Showing 60001 words to 63000 words out of 184554 words

Chapter 21 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1880

tace “kisa sakata a kofa kada ki bude sai Malam ya shigo” dasauri Ramla tace “ita ta isa ta tabani wlh saina mata tsinannen duka Ammi” Ammi tace “ke!” Dasauri tace “yakuri naji zansa sakatan Ammi”.

Adai area nan nasu duk wanda yasan Hawwa yasan Ni’ima duk wanda yasan Ni’ima yasan Hawwa, Mama na zaune a tsakar gida da Ni’ima daketa bambami tunda tazo gidan Mama dazu akai sallama aka shigo gidan matan makotansu ne suka shigo yima Mama Allah sanya alheri ganin Ni’ima ma azaune a compound din yasa sukace. “Ayiririri ga Babban kawan Amarya, yoo ba dole aganki yau ba ana daura auren kawarki labari yabaza gari anachan ana rabon kudi” daga Mama har Ni’ima confusion look suke musu ita Ni’ima ma bata magana Mama da gabanta yashiga fadi tace “wace kawar Ni’ima kuke magana akai Jamila?” Dasauri Jamilan tace “kaji Maman Ni’ima kuma, tsufa kika farayi ne? Ni’ima nada wata kawa data wuce Hawwa ne? Hawwa yar sanda mana yar wajen Baba gurgu muke magana gashichan an daura aure ana biki a unguwansu sai tafiya ake layin nasu” atare daga Mama har Ni’ima suka kalli juna Ni’ima tabuga wani ihu tana mikewa tana daura hannu aka. “Wayyooo na shiga uku na lalace, na bani, Mama na bani” dan duk atunaninta Baba ya aurama Baban Yaseer Hawwa tunda tamusu rashin mutunci dazu, ahaukace Mama taja hijabi daga igiya tace “sa hijabi Ni’ima muje zama bata ganmu ba, dena ihu kidau makullin mota sabida muyi sauri” su Jamila da mamaki da confusion suke kallonsu Hijabi Ni’ima tasaka ko silipas bata tsaya sawa ba suka wuce su Jamila suka fice daga gidan babu zancen kulle gidan ma ta shiga mota Mama ma na shiga suna tada aiko Samari sai gudu suke kaman ranan idi ana tafita layin koda sukakai tundaga bakin titi an cika tap parking motan tayi agaban wani pharmacy suka fito da karfin yaji da balam bala’i suka shiga kutsawa cikin mutane har zuwa cikin layin daga inda security suke tsaitsaye da bindigogi suma suka tsaya suna kallon Baba tare da wasu manyan mutane suna magana suna gaisawa, sosai Ni’ima ke kallon fuskan kowa one by one bataga wanda tasani ba chan idanunta ya yasauka kan Khaleel da she’s sure shine wanda tagani dazu daidai wasu gayu dake tsaye dasu sunahau gisting.

“Kai Baaba shinefa yaron Senate President shi kadai mutumin ya haifa, just farkon shekaran nan Forbes sukace baban shine number 5 richest man in the whole world, wai bakasan Mangal BeWeeCee ba?” Daga Mama har Ni’ima dakejin hiran faduwa gabansu yashigayi cikin karaman murya Mama na whispering tace “ke Ni’ima ba Baban Yaseer ta aura ba kinaji ana maganan Alai Mangal” daidai lokacin gayun dame bada labari yace “sadakinta Miliyan Hamsim da Darhamin gwal dari fa kai Baba gurgu da yarsa sun gama da talauci har abada, talauci bye bye” sake faduwa sosai gaban Ni’ima yayi, daga motan Baban Yaseer har gidan nasu da dan albashinsa 350k networth dinshi gabaki daya baikai sadakin Hawwa bama Innalillahi wa Innailaihi raji’un.

