Showing 36001 words to 39000 words out of 184554 words

Chapter 13 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1884

zuwa akwatin nata tadauki dogon riga na bacci tasaka ta zare zanin wankan ta shanya ta dawo gadon tahau ta daura kanta kan cinyan Ammi tareda sauke ijiyan zuciya tabude watsapp tama Ni’ima chat “Just got to Ammi’s place, Ni’ima why did you send Baban Yaseer? Why” tura chat din tayi taga yayi layi biyu alamun datan ta a kunne amman ba’a budeba jira tayi ta amsata but shiru ijiye wayan tayi ahankali tana lumshe ido kafin kaceme bacci yayi awon gaba da ita dan tagaji yau.

Yanda bacci ya shigeta yasa Ammi bata tadataba ta shiga dakin yammatan ta su biyu Amina da Ramla ta tadasu don salla itama tayi sannan tasa suka shiga kitchen cus taji Baban Yaseer yafice salla.

Wuraren 7 yashigo gidan a tsakar gida yaga Ammi tareda Ramla datake gwadama yanda ake buga kosai sun hada gawayi dan basu soya kosai a gas, ganinshi yasa Ramla tace “ina kwana Baban Yaseer” murmushi yamata yace “lpy lau” yace “ina kwana Ammi” murmushi tamai tace “an tashi lpy sannu da kokari fa Aliyu, Allah ya maka albarka, bari yanzun nan zan kawoma kosai nariga an dama kamu saina kawoma kayi karo kafin kashiga hanya” girgixakai yayi yace “no Ammi bazanyi kari ba bana kari da wuri yan sanda na barma motana chan hanyan kaduna dole nafita yanzu Ammi” yayi maganan yana ciro kudi daga aljihunsa daya samo a ATM fitan nan nasa a kujeran tsakar gida dake gefen Ammi ya ijiye kudin yace “aba Hawwa idan ta tashi, wannan kuma aba su mai girki” cus baisan sunan Ramla ba, hade fuska Ammi tayi tace “kaga dauki kudaden nan karna saba maka Baban Yaseer” dasauri yajuya yayi gate yace “Ammi nagode” yafice dasauri dudda har ranshi yaso yaga Hawwa kuma sarai ta tashi tun dazu har salla ma tayi kawai bataso ta ganshi ne kawai yasa bata fitoba, tanajin fitanshi tafito falo Amina dake gyaran falo na ganinta tai ihu sosai “Ramla Ya Hawwa ta tashi” tawani zo dagudu tai tsalle tafada jikinta Hawwa tai dariya sosai Ramla tasaki kosan datake ta rugo dakin aguje itama tai tsalle kawai Hawwa tai kasa suna kanta, Ammi ta shigo dakin ta kwadamusu duka abaya tace “Oya ku dagamin ita bance ku karyamin diya ba” kankamesu Hawwa tayi tace “Ammi I missed my babies” hararansu Ammi tayi tawucewarta tafito tashiga soya kosan da kanta tunda taga shirme suke Hawwa tafito tareda su tana Ammi wai ina su Hamza da Ahmadu? “Hamza na school, Ahmadu yace anjima zaizo da matarsa su gaidake, Baffan ku na dayan gidan sai gobe zai dawo nan amman hala anjima ki gansa” murmushi tayi ta karbi kosan tana soyawa su Ramla nabata labari she looks so happy Ammi tayi murmushi ganin ayanda idanunta sukadan kumbura jiya sabida kuka sun sauka sosai yanzu kaman batayiba.

Wuraren 12 Ni’ima taji ana bude gate, tunda tasan Hawwa bata taba taga miss call na Hawwa taki kiranta back ba sai yau, nor tai replying message nata, jiya tamata message shiru, da safen nan takirata sau biyu ba amsa sai tamata magana tace “call me idan kin dawo daga hospital Best, su Ramla nata tambayanki”.

