “Yes Sir” “good” ya amsa yana juyawa yafice security yadawo, tadaga wayanta tana kiran Abraham yazo ya karbi wayansu yashigo ta bashi ya karba yafice yashiga aikin shi bayan yabude some systems adayan office din, almost 1hour yadauketa duk tai magana da ma’aikatan gidan kafin Head Security yashigo yace “Ma’am Excellency yace na sanar dake ga matayen dukansu are available Maman Noor tace yanzu ta sauka daga jirgi but tana hanyan zuwa itama”.

Gyadamai kai tayi tace “ashigomin dasu one after the other, collect all phones nasu and give it to Abraham” gyadamata kai yayi yajuya fita baijimaba ya shigo tareda wata hadaddiyar mata kaman balarabiya, fara kal da ita taci riga da skirt dasuka matseta da dan karamin gyale da handbag a hannunta dakin tabi da kallo looking disappointed kaman akwai abinda taso tagani batagani ba, kujera Hawwa ta nuna mata tace “have a seat please” zama tayi tace “and who are you, where is Lee?” Dan kallonta Hawwa tayi tace “sorry Lee?” The way she’s asking the question zai nuna bata ganeba, ayangance matan tace “Khaleel nake tambaya ina yake” anatse Hawwa tace “I believe idan muka gama you can look for him, can I know how long u we’re married to Mr Khaleel Ma’am”? Kallonta matar tayi tace “why the question”? Anatse Hawwa tace “can you answer me kika fita you can ask them mesa nake miki tambayan nan” shiru matan tayi tana kallonta saikuma chan tace “kwanan mu arba’in da hudu bamu cika 2months ba gaskiya” Hawwa na kallonta tace “baki tsaneshi ba daya sakeki in such a short time”? Dasauri ta girgiza kai saikuma tai murmushi tace “when money is at stake nope, I will do everything to get Khaleel back, nakasa aure nakasa son wani” rubutu Hawwa tashigayi batare data kalleta ba tace “and why is that”?Wani kallon raini matan tamata tace “are you dumb? Wait Anya kinsan waye Lee kuwa? It’s seems like you’re just a worker bakisan who Khaleel is ba, that guy is every ladies dream” dan shiru Hawwa tayi tana kallonta the way she called her dumb batason tai wani abu dazai sake batama DIG rai hakan yasa ta hadiye sai kawai tace “you can go” tabe baki tayi ta tashi tajuya tana wani karkada ass kallo daya Hawwa tamata tadauke kai, kusan dukansu abu daya suke fada suna son mijinsu suke and ina Khaleel cus sun dauka shine keson ganinsu saisa ake nemansu suzo gidan, wuraren 4 tagama dasu Allah yasa bata salla yau, bude kofan security yayi yashigo da wata wacce duka duka bata wuce 27yrs ba, taci gayu sosai kaman zata gasan kyau yace “this is Noory’s Mother Ma’am” gyadamai kai Hawwa tayi tana kallon matan tundaga kafa, security yace “your phone please Ma’am” iPhone dake hannunta ta kankame tace “mezakumin da waya kuma daga zuwana? Why is Khaleel calling me all of a sudden today after how many years yanzu kuma nazo ana cewa nabada waya” anatse Hawwa tace “is just protocol I can’t talk to you waya natare dake give it to him idan nagama dake you will collect d phone kina fita” kallon Hawwa Matan tayi tace “and who are you”? Ahankali Hawwa tace “I’m Hawwarh!” Yanda Hawwa ta tsareta da idanu yasa ta bada wayan security yafice itakuma tazo ta zauna inda Hawwa ke nunamata Hawwa tace “can you discribe relationship dinki da Baban yarki for me please?”

