Showing 27001 words to 30000 words out of 184554 words

Chapter 10 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1873

tayi tana zaune kan dadduma tayi azkar nata da karatun Qur’ani har zuwa seven sannan ta tashi ta linke komi tazo gaban mirror tayi morning routine nata na skincare yau yawanci uniform sawa suke last Thursday of the month sabida suna meeting da ake kira da Intelligent Briefing, wanda harda chef of staff da manya manyan mutane na kasa dai, tundaga kan yan military da other security personnel, zama tayi tana kallon kayan makeup na gaban madubin Baba pressure her so much da yanzu gani take kaman ita mummuna ce batada kyau maybe saisa babu mai nemanta, hannunta tamika ahankali tadauki powder zata shafa a fuskanta saikuma ta ijiye, makeup bashine zaisa a sota ba, and abin will look somehow dan bata sabayi taje wajen aikiba, murya chan ciki tace “Ya Allah kasa wani yace yana sona, na burge wani awajen meeting din” tadanyi murmushin kunya tadauki kwalli tasaka tasa lipgloss dayama lips nata kyau yafito baby pink yir abinshi, tawuce ta bude sip tana ciro uniform nata, singlet tafara sawa fari kafin tasaka rigan police din mai dogon hannu, daman akwai skin tight short one black datasa tazauna ta saka safa sannan tadauki dogon wandon uniform din tasa tayi zanzaro da rigan ciki tadauki bakin belt nasu ta saka kayan sun mata kyau bana wasaba, wandon nada fadi bai wani nunata sosai ba, bakin veil tadauka tai rolling akanta ta tura gyalen cikin riganta sannan tasake maida boturan rigan, tadauki boot nata tasaka baki dake shinning yaji shoe polish.

Komawa wajen madubi tayi ta feffesa turaruka sannan takara kallon kanta a madubi takoma baya tace “Hawwa kinyi kyau” sannan tadauki handbag dinta ta tarkata yan tarkacen ta cikinsu tafito tarufe kofan dakinta tayi hanyan waje Baba na zaune a kofar gida yabita da kallo dukawa tayi tace “ina kwana Baba” anatse yace “kintashi lpy ya hannunki”? Smiling tayi tace “dasauki” “Alhaji Kabiru yace yanata kiranki baki dagawa mesa baki daga wayanshi”? Dauke kanta tayi tafara kokarin mikewa tace “bansan shi bane” shiru Baba yayi yana kallonta saikuma yahade rai yace “idanba kinaso nayi mummunan sabamiki ba makesure kin kirashi sannan kidawo dawuri dan zaizo anjima da yamma ya ganki” murya ciki ciki tace “to” tawuce tadan dudduba motanta tayi warming sannan taja motar tabar unguwan.

Parking motarta tayi tafito bayan tadauki duk abinda zata dauka tawuce ciki direct office din Hayatu tawuce knocking tayi tareda bude kofan yana cikin office din tareda Abraham duk suna sanye da uniform gani ta yasa Abraham yatashi da sauri yana murmushi yace “welcome back Miss Hawwa, how is your hand”? Smiling kadan tayi tace “fine ya jiki? Hope you guys are good”? Gyadamata kai dukansu sukayi saikuma tai shiru saikuma tajuya zata fita Hayatu yace “Miss Hawwa” juyowa tayi ta kalleshi duk kallonta suke yace “kina bukatan wani abu ne?” Dan shiru tayi kaman mai tunani sai kuma ta shigo office din da kyau tazo gabanshi ta tsaya tace “uhmm actually I kinda need your help dukanku biyun banda wanda zan tunkara sai ku” Hayatu na kallonta yace “whatever you need we are here” gyadamai kai Abraham yayi yace “yes Miss Hawwa” cus bata taba zuwa da sunan tana neman su mata wani abuba, sakeyin jimm tayi sai chan tace “wani mutumi nakeso kudan tsoratamin shi ya rabu dani” tasake shiru kaman maijin nauyin maganan dazata yi tace “arrhhhhh daga ta bangaren Babana yafito yanason ya aure ni and and…uhmm bana sonshi i just want him to leave me, so please can you scare him off”? Calmly Hayatu yace “we got you” anatse Abraham yace “always! Give me his number ta track him” dan murmushi tayi tabude wayanta tashiga kiramai number sannan tace “thank you guys” tawuce tafito hankalinta ya kwanta office nata tashiga ta zauna tadan fara paper work, she needs to write detailed report na abinda yafaru a field takai office na DIG, karfe 10 suke shiga meeting din, 10 daidai akai knocking kofan office nata Abraham ne rike da two cup of coffee yashigo ciki ya ijiye daya agabanta yace “let’s go” mikewa tayi tadauki coffee din tace “thanks” suka fito tare zuwa meeting din wanda 12 suke gamawa.

