Showing 42001 words to 45000 words out of 184554 words

Chapter 15 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1920

ta tawuce da sauri tana share fuskanta dan yau batada karfi, daga murya Khaleel yayi yace “seeing you like this is so satisfying” bude motanta tayi ta shiga ta tada motan taja da mahaukacin gudu tabar eatery kuka kawai take hannunta na mata radadi har lokacin jini na fita though ba sosai kaman d’a ba.

Ana magrib a masallaci takai gida Baba bayanan yana masallaci, fitowa tayi ahankali cus bayanta namata ciwo tarufe motan tashiga gida, daki tawuce ta zauna gaban madubinta tana jawo drawer tadauki spirit tazuba a tsakiyan hannu kara tayi tana fashewa da kuka sosai sannan tasa auduga ta goggege ciwukan hannunta, bottle water dake wajen tadauka tana kallo sai alokacin ta tuna tana azumi goge fuskanta tayı da bayan hannu takai ruwan baki tasha, ta lallaba tamike tafito tadauro alwala tadawo tahau kan dadduma tai salla, ta kwanta kan dadduma tana kallon saman dakinta bini bini tana goge hawayen dakebin fuskanta, saikuma chan tamika hannunta tadauki wayanta tai dialing number Ni’iman amman baya shiga busy busy taje watsapp tamata message baya shiga taga bata ganin DP dinta yau, blocking dinta kenan tayi.

Rawa hannayenta suka fara cus in wildest dream nata bata taba tunanin Ni’ima can block her ba, tadauka duk maganganun datake dazu fushi ne, blocking dinnan hit Hawwa daban kawai tafashe da kuka tayi harta godema Allah, kawai saitaji rayuwan yamata daci, bazatai karyaba harda Ni’ima as part of the reason da bata damuwa da rashin aure, sabida tana debe mata kewa, waya, chatting, labarai abinda yafaru wajen aiki da sauransu, zuwa outing all those abubuwa makes her forget about actual problem nata, kanninta duka sunyi aure banda ita, gabaki dayan layinsu itace babban dabatai aureba kannin kanninta sunyi aure, hannunta dake mata zugi da Ni’ima ta taka da takalmi tadaga ta kalla sai kawai ta lumshe idanu hawaye na zubomata daga ido masu zafi tawani kanannade kanta a dadduma kaman macijiya ahaka aka kira isha’i ta lallaba tayi tareda shafa’i da wuturi

Wayan takara dauka tasake dialing number Ni’ima but busy wayan nata tadaura akan fuska tafashe da kuka mai zafi hawaye na diddiga akan screen na wayan for all this years da abubuwan dake faruwa da ita bata taba feeling broken ba like yau, yau jitayi da defense system nata da will of power nata da komima ma yayi breaking she’s weak, cire wayan tayi daga kunnenta tai dialing number Ammi ringing daya Ammi tadauka tace “Hawwa yaya how is your Monday? Kindawo daga aiki? Ya Baban naki ince bai cigaba da rigima dake b…….” Rage murya tayi sabida yanda takejin sheshekan kukan Hawwa

Lumshe idanu Ammi tayi rabon dataji kukan Hawwa haka tun zamanin rasuwan mahaifiyarta cikeda so tace “Baba ne” girgizamata kai Hawwa tayi tace “Ammi Ni’ima tarabu da…da….d…..” takasa magana ma tsabagen kuka zuciyan Ammi bugawa ya shiga dan wlh tanason Hawwa sama da nata yaran ma bata wasa da ita, dasauri Baffa dake gefenta yace “Malam yasake mata wani abu ne?” Girgizamai kai Ammi tayi tamai alamu daya dakata tana sauraron yanda Hawwa kemata kuka batama iya magana ahankali Ammi tace “Hawwa ya isa, kukan ya isa haka? So kike hankalina yatashi nashigo hanya da daddaren nan?” Girgizamata kai Hawwa tayi Ammi tace “calm down Hawwa komi yayi zafi maganinsa Allah, kowace kaddara daga Allah yake, it’s okay Hawwa na, it’s okay kinji, ya isa hakanan ya isa”

