Showing 159001 words to 162000 words out of 184554 words
kaman ma yamutu but still dukanshi yake yaji saukan bindiga akanshi azuciye Hawwa tace “if you hit him again Khaleel I will pull the trigger!” Chak Khaleel yatsaya jin Hawwa tasamai bindiga akai sai kawai yajuyo yakalleta da jajayen idanunshi yana kallonta yace “ni zaki harba because of this man?” Azuciye Hawwa tace “yesssss!” Zafi da radadi kirjin Khaleel yake hawaye ya cika idanunshi ganin matanshi tasa bullet akanshi because of another man yace “zaki iya daukan raina sabida wannan mutumin”? Ahaukace Hawwa tace “yesss! yess! yess! Idan baka dena dukanshi ba I will shoot you so stop!” Rawa sosai kirjin Khaleel yafara ahankali Khaleel yace “do you love him that much?” Wani kalan ihu Hawwa tayi idanunta na chanza kala race “yes I love him! I love humanity! I love everyone! It’s my duty to keep everyone safe! This is my job! This is who I am! I took an oath for this, so I don’t give a damn who you are! I will protect him if you attempt another thing I will shoot you and make sure you rot in jail!” Wayyoooo Allah hawaye saukowa sukayi daga idanun Khaleel yayi baya ahankali ya matsa gefe yana daga hannaye sama alamun yayi surrender, Hawwa tayi kan Baban Yaseer dat is uncouncious dagudu batai wata wata ba ta zare hulan kanta tana gyara gyale tana rufe gashinta ta daga Baban Yaseer tana tare jinin dake fita daga kanshi Khaleel na kallon yanda take taba wani namiji, takalli mutanen wajen tace “please ku taimakamin nasashi a mota” zuwa wasu sukayi ta tashi da gudu tabude bayan motanta aka tayata saka Baban Yaseer duk
Khaleel da Salman na kallonta tarufe bayan motan, daidai zata juya tashiga gaban moran Khaleel ya tsaya agabanta takalleshi kaman yanda yake kallonta yadan fuzar da iska dataji how hot his breath was ahankali yace “Our marraige is over Hawwa!” Dum! Dum dum! Hawwa taji gabanta na bugawa, ta tsare Khaleel da idanu, ahankali yace “it’s over!” Dum! Dum! Dum! Anatse yace “daganan ki wuce gidan ku don’t ever and ever step into my house again!” Ya runtse idanu yabudesu fa kyar kaman ansamai barkono ciki cikin murya mai rauni yace “na barki har abada Hauwa’u!” Yayi shiru yana kallonta kaman yanda take kallonshi kirjinta na tsinannen bugawa, cikin murya mai mugun mugun sosarai yace “Hauwa’u Alhassan Na Sak….!!!!”.
GIVE ME ANALYSIS WAKEDA LAIFI!!!!!!?????
WAYYOOO MY CHEST???
IS THIS THE END OF THIS LOVE STORY????
EPISODE
Cikin murya mai mugun mugun sosarai Khaleel yace “Hauwa’u Alhassan Na Sak………!” Dawani mahaukacin sauri Hawwa tashige jikinshi takai duka hannayenta biyu tadaura kan lips dinshi ta taushe bakinshi da duka karfin datake dashi aduniya tana kallon kwayar idanunshi lips dinta nawani irin bari kaman takama da shocking na electricity tana kallonshi hawaye na fita daga idanunta tace “w…….wa……wat……are….yh…u…..trying to tell me”? Daidai hawaye na gangarowa daga idanunta majina daya tsinke sosai nafitowa daga hancinta wani irin automatic gumi na ketowa daga goshinta tana kallon Khaleel dake mata wani irin kallo kawai ya kabar da hannuwanta saida Hawwa tai tangal tangal tai baya kaman zata fadi ta dafe mota, Khaleel yanunata da hannu kirjinshi nawani kalan beating yabude baki zaiyi magana azuciye saikuma idanunshi suka shiga juyawa dawani irin sauri Hawwa tace “Khale….!” Kafin tai kanshi yayi luuuuuuu zai zube Salman yayi wani jumping yatareshi yana jijjigashi, Hawwa tazo dagudu zata tabashi strictly Salman yace “you are not allowed to touch Yallabai! Babu relationship daya rage tsakanin ku kuma! I’m sure he made that crystal clear” kafin Hawwa tamayi wani abu Salman yadaga Khaleel chak yayi wajen