12:15 suka gama tafito DIG yace “meet me in my office” gyadamai kai tayi tace “yes sir” tai discarding cup na coffee a trash na wajen tawuce Abraham yabita da kallo kawai yasan he doesn’t stand a chance ne but Miss Hawwa na burgeshi, she will forever be his crush.

Knocking kofan tayi aka bata izini ta shigo, DIG ne kadai a office din yana duba some files yasa glasses a idanu yace “yauwa Miss Hawwa” saramai tayi tace “Sir” ijiye file din yayi tareda zare glasses dinsa yace “ease please” sauke hannunta tayi yace “you solved that case brilliantly Officer kudos” dan murmushi kadan tayi tace “thank you Sir, you trained me after all” murmushi yamata ba karya bane yana alfahari da Hawwa in this task force yace “yanzuma I have another case for you” kai tsaye tace “nakira su Hayatu ne Sir?” Hannu ya girgixamata yace “no ke kadai sukai requesting for” kallonshi tayi alamun bata gane meyake nufi ba, yace “I got a call from Excellency they can’t find wani bodyguard nasu and they want you to look into it suna tunanin anyi kidnapping dinsa shima so they want you for the job” kawai jitayi ranta yabaci gabanta kuma yafadi, tadai daure tana kallonshi batare datai magana ba, DIG yace “please kije and investigate, Hawwa bance kije kifara fada da yan gidanba, rayuwansu da namu ba dayaba, this people ba’a Nigeria aka haifesu ba a kasan waje sukafi rayuwa so don’t expect them to act like us, masu kudi basa tunani kaman yaku bayi irinmu, just do your work without interfering in affairs nasu, be professional about it and keep me posted, am I clear?” “yes Sir” Hawwa tafadi ranta ba dadi, hannu yakai aljihunshi yadan zaro kudi yan 1k kusan na 15k yace “gashi kisa fuel a car naki” hannu tasa ta karba tace “thank you Sir” kofa yanuna mata yace “zaki iya tafiya” juyawa tayi tafice, babu yanda zatayi harkan police dama duk wani harka daya danganci hukuma ba’ama Oga gardama koda yace ka fada cikin wuta ne dole you must obey, obey before complain yana daga cikin slogan nasu, office nata tawuce zama tayi kan kujera tareda dafekanta tadan fuzar da iska taja drawer tadauki wayanta da car key tamike tafito tawuce wajen motanta tabude tashiga taja tafita saida ko ta tsaya tasha fuel cus gidansu da nisa ahaka har takai gidan tsayar da motanta akayi security suka leko yace “Hello Miss wakike nema”? Anatse tace “DIG sent me here” magana yashigayi awaya kusan 5min sannan yace “booth please” booth tabude musu suka duba akai scanning motan sannan aka bude mata gate din da sauran gates din daidai tana shiga gidan kawai taji gabanta yafadi hakanan, wani arnen Lexus jeep tagani black a compound din tinted ga security awajen daidai yarufe back seat din yajuyo yanabin motan Hawwa da kallo, parking tayi itama tadan fuzar da iska tareda kashe motan ta kashe AC tadauki wayanta tana kokarin kiran DIG ta sanar dashi ta iso akai knocking glass na motan hakan yasa ta dagokai ganin security da uniform yasa ta sauke glass na window cikeda girmamawa yace “afternoon Ma’am, Yallabai yace kishigo mota he will brief you aciki meeting gareshi and he’s running late” the thing is batasan Baban ne ko yaron ke nementa ba dudda tasan yawanci manyan mutanen nan haka suke basuda time amman saita bisu yanzu haka? Motanta ta kalla hakan yasa security yace “you don’t have to worry about motanki Ma’am ko ina kike za’a iya kawomiki kokuma adawo dake har nan kidauki motan ki wuce” dan ijiyan zuciya ta sauke tace “okay” hakanan she’s feeling so uneasy, bude motan tayi security ya matsa gefe tadauki wayanta da jotter tanada pen makale a aljihu already ta maida kofan tarufe tamai key tasa key a aljihu, Salman sai kallonta yake baitaba ganin police mace da uniform yama kyau kaman itaba, she’s damn beautiful, gashi tai rolling gyale akanta abinta sai tai kaman balarabiya, dan kallonshi tayi, cikeda good etiquette yanuna mata jeep nasu yace “after you Ma’am” gaba tayi yana biyeda ita har sukai wajen motan daidai takai wajen motan ta tsaya Salman yataho yasa hannu ya bude mata motan kamshi mai bala’in dadi yafara mata sallama da sanyi kafin idanunta su sauka kan Khaleel dake zaune cikin motan yayi crossing legs yana sanye da Ralph Lauren polo custom fit oxford shirt white dayayi folding dogon hannun, as usual babu kusan botura 3 na gaban rigan bai makala ba kana iya ganin kirjinsa, yasaka AMI Paris logo track short brown, short din yau ma baikai knee ba adan cinya ya tsaya, kafafunshi sanye da slides na Yeezy brown suma ga kumbunan kafanshi farare tass agyare diddigenshi kaman kasha sabida yau fari tass yasha spa pampering, writs nashi daure da agogon nexus pro smart watch, yasaka Burberry brown shades dasuka mai shegen kyau yana zaune cikin motan comfortably yana rikeda wine glass da wine keciki yana kallonta kaman yau yafara ganinta, juyawa Hawwa tayi azafaffe bawasa ko nonsense kan fuskanta takalli Salma dake tsaye abayanta tace “mai gidan nazo gani ba dan masu gidan ba!” Tajuyo ta kalli Khaleel tareda nunashi da hannu cikeda cin mutunci tace “Babansa nazo gani!” Wow! Har kirjinsa Khaleel yaji sigan maganan Hawwan cus she stepped on his ego and pressed it sooo hard!