Akwai wani kalan natsuwa da kalaman Ammi ke bata ahankali tasoma rage kukan Ammi tace “meya faru tell me everything” da kyar ta iya fadama Ammi komi dudda kuka nafin karfin maganan nata but still Ammi manage to understand komi, wlh deep down tasan za’ai haka, ahankali ta zauna abakin gadon idanunta sun ciko da hawaye da sauri Baffa ya girgiza mata kai alamun kartayi she will break Hawwa even more, hadiyesu tayi tace “Ni’ima is angry I understand don’t pay attention to much to maganganun ta, itama ko’ina take im sure tanachan tana kuka kalan wannan dakikeyi, kunyi building strong relationship da Ni’ima da banjin zaiyi breaking hakanan ba just give her some time Hawwa, and stop crying”

Ya isa ya isa, Ammi tai maganan cikeda tausasa zuciya maganganu masu dadi tashiga gayama Hawwa ahaka bacci yayi awon gaba da ita anan kasa kan dadduma. Ammi ta katse wayan takalli Baffa dayaji komi tace “nakira Ni’iman?” Gyadamata kai yayi dialing number Ni’ima tayi wayan yayi ringing harya katse ba’a dagaba saita sake kira but busy itama ansata a blacklist takira kusan 5times but haka zata sake kira Baffa yace “ya isa! Basai kin sake kiranta ba, bakomi rayuwa ce, bari zan ma abokanen aikina magana idan zan iya samana Hawwa wani aikin ağarın nan saita dawo nan zaria ta manta da damuwanta”

Around 5 ta Hawwa ta tashi cikinta namata ciwo dana yunwa dana MP, bayanta shima na ciwo, kayan aiki ta da bata cire jiyaba tacire ta daura zani tafito, wanka tayi da brush da alawala tadawo ta shirya yau cikin simple office gown black tasa tai salla, tadauki black shades tasa cus idanunta sun kumbura sosai tawuce tafito Baba na masallaci, warming Mota tayi kafin taja motar tabar anguwan, Awani eatery ta tsaya tasai abinci, koda ta shigo office nata tabude abincin tagumi tayi tana kallon food din, saiga hawaye sharewa tayi dasauri takai hannunta tasake daga wayanta tai dialing number Ni’ima but busy tayi blocking nata true true, ijiyan zuciya ta sauke gwanin ban tausayi ta debi rice din takai baki da kyar ta hadiye baya mata dadi bakinta is just dry, rufe takeaway tayi ta ijiye agefenta tai shiru tana kallon waje daya tunani kawai take, rannan takasa komi har saida aka bata break cus tace batada lpy and kowa yagani kam she looks sick da kyar take tafiya DIG yace taje taga Dr tahuta cus Hawwa is strong bata fashi, she’s serious da aiki he needs her healthy.

Around 1 takoma gida Baba na zaune awaje ya ganta

Da sauri ya yunkuro yana kallon yanda tai parking tafito ahankali tana daukan jakanta da kyar, ganin yanda fuskanta yayi jajir hakama hancinta yasa dasauri yayi wajenta kafin tama iso yace “meyasameki awajen aiki Hawwa?” Ahankali asanyaye tace “banda lpy ne Baba” dasauri ya shiga kama crutches nashi a hammata yakai hannunshi yana taba goshinta yace “subhanallahi sannu Hawwa kinsha magani konasa asayo miki”? Ahankali tace “eh nasha” cikeda damuwa yace “assha sannu, sannu kinji, kawo jakan muje ciki” yakarbi jakan yana ratayawa a kafadansa sukai ciki…

Har gaban dakinta saida yaga tabude ta shiga ciki sannan yawuce kitchen da kanshi ya shiga bude bude yadebo mata shinkafa da miya a kwano da zafinsa yafito yazo gaban dakin yana bugawa yace “nashigo”? Ahankali ba karfi a muryanta tace “eh” kofa yabude ya shiga da plate na abincin a hannunsa tashi zaune tayi dan tana shiga kwanciya tayi ko kaya bata cireba yabata abincin yace “ci, ci idan zazzabin bai kwanta ba saina kaiki asibitin su Ni’ima” sunan Ni’ima da Baba yakira kawai saiga hawaye sha hankalin Baba yatashi da sauri yaja kujera ya zauna gaban fadin yana ijiye crutches dinsa yace “Hawwa menene eh? Meke damunki? Wlh na hakura tunda kin nuna baki kaunar Alhaji Kabiru nimadai naga yamiki tsufa nafasa bari ki aureshi kinji, kiyakuri kome nagaya miki kwanakin baya eh Hawwa na, ya isa kukan, dena dena” yakai hannunshi yana sharemata fuska ta bala’in bashi tausayi, yashafa kanta yace “to ya isa ci abincin abinki ko kadan ne” yanda Baba yadamu yasa tadebi kadan takai bakinta da kyar tahadiye, yanda yaga tanayi yasa yace “kawo abincin bari naje nasayo kaza sai asoya miki kici abarbada cabbage da yaji da tumatir haka mahaifiyarki keson kaza” murmushi tamai kadan, tashi yayi yana dafa bango yasa mata filo akan gadon yace “kwanta da kyau kinji” kwanciya tayi yace “karki rufa jikinki na zafi” gyadamai kai tayi Baba yadauki abincin yana kallonta yawuce yafita yana gyaramata labule.