Gayun sukace. “Mangal din fa yabama masallaci miliyan dari a gyara, sannan yabama anguwan miliyan dari wai arabama kowa babba da yaro, tsoho da tsowuha sabida sun bama dansa yarsu, kai Baaba yauna kara yarda wani jinkirin alhairi ne, yaushe su Gwaggo suka gama Gulmanta agidanmu ranan da safe kan Hawwa ce kadai yarda batai aure a unguwan nan ba Kannin kannenta sunyi aure amman gashi yau dalilinta kalli anguwan mu yatashi da miliyan dubu dari biyu ba in total, Allah kaimana arziki!” Sake faduwa sosai gaban Niiima yayi yana wani jigijim! Jimdum! Dumjum! Dumdum! Lankwashewa kafafun Ni’ima yayi tai baya zata fadi Mama ta tareta tana salati sun shiga shock, dasauri Mama tace “kinga gobe zanje asibitin nabama su Baba hakuri da Hawwan Ni’ima, kokin hanani billahilazi sainaje, nine mahaifiyar babban aminiyan Amarya ko miliyan goma Alhaji Mangal yabani mena manta tuni zanja jari, 

jari, gobe da safiyan Allah zani ko asibiti ko nan gıda duk inda suke! Allah yasa banwani mata magana mara dadi ba kuma nasan ba lallai tafadi ma tazo wajena ba, gobe zanje na sasanta komi na shiryaku nasan da gudu zata karbeki da gudu ayanda Hawwa ke miki soyayya, gaba zuciya tuni anyi an wuce, kawancen shekaru ashirin da yan kai, Ni’ima ina chan zan kiraki kizo kibada hakuri! Goben nan zaku shirya!”.

EPISODE

Ni’ima nawani irin numfarfashi ta kama Mama tace “Mama ina ganin jira” dasauri Mama tariketa gam ajikinta tace “zomu bar nan wajen” Mama na rike gam da ita suka shiga fita daga wajen batama gani da kyau she’s just feeling suffocated, gaban wani shago suka tsaya Mama ta zaunar da ita da sauri tana jinginata da bango tashiga shagon tasayo ruwa tazo tabata da kyar Ni’ima ta kurba kawai taji ruwan na mata daci abaki tofarwa tayi akasa kaman taci magani takalli Mama tace “Mama jinake kaman an daura dutsen ukudu akan kirjina, Mama ni Hawwa zata maida mahaukaciya? Ni Hawwa zata rainama wayau? A ina tasamo mai kudin nan bata taba bani labarinsa ba? Mama yaushe suka hadu? Yaushe har akazo ana maganan aure har ina ganinshi asibiti dazu danaje? Mama ita harta isa taboyemin abu nata eh”? Taba wani irin huci ta bubbuga kirjinta tace “Mama ni mijin nawa ya sakeni yau ita a aureta yau ni za’a watsama kasa a idanu? Mama tayaya Hawwa zata fini eh? Tayaya zata fini”? cikeda rashin jin dadi itama Mama tace “Allah yasani banso ba, ke kinga yanda nake alfahari da mai kudi kike aure kuwa Ni’ima? Dukfa cikin kannenki kin fisu goshi, kece mai auren mai kudi, kece wacce tai makaranta, mijinki yabaki mota kina gidanki flat mai kyau kina aiki a hospital, Amman yau duk sai naga Aliyu jaririne a inda masu kudi suke, yo ai duka duka arzikin Aliyun ma baikai miliyan hamsin na kudin sadakin Hawwa ba” wani irin shedanin radadin zafi Ni’ima keji aranta har wani sosa gaban riganta take ta saman hijabi, tadauka she will be happy tunda Hawwa tai aure at least yanzu Aliyu nata ne ita kadai but kuma ganin yanda mijin Hawwan yahadu ga dukiya, ga kyau, ga gata saitaji kaman ciwone gareta ya warke amman wani ciwon yafito dayamafi nada azaba, tana kallon Mama tace “Mama tayaya Hawwa zata fini aduniyan nan eh? Tayaya Mama? Akanme zatayi s’a haka ta auri dan gidan Mangal, Mama kuma bata taba fadamin tamasan yan gidan Mangal ba wlh, ai badaga sama yafado ba sun hadu ne somewhere somehow amman taboyemini dayike makirace ita yar boko datai kwantai, yaushe suka hadu har suka fara soyayya? Mama ni Hawwa zataciwa amana eh? Ni zata ha’inta ta yaudara? Babu wani abu nawa da bana gayamata fa Mama, amman ni taboyemin, ashe saisa tace ko mijina kadai yarage aduniya bazata aureshi ba sabida tasami wanda yafishi akomi, Mama did you realize abinda Hawwa tamin ko? Hawwa play with my intelligence, she belittle me, tabuga wasa dani tanunamin tafini iya mind games” tashiga shesheka tana huci jikinta har kyarma yake, Mama na kallonta itama duniya ta mata zafi tace “munafuka ce, ke bakisan yanzu kasami mai kudi boyewa ake ba’aso asani ba, ai Hawwa bata sonki kwadayin Baban Yaseer yasa ta tsaya arayuwanki” cikin wani irin murya Ni’ima tace “Mama tayaya zan bata auren nasa gidan Mangal da dan su tsaneta eh? Mama tayaya zanyi? Inaso na gayamusu yar iska ce Hawwa maza takebi duk yan sandan office dinsu sun kwanta da ita, Mama help me, yazanyi Hawwa bata chanchanci irin gidan nan ba, tafi dacewa da gidan wahala da gidan kaskanci, Mama bai kamata Hawwa ta auri mijin dayafi nawa karfi ba wlh Yazanyi Mama? Mama banso tasami cigaba arayuwa Mama ni auren ma banso tayi tamutu ahaka, sonake Hawwa ta wulakanta na ganta on her knees tana begging dina for something, Mama ta yaya zan lalata auren nan” kanta Mama tashafa tace “yanzu ai saikin fara koma mata sannan zaki iya bata auren, kibari nafara zuwa na sulhuntaku tukunna, kidena damuwa shikuma Aliyu zan kirashi ya maidaki” Gyadamata kai Ni’ima tayi, Mama tamike tace “muje” tashi tayi sai alokacin tamasan bata saka takalmi ba haka suka wuce ta shiga mota ta tafi.

