Showing 165001 words to 168000 words out of 184554 words

Chapter 56 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1915

kwashe da dariyan manya yace “I want 20kids if possible, ayi abani jika Hawwa uhmm sarkin kunya” Hawwa taboye kai sosai, Excellency yabude kofan office din yace “let’s go” fitowa sukayi tare kan Hawwa na kasa suka shigo falon Mommy na hararanta Khaleel na zaune akan kujera kusada Baba yadan jingina kanshi a hannun Baba yayi shiru idanunshi a lumshe Hawwa tazauna akasa gefen Ammi kanta akasa Excellency ya kalli Baba yace “Alhamdulillah Malam naji dadi da kuka dawo da Hawwa immediately, this shows Hawwa tafito daga gidan manya gıda masu tarbiya da sanin yakamata, idan mata da miji sun sami matsala ba’a nuna anyi supporting yarinya dawo da ita ake hakan da kukayı ya kara nunamin yess! Danmu ya auro matan data dace dashi” Baba yayi gyaran murya yace “Hawwa ta kunyatani ta kunyatamu abubuwan datayi sam ba tarbiyan damuka bata kenan ba, amman ta sanarma da mahaifiyarta tariga ta janye zancen kotun tun aranan da taje kotun, kuma wlh duk randa kika kara batama Ibrahima rai gidan nan zanzo na ciccimiki mutunci kinajina!” Kanta na kasa tace “eh” cikeda fada Baba yace “kuma na sanar da ita bata babu aikin nan sabida harda aikin ke kara mata taurinkai da ji kaman ta isa tasama kowa bindiga akai” Baba yajuya yakalli Khaleel yace “Ina neman alfarma kabarta tace offis dinsu takai takarsan barın aiki da uniform bata da bindigar kaji Ibrahima” gyadama Baba kai yayi ahankali idanunshi a lumshe Baba yajuya yakalli Mom dake kumbure kumbure Khaleel yahanata magana yace “Hajiya nasan Hawwa ta batamiki rai muma duk ta batamana, abinda zaki la’akari dashi shine babu mata da miji da basa fada amfaninmu iyaye kenan idan sukayi saimu hadasu tare mu sosollesu tass mu ci musu mutunci, nasan duk maganganun da kikayi sabida kinason danki ne amman ina mai tabbatar miki Hawwa zata kula da danki da kyau, ki bama Hawwa dama tabiyu Hajiya zakiga chanji bazata kara abinda tayiba ayakuri ayakuri”

Dudda yanda Mommy ke fushi she loves how Baba looked at her yamata magana dudda ta cicci mutunci yarsu agabansu, sai kawai jikinta yayi sanyi ahankali Ammi tace “ayakuri amata afuwa tayi kuskure” shiru Mom tayi for the first time saitaji kunya kawai yakamata da itane wata taci mutunci danta haka wlh ko kallonta bazata karayiba ballema tamata magana but look at ya da suka bata hakuri sai kawai ta gyadama Baba kai tace “toh” dan batasan yanda zata amsasu ba

Baba yajuya yakalli Hawwa sai kawai yadan daga kan Khaleel dake kafadanshi yace “ina zuwa Ibrahaima” yatashi dagakan kujeran yawuce dayan kujeran dake gefen na Ammi ya zauna yace “je ki fara bawa mijinki hakuri yafi kowannenmu matsayi da mahaimmancin arayuwanki sannan ki bawa iyayensa hakuri dan hardasu kika ciwa mutunci tashi” Ahankali Hawwa tadan kalli Khaleel da yana dauke kanshi completely baya kallon inda take gently ta tashi kowa na kallonta adakin harda Mom tazo gaban Khakeel ahankali tana kallonshi yaki kallonta zuciyanta kawai taji yana breaking, gently ta duka sai kawai tasa guiwowinta akasa tai kneeling hakan ba karamin dadi yama yan dakinba barinma Mom now that is how to beg yaronta cus her Khaleely is a king!Hannuwanta Hawwa tahade ahankali tana kallon Khaleel dayaki kallonta sai kawai bakinta yafara rawa sosai ahankali tace “Kh……l….eel” Baba yace “au haka kike kiran mijin naki gatseee” girgizakai tayi dasauri tace “Husbyyyyyyy” ko moving jikin Khaleel baiyiba kaman ba shi ba, wayyoo kawai Hawwa tafashe da kuka tace “I am very very, I’m terribly sorry Husbyyyyy, I am super sorry! I’m genuinely sorry! I’m fully, wholeheartedly sorryyyyyyyyy”