EPISODE

Zafi kirjinshi kemai sabida abinda ta fadamai tamugun rainashi yarinyar, wlh baitaba haduwa da any of this creatures data rainashi ba like this girl in his 32yrs of life, but zaiyi maganinta, ko gezau baiyiba balle yayi wani alamu na zaiyi magana, cikeda girmamawa Salman yace “Excellency bayanan but he specifically made it clear kiga Yallabai on his behalf” da dan fushi kan muryanta tace “children like him manta sakon da aka basu suke” ba Salman ba har sauran security dake wajen da shi kanshi Khaleel din saida suka kalli Hawwa, ta kirne fuska tajuya tace “I need to check in with my Boss” tai maganan tana barin wajen motan tai chan gaba tana ciro wayanta tashiga kiran DIG ringing daya ya daga tace “Sir Excellency bayanan fa zan dawo” dasauri yace “ohh na manta ban gayamiki ba Mr Khaleel will attend to you, ki tambayi Mr Khaleel za’a kaiki wajensa kiyi magana dashi” wayan na kunnenta tadan juyo takallo motan dataga Khaleel yajingina abinshi da mota kaman ma bacci yake da dan damuwa kan fuskanta tadan rage murya tace “Sir naga Khaleel din wai saidai na shiga motanshi cus meeting zashi he will update me on our way” dasauri DIG yace “to kishiga mana, Senate president namu na bukatan service namu don’t ruin my reputation, kishiga tsoro kike duk rashin jinsa he can’t do nonsense with Nigeria asset, let’s take the case quick I have to go” ya katse wayan, zare wayan Hawwa tayi daga kunnenta tana kallon screen din gabaki daya zuciyanta bayamata dadi, ta tsaya awajen taki motsi Salman yataho yace “we are running late Miss” juyowa tayi takalli Salman da idanunta dahar sun kada sabida bacin rai sai kawai tawuce fuu azuciye kaman zata tashi sama, kai tsaye ta shiga motan ta zauna akan kujeran dake facing na Khaleel, Salman yazo yarufe musu motan ya zaga ya shiga gaba driver yaja motan mopol daya na gaba daya na baya suka shiga titi, dan ijiyan zuciya Hawwa tasauke no matter wat dai tasan ba kasheta zaiyiba with all this people around.