mota dashi Hawwa jitayi kaman ana daddatse mata ruwan da naman jikinta da kyar da dafa mota ta tashi ta tahozatai wajen motan Khaleel but har Salman yaja mota sunbar wajen. Hannu Hawwa tadaura akai tafashe da kuka sosai sai kallonta ake daidai wasu yan sanda na shigowa plaza guda biyu sanye da uniform, da kyar ta iya tashi tamusu bayani yar sanda ce ita office number nata da ID number nata, tace fada sukayi daya ya suma an tafi dashi cus bataso Khaleel yashiga trouble tace daya kuma gashi amotanta, sannan tazo tabude musu baya suka tayata daukan Baban Yaseer suka sashi a motansu suka tafi dashi taciro kudi masu yawa tabasu tace “please take care of the payment, I know him he’s a family friend” ganin kudi da yawa suka karba suka wuce sannan tawuce da kyar tabude motanta tashiga takai kusan 2min azaune takasa driving sai tashiga addu’a sannan jikinta yarage bari ta kunna motan tana da gudu zuwa asibitinsu tun a parking space take kallon wajen but babu motansu daidai tafito saiga wani baturen Dr tareda Dr ta na ranan zasu shiga mota dasauri tace “is my husband here please”? Atare sukace “they’re taking him home we are going to your house now” faduwa gaban Hawwa yashigayi sosai tajuya tawuce motanta ta kunna su Dr na fita tana binsu abaya har gidansu.
Scanning motan su Dr akayi aka barsu suka wuce direct ita take wucewa ciki ba’a duba nata motan tunda tai aure agidan, but sai taga bayan su Dr sun shiga an rufe gate, security gate yazo wajen motanta hakan yasa ta sauke glass kasa yace “Madam Salman yace Oga yabasa specific order not to let you into his house that aurenku yakare” Security yayi maganan casually no any emotions attach cus this is something dat always happens agidan nan, ana gamawa da mace bazata kara shigowa gidan nan ba kenan har abada, wani kalan faduwa gaban Hawwa yake tabude baki zatai magana taji kuka yazo mata kuma bataso taima security kuka, mutumin yace “I am sorry but I can’t let you go through unless I receive another fresh order, good bye Madam” yayi maganan yana komawa gate abinshi rike da bindigarsa.
Wani kalan sanyi Hawwa keji tundaga tip na fingers nata na toes har zuwa the smallest tiny silin gashin kanta, kaman Organs nata are shutting down haka takeji, kaman ranta da zuciyanta na barin jikinta haka takeji, jikinta na shaking sosai, like is this happening? She has always wanted saki, ita takaishi court da kanta, ita keta demanding ya saketa, but now da kusan ai yama saketan ne toh maybe ya aiko mata da takardan agida, but just gidan nan dataji ance she’s not allowed to enter taji kawai organs nata na shaking cikinta na duri ruwa, wlh kawai taji cikinta na kuka gululuuu wani mahaukacin zawo taji yataso mata, da bala’in sauri ta tada mota tashiga zuba gudu a titi 30min yakaita unguwansu babu kowa a kofar gida kashe motan tayi ko wayanda da purse nata bata iya ta dauka ba da gudun gaske ta shigo gidan saida Umma dake tsakar gida tace “wayyooo waye haka” Hawwa ta sunkuci buta sai bayi Umma tace “Hawwa! Lafiya?” Dasauri Ammi da Baba suka fito daga dakin Hawwa jin ankira Hawwa daidai Hawwa na sakin wani wawan zawo mai karan gaske. “Paratatatttaaaa!” Umma tace “ayya ashe gudawa takeyi haba nifa ince naga yarinya ta shigo a haukace tana gudu!” Hawwa zawo take mai kullewan ciki takai almost 10min abayin tagama komi amman ta tsaya abayin takasa fitowa bata tabaji arayuwanta tana shakkan Baba da Ammi ba kaman yau! Kawai taji Allah yasama zuciyanta wani mahaukacin tsoronsu da batama san ta yaya zatayi ba.
Baba da Ammi na tsaye dan ganin Hawwa a gida sunsha jinin jikinsu barinma labaran komi da Ammi tagama gayamai dan bata boyemai komiba.