Sai kawai takama kunnuwanta tana kallonshi tace “I will never ever hurt you again I promise kayakuri, forgive me kaji mijina!” Wlh kaman baisan abu na gabanshi ba sai kawai ya yunkuro ahankali yatashi tsaye dasauri Hawwa ta kalleshi ta gefenta yabi zai wuce azuciye Excellency strictly yace “Ibrahim” juyowa Khaleel yayi yakalleshi ahankali bai amsaba, Excellency yace “bakaji matarka na baka hakuri ba”? Yanuna Hawwa that is still kneeling, murya chan kasa ciki ciki Khaleel yace “uhm I heard her it’s okay!” Yafadi ba yabo ba fallasa hakan yama Baba dadi da Ammi dadi yes yaci uban Hawwa! She deserves it inba hakaba she will keep on taking him for granted, kawai yajuya zai wuce dawani kalan sauri Hawwa ta tashi ba zato ba tsammani kawai yaji Hawwa ta rungumeshi tabaya tsam tsam, gam gam tace “I LOVE YOUUUUUUUU!” Chak Khaleel ya tsaya komi nashi na tsayawa as well!

Kowa na falon murmushi yayi suka daddauke kai daga kallon yaran nasu, sheshekan kuka Hawwa takeyi like a baby, bawai kalan kukan datakeyi tun dazu ba this is a special cry just for mijinta kaman wata baby sosai kuma, cikin murya mai kashe zuciyan miji tace “Ibrahim I love you!” Manna fuskanta tayi abayanshi sosai har kamshin sa tayi missing yaushe rabon da tajita ajikinshi tace “Inasonka Ibrahim Khaleel!” Ahankali tasakeshi ta zagayo ta gabanshi tana kuka takai hannayenta tadaura kan kirjinshi ta kalleshi hada ido sukayi duk wani affection data saba gani nata a kwayar idanun Khaleel yau bata gani ba Heart nata na shattering into pieces tace “I can’t loose you sabida I love you! I’m sorry about everything, I love you Khaleel!” Wani shegen kallon tsana yamata, yace “ok so?“ ya Allah!That’s one of the coldest reply someone has ever given to her in her entire life jikinta kaman ya daskare, yatsine fuska Khaleel yayi ya kabar da hannunta daga jikinshi bluntly yace “whatever Yawucewanshi yabarta wajen tsaye yabude kofa yafice, jiri jiri Hawwa taji tanaji da sauri ta duka awajen tace “na shiga uku!”.

EPISODE

Mom tai murmushin jin dadi ganin yanda yaronta yatafi, Baba da Ammi ma sunji dadin abinda Khaleel yayi Excellency ne cikeda so yace “it’s okay Hawwa na, he will come around, je flat naku kihuta I want to talk to your parents” gyadama Excellency kai tayi tamike tsaye ahankali tana tafiya da kyar tasa hannu tabude kofa tafito, da hankali da hankali take tafiya har zuwa side nata tabude kofa tana shiga tawuce carpet na tsakiyan falon kawai ta kwanta tana kuka mai radadi da soya zuciya.

