Showing 150001 words to 153000 words out of 184554 words

Chapter 51 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1890

anywhere with you Ibrahim Khaleel!” Saikuma tajuyo zuciya na debanta fuuu tadawo gaban kujeran dayake zaune ta tsaya tareda bude jakan hannunta duk yana kallonta envelope na court taciro ta ijiye kan hannun kujeran dayake kai yabi sammacin da kallo tajuya tawuce fuuu tafara hawa staircase, ahankali kaman baisan metayi ba yace “hurry up Moonshine, I kept something on your bed shizaki saka” juyowa Hawwa tayi cikeda fada kaman wata zakanya tace “nace ba inda zani dakai so also I’m not gonna wear anything from you” kallonta yayi shima cikin ido yace “Baba ke neman mu wajenshi zamu, the clothes shiya aiko dasu plus this one I’m wearing” chak Hawwa ta tsaya tana kallonshi, karanta yakai wajen Baba saikuma ta juya zata wuce Khaleel yace “after magrib” dakinta tawuce tana shiga taga wani mahaukacin designer abaya sabo fil ajikin hanger irin wanda take gani a IG na 20M dinnan black ga duwatsu ya Allah kaman ka lashe abayan saiga wani takalmi dan heel na Dior pink sai wani bottega hand purse pink ya Allah sunyi kyau, note tagani dasauri takalla handwriting din Khaleel ne hannu tasa tadauka yace “can you please do makeup? Banso Baba yasan we are fighting” ijiye note din tayi da sauri sai kawai tafada bayi toh idan Baba baisan suna fada a maisa yake nemansu? Dawani kudi yasainusu kayan nan, bataso asan sunyi fada za’a hanata shigar da karan kotu.

Wanka tayi tafito tazauna kawai tafara makeup gabanta na faduwa, foundation ta shafa da hoda tai carving eyebrows nata tasa concealer ta tai highlighting yau pink lipstick tasa sabida takalmi da jakan taga pink ne, ta tashi tai salla sannan tawuce tasaka inner tafito tasa abayan tunda take bata taba saka abaya daya mata kyau like this ba heel din tasa tai wani irin kyau kaman aljana, tadauki purse din wlh kaman balarabiya tana fesa turaruka, kallon kanta tayi kyan yamayi yawa kaman taje ta goge makeup din daidai anyi knockin tareda bude kofan, chak breath na Khaleel ya tsaya sabida yanda Hawwa tayi kyau dauke kanta tayi from kallonshi sabida yamata kyau dayawa a idanu hakan yasa shima ya iya daidaita kanshi yace “let’s go” yajuya yayi gaba itama tafito gashi ta iya tafiya da heel tundaga staircase take kallon sammacin data bashi dake inda ta ijiye daga gani ko tabawa baimayiba, kofa yabude mata yajuyo yana kallonta yana jiranta tazo tana zuwa tafita kamshin datake yawani shaka yabiyota abaya taga wata sabuwan Maybach pink ke jiransu bude mata yayi tazo tashiga batare data kalleshi ba shima ya shiga ciki ya zauna, aka rufo musu kofa aka ja motan kamshin datakeyi da kamshin dayakeyi sun hadu sun gauraye motan, ahankali Khaleel yake kai hannunshi zuwa nata dake kan kujeran gabanshi har faduwa yake but he just wanna touch her ko kadan ne, tun safe bai riketa ba not yayi feeling skin nata, even if it’s just for a moment he wants to touch her, hannunshi yadaura saman nata ahankali dasauri Hawwa tajuyo takalleshi suka hada idanu tamai wani kallon fitinan bala’i ta fizge hannunta, dan ijiyan zuciya Khaleel yasauke yakoma ya jingina da bango kujeran.