Gajiya da tsayuwa Ammi tayi kusan 20mins tace “bacci kikayi abayin ne Hawwa bazaki fitoba”? Fashewa Hawwa tayi da kuka sosai duka jikinta rawa yake da kyar tabude kofa tafito daga Baba har Ammi kwayan idanunta kadai suka kalla sukasan wani abu yafaru Hawwa tai zuru zuru Ammi taga daga jiya data ganta zuwa yanzu har tadan fada,
Baba kawai yajuya fuuu yakoma dakinta cus ayanda yakejin kanshi zai iya daga sandunan nan yama Hawwa dukan da saita suma ya rantse da Allah! Ammi ta tsaya tana kallonta tundaga kan yanda Hawwa bamata iya tafiya da kyau kaman kwan cikinta yafashe Umma ta ijiye shinkafan datake gyarawa takalli Hawwa sannan takalli Ammi dake mata wani kallo tasan wani abu yafaru, Ammi itama tawuce takoma daki Hawwa kawai saita taho wajen Umma tafashema Umma da kuka tace “Umma ki taimakeni Ammi da Baba na fushi dani Umma” wlh ba karamin tausayi Hawwa tabama Umma ba har zafi jikin yarinyar yayi dudda batasan meke faruwa ba amman tasa hannu ta gogemata fuska tace “ya isa daina kuka komi yayi zafi maganinsa Allah, suna jiranki wuce muje” Umma takama hannunta yanda Hawwa ke tafiya ko da wani zai shigo gidan da baisan meke faruwa ba dariya zaiyi kaman wacce ke shirin guduwa Umma tabude dakin tana rikeda hannun Hawwa tace “Assalamu Alaykum” tashiga shigo da Hawwa dataki shigowa Ammi cikin fushi tace “saketa Umma tagudu taje duk inda zata ai tasan metayi” dasauri Umma takalli Hawwa tace “ki shigo ki zauna anan ayi magana Hawwa asan me ake ciki baki da wayanda sukafi Babanki da Mamanki, koma menene dai kinsan bazasu kasheki ba shigo”
Umma tashigo da ita yanda jikin Hawwa ke rawa Baba dake gaban kujeran kwalliyan Hawwa ke kallo, Ammi na zaune kan katıfa dukansu suna kada kafa, Hawwa tazo ta duka a tsakiyan dakin tai kneeling kanta akasa Umma tajuya zata fice Ammi tace “ki dawo Umma ki zauna diyarki ce rannan wanka ba’a boye cibiya she brought this upon herself kafin na sanar dake duka abubuwan da Hawwa ketayi tun bayan aure raina yariga yabani cewa wani abu yafaru dahar tazo gidan nan da safiyan Allahn nan” Ammi takalli Hawwa tace “Hawwa me kikayi? Meya kawoki gidan nan?” Har wani kalan ijiyan zuciya Hawwa ke saukewa tana kakkama riganta tana cin baki takasa magana kaganta kaman kamata kuka, Baba yawani buga karfenshi akasa da katuwan muryan nan kaman zai daga anguwan yace “badake ake magana ba” Wlh Hawwa jitayi kaman zuciyanta zai fito ta baki sabida ihun da Baba yamata, cikin muryan rudewa tace “yace yarabu dani karna sake dawowa gidansa, nakoma gidan security sun hanani shiga wai Oga yace kada akara barina nashigo!”
Daga Baba har Ammi kallon Hawwa suke babu wanda ya iya magana cikinsu Umma ce tai dauriya tace “Hawwa me kikama Ibrahima dazai koreki? Meya hadaku!”? Tana rirrike riganta tana sosa cinya tace “da…..da gari yawaye nacemai zanzo wajen Ammi yace toh saina fito toh…uhmm” wlh Hawwa takasa contructing good sentence tsabagen tashin hankali and fear tadan kalli Ammi dataga tana kallonta, takalli Baba dataga yana kallonta shima sai kawai tayi rarrafe taje wajen Umma tarike Umma gam tace “shine nabiya KFC nasai abinci ina fitowa zan shiga mota sai naji anamin magana abaya najuyo naga Baban Yaseer ne!” Sosai suke kallonta arude tace “dama shekaran jiya danaje kotu naganshi………” Hawwa tafadi komi daya faru ba karya har zuwa wajen da ta taushe bakin Khaleel dasu bindiga matter, Baba kawai ya zabura yadaga karfenshi yayo kan Hawwa gadan gadan, Hawwa ta kwala ihu ta tashi ta rike Umma sosai tace “Umma ki taimakeni Umma wayyoo Allah na, Ammiii” Ammi tai maza ta tashi tashiga gaban Baba tace “Malam banda duka, nima kaman na kasheta nakeji amman dubi hannunka karfe ne idan akwai abu a jikinta kuma fa wani abu yasameta iyye? Idan rai yabaci kar hankali ya gushe Malam”
Baba na kumfan rai yace “Zainabu ku banni na hallaka yarinyar nan nahuta! Anya y’ata ce Hawwa kuwa? Anya ba’a chanxamin yarinya a asibiti ba kuwa? Wlh bata dauko halina ba! Bata dauko halin mahaifiyarta ba!”.