**

Wuraren 11 sukakai gida, ganinsu sun shigo tareda Excellency yasa Momy tace “ahh tare kuke ne? Son ina kaje yau? Bakai baccin kirki ba Noor nata tambayanka tayi bacci yanzu” goro Excellency yamika mata da yawa da sweets a leda yace “aure mukaje muka dauramai Madam” da sauri Momy takalli Excellency dake zama looking confuse shikuma Khaleel yawuce side nashi abinshi babu abinda ke damunshi banda gajiya, Mom tace “wai wayayi aure Dear?” Khaleel dake wucewa abinshi yanuna mata yace “danki mana he just called me ina chambers yanaso nasameshi an address dazai turamin aure zaiyi shine naje da Mahe dasu Lawali and Co.” Maganan sauka kawai yake akan Mommy kaman saukan aradu tace “akanme zaka biyemai Alhaji? Kasan Khaleel is still a boy baitaba zaban mata da kanshi ba baimasan ya ake aure ba, I always do everything for him bayan nayi screening yaran, bama wannan ba, waya aura?” Excellency na daukan remote yana chanza channel zuwa news yace “that police officer, Miss Hawwa” dawani irin sauri Momy tace “inashi ina Hawwa? Ina Khaleel ina police woman? Idan tazo tana dukanmini d’a fa?” Dawani irin sauri Excellency yakalli Mommy yace “akanme kike magana haka Madam? Akwai wacce ta isa aduk fadin garin nan ta daki d’ana?” Cikeda damuwa Mommy tace “dole nayi magana haka Khaleel baida irin training da aka mata a police school, ba yarinya bace idan bata girmeshi ba zasuzo age mate I don’t want yarona to suffer” jawota jikinshi Excellency yayi cikeda so ganin hankalinta yatashi yace “ke Madam relax, yaranki just want to have fun ne, please let him have his way, kome yakeso let’s support him, karmu batamai rai, stop thinking of beating or anything, with all the security na gidan nan akwai wacce ta isa ta taba yaronmu? All I see is Khaleel is just a little bit fascinated about the gurl kinsan baitaba ganin Smart, young intelligent bold and fearless Muslim police officer ba” da sauri yace kawo kunnenki da sauri Mommy ta mikamai Excellency yace “yaronki just wants to have fun and play with the girl ne, we have the Momy babu wacce Khaleely na bazai iya samu ba, allow him, kinganshi kuwa yau he looks so happy and excited that happiness was worth everything to me, so don’t ruin that for him and don’t think much, let’s watch him have his way kome yakeso mubarshi yayi” dan ijiyan zuciya Mommy tasauke tace “toh ina matan? Ya baku taho da ita ba”? Ahankali Excellency yace “I don’t know, gobe da safe ma tambayi Khaleel din koma meyakeso it’s okay, lokacin sa ne zamaninsa ne mubar danmu ya huta, yanzu dai aikamai yarinya muje mu kwanta ki matsamin jiki” dan murmushi tayi kadan hankalinta ya kwanta tace “dukku yaranku suka biyo” dariya Excellency yayi yace “kyau kenan d’a ya gado ubansa” ya kashe mata idanu tana kwalama PA kira tasa akaimai yarinya.