Jin ana bude gate yasa ta tashi dagakan kujeran tawuce da sauri tashiga kitchen, ita kadaine agidan su Yaseer na school sai though 1 suke tashi on Friday, sallama taji yayo yashigo abu kawai taji yatokare mata zuciya tama kasa amsa sallaman, kofan bedroom nasu taji yabude ya shiga sannan tasauke ijiyan zuciya tashiga fito da flasks da plates tana ijiyewa a dinning tazauna a dinning din saikuma chan tamike tawuce bedroom din nasu ta zauna bakin gado tanajin karan zubam ruwa ba’a wani jimaba yafito daure da towel a waist yadan kalleta hada idanu sukayi tana kallonshi kaman yau tafara ganinshi dauke kai yayi da sauri yawuce wajen wardrobe nasu yace “wife ya gida? Su Yaseer basu dawo daga school ba”? Tana kallonshi kaman gunki tace “basu dawo ba tukunna” gyadamata kai yayi ya tsaya gaban mirror yadau mai yana shafawa yakasa wani maganan, kalulu ta hadiye a wuya tadan bude bakinta kadan saikuma tarufe sai chan kuma tace “ka kuwa sanar da Hawwa kana sonta?!” Dum! Haka maganan yadaki kunnenshi man daya diba zaikai jikinshi yashafa kasa shafawa yayi yajuyo yakalleta suka hada ido yace “wace irin magana haka kikeyi Ni’ima”? Mikewa tayi a fusace ta nunashi da hannu tace “don’t you dare lie to me, nasan son Hawwa kawata kake why are you hiding it? Eh maisa kake boyewa bayan ka kamu da mugun sonta” hade giran sama dana kasa yayi yadan dafe kanshi yace “kinsan mene? I don’t want your drama this afternoon I had a long journey I just want to sleep peacefully, dan Allah ki kyaleni I don’t know wat you are talking about” yajuya zai wuce yanda abu kecin zuciyan Ni’ima batasan sanda tai ihu ba tace “Namiji munafuki, namiji mara amana, namiji butulu! Aliyu I know everything! I know about hotunan Hawwa dake wayana da duk ka sace suna wayanka, I know kana stalking friend dina kana biye biyenta kana mata hotuna without her knowledge, how dare you kana karyata cewa sonta kake don’t be a coward, kaji be a man for once mayaudari kawai” “Ni’eematullah!” Baban Yaseer yakirata azafafe idanunshi sun kada sunyi ja, yace “yes yes yes I love Hawwa! Yes inason kawarki! Yes I love your best friend Ni’ima and so what!?” Hannu Ni’ima takai tadaura kan bakinta tana kallonshi completely heart broken hawaye masu jarababben zafi na saukowa daga idanunta, yace “do you think I’m happy with the fact that I’ve fallen in love with your friend? Kin dauka choice dina ne? Kokin dauka son Hawwa ya tambayi izinina? Why are you insulting me calling me names mena miki? Tayaya na yaudareki? Kinga na sanar da ita ina sonta ne? Ko kinga nayi wani abu ne? I love Hawwa yes and I also love you! Sabida I don’t wanna hurt you saisa all this years ban auri Hawwa ba, I can’t bring kaina into to hurting u that much, nasan yanda zakiji, I know wat kishi is! Yes I love Hawwa, and I also love Ni’ima, nima I don’t know mesa Allah zai dauramin soyayyan kawaye biyu kuma best friends, I know this same reaction kikeyi maybe na gayama Hawwa ina sonta zatamin more than yours, so just let me be, ban miki komiba ban yaudareki ba, and bance zan auri Hawwa ba cus nasan bazata yardaba, but all I know is harna mutu bazan taba daina son Hawwa ba, son danake mata yawuce tunani na, when it comes to Hawwa banmasan me nakeyi ba, I just want her to always be happy, I want to protect her, and always be there for her and make her happy, that’s just it” yayi maganan yana komawa wardrobe yadauki kayan dazaisa yafice daga dakin, Ni’ima tafashe da kuka bana wasaba gwanin ban tausayi tana zubewa akasan dakin…….

TOH JAMA’A IMAGINE MIJINKI NA SON BEST FRIEND DINKI, YAYA ZAKIJI???

HOW WOULD YOU HANDLE THE SITUATION???

KAI YAYA ZAKIYI NE????

IDAN KECE NI’IMA MEZAKAYI KO YAYA ZAKIYI DA HAWWA???