EPISODE
Baba nama Ammi ihu data taresa cikin bacin rai yace “Mijinta zata sama bindiga akai sabida wani katon banza da wofi iyye hauka Hawwa zatayi ne? Akwai wanda yafi mijinki daraja da kima da iko awajenki ne?Bakison aure kinfi son zaman gida? Billahillazi yaron nan ya sakeki idan kin zauna a gidana Allah ya tsinan albarka saidai kije kiyi zaman kanki koki shiga duniya, shegiyan yarinyar mai zuciyan arna! Ni ku banni na mammake tambadaddiyar konaji dadi” Baba yayi kanta Hawwa tasaki Umma tahau gado taje chan karshe tana kuka cus Baba can injure her ayanda ranshi yabaci, sosai Umma da Ammi suka rike Baba dake nishi kaman zai mutu sabida bakin cikin Hawwa, muryanshi har rawa yake yana shaking irin na wayanda suka tsufa din nan yace “da aurenki ki bude baki kina cewa mijinki eh kinason wani sabida ke sokuwa ce, katuwar banza ko Miemie autan gidan nan bazatai kalan sokoncin nan ba, eh mijinki da babu abinda baya miki, kullum tsakaninki dashi saidai kice kin tsaneshi eh, Hawwa ni zaki tozarta ki ciwa mutunci? Ni zaki zubama toka a idanu? Sabida kinga yaro na sonki yana bibiyanki kaman wata sarauniyan mata shine kika sami waje kina shuka iskanci kinama yaro kaman kece uwarsa harda zagin iyayensa, kai wlh idan ban kashe yarinyarvnan ba bazanji dadi ba” Baba ya fizge hannunshi zaihau gadon Umma takama Baba dasauri tayi ihuuu sosai tace “Malam dan Allah, dan Allah kayakuri, Malam kayakuri ka zuciya dayawa, Malam idan tana dauke da juna biyu fa iyye? Baka daki Hawwa da ba sai yanzu? Dan Allah Dan Allah Malam kayakuri”kirjinshi Baba ya daka yace “kinsan me Hawwa tayi kuwa? Zan iya kara kallon yaron nan kuwa? Dan ubanta batasan kishi yake ba yasa yake dukan watsastsen makirin yaron nan Aliyu, idan tahanashi yaki hanuwa meya hanata kama mijin nata kaman yanda kika kamani yanzu eh? Miyahanata yin haka? Amman saidai kisamai bindiga aka kice zaki harbesa akan wani katon banza ke gaki yar sanda, to bari kiji na rantse da Allah dagayau baki ba aikin yar sandan! Kika kara zuwa wannan aikin ban yafemiki ba Hauwa’u! Abarma maza aikin, kaico! Nagama jin haushin Ni’ima yau da raina Allah ya nunamin tawa diyar zata iya abinda yafi na Ni’ima ban kunya tir da hali irin naki, Hawwa yau naji takaicin da kika kasance diyata!” Ya fizge jikinshi daga Umma yajuya yafita kai Baba ya zuciya bakadan ba, Hawwa ta taho wajen Ammi tana kuka sosai ganin Baba yafita tace “Ammi dan Allah kuyakuri wlh na rantse bazan kara abinda nayib……” hannu Ammi tasa takaimata mari bataso tacigaba da marinta hakan yasa takalli Umma tace “bani dorina!” Umma zatai magana Ammi tace “bani dorina nace Umma banson wani magana” Ammi takalli Hawwa dake wani kalan kukan ban tausayi tace “zamanin mu duk girman mu iyayenmu na cin kaniyan mu idan munyi kuskure ko bayan mun haifi yara goma, ban bari Babanki yadakeki ba sabida namiji ne shi karfe yadaga but that doesn’t mean ni bazan hukuntaki ba, Hawwa magana da wa’azi basa aiki akanki ko? You feel kaman kin girma you are out of reach ko? Zakici gidanku” daidai Umma na shigowa rike dawata yar karaman dorina karama