Kallonsu Baba Excellency yayi yace “daga Khaleel har Hawwa duka yarane, duk mu bisu a sannu muna correcting nasu, shima Khaleel din bawai he’s innocent bane, duk matsalan shi ta haddasa wannan fadan, d’ana na shaye shaye” Excellency yafadi ahankali there no point aboye an zama daya yanzu, daga Baba har Ammi suka kalleshi dan basu dauka zai iya fadin kalan maganan ba, ahankali Excellency yace “duk laifi nane inason Khaleel da yawa da nakasa gyara kuskuren shi but namuku alkawari komi zai chanza daga yanzu zamu tsaya tsayin daka akanshi ya gyaru”Excellency yace “kuma dan Allah Malam da Hajiya kada ku kara tabamin yarinya kuka kara dokanmin diya shari’a zanyi daku sosai” dan murmushi both Ammi da Baba sukayi Ammi tace “diyar taka akwai taurin kai ne amman za’a kiyaye harda fushi” Excellency yace “ga abin doka Khaleel ba’a dakaba sai iya” Mom ta tashi kaman ba itaba anatse tace “ko ruwa ba’a baku ba” shi kanshi saida Excellency ya kalli Mom but harta wuce Excellency yakalli su Baba yace “kar maganganun da Zainab tayi yasa ku dauka Hawwa zata wahala ko zata takura mata bar Zainab da masifa amman batada mugunta, abu kadan Hawwa zata iyayi ta sace zuciyanta” Baba da Ammi sukai murmushi saiga Mommy tareda ma’aikata dasuka dauko hadaddun ubansun trays dake dauke da drinks da ruwa da kulolin abinci da su fruits duk aka ijiye a tsakar falon Excellency ya sauko yace “bismaillah Malam” Mom ta kalli Ammi ahankali tace “ni banson bakunta fa” Ammi cikeda raha tace “kikazo gidana Allah sa kada kiyi” Mom ta sauko Ammi ma ta sauko suka shiga hira da Mom har tana tambayan Ammi garinta suna hira sosai kaman ba fada yaransu suka gamayi ba sai wajajen shabiyu sukace zasu tafi har waje su Excellencu suka rakosu Ammi tace “bari taga Hawwa” tawuce

Hawwa na kwance akasan Ammi tabude kofan dakin ta shigo tana kirne fuska Hawwa na ganinta ta tashi zaune da sauri tana goge fuskanta Ammi tayi kaman bataga tana kuka ba, tace “abu daya nazo gayamiki kije tiktok ko IG kiyi searching M Shakur ki shiga class dinta na Kissa training da Intimacy ki koyi yanda ake abubuwa, idan zaki zage damtse kiyi zaman aure kiyi Hawwa, ga mijinki nan yayi fushi dake, tun wuri kafin dare yamiki kisan yanda zakiyi ki lallaba ki shawo kansa ku shirya, ni natafi zaria bazan kara dawowa Abuja sabida kin tapka hauka ba kome kika shirya yi kiyi, duk abinda zakiyi ki tabbatar kinyi kin shawo kan Khaleel kafin ya tsaneki da gaske” Ammi tayi kofa daidai zata fita taji Hawwa ta kama mata hannu dasauri Ammi tajuyo sai kawai Hawwa ta rungumeta tama kasa magana kuka kawai take jikin Ammi, ga jikinta yayi zafi, Ammi na so ta karaya but ta tuna this is the same thing she did jiya ta tausaya mata tahakura amman da safiyan Allah tayi shirmen dayafi na jiya so taji ajikinta, cireta kawai tayi daga jikinta tajuya abinta tafice tarufo mata kofa Hawwa ta tafi wajen window taga su Ammi sun shiga wata mota daban da yaron daya kawosu sun tafi.