Daidai yafito daga wanka aka bude kofa wata tashigo kallonta yayi yadauke kai yazauna kan chair yana zuba wine a cup yabude towel nashi yace “come here” zuwa tayi yace “kneel” kneeling tayi ba musu jiki na bari gani take wannan da aka kawota for the 3rd time she don’t think zai saketa yanzu, yace “suck” gindinshi tashiga sha ya lumshe idanu yana kurban alcoholic wine nashi fuskan Hawwa yake gani datanamai rashin kunya, bude idanunshi yayi kadan yamika hannunshi yadauki wayanshi yabude yashiga gallery hotonsu da akamusu na pool yake kallo yanadan lumshe idanu sabida yanda ake tsotsemai gaba, yadade yana kallonta sannan yayi dan murmushi ya ijiye wayan ya fizge abin nashi yamike kawai yajuyata yashige, shifa he’s doing this sabida kawai yanason sex ne, he loves yayita cin vijay not because he loves any of this creatures da Mom ke kawomai, da ace akwai yanda ake cire vijay a ijiye basai yaga creatures dinba dayafi zaban haka, ihu yafara sosai yana buga yarinyar da kyau datakeji kaman zai xazzago mata da mahaifa yakai kusan 3hrs har kuka take but maka mata yake sannan ya feso yadago kawai ya tureta abuge yace “na sakeki leave my house na sakeki get outtttttt!” ya hankadeta waje abuge tareda datse kofan yawuce yafada gado sai bacci PA dake waje tabude kofa dan babu wanda baya sanin sanda Khaleel ke sex agidan nan sabida ihu duk wani mai aiki a gida yasani idan yagama zakaji shiru tazo tafice da yarinya.

EPISODE

Wuraren 5 Hawwa ke bude idanunta tana kallon saman dakin komi daya faru nadawo mata, hawaye masu dumi ne sakko daga idanunta, ahankali tafara mosti da idanun dake mata nauyi sosai tana juyowa kanta yayi sauki kaman ba nata ba yanzu tana iya juyawa yadena banging, Ammi ta gani a tsakar dakin kan dadduma ga charbi a hannunta tanaja maida idanunta tayi tarufe she can’t look at Ammi, knocking kofan akayi da sauri Ammi ta tashi tace “shigo” tadaga dadduma tana linkewa daidai Dr yashigo tareda Nurses yazo gaban gadon yana kallon Hawwa data lumshe idanu Ammi tace “Dr har yanzu bata tashi ba nadamu abinci fa”? Murmushi yama Ammi yana duba BP Hawwa dayasan ta tashi yace “maganin hawan jini nasa bacci amman karki damu zata tashi saitai wanka” ijiyan zuciya ya sauke yace “Alhamdulillah BP yasoma sauka” anatse yace “Miss Hawwa open your eyes” ahankali Hawwa tashiga bude idanunta tadan kalli Doctor kadan saikuma ta sauke idanun kasa kawai nauyin kowa takeji, Dr yace “ya ciwon kan? Akwai wani abu dayake miki ciwo yanzu?” Girgizamai kai tayi murya kasa kasa dabaya fita da kyau tace “no” Dr yace “okay that’s great” yakalli Ammi yace “Mama help her to change tadan gyara za’azo a gyara gadon akawo mata abinci kuma, an mata booking massage Yallabai yace bayanta na ciwo, masseuse zasu mata massage din, zatasa hospital clothes bama barin patient namu nasa kayan gida” gyadamai kai Ammi tayi tace “to” Nurses suka ciremata drip din suka fice Ammi taje gaban gadon tana kallon Hawwa da idanunta ke kasa ta kauda kanta gefe dasauri jin Ammi tazo wajen, Ammi dake kallonta tace “Jidda na ya jikin? Babu abinda ke miki ciwo kuma”? Gyadama Ammi kai tayi ahankali batare data kalleta ba tace “eh” cikeda so Ammi tace “tashi muje to kiyi wanka ki chanza” Ammi takai hannunta tadagota tasowa tayi da karfin hali ta sauka daga gadon Ammi tariketa har bayi tabata gadon Ammi tahada mata ruwan wanka, tadawo dakin tabude jakan kaya da Baba da Ramla suka kawo musu jiya taciro brush da zani, saikuma pad datasa Ramla tasa ajakan tadauki daya da wando takoma bayin ta ijiye mata tasake fitowa ta yaye zanin gadon daidai nurse tashigo da wani ta shimfida mata da hospital gown mai kyau na yan gayu sannan tafice saikuma masu abinci suka kawo mata fruits da oat, dasu chips da egg da salad da sausage ga bread saikuma maganin dazata sha a gefe cikin wani glass covered container Ammi sai kallo take komi na masu kudi daban ne.