Gaban wani babban teaching hospital yaga sunyi parking already saitaga ma’aikatan Khaleel dasu bodyguards duk tsaye wajen kaman ansan da zuwansu, ga CMac na asibitin da wata HOD da couples of Doctors and metrons, budu musu akayi Khaleel yasauko yakalleta yace “come” adan tsorace tace “something happened to Baba ne?” Girgixamai kai yayi yace “No” sakkowa tayi ahankali suka fara tafiya looking elegantly cute together sai kawai yarike mata hannu akwai mutane awajen kuma kallonsu ake ga ma’aikatan sa hakan yasa bata karbe hannun ba, CMac din yakaraso da sauri yana bama Khaleel hannu yace “welcome Sir and Ma” gyadamusu kai yayi suka babbama Khaleel hannu sauran likitoci kafin Cmac yayi gaba suka shiga cikin hospital din gaban wani newly built abi renovated ICU taga sunyi Khaleel na rike da hannunta sai kawai aka bata tray da scissors akai jama’a ma taruwa awajen harda patient, CMac yace “Ma please”Khaleel yasaki hannunta da idanu yace mata tabude looking confuse tadauki scissor da ake bata ta yanke ribbon din aka shiga sabon ward din da gadaje daban daban keciki ga machines, devices, har chairs komi sabi da laptops and desktop, an rubuta renovated by Hawwa in some space haka, ana gama shigowa kawai sai Cmac yace “adakata akwai statement da ake fadi honor who honors you” sai kawai yafara tafi yana kallon Hawwa da Khaleel yace “Happy birthday day to you” haba kowa yadauki wakan ana kallon Hawwa ana clapping akace “Happy birthday Dear Mrs Hawwa, Happy Birthday to youuu” dasauri Hawwa takalli Khaleel dake mata murmushi sosai shima yana clapping yana singing dasu for a moment Hawwa was confuse saikuma dasauri tafito wayanta daga wallet ta taba tana kallon todays date no wonder taga banks nata sun mata message but bata duba ba, today is her birthday, daidai lokacin sukace. “Happy birthday Mrs Ibrahim Khaleel, hip hip hop hip” akace “hurray



Cmac yakarbi flowers da aka kawomai yace “Ma thank you for what you did to our hospital, thank you for the donation, we will never forget this, komi na dakin nan is embedded da name naki duk wanda yazo dakin nan kinada ladansa, there’s no better way to celebrate birthday than this Ma, thank you Ma’am and thank you Sir, our entire hospital is saying what” jama’a akace “Thank you Mrs Hawwa”sauran Doctors sukai shouting “once again Happy Birthday Ma” akai tafi Hawwa tai shiru tana kallon Khaleel dake mata murmushi sosai shima yana clapping yana kallonta with so much admiration and love zuciyan Hawwa kawai taji ya tsumu tanajin goosebumps ajikinta, sai kawai Khaleel yakama hannunta sukaje O&G ward bangaren Female surgical, Ma’aikatan Khaleel su Salman na shigowa da envelops dayawa masu kiba, dawasu manya manyan bags na goodies, ya karbi envelops din yakama hannun Hawwa yasaka aciki murya chan ciki yace “share it’s your birthday” Khaleel yakalli mutanen ward din da duk suka mike anga goodies yace “it’s my wife birthday” Ya Allah zokaji yanda akema Hawwa addu’a suka shiga raba abubuwan bed by bed wata mata data bude envelop nata taga kudin dake ciki kawai saitazo tai kneeeling gaban Hawwa ta rungumeta tana kuka security Khaleel zasu dakatar da ita Hawwa ta hana, ahankali ta duka tace “Mama ya isa dena kuka, menene”?

Matan tace “kinga y’ata raping nata akayi ciki yaki fita haihuwa yazo operation bamu da kosisi, da karo karo muka iya biyan kudin aiki, abinci saidai yan nan ward su tsammana, wannan kudi jinake kaman kin bani duniya da lahira Hajiya, Allah ya barki da mijinki, Allah yabaku yara masu tausayi da imani da kirki irinku” yan ward sukace Ameen, tace “nagode nagode nagode yallabai nagode nagode nagode” yarinyar itama tana kokarin saukowa daga gado dasauri Hawwa takamata tace “no karki tashi” yarinyar tace “nagode Anty kinji, ki taimakeni ni da Mamana” kuka Hawwa taji yazo mata idanunta sukai jaaa yarinyar is so small, ahankali Khaleel yazo kusada ita ganin tana shirin kuka and baiso tai kuka yace “do you want to help them”? Gyadama Khaleel kai tayi ahankali anatse yace “okay we will sponsor her treatment and help them financially agida” gyadamai kai Hawwa tayi yariketa sukai komi suka wuce ward uku sukaje sunsha addu’a sannan suka wuce mota suka tafi.

