Showing 9001 words to 12000 words out of 184554 words
parking Excellency da Momy suka shiga gudu suna tahowa wajen motan, tana parking mota Excellency yabude gaba Mommy tafashe da kuka tana kallon Noor datai bacci yarinyar ta rame tace “look at my Noor oh no no” takai hannunta tana karban Noor daga hannun Khaleel, shikuma Excellency yasa hannu yana fito dashi Khaleel yasauko yace “Dad did you call her Dr”? Dasauri yace “yes yes everything is set, yana clinic” Mommy tashiga shafa Khaleel da hannu daya tace “hope babu abinda yasameka Khaleely na welcome Alhamdulillah, babu abinda yasame ka”? girgiza mata kai yayi ahankali, Hawwa tadan matso taja kofan motan duk suka juyo suka kalleta takoma driving sit, Excellency yace “you guys did a great job Miss Hawwa welldone, dare yayi kuzauna anan zuwa safiya” calmly and politely tace “my team are down zan kaisu clinic dinmu” dasauri Excellency yace “ai da kin bari Dr ya gansu anan we have clinic anan” anatse tace “DIG yariga yace na kaisu clinic dinmu” dan ijiyan zuciya Excellency yace “okay but drive safe, bari nakara muku mopol su biku for extra security is night” dan gyadamai kai tayi cus batason ta kara gardama tai reverse da motan sannan tai kwana hakanan Khaleel samin kanshi da kallonta yayi daidai tana figar motan da gudu Excellency yace “ayi gudu a sannu” Khaleel yajuya ahankali yayi ciki.
EPISODE
Har clinic dinsu ta kaisu tajuya zata wuce Abraham daya bude idanu cikeda ciwon kai yace “kefa i think you need to see Doctor kema” yayi maganan yana kallon hannunta, yatsine fuska tayi takalli hannun tace “no I’m fine is not that serious, office zanje nacire vest din nan na wuce gida” tayi maganan tawuce tafita da sauri, office nata taje tadauko jakanta tafito tazo parking space nasu tashiga motarta kiran corolla na 2006, taja motan sannan taciro wayanta tai dialing number da tai saving da Best N, ringing daya ta daga ahankali tace “kina clinic dinku ne? Wannan dakika dauka u must be on night duty, kina nan”? Daga ta dayan bangaren wata murya mai dadi tace “yes inanan but inadai shirin tafiya around 5 nadau permission, kaman kina driving me kikayi da kikakai ware haka an office? Anyways just come I know u will tell me, Yau kwana nawa bamu hadu ba? Please come ko 1minutes ne kiganni” dan murmushi kadan Hawwa tayi tace “bribe me” dasauri tace “I will not beat Yasmeen da Yaseer all through this month I promise” murmushi Hawwa tayi sosai tace “good girl” dan tsuki tayi tace “you’re just lucky I’ve missed you ne da dagake har yaran naki nayi biji biji daku” tabe baki tayi tace “shege kafasa sabida kinga ina gate, barima najuya” da sauri tace “yakuri mana Hawwa” dan dariya kadan tayi tashigo asibitin tai parking motanta tadanyi jimm sannan tabude tafito tafara tafiya tawuce ciki, direct wani office tawuce daidai takai hannu zata bude aka rigata budewa wata mata ce aciki fara ce tsawonsu daya da Hawwa kawai dai tafi Hawwa jiki ne saidai itama bawai irin kiba sosai din nan ba ne kawai dai tadan ciko ne, tana sanye da kayan nurses dark blue riga da wando, wani irin rungume Hawwa tayi da sauri tace “oyoyoooo” “asssshh Ni’ima My Hand” Hawwa tafada ahankali dayasa Ni’ima ta saketa da sauri takalli hannun tace “wat happened to your hand kikaji ciwo haka eh?” Dasauri tajata suka shiga office din ta maida kofan tarufe tawuce ta daurata akan kujera tana kwaso abubuwan dressing tace “wat happened ya akayi kikaji ciwo?” Dan yatsine fuska Hawwa tayi tace “banmasan tayaya naji ciwon ba ni karan kaina Best, na manta” zama Ni’ima tayi akujeran dake facing nata takama hannun tana wankewa da ruwan spirit tace “I thought we had