EPISODE

Komawa Hawwa tayi tasake zama sai kallon kofa take jira kawai take Khaleel yashigo ahaka wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita, tana cikin bacci taji motsi dayake batai nisa a baccin ba da gudu tabude idanunta Khaleel tagani awajen kofa yana fita dawasu manyan akwatinan shi na LV guda biyu, mugun faduwa gabanta yayi da gudu ta tashi kirjinta nawani irin bugawa tayi wajen kofan tace “Khal…..” mugun kallon daya mata yasa takasa karasa kiran sunansa kawai yaja kofan ya kulle yawuce abinshi, Hawwa tayi wajen window dagudu tadaga labule taga flat dinsu yashiga da akwatinan sai kawai taji kuka yazo mata saida taji ana salla ta iya barin wajen tawuce dakinta bayi ta shiga tayi alwala, tafito tazauna kan dadduma tayi salla ta kwanta akan dadduma tana wani kalan sauke ijiyan zuciya her heart is so heavy kaman an daura mata manya manyan duwatsu, takasa cin abinci takasa bacci sai kuka har bayan sallan isha da kyar ta tashi tajawo wani first aid box taga PCM tadauka tasha ta mike ta tsaya tsaye wajen window ta tana kallo babu Khaleel a compound din, ina yaje? She’s missing him, wayanta ta dauka ta zauna bakin gado tai dialing number shi saitaji ana cemata number shi bayama kan network gabaki daya ijiye wayan tayi ta tashi tafada bayi da kyar tai wanka tafito tasaka wani sexy rigan bacci ta feffesa turare sai kawai tawuce ta tafi dakinshi tabude ahankali everything smells like him, zama tayi abakin gadon ahankali tana kallon gadon tana tuna how happy Khaleel use to be, his full smile yana kallonta, his loving eyes, his erotic talks, his sleep, yanda yake kankameta, yanda yake bacci ajikinta, yanda yake tashi da kyar, the way yake amsawa ummm idan ta tadashi, the way he acts like a baby, the way he dances for her, the way yake tsokanan ta, the way he calls her Kulu, Yar Sanda, muguwa menene menene, bata taba sanin she loves all the moments ba sai yanzu, like she will give anything just to experience those moments one more time yanzu, hawaye masu dumi taji yana bin hancinta yana diddiga ta tip na nose nata yana sauka a hannunta dasauri ta share da bayan hannu kaman mai mura cikin wani irin murya na ban tausayi da nadama da dana sani tace “I am sorry Khaleel!” Sake goge hawayen tayi tace “I really am, I’m badly sorry Khaleel, I miss you, I missed everything about you, please come back to me kayakuri” tayi maganan tana kwanciya ta kifa kanta jikin pillow dinshi Hawaye na gangarowa daga idanunta tana kallon kofan tamika hannu tadauki pillow daya ta rungume a kirjinta tana kallon kofa har 2 nadare takasa bacci ta tashi taje ta dauro alwala tadauko hijabinta tadawo dakin tai salla har four sannan bacci ya iya kwasheta akan dadduman.

Ahankali take iya bude idanunta ganin gari yayi haske yasa ta kalli wayanta da sauri taga 7:45, Subhanallahi tafadi da sauri ta tashi tashiga bayinshi tadauro alawala tazo tai salla ta idar tai azkar ta karatu ta gyara dakin tass ta kunna turare tawuce bayinta tai wanka har yanzu idanunta a kumbure closet nata ta shiga tasaka wani atampa riga da skirt dakeda red ajiki batasa komi a fuska ba tafito tasauko kasa kitchen ta shiga tayi tea a cup tafito tazauna tana kallon tea din wlh takasa sha sai kawai ta tashi taje kitchen ta ijiye tasa marfi tarufe tafito takoma sama ta shiga closet red mayafi ta dauka babba tayafa tafito tasauko kasa, crocks dake nan kasan falon na Khaleel tasaka tabude kofa tafito tana tafiya ahankali tawuce side nasu Mom.

Gently tabude kofan da sallama a bakinta ta shiga ciki Momy ne kadai afalon ga plate na fruits tanaci cus yanaci fruits take faraci dasafe idan Excellency na gari tana breakfast da wuri but jiya da night yatafi France saisa take breakfast ita kadai ga ma’aikata a dinning na jera warmers, kallo daya Mom tama Hawwa ta dauke kai tacigaba da cin fruits abinta, dudda gaban Hawwa na fadi but har gaban Mom tazo ta duka ahankali tace “ina kwana Mom” dauke kai Mom tayi kaman bada ita take magana ba chan tace “lafiya” shiru Hawwa tayi still tana gabanta chan tace “Mommy dan Allah kiyakuri kiyafemin kinji Mom” kallonta Mom tayi tamata wani banzan kallo tace “tashi agabana” ahankali Hawwa ta tashi, gently tawuce wajen dinning saikuma tawuce kitchen, 3workers ne ke aiki an riga an gama breakfast na Mom dasauri suka gaida Hawwa. “Good morning Ma” gyadamusu kai tayi ahankali Hawwa tace “me kuke dafawa” babban ma’aikaciyan tace “an gama breakfast na Madam, tace ama Mr Khaleel kunu da akara shine zan fara yanzu” Dasauri Hawwa tace “ki barshi zanyi” batama jira amsan su ba tace “ina wajen wake? Da gero”?

EPISODE

Dukansu suka nuna mata store sai kawai tawuce store ta debo wake da geron kunu tafara aiki sukace mezamuyi tace “no karki damu, kawai zan dinga tambayanki unda abubuwa suke” tafara aiki she will do everything in her power to win Khaleel’s love back.