Tunda ta shiga motan taki dagakai ta kalli inda yakema tsabagen yanda batason ganinshi jiranshi take yagayamata abinda zai gayamata amman shiru. Tundaga boot na kafanta Khaleel ke kallo dake kyallin polish gwanin kyau har zuwa fuskanta, kusan 5min kallonta yake baya ko kyafta idanu, sannan yakai wine glass din bakinshi ya kurbe duka tass ya ijiye glass din yabude dan fridge na wajen yaciro kwalban wine yana budewa yashiga zubama kansa cikin wine glass, cikin murya datake adan shake mai bala’in dadi da zaki and calm yace “Hawwa Mamman Alhassan! Age 29, graduate of Bwari LGA school, BSC and MSC degree holder in criminologist, a police officer assign under a special Anti Kidnapping task force led by DIG, currently running PHD in same field, First daughter of crippled old man with 6 younger siblings, 4girls married, brother in uni last sis in boarding house at Minna, Mom died when you’re young, raised by step mom” dago kanta Hawwa tayi ahankali tadaura dara daran idanunta akanshi daidai yagama zuba wine din ya ijiye bottle din yadauki glass din da hannun dama yajuyo yakalleta kaman yanda take kallonshi, heart melting smile yasakin mata tareda nuna mata wine glass cup din yace “cheers” sannan yakai baki, ya akayi yasan everything about her like this daga jiya zuwa yau? Zare cup din yayi daga bakinshi yarike yana kallonta, danne duk wani tsoro Hawwa tayi tadanmai murmushin keta tace “wow I must be interesting! Wannan daga tsakanin jiya da yau harka haddace bio na” dan murmushin tayi tai bending head kadan like a little baby cikeda raini tace “interesting, tell me how many hours kabata akaina kana kokarin haddace all this? You don’t look like wanda keda saurin hadda” cikeda bakin iskanci Hawwa ta zaro idanu tadaura hannu abaki kadan tace “don’t tell me Pops boy baiyi bacci ba all night cramming information dina yake dan ya karanto mini first thing daya ganni today” baki zuciyan Khaleel yafarayi yadan fara huci, cikeda son ta cusamai bakin ciki tace “dama wat was I expecting from a jobless guy? You have nothing doing, so u have all the time dazaka dinga binciken background din mata” Kaman wuta haka Khaleel yaji maganan aransa amman saiya daure ya danne yana kallonta yace “a jobless guy that have the whole time in this world to put arrogant girls like you in their rightful place” murmushi kadan Hawwa tayi tace “kanka akeji, can you skip the talk and cut to d chase? Wani sako Babanka yabaka kabani”? Yatsine fuska Khaleel yayi saikuma yasa hannu yazare glasses na idanunshi ya ijiye a gefe ya juyo ya watsamata sexy mugayen idanunshi dakeyi kaman zasu kulle sabida bacci and bawani bacci yakeji ba yace “there’s no any bodyguard that’s missing, I just wanna play with your time and have some fun with you!”.

