Showing 147001 words to 150000 words out of 184554 words
gyale tasa ta gyara fuskanta saita dauki bakin glasses din tasaka tabude kofa tafito tashiga ciki tabiya kudi ta karbi number itace number 3, kusan 10min tana zaune akakai kanta tashi tayi tashiga office din wata dattijuwan matace sanye da hijabi looking very decent and modest, glasses Hawwa ta zare daga idanunta tace “good morning” matan tabita da kallo tana nunamata chair ta zauna tace “me kikeso?” Dan kallonta Hawwa tayi saikuma ahankali tace “inaso nai filing divorce ne, mijina yaki sakina” anatse matan na jawo wani drawer tace “can I know your reason?”
Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma tai shiru matan ta kalli Hawwa tace “idan bazaki iya bamu dalili mai kwari ba kotu bazama ta dauki karan da kika kawoba balle harmu mishi sammaci” cikin wani irin murya kaman na marainiya Hawwa tace “uhmmmm ban…..bana sonshi ne” cigaba da jawo drawer matan tayi tace “auren dole aka muku ne? How long da aurenku yanzu? Sannan mesa baki sonshi? Tun yaushe kika daina jin sonshi tun dane ko yanzu?” Baki Hawwa tabude zatai magana saikuma ta runtse idanunta kuka na neman kufce mata tadan fuzar da iska sannan ta kalleta tace “dole saina amsa all this tambayoyin nan? Ni yar sanda ce, I think bana sonshi alone is enough reason na nemi kotu taraba auren cus islamically ya halasta” Hawwa tadanyi shiru chan tace “Ma’am can you just tell me how to go about it batare da all this questions dinba kawai banson Khaleel” sosai matan ke kallon Hawwa sai kawai tace “okay” tazaro wata paper tayi signing akai tasaka stamp tace “fill this form ki bani nasake signing da stamping then it’s done idan har yanzu a gidanshi kike zamu baki takardan sammaci ki bashi da kanki idan ba’a gidanshi kikeba maybe kina gidan iyayenki zaki bamu adreshin sa ko inda z’a sameshi akaimasa” tabama Hawwa paper hakanan sai hannun Hawwa datakai zata karbi paper yashiga rawa sosai matan tabi hannun Hawwa da kallo, da kyar Hawwa ta iya karban takardan Matan tabata pen Hawwa ta tsaya tana kallon pen din takasa karba matan tace “karba mana” ahankali Hawwa tasa hannu ta karba hannunta yashiga rawa sosai zata fara rubuta a paper takasa wlh, duk matan tana kallonta kusan good 3mins Hawwa takasa saka ko A akan paper ahankali tadago kanta takalli matan tace “I need a moment please zan iya fita na cike a waje saina kawo?” Gyadamata kai matan tayi tace “sure tashi kije” ahankali Hawwa ta tashi tafito tawuce parking space tabude motan ta shiga ta zauna tarufo kofan takai pen kan takardan still takasa rubutu what is wrong with her? Idanunta sukai jazur, knocking motanta akayi wlh saida ta zabura dasauri ta juyo Baban Yaseer tagani yana sanye da wata faran shadda mai kyau ya kafa hula akai yayi kyau faduwa gabanta yayi ganinshi dasauri ta ijiye paper da pen a jaka tai maza ta gyara gyalenta tana kara rufe wuyanta da kirjinta da kyau like matan aure tasauke glass na motan kasa, murmushi Baban Yaseer yamata yace “Hajiya Hawwa rai kanga rai” adan kunyace cikeda jin nauyin sa tace “ina yini Baban Yaseer” anatse yace “Alhamdulillah ai tunda naji kinyi aure bansamu mun hadu namiki Allah ya sanya alkhairi ba, ai tundazu dayake nazo ne Boss dina ya aikoni nazo nasami yarsa anan na karbi this” yanuna mata wani file dake hannunshi yace “na karba zan shiga mota kenan sai gaki kin fito kin shiga ciki baki lurada ni ba, this is my car” yanuna mata motanshi dake next to nata yace “shine na tsaya na jiraki dole mu gaisa” dan gyadamai kai Hawwa tayi anatse tadan sauke kanta tace “yaya su Yaseer Da Yasmeen da Maman su?” Murmushi Baban Yaseer yayi yace “Hawwa kenan wato ko banjin za’a taba samun mace mai halinki aduniya ba, ace duk abubuwan da Ni’ima tamiki you are still asking yatake” yayi murmushi yace “anyways mijinki yasa an fito da ita daga prison bayan sati daya bayan tayi signing undertaken if anything yasameki in the next 5years itane, an mata iyaka dake wai ko layinku takara zuwa za’ayi inviting nata for