THINK AND TELL ME

EPISODE

Ni’ima kuka kawai take bana wasaba, tana ganin tunda aka haifeta bata taba feeling wannan kalan zafin da zuciyanta kemata yauba, for years sunyi aure itada Baban Yaseer basu taba having issues ba like babban issue haka, batada wani complain akanshi but yau yayi hurting nata kwarai, kalan soyayyan datagani a idanun Aliyu ko ita baitaba mata shi ba, duk soyayyan dazaisa kafara stalking mace kana bibiyan hotunanta harda na kusan tsiraici ma dan kayan bacci ne ba karaman soyayya bane, soyayya ce ma dakana bukatan kaga therapist, he is sickly in love with Hawwa that’s idan akwai word din, ciwon son Hawwa yake, yanzu Hawwan ta Baban Yaseer zaiso? They’ve been through so much together with Hawwa, Hawwa is her biggest support bazata taba manta sanda Hawwa tasayo mata form na school of Nursing takawo mata ba, sabida lokacin Babanta baida lpy basuda kudin daza’a saimata form agida haka Hawwa tadinga dinki tahada kudin tasayo mata form 5k takawo mata that day was the happiest day of her life, Hawwa tarakata taje tai entrance exam na shiga school of nursing din, dataci Hawwa was happier than her ma datai jarabawan, bayan 2days aka kirata zuwa interview still Hawwa tabita sukaje tajirata awajen tayi tafito suka tafi gida dagabaya aka saki admission taci an bata admission, babu kudin registration Hawwa tadinga dinki day and night, tasaida babban wayanta alokacin tasa sim nata akaramin waya takawo mata 30k itama Maman Ni’ima tasaida sarkanta da dankunne aka hada 20k daga wajenta aka hada mata taje tai registration da 50k, the first ever book da pen datai rubutu dashi a school of nursing Hawwa ta siyamata su, hawaye ta share tana tuna rayuwansu da Hawwa duk yanda mutum zaiyi tunanin friendship, kawancenta dana Hawwa yawuce haka, sabida kawance ne mai asalin amana, Hawwa harda Maman Ni’ima take fada akanta just like yanda take fada da Baba akan Hawwa tanajin haushinsa kan Hawwa haka sukema junansu wajen iyayensu, they supported each other like better half, kawance su babu ha’inci, babu kyashi ko rowa, babu bakinciki, they’re always happy for each other, dudda tayi aure Hawwa bata taba mata bakincikin wani abuba, datana da ciki wlh wlh ko Baban Yaseer mai cikin baikai Hawwa kula da ita ba, idan tana craving wani abu Hawwa zata iya barin aiki taje ta nemo takawo mata, yanzu haka yaranta su Yaseer sun fison Hawwa kan mahaifiyarta grandmother su sabida aminci da kaunan dake tsakaninsu, she’s just crying bitterly bamatasan ina zata saka kanta ba, kawai taji ta bama kanta tausayi bamatasan inda zatasa kanta ba wannan wani irin intertwine situation ne haka? Wani irin kaddara ne wannan? Ita da Hawwa started friendship ana maganan tun suna around 6yrs old cus primary one suka hadu, yanzu suna 30yrs, 20yrs plus friendship kifa kanta tayi akafanta tana shesheka tajiyoshi an budemai gate yafita tasan mosque zashi yau juma’a.

**

Har yamma na rannan Friday din nan shiru ba kiran Ni’ima which is so unlike her, dudda su Ramla dake damunta da labarai but still binibini Hawwa na duba wayanta ko Ni’ima tamata watsapp message ko kira ko wani abun amman shiru, tasake kira but still ba amsa dan damunta abin yafarayi sosai.