EPISODE

Baccin ma dataso tayi batayishi ba yaki zuwa, wajajen 4 ta tashi ta chanza kaya zuwa abaya tadauki car key tafito Baba na zaune a tsakar gida yana wanke kaji shi kadai gaban pampo ganinta yasa yace “ina zaki ya jikin”? Ahankali tace “bari nadan sayo magani Baba” da dan damuwa ya gyadamata kai yace “toh shikenan kije karki jima” gyadamai kai tayi tafice shiga mota tayi ta tada tawuce gidansu Ni’ima babu wani nisa sosai daga layinsu shiga layin tayi har zuwa gaban gidan tai parking tafito tashiga da sallamanta, Mama na zaune a tsakar gida tana gyara wake itada yar makotansu da aka aiko yaranta duka sunyi aure yar aikin ta kuma ta aiketa tana ganin Hawwa tai dan murmushi tace “ahh yau su Hawwa ne agidan” shigowa ciki Hawwa tayi cike da girmamawa tace “Mama ina yini” murmushi Mama tayi tace “lafiya lau ya kike Hawwa yasu wajen Baban naki” ahankali Hawwa tace “lpy lau” tazauna awajen tai shiru takasa magana kaman wata marainiya, Mama ta kalleta sosai tabata tausayi dan tausayi duktai wani iri, yarinyar dake zaune Mama ta kalla tace “tafi Husna ki gaida Mamanki kice mata zan shigo anjima” tashi yarinyar tayi tafita, Mama ta kalli Hawwa tace “sabida Ni’ima kikazo ko?” Gyadamata kai Hawwa tayi, Mama tasauke ijiyan zuciya tace “Hawwa dagake har Ni’ima ba yara bane, tariga ta sanar dani komi dake faruwa, she’s just trying to protect her home so I think is best idan kinyi respecting decision nata and give her space datake so, idan tanaso kudawo da kawancen zata nemeki, don’t blame her rayuwa yazama abin tsoro, sai ana sara ana duban bakin gatari fa, kibarta and move on ba dole Hawwa, tunda abu yakai ga haka kifita daga rayuwanta kinji” sosai Hawwa ke kallon Mama dake maganan irin ko ajikinta dinnan, wani iri Hawwa taji hawaye na taruwaa idanunta, Mama tace “kidena nacin nan dan Allah antaba kawance dole? Yo amintan dole ne? Idan kuma kin nace sai kinyi to kema Hawwa ki yarda da mijin da Baba yamiki mana Malam Kabiru kiyi auren kowama yahuta kinayi nasan Ni’ima zata dawo gareki, kinji kiyi tunani akan abinda na fadamiki” Hawwa takarayin shiru zaune awajen akasan simenti, Mama tace “tashi to kitafi” ko motsi Hawwa takasa yi, Mama ta tabe baki tace “Allah kyauta, tashi kije dan Allah nima kada ki sake zuwan gida, wacce ta hadamu tace batayi, kowa nasa yasani aduniyan nan ba’a kuma dole, just don’t take it personal, Ni’ima is protecting her space ibada take, a musulunce miji yafi kawa sau dubu ko nine mijina zan zaba bawata kawaba ana zaune lafiya, yanda kikeda wayau da ilimin nan ko kece a situation din Ni’ima haka zakiyi wlh put yourself in her shoe, y’ata ta samu gidan hutu yo idan kawa zata mata summun bukumun basai aja mata layi ba kowa yayi takansa? Kingani saida safe bari nahadama Malam abincin dare” tawuce kitchen abinta, Hawwa kawai tafashe da kuka da kyar ta dafa bango ta mike bayanta har yanzu ciwo yakemata fita tayi ta shiga motanta, taja ahankali tabar unguwan takoma gida.