questioning cus basu da yan uwa alayin, bata baki, toh shine fa su Mama da Yan uwan marigayi Babanta da iyayena sun shiga maganan na yafemata sabida yaranmu wlh, so she’s at home waiting for license nata da har yanzu basu dawo mata dashi ba and it serves her right, alhakin ki ne” shiru tayi Hawwa batace komiba, Baban Yaseer sai kallonta yake kaman zai hadiyeta da idanu, kasa daurewa yayi yace “why are you here? Me kikazo yi a sharia court?” Yake Hawwa tamai tace “ahhhhh, abu……Abu nazo amsa” gyadamata kai Baban Yaseer yayi yace “tom shikenan agaida mai gidan” yajuya zai bude motanshi saikuma ya juyo daidai Hawwa na daga glass nata sama dasauri yace “Hawwa!”
Kallonshi tayi tana dakata da daga glass nata sama yace “please I have few things to say to you dudda ga yanda abubuwa suka faru between us but I still consider you kanwata, the way nake kula dake ada and protected you ada I will never stop doing that Hawwa cus I mean well”
Hawwa tai shiru tana kallonshi anatse Baban Yaseer yace “I don’t want to poke nose into affairs naki ko aurenki but for me to see you anan this early morning with those red swollen eyes means one thing you’re not happy in your home!”
Faduwa gaban Hawwa yayi sosai bakinta yashiga rawa tace “me kake fa…fad….” Tare mata numfashi Baban Yaseer yayi yace “i know you will never admit, anyways i dig into rayuwan wanda kika aura na gano rannan shine mutumin motan nan ranan dakika cemin kin fada a pool”Baban Yaseer yace “don’t get me wrong nasan jaraban Ni’ima yasa Baba yabada aurenki desperately for peace to reign, Hawwa listen to me attentively don’t you ever think sabida kin manyanta ba miji you can just settle for any kind of miji that come your way, banwani san mijinki sosai ba but I know wat yaran masu kudi are like cus I work for one naga kalan rayuwan da yaran Boss dina keyi, they don’t respect women infact bama susan menene aure ba! Kula da mace, daraja aure sai dan gidan talakawa fakiri mai lallaba rayuwa ba irin yaran nan da sunada kudin auro mata dubu alokaci daya ba” yadan rage murya ganin Hawwa ta natsu tayi shiru tana kallonshi ahankali yace “Hawwa akwai good decent men out there da they will respect you for you! They will love you right! They will treat you like queen nasu! Maza masu tsoron Allah da sanin yakamata, don’t ever be afraid to stand up for yourself! Be you Hawwa! Leave idan you are not appreciated ko respected a inda kike, gidan miji baya nufin you make it in life, making it in life shine idan kasamu peaceful and serene rayuwa hassle free and trauma free, stand for yourself kinji Hawwa and fight for what right! Don’t compromise kanki for anyone okay!” Shiru Hawwa tayi sai kallonshi take, ahankali yanuna kanshi yana mata wani kallo yace “just like before I am always here! I will forever be here for you kinji, remember you watch rayuwana da Ni’ima bawai inada kudin bala’i ba but you saw how I treated and respected Ni’ima, that is how a husband should be, mai ilimi, mai hankali, a leader! So think about abinda nace” kasa magana Hawwa tayi yamata murmushi kadan yace “bari naje you take care” yajuya yashiga motanshi yaja yabar wajen
Hawwa tabi motanshi da kallo ta madubi harya fita daga building din takardan tasa hannu ta dauka tana kallo kirjinta na bugawa tun dazu she couldn’t find the courage and confidence na cikawa but maganganun da Baban Yaseer yamata gave her the confidence sai kawai tashiga cikewa tacika tass tai sigining tafito tashiga ciki tabama matar ta karba takalli Hawwa tai murmushi tai signing tai stamping sannan ta tashi tadauki wani envelop na Shari’a court tai rubuce rubuce tai sealing tabama Hawwa tace “give it to mijinki zamu ganku on the 20th na this month yau 9th” ahankali Hawwa tasa hannu takarba tawuce kofa harta daura hannu zata bude matan tace “incase you have a change of heart” ahankali Hawwa tajuyo ta kalleta matan tamata murmushi tace “you can always withdraw application din okay” gyadamata kai Hawwa tayi kadan tabude kofan dasauri tafita.
