Showing 168001 words to 171000 words out of 184554 words
gabaki babu abinda kemai dadi yace “ni yaro ne zaki wani bini hospital they will send the result to Dad” Murmushi Mom kawai tayi ganin first of all he’s hurt and not in good mood tace “to shikenan yarona uhmm cigaba da cin abincin ka” baki yabude mata tadebo kunu a spoon zatakai bakinshi ta gefen idanunshi yafara ganin kaman yaga Hawwa wai idanunshi gizo sukemai ne yadai daure yaki motsi gently Hawwa tafito daga kitchen din tazo wajen kirjinta na bugawa kawai saita kara kneeling awajen batare dataji kunyan Mom ba ko yan aikin dake kitchen ahankali tace “go……g…good morning Husby” Kaman Khaleel baisan mutum na wajenba yakalli Mom batare daya sha kunun datake bashi ba, voice nashi ba dadi yace “did she make this food?” Yatsine fuska Mom tayi tace “ban sata ba taje takama aikin daga hannun masu yi tahau yi” mikewa Khaleel yayi cikin kakkausan murya yace “this should be the first and last time za’a bani abinci made by her Mom!” Wani irin katsewa zuciyan Hawwa yayi tana wajen aduke tana kallon Khaleel sai kawai yadauki tissue ya share bakinshi ahankali yace “bye Mom” yajuya zai tafi karaf Hawwa takama hannunshi tarike dasauri yajuyo ranshi a masifan bace, tashi Hawwa tayi ahankali takalleshi kaman yanda yake kallonta da tsana akan idanunshi gabanta faduwa yake sosai, bakinta dake rawa sosai tashiga budewa zatai magana but zuciyanta ma ba karfi kawai tafashe mai da wani sassanyar kuka yakalli hand dinshi data rike yace “sakeni! Let goo off my hand!” Kin sakinshi Hawwa tayi tana kallon kwayan idanunshi ganin yanda rayuwa juyi juyi ne, da fa ita Khaleel ke rikewa haka tadinga bala’i tana gaggayamai magana tana cewa yasaketa kawai saitaji she’s regretting everything more, cikin murya mai bala’in rauni batare data sakeshi ba tace “Husbyyyyy I want to talk to you! Please give me just a minute, dan Allah” dauke idanu daga kallonta Khaleel yayi yace “for the last time let go off my hand and kada bakinki yakara kirana da that name my name is Ibrahim Khaleel” Kirjin Hawwa bugawa kawai yake da tsoro da fargaban ganin mijinta ya tsaneta muryanta babu ragowan kwari tace “I love……” “Ke!” Khaleel ya fizge hannunshi daga nata ya nunata da yatsa idanunshi na kadawa saikuma ya matso dab da ita ta yanda dagashi sai ita zasuji maganan yace “don’t you dare say that word cus it makes me even hate you more! Na tsaneki!” Baya Hawwa tayi kaman zata fadi dasauri ta dafa chair Khaleel ya watsamata mugun kallo yawuce yayi kofa abinshi.
EPISODE
Khaleel na fita yashige motanshi yana sauke ijiyan zuciya.
Momy da fadansu kaman tana kallon tv haka abin yake mata tana xaune abinta a dinning tana kallo tawani harari Hawwa dake zaune akasan falon tana goge fuska sai kawai ta wuce dakinta abinta.