Wani fancy restaurant sukaje da babu kowa aciki kaman yayi reserving gabaki daya an gyara anyi decoration na love kuma ba haske sosai wajen wani kujera yaje yajamata yana kallonta cikeda so wani iri kirjin Hawwa keyi, no one has ever done abubuwan da Khaleel yamata har samarin datayi a da like babu wanda ma yataba attempt din nan, all of them behave da ita kaman they’re doing her a favor na cewa ma suna sonta, kaman kartazo ta tsaya tana kallon Khaleel dake kallonta amman saitazo ta zauna ahankali daidai an kunna wani kalan wuta wajen yayi mahaukacin kyau saiga ma’aikatan sun taho rike da cake da aka kunna fireworks masu kyau ajiki anyi playing wakan happy birthday akazo aka ijiye agabanta ma’aikatan na waka tareda Khaleel yana mata murmushi sosai Hawwa na kallonshi ko kyafta idanu batayi, he should be angry! They had a serious fight this morning, bata gida tun safe, takawomai letter from court seeking for divorce but he’s celebrating her birthday with her smiling from cheek to cheek yana mata kallon that screams i love you! What is going on? Why is she feeling kaman tana nadaman kaishi court? Why is she feeling kaman bata kyauta ba? Why is she feeling bad all of a sudden?? Tun shekaran jiya yake cemata kartai girki they’re going on a date, from the look of things yadade yana planning all of this, no one has ever celebrated her like this! This is the best birthday of her entire life! Cikin very very beautiful voice Khaleel yana kallonta right in the eye yace “Happy birthday Hauwa’u!”.

EPISODE

Hawaye Hawwa taji sun shiga tsatso mata daga idanu dasauri ta dauke kai takai bayan hannunta tana share idanunta ahankali Khaleel dake kallonta yace “make a wish and blow your candle” juyowa tayi tasake kallon Khaleel da red idanunta zuciyanta nawani iri sai kuma ta kalli candle din kafin ahankali tai blowing nashi Khaleel yayi clapping hands nashi yace “yayyyyyy” kallonshi Hawwa tasakeyi the way Khaleel is smiling looking happy ko birthday nashi sai haka “taste your cake Shiny” Shiru tayi jin yakirata da sabon suna Shiny, Moonshine dinne shine yakoma Shiny yanzu? Wukan ta dauka tai cutting cake din a plate tadauki spoon tasaka aciki sai kuma ta kalli Khaleel dake kallonta still smiling kawai hakanan taji no he deserves to eat the cake before her sef tadauki plate din ahankali tamikamai batare datai magana ba, shiru Khaleel yayi yana kallonta yanda ta mikomai cake din, gently ya tashi daga kan kujera yataho dab da ita ya tsaya saikuma yasa hannu ya karbi plate din ahankali yasa spoon din ya gutsiri cake din yakai bakinta tsayawa tayi tana kallon kwayan idanunshi shima haka, he’s so selfless, he’s still making it about her, it’s her birthday! Lumshe mata idanu yayi yabudesu cikin murya dake kashema mace jiki da zuciya da soyayya yace “Happy 30th birthday My Kulu! I love you!” Wannan karan haka hawayen yacika idanunta tam sai kyalli suke tana kallonshi, cikin muryan so Khaleel yace “I love you soooooo much Hawwa!” lumshe idanu Hawwa tayi kawai hawayen suka gangaro kasa, ahankali Khaleel yace “May Allah bless your new age! May Allah bless you! May Allah grant you all your heart desires! May you be always alwaysss happy my Baby! I love you! I will always love you and I will never stop loving you! Inasonki sosai Hawwa na!” Bude idanunta Hawwa tayi takalli Khaleel shima yana kallonta hawaye sun cicciko mata she feels like hugging him, cikeda wasa yakai hannunshi kan fuskanta yace “bakisan birthday girls basa kuka ba, eat your cake, haaaaa” ahankali Hawwa tabude bakinta yasamata cake din acikin baki ahankali yasake murmushi sai kawai ya gutsiri cake din shima kadan cus baison cake hakanan yakai bakinshi yace “Uhmm it’s yummy” ya ijiye plate din agabanta aka shiga kawo musu appetizer yazauna, chan sai main course kafin dessert, Hawwa bini bini tana kallon Khaleel dake cin abinci dudda ba sosai ba tun aman dayayi dazu cikinshi is tight, aka samusu very soft song tanata kallonshi ko zaiyi rawa, but baiyiba, everything was cozy and just perfect, it looks like a dream, wat a romantic birthday celebration dudda suna fada. Sai around 11 suka fito daga wajen cake dinta kadai yasa akai packaging nashi ya karban mata suka fito aka bude musu bayan mota ta shiga, shima yashigo hakanan taji she’s feeling kaman yasake holding hand nata yanzu bazata fizge ba tadaura hannun kan seat but har sukakai gida ko attempting riketa baiyiba kaman ba Khaleel ba, parking akayi aka fita aka bude musu zata fita karaf taji yarike hannunta key motan ya karba yasa a hannunta ya maida hannunta yarufe yace “your birthday gift” hannunta yasaki yarigata fita Hawwa tabude hannunta takalli key sabuwa pink Maybach din dasuke ciki ga leda tako’ina wai nata ne.