Bayan sallan magrib suna zaune sunacin abinci duka tare harda Hamza wayan Ammi yahau ringing wayan ta kalla taga Baba ne hakan yasa tadauki wayan tafito daga dakin dan bataso yaran especially su Ramla susan maisa Hawwa tazo tawuce ta shiga side nasu Hamza zama tayi kan katifarsu tayi dialing number Baban ringing daya yadaga ya buga mata sallama yace “ya wajen naku Rukayya” Ammi tace “Alhamdulillah” ijiyan zuciya Baba yasauke yace “Baban Yaseer ya sanar dani Hawwa na wajenki kice mata ni ban koreta ba ta tattaro tadawo gidan nan” anatse Ammi tace “sabida kacigaba da tallatata a masallaci kana neman kai da ita” dan shiru Baba yayi saikuma chan yace “kinga Rukayya ni ba kira nayi fada dake nayi ba, tun fadanmu na farko bayan rasuwan mahaifiyan yarinyar nan kikaso tafiya da ita nace a’a kika dinga bala’i dani nasan ba kaunata kikeba da akwai yanda zakiyi ma da rabani zakiyi da yarinyar, ni duk wannan ba itace matsalata ba kawaidai kice mata tadawo gida kar fushina yabita” dan sauke ijiyan zuciya Ammi tayi tace “yarinyar nan kawai sabida kaine mahaifinta saisa muka barmaka, wlh na sanar da Baffan ta saidai duk abinda zai faru yafaru, aure na Allah ne ba nakaba, da iyaye ke aurar da yara da tuni kowa yayi, Allah shine komi ke hannunsa, kaida yakamata ka godema Allah dayabaka irin wannan yarinya a’a sai tsalle tsalle kake” katse wayan Baba yayi danshi dama da Ammi basa jituwa kona sakan daya.

Around 8 nadare Hawwa taga Ni’ima na online ta karanta duka messeges nata amman bata kulata ba, watsapp call ta danna mata but harya katse bata dauka ba abin ya bala’in damunta voice note ta danna tace “Ni’imyyyyy sorry please kidena fushi, wlh I know kema na sanar dake abinda yafaru ni da Baba you will not be happy with abinda yayi, banson na tadamiki da hankali koki hanani zuwa wajen Ammi saisa ban sanar dake ba sorry, ina Yass dina da Meen” ta aika mata voice note din tarike wayan tana kallo ganin yaje but still ba asaurara ba kuma tana online abin yafara damun Hawwa sosai bahaka Ni’ima ke fushi da ita ba saidai tai masifa dukansu basu iya gababa saidai suyi fada ayi zage zage da baki a shirya, dukji tayi ba dadi haka ta tasa wayan agaba tana kallo kusan 20min kuma tana online chan saita sauka ijiye wayan Hawwa tayi ta kwanta kan gadon Ammi tana sauke ijiyan zuciya.

Yau Saturday Baffa (mijin Ammi) na gidan tun goma dayazo baibarta tahuta ba da labarai da surutai dan yana mutuwan son Hawwa, tana yawan turamai kudi akai akai kaman yanda takema Ammi ta, surutunsa yasa tadan manta da damuwanta sai dare kuma tashiga kiran Ni’ima harsaida Ammi talura tace “banji kinyi waya da Ni’ima tunda kikazo ba da tuni tace abani waya tai magana dani, Ni’ima dana sani da saita kawo karinki kin shiga hanya da daddare” dan murmushi Hawwa tayi tace “tana hospital ne Ammi shift take covering, chatting mukafiyi this days Ammi” dan murmushi kawai Ammi tayi bata sake magana ba tace “bari nakaima Baffan ku shayi” tafice.

Washegari Sunday around 11 tafito su Hamza na samata komi a booth, Baffa yace “Hawwa ayi tuki ahankali kinjini” murmushi tayi tace “toh Baffa na” Ammi tace “Allah kiyaye hanya, dan Allah banda gudu” Gyadamata kai Hawwa tayi su Ramla suka rungumeta tamusu sallama tafito, text tama Ni’ima tace “gani nashiga hanya zan dawo office gobe”.