Baba bayanan but tana shiga dakinta taga ya ijiye mata kula zama tayi ahankali tabude kulan kaza ce ta soyu ansaka kulikuli da yaji gasu cabbage, tana ganin girkin tasan Baba yadafa mata dama yace dayana saurayi yayi sana’an balangu da su gasassun kaji, hannu takai ahankali tadauki daya takai bakinta daidai nan Baba yayi sallama ya shigo yana rikeda leda ganinta zaune gaban kulan yasa yayi murmushi yace “yauwa Hawwa gashinan naje bakin hanya na sayomiki chivita na grape mai sanyi, ranan nan na dandanashi yamin dadi zakiso shi”

Yazo yazauna kusada ita yana ijiye karafunan a gefe lumshe idanu Hawwa tayi jin Baba ya zauna kusada ita tabude su tana ganin yanda duk yadamu yana bude mata juice din, this is the first time takejinta so vulnerable she’s tired of being a strong girl, komima na duniya yamata ahankali tadaura kanta jikin hannun Baba gently tasaka hannunta takama hannunshi ta kankame sosai a kirjinta tafashe da kuka mai tsuma zuciya, bala’in tashi hankalin Baba yayi dasauri yajuyo yace “Hawwa, ke, Hawwana? Me akamiki mesa kike kuka haka? Hawwa” sheshekan kuka take jikinta har rawa yake tarike Baba sosai takasa magana dasauri Baba yadago kanta saikuma yajuyo da kyau idanunshi sunyi jaa yace “zonan Hawwa zo” yajawota yasata a kirjinshi tai hugging Baba so tight this is abinda bata tabayiba hugging Baba saidai maybe datana yarinya, bayanta Baba yashiga bubbugawa yace “ya isa Hawwa ya isa, zakisa hankalina yatashi, koma menene ke damunki baifi karfin Allah ba, ya isa Jiddalo na, ya isa, yi shiru yi hakuri kinji, kinada matsala awajen aikinki ne?” Girgixamai kai tayi alamun a’a tana tsagaita kukan tana sauke ijiyan zuciya ba kakkautawa a kirjin Baba, ahankali yace “to menene ke damunki”? Murya chan kasa tace “Baba aure nakeso nayi nagaji da yanda kowa keyi dani sabida banyi aureba” ahankali Baba na buga bayanta yace “karki damu zaki aure, anmini kwatancen wani Malami na Islamic chemist ranan asabar tunda ba aiki zan kaiki muje muji ko aljanu gareki dake hanaki aure, kokice baki sonsu kosu sugudu zamuji dalili kidena damun kanki namiki alkawari bazan kara takura miki ba, lafiyanki yafi komi mahimmanci agareni Hawwa na, kiyakuri kinji yarinyana yar albarka kiyakuri da rayuwa, komi tsari ne na ubangiji kizama mai juriya da hakuri akwai Allah Hauwa’u kinji” gyadamai kai Hawwa tayi, Baba yayi shiru chan yadago ta daga jikinshi yace “zafin jikinki ya baci kinsha magani kuwa?” Gyadamai kai tayi ahankali Baba yace “to zai sauka, sha lemon kici naman bari naje masallaci, kada kuma kisake kuka kinajina” gyadamai kai tayi yadafa gadonta yana mikewa daukan crutches din tayi tabashi ya karba yafice tabishi da kallo saikuma ta kalli abincin bata iyaci, wayanta ne yahau ringing da mugun sauri takai hannunta ta dauki wayan Ammi tagani a screen sanyi jikinta yayi tadauki wayan Ammi ma sake kwantar mata da hankali tayi sun sade suna waya ahaka bacci yayi gaba da ita koda Baba yadawo ganin tayi bacci yawuce yana jawo mata kofa duk ya damu ganin bataci abinci ba. ‎<This message was edited>