EPISODE
Tana fitowa tawuce mota tashiga taja motan tabar wajen wlh bataso tama koma gidan but tana zuwa gidansu Baba zai fara maganganu, wani cafe ta tafi tashiga tai order su coffee da croissant tasha takasamacin croissant din, sannan ta tashi motanta tashiga ta zauna ta ciro number DIG takirashi harya katse bai dagaba sai chan yakirata yace “Miss Hawwa yanzu tazama Mrs Ibrahim” ahankali tace “Sir ina kwana” “ya kuke ya aiki” ahankali tace “fine” yace “yaya hope komi lpy”? Ahankali tace “Sir I wanna make inquiry ne zan iya resuming aiki ko dole sainayi exhausting leave dina”? Dasauri DIG yace “as far as I know you can always resume aiki anytime idan kinaso, kawai dai hutun da aka baki hutu ne na aure if you feel you don’t need it zaki iya dawowa we can’t force you to take leave din da bakiso” dan murmushi tayi tace “Sir zan dawo aiki gobe in sha Allah” kai tsaye yace “Allah nuna mana” ya katse wayan ta ijiye kawai ta tada motan ta tafi park bataso takoma gıda yanzu she just needs fresh air.
Baba na zaune a kofar gida yana duba wani littafi Umdatul Ahkam yaga mota na zuwa da sauri ya tsaya yadago kanshi ganin motan Khaleel yasa yamike da sauri yana washe baki parking motan Salman yayi yafito Baba yashiga leka motan Salman yakaraso wajen cikeda girmamawa yace “ina kwana Baba” dasauri Baba yace “sannunka a’a banga Ibrahima ba banga Hawwa ba”? Anatse Salman yace “Oga yace nakawo ka yana asibiti ne” Dasauri Baba yabude idanu yace “Subhanallahi meya sameshi?” Anatse Salman yace “Oga bai bani izini na sanar dakai komiba yadaice nakawoka” Dasauri Baba yace “muje muje” budema Baba bayan mota Salmab yayi ya taimakamai ya zauna ya ijiye karafunan shi sannan suka wuce har zuwa asibitin yasake fito da Baba sukai ciki har zuwa oncology ward, gaban wani special daki dake cikin wani bangare daban kaman flat Salman yabude kofa Baba yashiga ciki gabanshi yayi wani mummunan faduwa Khaleel yagani da hospital gown a jikinshi an samai bakar safa a kafafu ga drip dawasu yellow water an makalamai wasu abubuwa da dama a kirjinshi yana kallon Baba daya dakata ya tsaya chak yakasa motsi cus babu wanda ya sanar da shi Ibrahima ba lafiya and kana ganin Khaleel zakaga kaman yadade ba lafiya idanunshi sunyi ja sun kumbura, hannu Khaleel ya mikama Baba asanyaye yace “Baba” wani kalan ijiyan zuciya Baba yasauke har kirjinsa na motsi yataho ahankali ya tsaya gaban gadon yaduko da kanshi yana kallon fuskan Khaleel sosai yace “Ibrahima na meke damunka? Eh? Meya sameka? Wannan machinan da karafunan da kwankwalatan nan da aka makala maka a kirji duk na menene su eh?”