Tashi tayi tafito tashiga flat nasu itama, Khaleel baya falo idanunta sauka sukayi kan later sammacin data kawomai akan hannun kujera ta maida kofan ahankali tarufe tana kallon latter harta shigo falo takarasa wajen hannunta tamika ahankali dakedan rawa takai zata dauka saikuma ta dakata kirjinta na bugawa takai almost 60secs tana kallon envelop din kafin ahankali tajaye hannunta duka tawuce staircase tahau tana kallon kofan dakinshi data gani a rufe tawuce nata dakin tabude ahankali ta shiga saitaga manya manyan paper bags na kusan all designers, Hermes, Bottega, Dior, Gucci, Prada, Louis Vuitton, tana gani tasan gifts daya saya mata ne maida kofan tayi tarufe taji bazama ta bude ko daya kicinsu ba sabida yanda takejin guilt amman sai idanunta ya dauka kan flowers da note dake kai, ahankali ta zare heel na kafanta tawuce wajen tadauki floweres din kamshi sosai note din tafara dauka tana kallo.

Dearest wife today is an important day for you while for me nothing is as important as you in my life! I’m grateful to Allah for bringing you into my life! I love you Hawwa! I will always be here even if it doesn’t look like it! But I’m right here!

Lumshe idanu Hawwa tayi kawai saita sami kanta da kankame flowers din da note din a kirjinta takai almost 30mins ahaka tunawa da batai salla ba yasa ta ijiye komi tafada bayi taje tai salla tana idarwa ta linke komi tasake fadawa bayi tai wanka tafito daure da towel duka gifts din tashiga kwashewa tana kaiwa closet daidai tagama kwashewa taga wani envelop dasauri tadauka kawai taga open ticket ne na Qatar business class seat na honeymoon yarubuta note dasauri tabude.

“l don’t wanna force you, anytime you feel you’re ready to go on honeymoon with me just put the date and give me together with you passport, I can’t wait for us to have our honeymoon! I love you Wifey”.

Ya Allah wani iri Hawwa taji zuciyanta yayi ahankali tamaida komi ta ijiye a closet nata harda ticket din tafito tazauna akan gado tai shiru tana kallon kofanta chan kasan zuciyanta tana addu’a he should just walk in through the door but bataso tai admitting abinda zuciyanta keji kenan dasauri ta juya tabama kofan baya tana kashe wutan dakin tana sauke ijiyan zuciya ahankali tana runtse idanunta.