EPISODE

Washegari around 5 ta farka da ciwon kai har bata iya bude idanu da kyau, gashi tai staining kayanta da wajen abinda bata tabayiba, ta tashi tacire kaya da zanin gadon batada karfin wanki a basket na laundry tasa, tasake kwanciya ko daga kafa tayi saitaji akanta, tana ahaka Baba yayi knocking da sallama da katuwan muryan nan nasa yace “zan shigo” kofan yabude ya shigo dakin yaganta kan gado hankalinshi yakara tashi ganin sosai Hawwa fa batada lpy, batama iya bude idanu, cikeda damuwa yace “Hawwa na” yazo wajen gadon yana dagota jikinta kaman fire Baba yace “subhanallahi, Hawwa zoki lallaba kiyi wanka muje asibiti, kokuma bari kiga nakira Ni’ima” wayansa yaciro daga aljihu yashiga kokarin kiran Ni’ima Hawwa na kallonshi da kyar harya katse bata dagaba yace “bata dagaba bari kinsan asuba ne hala bata tashi ba, bari nasake kira” yasake dialing number saiya cema Baba busy kusan sau 4 yana trying yace “busy busy yake gayamin” dan murmushi kadan Hawwa tayi ganin shima Baba tai blocking nashi, cikeda karfin hali muryanta baya fita da kyau tace “Baba karka damu bari naci abinci zan lallaba naje asibitin nasu adubani” gyadamata kai Baba yayi yajuya yace “shirya wankan bari nahada miki ruwa” sosonta yaduka yadauka yafita yana dungura sanda yashiga kitchen Umma na kitchen din ta banka uban tsaki ko kallonta baiyiba, ruwan da aka ijiyemai nashi na wanka yajuye mata yadauka yafito yatara na sanyi ruwan yayi dalam dalam dan jikinta akwai zafi sosai yakaimata bayi sannan yadawo dakin yabuga mata yace “fito Hawwa” fitowa tayi da hula akanta ahankali take tafiya tana dafe kanta da hannu daya hannu daya tana dafe bango, Baba yakama hannunta gwanin ban tausayi ya jinginata a bangon wajen yaci bari nakawo miki kujera, kujera ya dauko yasamata abayin sannan ya shigar da ita yarufo mata kofa, bata taba sani ana irin ciwon kan nan aduniya ba, kowani motsi tayi sai kan ya amsa, tadan jima tabude kofan Baba na jiranta, brush yabata daya koma daki yadauko mata tayi yariketa yakai daki ya zaunar kan gado, Allah sarki da kanshi yabude sip yazaro mata yar doguwan rigan da yagani na atampa green, ya ijiye mata kusada ita, tabishi da kallo yanda yake dingisawa yadauko mata mayyukanta yakawo gadon ya ijiye duka kusada ita murya chan kasa yace “sa kaya ganinan zuwa” yawuce yafita, da kyar ta tashi tadauko su pad, pant bra tashiga shiryawa ahankali tasaka green atampan da Baba yadauko, dogon riga very simple yet stylish dinki dan har collar gareshi rigan, ta zauna ahankali kome zatayi kaman kanta zai fadi, dan karamin gyalenta green ta dauka ta yafa tasake kwanciya agadon Baba yashigo da shayi a hannu yazo gadon yazauna kusada ita yace “zoki sha muje” hannu tadagamai alamun bazata iyasha ba, tana lumshe idanu saikuma dan gajeren bacci yayi gaba da ita wuraren 7 ta farka, jikinta har kyarma yake sabida zazzabi kaman ana tsinka hanjin cikin jikinta, idanunta sunyi jajir, gyalen tasake dauka tayafa dan bazata iya daurin dankwali ba ta lallaba ta mike tana daukan wayanta da handbag da car key a hannu tasaka flat shoe black tafito, Baba na compound tafito yamike dasauri yataho da sauri yana kallonta yace “kin tashi” dan murmushin karfin hali tamai tace “bari naje asibitin su adubani” Baba yace “zaki iya tuki kuwa da ciwon kan nan”? Murya cha kasa tace “zan iya Baba karka damu” har mota yarakata ganin hankalinshi bai kwanta ba da fitan ita kadai yasa ahankali tace “Baba ko Ni’ima zata iya dawo dani kazauna kaji” gyadamata kai yayi ya maida mata kofan yarufe ta tada motan taja Baba yabi motan da kallo.

Ahankali take tukin, da kyar take iya bude idanu har jiri jiri take gani amman sabida karfin hali haka tashiga hanya jikinta kaman wuta, ko kadan bata gudu sosai cus jiri take gani, har layi take, hospital nasu na yan sanda takeso taje tunda Ni’ima tace tadaina zuwa hospital nasu wanda shine hospital datake using idan batada lpy,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login