Hawwa tazabura zata gudu Ammi tawani riketa duk karfin Hawwa takasa guduwa, hannayenta biyu Ammi takama tahada ta zubamusu dorina tace “hannayen nan dakike dukan mijinki dasu kina dauramai bindiga aka duk randa kika sake attempting yi wannan bulallan zaisa kituna mahaifiyarki ta taba hukuntaki akan haka” Ammi ta shauda mata guda biyu a hannun masu kyau Hawwa nawani irin kuka cus sun shigeta dorinar da zafi, Ammi ta saki hannunwan da gudu Hawwa tai baya zata gudu Ammi kawai tarike kafafunta gam ta hadesu Hawwa takai hannuwan takama hannun Ammi dake rike da dorinan tace “Ammi kiyakuri, baki taba dukana ba ko Baba bai taba dukana ba dan Allah kiyakuri, wlh zafi Ammi dan Allah” fizge hannunta tayi Ammi ta zubamata bulala biyu akafafu tace “this is for saka kafafun nan a hanya kifice daga gidanki batare da izinin mijinki ba next time idan zakiyi haka remember this” Ammi tasaki kafan kawai Hawwa taga Ammi tarike fuskanta dasauri takulle bakinta cus tasan next thing is her mouth, Ammi tace “ai baki isa release bakin dayafi iya rashin kunya da zage zage da maganganu marasa dadi, saki bakin nan!” sakin bakin Hawwa tayi ta tsorata da Ammi sosai, Ammi babu tausayi ko wani abu ta kaima bakinta duka mai kyau da lafiya saiga jini a lips nata cus sun datse da hakoranta Ammi tace “good jinin dama nakeso ya zuba, stupid girl mara tarbiya mai bama iyayenta kunya, mai zagi da dukan mijinta” Ammi ta yarda dorinan akasa tajuya tafita daga dakin itama fuuuu Umma tawuce wajen Hawwa data rungumeta sosai tana kuka tana bata hakuri tana mata kuma fada.
Azaure Ammi taga Baba yazauna flat akan simenti ya yarda sandanshi a gefe yabuga tagumi idanunshi sunyi jaaa gwanin ban tausayi ahankali Ammi ta zauna kan kujeran wajen tace “kayakuri Malam na zaneta yanzun nan kafin nazo nan nahukun tata, dan Allah kayakuri yanzu yaza’ayi bazamu barta anan ba, muka barta mun nuna munyi supporting bad dabi’unta ne hakan ba halinta dattaku bane” Muryan Baba yayi rauni yace “Zainabu kunyan Ibrahima nakeyi Zainabu kinsan yanda yaron nan ke sona kuwa”? Baba yayi shiru saikuma ya matse hawaye yace “na gayamiki ai yakawomin takardun babban gida ya sayamin nakoma ciki nacemai a’a bazan taba barin gidan nan nawa ba har abada, Zainabu na gayamiki yakawomin katuwar mota da driver dazai dunga kaini duk inda nakeso wlh naki amsa nagayamai badan kudinsa nake sonsa ba and sabida ya auri yarinyata basaiyamin abubuwa ba, namai tatas naki amsa, na nunamai idan yacigaba yanamin irin abubuwan nan zan batarai dashi, Zainabu still yakara zuwan mini da maganan zai kaimu aikin Hajji dukanmu da yaranmu, daganan yanaso yawuce dani turkey amin aiki asamin kafan karfe nadinga tafiya da kaina batare dana amfani da karafunan nan ba, wannan ne kadai maganan Khaleel dana aminta na yarda ko jiya saida yagayamin zai aiko ranan asabar har gida azo amana passport nakira su Hafsa dasu Aminu da ke dasu Ramla duk suzo gida amana baimasan zakizo Abuja jiyan ba a asibiti yakemin magana” Baba yayi shiru yasake share hawaye yace “Zainabu kunyan Ibrahima nake yaron daya girmamani ya daukeni tamkar ubansa, yayi kuka ajikina yarikeni, Ibrahima baitabamin kallo kaman baban matarsa ba saidai mahaifinsa, Hawwa tarasa wanda zata ciwa mutunci sai shi, dakuma iyayensa, nima ai