agreement cewa bazaki dinga involving kanki in field work ba saidai office work” ahankali Hawwa tace “and it has always been like that, koda naje field ma bana shiga aikinsu, yau ne kawai and its circumstances saisa but ai I’m fine ba zafi sosai ma ciwon” kallonta Ni’ima take fuskanta duk ya nuna damuwa da rashin jin dadi hakan yasa Hawwa tace “common I’m fine it’s just a scratch” anatse Ni’ima tace “da inada wata kawa daban damu ba, but you’re all I got tun ina yar yarinya” murmushi Hawwa tayi tace “tun zamanın primary school” ahankali Ni’ima tace “please take care of yourself kinji Hawwa” gyadamata kai Hawwa tayi tana dan yarfe hannu da style cus shegen zafi yake mata and bataso Ni’ima tagane ta damu, hannun Ni’ima ta karba tadauki wata paper daga kan table tashiga fifita mata ciwon tana kallon ciwon ahankali tace “Hawwa I was never against kinason ki zama police sabida I know yanda kikeson justice, da kare hakkin dan adam but deep down Allah yasani banason aikin, my worst fear arayuwana shine wani nawa wanda nakeso yazama soja ko dan sanda cus I always believe mutum yazama police ko soja kaman ya yanki automatic ticket na mutuwa ne” taidan shiru tace “dakika fadamin anyi promoting naki bayan kinyi solving that kidnapping case an saki under special kidnapping task force u are not even in shi asalin police station I was happy, very happy sabida i know talent dinki is identifying, profiling criminals and knowing criminal minds kina taimakawa wajen kamasu da relating dasu da gane abinda zasuyi ko suke shirin yi, understanding zukatansu nasan that is basicially your work ba aikin dazakije filin daga ba kina combat da maza ba” dan murmushi kadan Hawwa tayi tace “kai Best is just a scratch kike surutan nan randa za’a kawo miki ni kiciremin bullet f…..” “Hawwa!” Ni’ima takirata adan fusace tace “will you stop joking around I’m serious, Hawwa I will always support you kinsani but not in this” tanuna ciwon hannunta tace “kodai kidena zuwa filin daga and stick to office paper work helping to solve crime behind the mask ko kibar aikin” Dasauri Hawwa ta kalleta, hawaye taruwa yayi a idanun Ni’ima tace “akanme kina mace zaki dinga fada da maza duk abi ajijjimiki ciwo amiki tabo ajiki” dan turomata baki Hawwa tayi looking damn sexy tace “ni bance kimin kuka ba sarkin kuka, I swear Ni’ima circumstance yasa dole na shiga field, shima ciwon is a mistake, don’t forget I got training fa a police academy, na iya fada, nasan how to attack and how to defend myself, I can shoot and so much more, this was just a mistake trust me and I promise you bazan kara barin kaina naji ciwo ba” gyadamata kai Ni’ima tayi tadauki tissue tana goge idanunta kar hawayen su fito, Hawwa tai dan murmushi cikeda tsokana tace “yan Nigeria da ganin mace musulma police as wani abu hmmmm” ballamata harara Ni’ima tayi dayasa tai shiru tasa hannunta a lips, Ni’ima ta karbi hannunta tacigaba da fifitawa cikeda masifa tace “naga kin kara jima kanki ciwo kiga abinda zan miki wlh” dariya sosai Hawwa tayi tana cire hannunta dagakan lips cikeda tsokana tace “I’m sorry Maman Hawwa” zabura Ni’ima tayi da sauri Hawwa ta tashi tana dariya tayi gadon office din tahau tana zare gyalenta ta ijiye a gefe tasa kanta akan filo tana sauke ijiyan zuciyan gajiya, shiku ne akanta dayayi mata kyau gashinta so black ga tsayi, tasaka stud gold earring dan karami dashi tace “bari nai bacci kadan, kitasheni by 5 natafi gida” ta lumshe idanu Ni’ima ta kalleta saikuma takoma ta zauna.
EPISODE
Tabuga tagumi, a girl is a girl and will always be a girl, while a Man is a man kawai, daga gani kasan tagaji bacci kawai take.