Murmushin karfin hali Khaleel yamai yace “bawani abu bane Baba karka damu”? Muryan Baba har rawa yake yace “ina…..ina matarka? Ina Hawwa? Maisa Kai kadaine anan tana ina?” Murmushi Khaleel yasakema Baba yace “na barta agida ban sanar da kowa ba banso su damu kai kawai nasa akawomin” hannun Baba ya kankame ahankali yace “I am scared Baba tsoro nakeji!” Hawaye ne suka shiga taruwa a idanun Baba dasauri yajuyo yakalli Salman dake wajen bakinshi na rawa cikin tsananin tashin hankali yace “wai meyake damun d’ana eh”? Hannunshi Khaleel yataba hakan yasa Baba yajuyo ya kalleshi ahankali, cikin wani kalan sanyin murya yace “Baba natabayin cancer da ina yaro tun ina dan shekara takwas saida nakai sha uku sha hudu na warke ciwon yarabu dani” sosai kirjin Baba ke bugawa ahankali Khaleel yace “kwanan nan
I’ve been having signs and symptoms na ciwon ina yawan suma, yau na suma and banjin dadi shine nakeso nayi running tests yanzu” muryanshi nadan rawa yace “Baba I’m very scared” kawai Baba rungume Khaleel yayi kaman dan yaronshi yadagoshi yana sakashi ajikinshi sosai kawai kukan da Khaleel yadade yana rikewa kawai yasaki ajikin Baba jin yanda Baba yasashi ajikinshi Salman yajuya yafita daga dakin yarufo musu kofa, Baba najin yanda Khaleel ke kuka ajikinshi sosai, cikin murya mai rauni yace “Baba cancer azaba ne banso yadawo, Baba banso na mutu yanzu inaso mu haifi yara dayawa ni da Hawwa, gidanmu babu mutane, I don’t want to die Baba, 12 children nakeso” kai Baba zuciyansa ya tsinke it takes alot from him yahana kanshi kuka ganin yanda Khaleel keyi yaron dayasa akawoshi dan yabashi kwarin guiwa sai shima ya karaya agabansa No kankamesa yayi yana patting bayansa yace “it’s okay it’s okay ya isa! Babu abinda zai sameka Ibrahima, babu ciwon da Allah ya halitta a duniya face yayi maganin sa, babu abinda zai sameka kaji d’ana, kaji” gyadama Baba kai yayi ahankali, Baba ya tattaro riganshi yakai kan fuskanshi yana sharemai fuska Khaleel sai ijiyan zuciya yake saukewa daidai Dr na shigowa dakin tareda nurses yace “okay an kawo Baba, shine Baba from all indication” Dr yakalli Baba cikin turenci yace “Baba patient dina yaki yarda ayi test wai saikazo” dudda Baba bai iya turenci sosai ba but yagane abinda baturen ke fadi, Dr yasake kallon Baba yace “ready” kama hannun Khaleel Baba yayi gamgam yace “yes dakta ready” gungura gadon akayi Baba na rike da hannun Khaleel suna tafiya ahankali sabida sandar dayake amfani dashi har zuwa wani dakin da za’asa Khaleel a machine, wani abu kaman basket Baba yaga ana sama Khaleel a kai sannan akace “Baba ka sakeshi” kallon Khaleel Baba yayi yace “ina nan bazanje ko’inaba kaji, karkaji tsoro kaji”? Gyadamai kai Khaleel yayi ahankali yace “Baba karkaje ko’ina” Baba ya gyadamai kai, Baba yakalli doctor yace “is machine hot? Zafi? Fire wuta-wuta”? Murmushi Dr yayi yace “No Baba he will feel a little uncomfortable but no pains I promise” juyawa Baba yayi yashafa fuskan Khaleel yace “kaji likita yace ba zafi kadena tsoro babu abinda zai sameka kaji”? Gyadamai kai Khaleel yayi Baba yawuce yafita aka shiga da Khaleel cikin machine din gabansa na faduwa memories na rashin lafiyanshi na dawomai fresh arai, the most traumatic experience na rayuwanshi kenan.