Kunu tashiga yima Khaleel, Mom na zaune a falo kusan 30min saikuma ta juyo badai yarinyar nan taje tana taya yan aiki yin aikinsu ba, juyowa tayi but bata ma iya ganin kitchen daga wajen, tashi tayi ahankali rike da empty plate na fruits nata tazo wajen kitchen din duk basu ganta ba turus ta tsaya tana kallon Hawwa dake buga kosai yan aikin sun zazzauna suna kallonta, yaune rana na farko da Momy ke ganin Hawwa babu mayafi dan ta rataya gyalen a kofa tana aiki gaskiya yarinyar is very very beautiful she cannot even lie and she’s tall and very pretty dan kitson datayi dan ya zubo a bayan wuyanta kuma gashinta da tsayi, tai shiru kawai tana kallon Hawwa somehow she’s seeing why yaronta ke sonta, Hawwa kaman taji ajikinta ana kallonta juyowa tayi ganin Mom yasa gabanta yafadi da sauri ta ijiye bowl din ta taho wajen kitchen din bayan taja gyalenta daga kofa ta yafa cus is her own way of showing iyayen mijinta tana girmama su, yan aikin na tashi suma dasauri, ahankali cikeda respect Hawwa tasa hannu takarbi empty plate dake hannun Mom, cikeda girmamawa tace “Momy kina bukatan wani abune namiki?” Tsayawa Mom tayi tana kallon Hawwa shekeke sabida mijinta yayi yaji itama tazo tawani biyoshi nan, saikuma cikeda masifa tace “me kikemin a kitchen nina aikeki”? Kanta na kasa tace “Momy kiyakuri kosai zanmai” dariyan takaici yakusa kufcema Mom tace “eh kin iya kosai amman baki iya kulamin da yaro ba mara mutunci kawai, kinaso ki kashemin dan dayadaya ne” Mom tajuya fuuu Hawwa tajuya takoma kitchen she just promise kanta she will show Momy she’s a good person and she will win Momy da Khaleel dukansu, komawa tayi tashiga soya kosan da ko’ina yacika da kamshi.

Sai bayan yadawo daga masallaci yasami bacci, kamshin kosai daya ratsa hancinsa yasa ahankali yabude idanu hardly kamshin abinci ke shigowa side nashi wat happened yau kodan ba’a cika kosai bane anan he just hopes kosan will taste good kaman na Hawwa. Yadan sauke ijiyan zuciya sabida fadomai zuciya da Hawwa tayi, sannan ya tashi yafada bayi yayi wanka but still idanunshi jaaa closet nashi ya shiga yasa AMI Paris shirt just 2 buttons na kasa yasaka yana yasa wani 3qyater dark blue ya feffesa turare har wani dan ramewa yayi yasaka flops yashiga saukowa yana folding hands na riganshi Mom dake zaune tana bude news paper ta dago kanta takalleshi yarinta duk ya susuce yadawo wani kala tashi tayi tana ijiye jaridan cikeda so tace “Khaleely” he’s not happy kawai bayama walwala ko kadan tarasa wani kalan so yakema Shegiyar yar sandan nan mara kirki bayan ga mata wayanda suka fita sosai, ahankali yace “good morning Mom, an mini kosan”? Gyadamai kai Mom tayi takama hannunshi tace “let’s go lemme feed you” Hawwa na tsaye a kitchen tana karasa tuyan kosan taji Kamshin Khaleel ijiyan zuciya ta sauke ahankali kirjinta yahau bugawa.

Zama yayi Mom tabude flask na kosan dasauri yadauki daya yakai baki asanyaye dan baida energy yace “it smells good Mommy” yakai bakinshi Mom tashiga zubamai kunu, hakanan kosan na shiga bakinshi kawai it reminds him of Hawwa again yayi shiru ya dakata da taunawa, ganin ya tsaya yadena taunan yasa Mom tace “ba dadi ne”? Girgiza mata kai yayi baice komiba sai kawai yacigaba da ci, Mom ta zauna kusa dashi tana juya kunnun ta a spoon takai bakinshi tana bashi yasha why does it taste like Hawwa made this? Rabon dayaci abinci dayama bakinshi dadi tun ranan daya tafi office around after twelve sai yau dayabi Sam party, taba wuyanshi Mom tayi tace “Alhamdulillah temperature ya sauka sosai, idan kagama saimuje hospital ko?” Dan turomata baki yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login