Ahankali Hawwa ke bude idanu ta saukesu kan agogon dakin ganin 7 yasa da sauri ta tashi zaune babu kowa a office din, ahankali ta sauka daga gado tawuce bayi bata wani dade ba tafito daidai Ni’ima na shigowa tace “kin tashi”? Ahankali Hawwa tace “maisa baki tadani ba nasa kin dade” murmushi Ni’ima tamata tace “muje kiyi breakfast a canteen” dasauri Hawwa tace “not now banyi brush ba sainaje gida” hararanta Ni’ima tayi tace “brush idan kin koma gida kindaisan that woman ba baki abincin zatayi ba ko, don’t tell me zaki girki idan kin koma gida you can’t cook, kin gaji and kinada ciwo a hannu let’s just go na saya miki” tana maganan tazo gaban gadon tadauki gyalen Hawwa ta yafa mata saman kai batare data mata rolling ba takama hannunta suka fito suka shiga canteen abinci tamusu order sukaci still tamata takeaway wanda zataci da rana sannan suka fito tace “wai kinsan tun dazu Baban Yaseer na nan”? Dasauri Hawwa ta kalleta tana haderai, Ni’ima tace “ai daman nasan dana gayamiki bazaki tsaya kici ba, wlh tun kina bacci yazo ya daukeni, kuma shima yace makesure na tsaya kinci abincin, muje ku gaisa” taja hannun Hawwa batare data jira tai magana ba, yadade zaune cikin mota cus tun around 6:30 yazo daukanta, kallonsu yake kyar bayako kyafta idanu, yanda Ni’ima ke jan Hawwa itakuma tadan haderai kana gani kasan bataso tazo har zuwa wajen motan dayake nan Lexus na 2022 hadaddiya baka, ahankali yabude motan yafito
Bakin dogon gaye ne kyakkyawa gashi da tabon salla a goshinsa, duka duka bazai wuce 36yrs ba yana sanye da farin jallabiya mai kyau yasa faran hula akai sai zuba kamshi yake, a kunyace Hawwa tasauke kanta kasa dan tanajin kunya da nauyin Baban su Yaseer aduniyan nan, she always regard him as Yayanta, sabida shida Ni’ima su dauketa yar uwarsu tajini sun tsayamata, adan kunyace tace “ai dakai zamanka aciki Baban Yaseer Ina kwana, dan Allah kayakuri munbata maka lokaci” kafin yayi magana Ni’ima tarikemai hannu tace “Baby kaga kamata fada, niko na mata fada batajin tawa amman kai nasan zataji naka tunda tana kunyarka, field taje yau harda injury a hannu kalli hannun” tanunama Baban Yaseer hannun dayake tai folding hannun riganta sama, anatse yana kallon hannun sounding serious and caring yace “Hawwa why did you go to the field eh”? Adan kunyace tace “kidnapping jikan senate president akayi shine Oganmu ya aikamu I have no option saisa” dan ijiyan zuciya yasauke yana kallonta yace “but yaya hannun yanzu? Are you sure you’re fine? Babu wani abu dake miki ciwo kuma? Tayaya kikaji ciwo haka eh Hawwa”? Ahankali tace “wlh I’m fine is just a minor injury I can’t even remember ta yanda na samu” anatse yace “Hawwa!” Ahankali tadago kanta ta kalleshi kasa jure kallon dayake mata tayi da sauri ta sauke kanta Baban Yaseer kwarjini yake mata sosai ahankali tace “karki kara wani aiki dazaisa kiji ciwo haka, ni da Mom Yasmeen will support akoma mekikeso but we will never support something dazaiyi harming lafiyanki ba, you’re a criminologist not a fighter am I clear” cikeda jin dadi Ni’ima tace “yauwa bada amsa muji” Baban Yaseer cikin dan kakkausan murya yace “kada ki kara bari something yayi tampering da lafiyarki kinji” gyadamai kai Hawwa tayi tace “naji” dan murmushi kadan tayi tace “thank you” tafi Ni’ima tafara tace “Baby kome kakeyi da wannan mai taurin kan kejin maganan ka nima zan koya sabida tadingajin maganata” dan hararanta Hawwa tayi, kallon Ni’ima yayi yace “tana tareda motarta ne komu kaita gida wife?” Dasauri Hawwa tace “zan iya tuki” strictly Baban Yaseer yamika mata hannu yace “bani your keys zansa akawo miki motan gida muje mu kaiki” wlh kawai dan tanajin nauyin Baban su Yaseer ne saisa, jakanta tadauke daga kafada tasa hannu taciro key motar ahankali tabashi ya karba Ni’ima tabude mata bayan motansu tace “zoki zauna” zuwa tayi tana ballamata harara Ni’ima tai mata gwalo tai kwafa ta zauna tarufe mata kofan takoma gaba ta zauna sannan shima ya shiga gaba yaja motan.