Khaleel na zaune cikin mota wayanshi yahau ringing Baba ne hakan yadaga Baba yace “kazo gida ina nemanka” ahankali yace “toh” har unguwansu yaje ya gyara buyuran rigansa yafito daga mota Baba namai murmushi sai kawai yakama hannunshi suka shiga xaure dayayi shimfida ya zauna shima ya zauna, Baba yace “ya jikinka?” Anatse yace “naji sauki Baba” Baba yace “yau result dinka zai fito ko”? Gyadamai kai yayi yace “amman inaso Dady na ya karbo I told Dr yabashi result din” murmushi Baba yayi cikeda so yace “zamuji alkhairi in sha Allah” yayi shiru hakan yasa Khaleel yace “Baba menene?” Cus yaga yanayin shi, anatse Baba yace “maisa kake shaye shaye Ibrahima?” Dasauri Khaleel ya kalli Baba saikuma ya sunnar da kanshi kasa kunya na kamashi sosai, ahankali aba yace “jiya mahaifinka ya sanar damu” Baba yayi shiru yace “ko kadan bakai kama da mai yiba Ibrahima yaran arziki basa shaye shaye kuma nasan kai yaron arziki ne dan haka nace saina kiraka namaka fada, inaso ka bari kaman yanda mahaifinka yace bayan kayı aure karage yi, inaso ka cigaba ahaka kama daina gabaki daya, sabida Allah sannan sabida lafiyan jikinka, inaso kazama mutumin arziki kamili yanzu kai ba yaro bane, kanada mata da yarinya duk rayuwan banzan nan abarma yara kaji, akwai mutum biyu yanzu da hakkinsu na kanka dole kazama namiji kafita daga sahun yaro ko yaron Mamanshi kadawo namiji tsayayye kaji” gyadamai kai Khaleel yayi Baba yace “inaso ka rike kanka, kaji tsoron Allah ka gyara rayuwanka kanunama matarka kasan mai kakeyi kayı haka zakaga bazata taba rainaka ba kajini”? Anatse Baba yace “inasonka ne Ibrahima saisa nake maka fada, inaso kazama mutumin arziki a better person, na hana Hawwa aiki but kai inaso ka dinga zuwa naka aikin dazaran ka gama samun lafiya kaji” gyadamai kai Khaleel yayi, Baba yadanyi shiru chan yace “Hawwa batason Baban Yaseer wlh, bata taba sonshi ba kuma bazata taba sonshi ba wlh” lumshe idanu Khaleel yayi, ahankali yace “I know! Nasan dalilin dayasa tai magana kawai kalman yacimin……” saikuma yayi shiru yadan sauke ijiyan zuciya yace “Dady yagayama min everything da maganan da sukayi, yan sandan da aka tura hospital din sun karbi wayansa sun tabbatar min yajeyi stalking Matana yakeyi, ga hotunanta tundaga sanda tafito daga gidana ma, da every move nata” Gyadamai kai Baba yayi yace “rayuwan nan zomu saba ne zomu shirya, Hawwa tayi ba daidai ba amman yanzu tasan tana kaunarka kayakuri kaji, Ibrahima ina sonka da diyata sosai tayi kuskure ka gwada mata tayi sabida nan gaba kada ta karayin makamancin sa, amman kada ka tsaneta yarinya ce kasan mata da kalan tunanin su gasu da tapka shirme, kayakuri” gyadama Baba kai yayi ahankali, Baba ya shafa fuskanshi, dan kallonshi Khaleel yayi for the first time sai yayi dan murmushi kadan yace “thank you Baba namaka alkawari zan gyara halayena kamin addu’a kaji Baba” Baba yace ina maka yarona, Khaleel yatashi yace “zan tafi” Baba yarakashi har waje yatafi.
Wuraren 12:30 na rana Mom ta farka daga baccin safiyan datayi ta watsa ruwa tafito tana sanye da waya mahaukaciyan lace tazuba gwalagwalai da 2friends nata zasuzo ta tsaya turus ganin Hawwa a falo ita kadai zaune akan kujera takife kanta a hannun kujera bacci yadan kwasheta mamaki abin yabama Mom badai tun safen nan yarinyar nan tana nan bata koma side nata taje ta kwanta tayi bacci tahuta ba.