Tun jiya batai bacci ba tanaso tayi but tunanin Khaleel ya addabi zuciyanta, dasauri tasake juyowa tana kallon kofan again still tai shiru takasa bacci wlh takai 1hr tana kallon kofan saikuma tasaka hannunta tadauki wayanta ta danna data ta kunna tashiga instagram page dinshi taje tashiga hotunan shi tashiga kallo tana murmushi sosai saikuma tashiga hotunan su na biki tana kallonshi, hawaye taji sun taru a idanunta batamasan takamaimen meke damunta ba, Khaleel yamata laifi okay, and yes bataso tayi zaman aure da mutum mai halinshi, but kawai she’s feeling bad, tanaji kaman kotun datakaishi she went tooo far kaman bata kyauta ba, she’s feeling guilty, maisa tai acting kaman wacce bata da iyaye? Yes ansan ita ke zama da Khaleel not iyayenta wat she did shows batada any respect ko courtesy towards iyayenta da iyayenshi, nor Ammi not Baba not kuma Baban Khaleel da mahaifiyarshi ai da takai kara, why is she acting kaman babu wanda ya isa da ita aduniya? Koma menene data fara kiran Ammi ta sanar da ita kafin taje court she overreacted right? Ijiyan zuciya ta sauke tana sake tashi ta jingina da bangon gado ta kunna side lamp na gefen gadon tarasa yazatayi she’s feeling so badddd zuciyanta baya mata dadi ko kadan kaman akwai wani abu akan zuciyanta haka takeji.

EPISODE

Har 2:00AM Hawwa na zaune awajen jin kaman tana loosing mind nata akan zancen kotun nan takasa samin natsuwa azuciyanta sabida abin yasa ta yaye bargo dagakan kafafunta tazura flops nata tabude kofa ahankali batare data bari kofan yayi kara ba ta kalli kofan Khaleel sannan tawuce tashiga sauka kasa taga letter na inda tabari tawuce har wajen ta tsaya tana kallon envelop din hannunta na rawa sosai sai kawai tadauka dasauri tajuya tayi staircase tashiga hawa tawuce sama tabude dakinta ahankali tamaida kofan tarufe tazauna dasauri tama manta dare yayi tashiga daukan number jikin envelop din wanda she believe number matar data mata abin ne yau, dialing nunber tayi kafafunta na rawa takai wayan kunnenta dasauri she just wants to tell them tafasa amman har wayan yagama ringing ba’a dagaba, sake dialing number tayi still ba’a daukaba, ahankali Hawwa tace “dan Allah ki dauka” ana uku ma bata dauka ba, ijiye wayan tayi tashiga yaga envelope din dasauri saida tai gutsi gutsi da komi sannan ta tattara komi tasa asaman riganta tawuce bayi ta zuba a pit tai flushing tana sauke ijiyan zuciya tadauro alwala tafito tasaka hijabi ta shimfida dadduma tahau kai tafara salla kawai tana kaiwa sujjada saita fashe da kuka ahaka ta idar ta zauna tadaga hannunta tace “Ya Allah I know I’ve been praying ina rokonka kabani miji nagari kamili nutsasse wanda yake bauta maka da kyau, wanda zai soni, Ya Allah I’m confused about Khaleel, he’s complete opposite of abinda na rokeka and bansan mesa ka kawoshi rayuwana ba, Ya Allah I’m really really confuse, Ya Allah help me, make my heart understand,

I want my heart to know him, I want to know shine zabin dakamin? Ya Allah guide my step, idan bashi bane kabani mijina my right man, Ya Allah help me I don’t even know menakeji? I’m feeling bad na kaishi court somehow somehow I feel koma menene he doesn’t deserve na makashi a kotu, koba komi he helped me in so many ways” tai dan shiru kunya na kamata tayi admitting abubuwan daya mata

Ahankali tace “he saved me time without number, he is always there for me, he, he, he loves Baba na so

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login