Sosai Ni’ima keta musu hira a motan Baban Yaseer na amsata jefi jefi, bini bini yana kallon Hawwa ta mirror datai shiru tana hamma once in a while cus harda gajiya ke damunta, har unguwansu, unguwa ce dake cikeda mutane da dama yara anata wasa, ga manya haka yan anguwa da samari, mahaifinta ta hango kofar gidansu zaune, kana ganinshi kaga mahaifinta don tayi kama da Babanta ya manyanta sosai, yana zaune akan wata yar tsohuwar kujera 2sitter dake wajen ga crutches dinsa guda biyu a gefe a jinginasu dan kafansa ta haggu an guntule daidai wajen guiwan sabida wani hatsari daya tabayi da dadewa, tunda molar ta shigo anguwan yake kallonta, dan layin nan kakap idan kana neman wanda yasan yaro da babba da jika da duk wani labari na anguwan da dangin kowa to aka sami Baba an gama danshi kofar gidane wajen zamansa, to baya aiki the only abu dake shigar dashi gida shine idan lokacin bacci yayi ko zai zaga bayan gida. Parking Baban Yaseer yayi yabude motan yafito hakama Ni’ima itama Hawwa tafito, Baba naganin Baban Yaseer da Ni’ima fuskansa ya yalwatu da murmushi shiga rumfar sukayi yana nuna musu tabarma yace “maraba maraba yau Baban Yan biyu da Maman yan biyu ne agidan namu ga waje bismillanku, ku zazzauna yan albarka” hannu Baban Yaseer yabasa suka gaisa yace “ina yaran mesa baku kawominsu ba” daidai lokacin Hawwa takaraso wajen ahankali tace “Baba ina kwana” kallonta yayi saikuma ya dauke kai yakalli Ni’ima yana nunata da hannu yace “kalli kawarki ke bakijin kunya kinama binsu zindimemiya dake ba aure ba miji sai kwana awajen aiki, kap layin nan yaran dakuka taso tare sunyi aure, kannensu sunyi aure, kannin kannensu ma sunyi aure banda ke” sosai Ni’ima kirjinta yahau zafi cus Baba irin mutanen nan ne masu katon murya sai kallonsu ake sabida duk anajin maganan sa, juyawa Baba yayi ya kalli Baban Yaseer da kansa ke kasa yace “Aliyu” ahankali Baban Yaseer yadago kanshi yace “na’am Baba” nuna Hawwa da kanta ke kasa Baba yayi yace “cikin Abokanenka babu me neman mata? Koda yake karnaje da nisa ni wlh ko bakaniken ka ne ma idan zai aureta zan bashi, kannin Hawwa biyar hudu sunyi aure, Miemie ma datake sha hudu yanzu inamai tabbatar maka tsaf zata iya gama makaranta tazo tai aure wannan batayi ba, wlh wlh nagaji, Hawwa taxame mini abun kunya arayuwata nine mai kai karan yaran wasu kan amusu aure nagansu suna zance da samari sunyi girma yau gatawa diyar taki aure, nagaji da Hawwa agidan nan, nadauke ka amatsayin d’ana Aliyu kaganta nan da iyalinka tun suna yan kankanu yan dugul dugul dasu suke kawance, jibi Ni’ima tayi aure abinta ga yan biyunku sun girma dabadan barin datayiba dakuma wanda ta haifa last year ya mutu da yanzu yaranku hudu ni tawa diyar taki aure sai operation din dare” tashi Ni’ima tayi dan bazata iya daurewa ba tayi wajen Hawwa dake tsaye tace “mushiga ciki, kinji ciwo a hannu Baba na magana da Baban Yaseer” tayi ciki da ita dasauri dudda haka suna jiyo maganganun Baba daga cikin gidan ma, tsakar gidan tsaf ko ina yasha fenti flat ne Babba saiga wani daki dake facing flat din sukai wajen, Ni’ima ta karbi jakanta taciro key tabude dakin suka shiga daidai lokacin hawaye na saukowa daga idanun Hawwa dasauri ta share but saida Ni’ima tagani.