Wucewa dakin ma’aikatanta tayi suna ganinta duk suka tashi zaune tace “an gama girke girken danace ayi?” Babban Chef nata tace “Mrs Khaleel cooked everything Ma, she asked us to rest” baki Mom tasaki saikuma ranta abace tafito tawuce dinning tashiga bude warmers ya Allah! Lafiyayyen biryani Mandi, gizzard dodo, pepper chicken, kofta, samosas, moimoi, salad, sai juice na fresh juice zobo da cucumber juice Hawwa tayi, sannan ta yankama Mom fruits in very very fine shapes cus taga Mom na shan fruits dazu, Mom bata taba ganin irin fine shapes na slices din nan ba sai kawai tajuyo takalli Hawwa daidai PA na zuwa wajen da suit tace “yanzun nan tai baccin Ma” Dasauri Mom tace “ba dole ba ta daurama kanta aiki kaman jaka ga masu aiki duk suna nan” dan murmushi PA tayi tace “the food is delicious Ma tazubamana namu all of us ate” kallon PA Mom tayi saikuma ya harareta ba yabo ba fallasa tace “wake her up taje ta kwanta ta huta please” tana maganan tawuce sabida wayanta dake ringing PA tai wajen Hawwa ahankali tayi taping chair dasauri Hawwa tabude idanu PA tace “Ma tace kije side dinki ki kwanta ki huta” dasauri tace
Bangaji ba daidai bakin Mom na parking motocinsu PA tawuceta tai gaba Hawwa tawuce dinning tana gyara komi tana kara gyara mayafinta Mom tafito zatai magana pA na shigowa da bakin wasu matan ministers ne dasauri Mom tai wajen su suka rungume juna tace “welcome Hajiya Hajara, Welcome Hajiya Shema” suka shiga gaishe gaishe ahankali Hawwa tazo wajen tadan duka cikeda girmamawa tace “sannunku da zuwa ina yininku” murmushi dukansu sukama Hawwa sukace “your daughter Inlaw ko wow she’s so beautiful kinsan lokacin bikin ina Qatar ban samu nazo ba” Hajiya shema tafadi tana kallon Hawwa, ahankali Mom tace “muje muyi lunch first before anything”
Ma’aikatan Mom da uniform suka fito zasuyi serving Hawwa tace “don’t worry I will do it” Hawwa tazo wajen anatse tana bude komi takalli kawayen Mom tace “Anty wat do you want me to serve you”? Hajiya Hajara tace “wow your daughter Inlaw is so homely and cultured” dan murmushi kadan Mom tayi, Shema’u tace “serve me Mandi da kofta salad dai this cucumber juice” zuba musu Hawwa tayi sannan takalli Mom data mata wani shegen kallo but bata damuna, cikeda girmamawa tace “Mommy mezan zuba miki ko kinason wani abu daban na dafa miki “? Atare duka kawayen Mom sukace “wowwww Hajiya Zee we want daughter in law like this oo” dan murmushi kadan Mom tayi tace “samin moimoi da sauce” Hawwa tadau plate mai kyau tasama Mom da nama ta ijiye gabanta tasamata spoon tace “Mommy zakici fruits na yanka miki naga kinason avocado harda shi” sosai Mom ke kallon Hawwa saikuma tace “give me small” sama Mom tayi sannan tabar wajen sai kawai ta shiga kitchen ta zauna kan kujera dake island din batasan wani daki zata shiga ba
Kawayen suna fara yaban abincin Hawwa Mom ba yanda zatayi tana kai moimoi bakinta Ya Allah! Saida taji kunnenta yayi motsi sabida dadi this girl can cook like this? She has chef oo but akwai wani homely and love taste da abincin Hawwa kedashi tass ta cinye ta kara saida tacı moimoi uku kawayenta sunci sukai nak Hajiya Hajara tace “Hajiya Zeenatu anya bazan kawo matar d’ana Muhammadu tazo wajen matar danki ta koyi girki ba kuwa? Kinga har cooking school na sata but duk abanxa gaskiya matar danki ta iya girki wat! Please can I package this kofta naje dashi gida with this fresh juice” murmushi sosai Mom tayi tace “sure sure haba” sunci abinci sosai Mom was just feeling herself suka dawo falo suna hira saiga Hawwa tafito rike da tray na Bowl of ice cream da brownie Hajiya Shema tace “anya kinaso mu koma gidanmu kuwa Hajiya Zeenatu diyarki ta karyamin wait loss see standard dessert ice cream da brownie” suka daddauka Hawwa taja stool ta ijiye gaban Mommy tawuce kitchen Mom ta kalli kawayenta tace ina zuwa
Kitchen tabiyo Hawwa tana rufe kofa dasauri Hawwa ta juyo cikeda masifa Mom tace “so kike ace na maida matar d’ana yar aiki na?” Kan Hawwa na kasa Mom tadan dafa goshinta tace “wat are you still doing in my side eh? Wuce kitafi nagaji da ganinki wlh” Mom tana maganan tafito tana murmushi.