Kusan 15min tayi abayin Ammi takoma wajen bayin tace “kin gama Hawwa”? Ahankali tace “eh” Ammi tabude tashiga tana kallon yanda taki yadda su hada idanu, maidata gadon tayi tana kallon yanda white and blue flowers hospital gown din yamata kyau ta zaunar da ita tana daga tray na abincin tana ijiye mata tace “yi maza ci kafin sudawo” yatsine fuska tayi batada apatite ko kadan kauda kanta tayi asanyaye tace “Ammi bazan iya ci ba” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta matso ta zauna abakin gadon anatse tace “Hawwa” asanyaye Hawwa tace “Naam” batare data kalli Ammi ba, lumshe idanu Ammi tayi tabudesu tace “look at me Hawwa” girgizama Ammi kai tayi dasauri lips nata suka shiga rawa tace “Ammi bazan iya ba” wani iri Ammi taji, hannunta tasa tadauke tray na abincin ta ijiye akan table na dakin sannan ta matso dab da Hawwa ahankali tace “Hawwa look at me” daidai lokacin hawaye yasauko daga idanunta tace “Ammi bazan iya kallonki ba, Ammi banmasan ta yaya zan kalli keda Baba ba” sai takai hannayenta biyu tadaura kan fuskanta tafashe da kuka mai tsuma zuciya she’s hurt, Ni’ima hurt her beyond duk yanda zatayi bayanin tace “wlh, wlh, wlh Ammi ni ba yar iska bace bantaba amfani da kaina ba, Ammi that’s not me, bazan tabama wani fyade ba” hawaye Ammi tashare daga fuskanta Hawwa tabata tausayi sannan takai hannunta takama hannun Hawwa tasauke takai hannunta tajuyo da habanta fuskan Hawwa yajuyo Ammi tanuna kanta tace “Hawwa ni mahaifiyarki ce kina gani aduniyan nan akwai wanda yasan yarsa sama da mahaifiyar ta? I know you Hawwa, nasan tarbiyan da muka miki, I know who you are? Dagani har Babanki babu wanda yama dauki maganar da Ni’ima tayi da mahimmanci, Hawwa yau koda haka kike ko kinfi hakama muna sonki and we will always love you, Hawwa ke y’ata ce inasonki aduk yanda kike aduk yanda kika zama, kinji yarinyana, ki manta da duk wani abu data fada, come here” dasauri ta rungume Ammi tana sake samin wani karfin guiwa iyaye daban suke idan suka nuna they’re with you and they stand with you kafi jinka very strong kankame Ammi tayi tana kuka harwani rera kukan take kaman marainiya tace “Ammi menama Ni’ima? Why all this hate? Sabida ni Ni’ima tazageku ta ma Baba rashin kunya, Ni’ima tamin gori tama Baba gori, Ammi me namata eh”? Tawani ja numfashi tana rera kuka tace “bazan taba auren mijinta ba, Ammi sabida bansami miji ba banda aure shikenan na zama dustbin? Kowa yadauko shiritanshi akaina? Ammi inaso nai aure nahuta maybe only then Ni’ima zata yarda dani I’m not after Baban Yaseer, Ammi babu abinda kemin dadi“ cikin dan fushi kadan Ammi tace “zaki kashe kanki akan Ni’ima ne? Hawwa that girl obviously doesn’t deserve you, abu dayane bazanyi supporting naki ba shine kisamakanki damuwan Ni’ima, Hawwa don’t kill yourself akanta, Ni’ima don’t deserve you Allah use this

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login