EPISODE
Daki ne kwara daya yanada girma ga window da akasa curtains mai kyau pink dakeda zanen flower dayawa, katifa ne number one mai tudu akasa shima an shimfidamai pink bedsheet yayi kyau sosai, ga dan table data jera Kayan shafa da kwalliya gwanin ban sha’awa dasu turaruka da stool na zama awajen, sai kuma dan wardrobe mai 2 rack wanda daga gani kayanta ne aciki sai kuma gefe daya da keken dinki ne mai bala’in kyau ga basket a gefen keken dinkin wanda da alamu abubuwan dinki ne aciki, tsakiyan dakin akwai carpet mai laushi bakin gado, Hawwa tawuce dasauri tazauna tana kokarin danne hawayenta itakuma Ni’ima ta tsaya jawo net na kofan tasa sakata tana sauke labule sannan tajuyo ta taho bakin gadon da sauri tazauna kusada Hawwa dake bude jakanta tana kokarin ciro wayanta tana kallonta, ahankali takai hannunta zata tabata sai kawai Hawwa ta rungumeta da sauri tareda fashewa da kuka, wani irin tsinkewa zuciyan Ni’ima yayi sabida da wuya Hawwa ke kuka, it’s being years bataga kukan Hawwa ba, tariga takoyama kanta dauriya dan taga rayuwa, banda haka duk duniya ita kadai ke ganin kukan Hawwa wanda idan tayishi kasan ta tara abu dayawa aranta ne, cikeda damuwa Ni’ima tai patting back dinta tace “wlh Hawwa idan kina kuka sani kike inaji kaman tawa takare aduniya cus you are the strongest woman dana sani aduniya, please kidena minding maganganun Baba inda sabo yaci ace kin saba, wlh harda tsufa ke damunshi cus make it make sense for me idan kika barsu haka wazai iya ciyarwa agidan nan? Dagashi har matar nasa da yaransa wazai ciyar dasu? Ba aikin dayake zagi kullum ke ciyar dasu ba? Kece cinsu, shansu, suturansu, da kudinki aka aurar da yaransa hudu, kene school din Aminu, kene school din Maryama, still kece magungunan sa, I’m sorry to say baida aiki sai zaman kofar gida baya taba fahimtanki, an gayamai kene kika hana kanki aure? Ni wlh iyayen dake takurama yaransu kan zancen aure na bani mamaki aduniya bayan sune yakamata su dinga bawa yaran nasu karfin guiwa suna gayamusu cewa aure lokaci ne, suna nuna musu su yarda da kaddaransu, duk sanda auren yazo za’ayi saidai su tasa yaran agaba suna kyaransu, ana gayama yara bakaken magana, ana gwanzaban su da addabansu da aure, so yake kije titi ki kama hannu kowani d’a namiji kika gani kikawoshi gidan nan ya aureki? Bakida samari so yake kije kijawo wani karfi da yaji yazo ya aureki? Maza nawa sukazo gidan nan neman aurenki dazaran an tsaida magana su gudu so yake kije ki damkosu karfi da yaji suzo su aureki? Kidnapping na maza yakeso ki fara? Besides duka duka you’re 29 why is he rushing you when bawai kinkai 50yrs baki auren bane? Wlh banso na amsa Baba ne I know it will look disrespectful saisa kikaga natashi najaki munbar masa wajen but I can’t take it idan yana miki irin maganganun nan, when he should be thanking God Allah yabashi diya nutsassiya, kamila, educated and