Maman Noor na kallon Hawwa tace “there’s no relationship cus bama tare, we don’t talk, da Nany Noor kawai nake magana a duka gidan nan itama ranan Saturday kadai ne ake barina magana da ita” ahankali Hawwa tace “are you happy about that? Yarki ce Noor ke kika haifeta but sai an gayamiki sanda zaki magana da ita? How do you feel about that”? Dan ijiyan zuciya ta sauke tana kallon Hawwa dake kallonta tace “ai sai su cinyeta all i know is nina haifeta kuma idan ta girma she will look for her Mother”Hawwa na kallonta tace “how long kukai zaman aure da Babanta”? Dan ijiyan zuciya Maman Hawwa ta sauke tana huci tace “satinmu shidda da kwana shidda ya saken” ahankali Hawwa tace “kece matarsa tanawa”? Shiru tayi sai chan tace “I think ta hudu” taidan huci da saida yafito tace “ko kwana goma banyi agidaba bayan ya sakeni ya auro wata” anatse Hawwa tace “how come kika aureshi? A ina kuka hadu kuka fara soyayya” kallon Hawwa tayi tace “ai aduka aure auren da Khaleel yayi aduniya banjin akwai wacce yahadu da ita ba, kawali ke hada auren Hajiya Daraja, best friend din Mamanshi, fita ake musamman asamo kyawawan yan mata ahada aure abama iyayenmu kome sukeso a auremu” tai dan shiru tana huci anatse Hawwa tace “why are you angry Maman Noor”? Kallon Hawwa tayi takasa hadiye abinda ke ranta tace “kullum addu’ana shine Allah ya gwada musu abinda sukema yaran mutane” dasauri Hawwa tace “me sukeyi? Yana dukanki ne ko yana miki wani abu”? Dasauri ta girgiza kai tace “no ba duka ba, kai aure agidan nan bazaka taba rashin kudi ko yunwa ba wlh za’a kula dakai kawai basusan menene darajan dan adam ba, Khaleel thinks mata are like riga yacire wannan zai dauki wata sabuwa yasaka, iyayensa basa kwabansa suna supporting halinsa tsaf, I hate them” anatse Hawwa tace “is that why kikasa akai kidnapping yarki?” Dawani irin sauri Maman Noor ta kalli Hawwa gabanta yayi mugun fadi saikuma ta tashi tsaye da sauri tana zaro idanu tace “mene? Wat? Wait? Kidnapping wane akai kidnapping? Did I hear you say y’ata? Anyi kidnapping Noor? Innalillahi wa innailaihi raji’un” duk Hawwa na kallonta ko gezau batayi, tsawa Maman Noor tamata tace “talk to me wat happens to my daughter?” Dan murmushi Hawwa tayi tarufe jotter ta ta ijiye ta kalleta tace “I don’t know you, but someone I understand situation naku dukanku matansa wanda cikinku babu wacce ta nunamin auren dole tayi, babu wacce tai complaining an taba dukanta ko wani abu makamancin haka, kudi dama makes masu shi suyi feeling power, kome sukeso they will use kudinsu su samu, suna chanza mata kaman riga but still yet is using yarki the best solution for your problems? Yarinyar 4yrs”? Dasauri Maman Noor tadawo gaban table din hawaye na saukowa daga idanunta tace “kinsan what it means a sakeki sati uku babu wani dalili? Bayan an gano inada ciki suka sake dawo dani gidansu aka ijiyeni waje guda ana kula dani dansu na aure aure yana sheke ayarsa yana shaye shaye baitaba zuwa yadubani ba koyamin sannu, ina haihuwa suka karbe yarinyar suka aikani gidanmu Noor batasha nono na ba” ta nunama Hawwa nononta tana kuka, tace “I will cry all night nonuwana sun kumbura sun kwacemin yarinya ana bata abincin madara, and suka sani a kotu suka karbe custody da kyar nasamu ana kirana na ganta ta video call sau daya a sati, waye Khaleel is he God dayake tunani he can do anything dayakeso? Haaa” dan lumshe idanu Hawwa tayi batason ta nuna ta bata tausayi tace “hakan yakai kisa ayi kidnapping yarki a karbi 100M kuma kunki badata” dasauri tace “zanyi using kudin mubar kasan wlh bazai kara ganin Noor ba” ahankali Hawwa tasauke ijiyan zuciya tace “tell me Noor na ina I can help you out” dasauri tace “bansan inda takeba nima” dan manne lips Hawwa tayi tana kallonta sai kawai ta tashi ahankali tace “I wish I can help you” tawuce tafita daga dakin Maman Noor na biyota dasauri security yatareta dan yana bakin kofa Hawwa ta shiga office din Excellency kowa ya bita da kallo banda Khaleel da kansa ke kafadan Babanshi ya lumshe idanu kaman yana bacci.

EPISODE

DIG na ganin Hawwa yace “are you done? Any progress? What is the result of your findings”? Dan shiru Hawwa tayi tana kallonshi saikuma ahankali tace “Sir can I talk to you in private”? Dasauri Excellency yace “talk koma menene anan” kallon DIG Hawwa tayi gyadamata kai yayi alamun koma menene tafada anan din hakan yasa ta sauke ijiyan zuciya tace “I have a suspect!” Kowa kallonta yake barinma Khaleel da gabanshi yahau fadi dum dum dum, yabude idanunsa kadan yasaukesu akan Hawwa dake tsaye, adan birkice Momy tace “Suspect? In this our house? Who? Tell us waye?” Abu Hawwa ta hadiye awuya anatse, she just pity the woman dan tasan bazasu barta ba, dasauri Excellency

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login