Karfe biyu dawani abu anadai neman karfe uku Hawwa ta shigo Abuja hanyan hospital din su Ni’ima tawuce direct ta shiga tai parking ta kashe motan, wayanta tadauka tafito abayane ajikinta baki tawuce ciki office din Ni’ima tawuce tareda knocking tana budewa wata nurse ce aciki tana ganin Hawwa tai murmushi tace “wajen Ni’ima kikezo? Bakuyi wayaba ai batanan yau is her off” amutunce Hawwa tace “okay okay nagode” tajuyo tafito motanta tashiga tafita daga hospital din wlh she’s so worried rabon datai magana da Ni’ima tun Friday wani irin fushi Ni’ima keyi da ita haka, hanyar gidansu Ni’ima tayi har zuwa layinsu mai kyau, gaban gidansu ta tsaya tai horn maidaidaicin gidane mai kyau ga babban bakin gate nasu, lekowa mai gadin yayi Hawwa tadanmai murmushi tana jiran taga yabude gate saitaga yabude karamin gate da fara’a kan fuskanshi yace “Hajiya barka da yamma” gyadamai kai tayi tace “ya kuke” yace “Alhamdulillah” saikuma ya tsaya sakaka yana kallonta Hawwa tace “budemin gate ko basanan ne”? Bazai taba iya maimaita abinda Ni’ima tacemai ma hakan yasa dasauri yace “eh basanan tun safe suka fita” danjimm Hawwa tayi kaman daga sama sukaji muryan Yasmeen ta tsandala ihu tana kuka wayyo kafanta dasauri maigadin yakalli gate saikuma yajuyo yasauke kanshi kasa, Hawwa dake juyo muryan yaran tace “kace basanan ba muryan Mims naji na kuka ba” dan sosa kai yayi da hannu kanshi na kasa yakasa kallonta yace “ahhhmm Madam tacemini duk randa nakara barinki kika shiga gidan abakin aikina kiyakuri Hajiya” dasauri da kunya yajuya ya shiga gidan tareda maida gate din yarufe Hawwa tai shiru tana wajen she don’t even know wat to think, her mind just went blank wlh takai minti ashirin awajen kafin tadan fuzar da iska taja motan tabar wajen.

EPISODE

Batason ta shiga gidan da force, she knows Ni’ima, ba hakanan zatabada sakon nan ba, she have to respect her home, layinsu ta wuce duka zuciyanta ba dadi harzuwa gida tundaga nesa da Baba yahango motanta yamike tsaye yana murmushi hankalinshi ya bala’in kwanta, tana parking ya hade fuska kaman bashi ke murmushi ba ganin tadawo, kashe motan Hawwa tayi tafito batare data kalli inda Baba yakeba dan yanzu saidai su dinga bura’uba da Baba amman bata auren mutumin nan wlh, Booth tabude tasauko da akwatinta kasa ta goya na baya tarufe motan ta gunguro jakan daidai tazo inda Baba yake batare data kalleshi ba murya ciki ciki irin na yaron dake fushi da iyayenshi din nan tace “Assalamu Alaykum Baba ina yini” dan kyafkyafta idanu Baba yayi yace “sannu uwar zuciya ladingo mai fada da mahaifinta, sannu da zuwa jeki huta ni da kene agidan nan” wucewa tayi abinta tana shiga gidan suka hada idanu da Umma data haderai ganinta kaman bakin ciki zai kasheta tadauke kai itama haka Hawwa tawuce tabude dakinta ta shiga da komi, kayan jikinta tarage tafito tai alwala takoma daki tai salla sannan ta kwanta akasan tadauki wayanta tashiga kiran Ni’ima koma menene they need to iron it out, tabama Ni’ima sama da 15missed call babu wanda tadaga, bala’in damun Hawwa abin yake, she’s confuse ma, basu taba kalan fadan nan ba itada Ni’ima, Ni’ima bata iya gaba ba nor shariya, toh wat is happening da Ni’ima is not talking to her? Whatsapp tashiga tashiga typing.

“Best enough please, talk to me Dan girman Allah, I’ve been saying sorry amman kinki kulani, daman akwai abinda zanyi da u will not understand me? Baba ne yace nabarmai gidafa, I’m sorry ban sanar dake ba naje gidan Ammi, banson kice nazo wajenki ne kuyita dawainiya dani, naje hospital yau ina shigowa garin nan bakinan nazo gidanki i learned that u don’t wanna see me, I’m very very worried, Best I’m sorry, sorry, sorry” Hawwa tashiga tura mata sorry sunfi guda dari cus ta bala’in damu sabida Ni’ima is already part of her, this few days dabasuyi magana ba ko chatting she’s feeling kaman wani part of her is gone, duk uban sorry nan amman har 8 nadare Ni’ima bata bude chats din ba, ashe harda gidan Ammi kesa abin baiwani dameta ba amman yanzu data dawo nan ita kadai sai Hawwa tashiga bala’in damuwa, sai tunane tunane take, taba cracking what could make Ni’ima this angry?

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login