Sosai Baba ke kada kafafunshi yana jira likata yafito kusan 30mins yagaji dagashi har Salman sai kawai yatashi yana bude kofa daidai Khaleel na fitowa daga machine din haba sai amai salati Baba yasaki. “Innalillahi Likita meya sameshi yake amai” yayi wajen nurses na tara abun amai Khaleel nashiga ciki, Dr yace “is normal machine din nasa mutane feeling nauseated da dasauransu” Baba yadafa Khaleel dake amai sosai gashi babu wani abu a cikinsa ma, idanun Baba sukai ja, ruwa aka kawo Baba yakarba yabashi ya kuskure bakinsa kawai yakama Baba yana daura kanshi ajikinsa yana nishi da kyar da kyar Baba namai sannu gwanin ban tausayi, saida yadan huta sannan aka tafi dasu another waje abubuwa daban daban akema Khaleel har wajajen 4.
Ahankali Khaleel yace “Baba karfe nawa?” Dasauri Baba yace “hudu tayi” ahankali yace “zan koma gida” dasauri Baba yace “saura test daya haka likita yace” murya chan kasa yace “gobe zan dawo nayi yau birthday Hawwa nariga nayi making arrangement” cikeda masifa Baba yace “bakada lafiya ta birthday kake test din daza’a maka baifi zagayowan shekarun Hawwa ba” idanu ya lumshe murya chan kasa yace “nothing can be more important than Matana Baba” baki Baba yasaki yana kallon Khaleel dake ciwo sosai yama rasa mezaice Dr yashigo Khaleel yace “I want to go home I will come tomorrow for the last test” Dr zaiyi magana but yasan halin Khaleel hakan yasa yace “okay but akwai magungunan dazaka sha kadan sami karfi da kuzari” gyadamai kai Khaleel yayi ya cicciremai komi Salman yakawo kayanshi ya karba Baba da kanshi yatayashi saka rigan wandone dai yajuya Salman yatayashi sawa, Dr yabashi magani yasha suka rikeshi suka fita har mota Baba ma yashiga ya zauna, kwanciya Khaleel yayi yasa kanshi a cinyan Baba, Baba na shafamai kai cikin duka surukan shi babu wanda yakeda this bond dashi like Ibrahima, Ibrahima ya daukesa kaman mahaifinsa ba suruki ba, shima haka yakejin Ibrahima kaman dansa na cikinsa.
Har gidan Baba suka sauke Baba, Baba yace “gobe asuba a asibitin zatamin likita yafadamin duk abinda kakeyi kana guduwa ni da kaine, kahuta kaji, kaci abinci kuma, kace Hawwa tamaka shayi da kayan kamshi, karku fita dan Allah kome mene zakiyi kuyi agida kajini bakada lafiya, Salman karka bari yaje wani waje” gyadama Baba kai yayi ahankali hakama Salman, Baba yakara shafa fuskanshi cikeda so dakuma damuwa yace “Allah yabaka Lpy Ibrahima kayı kokari ka sanar da
matarka da iyayenka kaji” hannun Baba Khaleel yakama dake kan fuskanshi yayi murmushi yace “okay Baba” sakinshi Baba yayi yarufe musu kofa suka tafi yanama motan bye duk bayajin dadi.
Har gıda sukakai motan dayaga Babu kawai yagane har lokacin Hawwa bata dawoba parking sukayi yafito thank God ba kowa agida cus Mom daman tace yau zata fita tareda Noor sunada event, flat nasu yashiga Salman yakaishi har dakinshi wanka yayi yafito ya shirya da kyar yayi kyau sosai sai kamshi yake zubawa yaciro wasu abubuwa daga wani expensive bag yakai dakin Hawwa.
6 dot na yamma Hawwa tashigo gidan tawuce tai parking motan tafito, wucewa flat nasu tayi tabude kofa ahankali tashiga ciki, Khaleel tagani zaune afalo yana sanye dayadi mai shegen kyau, riga milk jumper da wando yayi bala’in kyau yana zuba kamshi, suna hada idanu tadauke kai tashigo tamaida kofan tarufe tashigo tawuceshi zatai staircase batare datamayi sallama ba balle ta gaidashi yace “Hawwa!”.
EPISODE
Chak ta tsaya yanda ya kirata har cikin ranta taji muryansa gabobin jikinta na amamsawa, amman bata amsaba bakuma tajuyoba, ahankali Khaleel yana gyara voice nashi dan baiso tagane wani abu gamedashi yace “change and come down we are going out” batare data kalleshi ba tace “I’m not going