Faduwa sosai gaban Hawwa yayi ta dake takalleshi tareda zubamai idanu kaman yanda yake kallonta shima yakai glass cup din bakinshi yana sipping wine but still kallonta yake kaman wani bakin aljani, kafin yacire glass cup din daga bakinshi daidai ana budemusu wani dataji karan music kota ina, another gate aka bude musu, nan taga mata da maza ana party a pool wasu ma tsirara suke wlh babu komi ajikinsu matan, ga disco, ga security ta ko’ina ana gadinsu, ga abinci, ga drinks, gasu shisha, ga DJ, wai dama a Nigeria ana irin party haka da rana tsaka? A unguwa? Dasauri Hawwa tadauke kai daga kallonsu dan bata saba kallon tsiraici ba? Hawwa tajuyo ta kalli Khaleel dasauri tana hade fuska tace “ina ka kawoni”? Kallonta yayi yanadan biting lips nasa kadan sai kawai taga yayo kanta kaman zaki saida ta manna kanta jikin kujera tana numfashi da sauri dasauri, dab yakawo fuskanshi to nata yana kallon kwayar idanunta kaman yanda take kallon nashi, murya ciki ciki ta yanda koda wani zaizo wajen bazai iyajinsu ba yace “I’m here to have fun with you, you call my attention and you have all of it now” lumshe idanu Hawwa tayi dan kamshin da bakinshi keyi yau da breath dinshi kaman blackberries da akai mixing da rosted mints and cinnamon, kaman yasa turaren baki, bin dogayen eyelash nata Khaleel yayi da kallo kafin yadan koma baya ahankali jin hakanan heart beat nashi yayi destabilizing yayi knocking kofan batare dayayi magana ba hakan yasa Salman yabudemai kofan ya sauko ahankali yace “ask the gurls to bring her over” yawuce abinshi, Hawwa tabude idanu da sauri tawani taho amman sun rufe kofan tashiga buga kofan da karfi tana kiran “Khaleel, Khaleel, what is wrong with you? Menakeyi anan? Kubudemin kofa nakoma office, open the damn door” gafa security tsaitsaye jikin motan tana bugawa tana ihu amman kota kanta basubi ba, wani tunanine yazo mata da sauri takoma tashiga ciro wayanta daga aljihu but taji wayam ba waya da sauri ta tashi tashiga duba sit din data zauna amman ba wayanta ba alamun wayanta, gashi bata dauko bindiga ba, tasake leko glass na window taga harya wuce wajen wasu gayu irinsa suna gaisawa yakai shisha bakinsa yanasha yana murmushi dake karamai kyau kadan kadan, sai kawai takoma ta zauna taredasa hannu ta buge glass cup daya gamashan wine tayi ihu. “Ahhhhhh! Wannan wani kalan dan iskan yaro ne” glass din yafashe a motan, hannayenta tasa ta dafe kanta trying to calm herself down, taji ana kokarin bude kofan da sauri ta dago kanta wasu basamudayen mata ne guda uku sanye da swimsuit irin bodybuilder girls din nan ne, kaman security ne suma irin bouncers din nan, suna ganinta sukai murmushi sukace “Hi Officer, let’s go Oga yace akawoki” cikeda masifa Hawwa tace “shege kafasa wani cikinku yatabani yaga” babban cikinsu takallesu tace “awwwn isn’t she too cute? Soo angry! Waya batama baby rai” takai hannu zata taba Hawwa, kwasheta Hawwa tayi da kafa ta zube akasa, ta gyara tsayuwa da sauri a motan tai making fist da hannunta kaman mai shirin wrestling babu tsoro kan fuskanta takalli duka matan cus biyu na kasa dayace acikin motan tace “kuzo, kuyi mistake din tabani” shi kanshi Salman da sauran security kallonta suke aranshi yace “wowww, this girl is fun” wacce Hawwa ta kwashe dake kasa tafashe da dariya kafin ta tashi ahankali tana kallon Hawwa tace “let’s go ladies” kawai suka shigo motan suna kokarin kamata Hawwa ta shiga kokawa dasu tana kaimusu good good punches kawai suka dagata chak dan kattai ne su har uku suka fito da ita, Hawwa na ihu tana kokarin kwace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login