EPISODE
Kofan kitchen Hawwa tayi tayi alwala anan pampo baya tashigo tafito tashiga dakin masu aiki tayi salla aciki tanaji kawayen Momy na tambayanta Mom na cewa ta kwanta taji sunce agaisheta please, tana nan cikin dakin kusan 10min saiga PA tazo dakin tace “Madam tace nakiraki” tashi Hawwa tayi tafito kanta akasa Mom ta kalleta so take tarufeta da masifa but saitaji kuma takasa ba yabo ba fallasa tace “kinci abinci?” Girgiza mata kai Hawwa tayi, cikeda masifa Mom tace “wuce kije kidiba kibarmin flat dina kitafi naki” batai musu ba saitaje dinning din dahar an gyara tadauki karamin plate ta debi abinci kadan tasa spoon ta zauna takai bakinta wlh takasa ci, damuwa yamata yawa da bata iyacin abinci Mom takai kusan 3min tana kallonta, tadan sauke ijiyan zuciya tace “jiranki nake ki cinye abincin nan kitashi ki bar bargarena” dasauri tashiga cusama kanta abincin, sai kawai ta kware tafara tari dasauri Mom tace “give her water PA” wucewa wajen PA tayi da sauri tasama Hawwa ruwa a cup tabata da sauri ta karba tasha Mom duktana kallonta, ita kawai tabarmata flat cus bamataso ganinta tazo tafara tausayinta danta farajin wani iri iri game da yarinyar itakuma tasan batason Hawwa ta tsaneta sabida abinda tama danta, ijiye cup din Hawwa tayi ta karasa dannama kanta abincin sannan tadauki plate din Mom tace “bama PA na plate din zatakai kitchen wuce kitafi” ahankali Hawwa tabata ta taho tana tafiya kaman bataso tawuce kofa Mom na hararanta saikuma ta tsaya wajen kofan tadan juyo ta kalli Mom dasauri Mom tadauke kai tana tabe baki hakan yasa Hawwa tabude kofan tafita daidai Motan Noor na shigowa gidan tadawo daga school tun kafin ayi parking tafara ihu Hawwa ta tsaya Noor tafito ana parking tazo da gudun bala’i kaman tai shekara bataga Hawwa ba tace “Mommy FAA” Hawwa tabude mata hannu tawani rungumeta kawai Mom tabude kofa tace “saken mini yarinya, Princess come here” sakin Noor Hawwa tayi Mom ta dauketa suka wuce ciki Noor nama Hawwa bye, Hawwa tawuce flat nata ahankali zuciyanta ba dadi.
Tana zama taji ana sake bude gate dasauri ta daga labule ganin motan Khaleel ne sai kawai tawuce wajen kofa tabude kofan tafito tundaga mota Khaleel yake kallon Hawwa da tsabagen sauri bama ta yafa gyalenta tarufe kirjinta ba, kawai akanta gyalen yake, kirjinta duka abude kana ganin tundaga wuyanta har kasa tana tahowa dasauri, yashiga bin compound din da kallo ga few security nasu maza gashi atampan yamata kyau, dinkin yakamata, abu yaji ya tsayamai a wuya dasauri yarike, Salman na parking yafito batare daya jira an budemai kofan ba zai wuce, daidai Hawwa tasha gabanshi looking very emotional kawai tai hugging nashi chak Khaleel ya tsaya! Hawwa ta manna kirjinta a kirjinshi sosai ta manna fuskanta awuyanshi tace “Husbyyyyy please talk to me dan Allah, dan Allah” cikin kakkausan murya Khaleel yakasa tureta yace “I will count three idan baki fita daga jikina ba saina fitar dake na yardaki I don’t care muna outside!” Wani iri kirjin Hawwa yayi jin upon all the boobs data manna mai a jiki did not work another kuka kawai taji yana taso mata, ahankali Khaleel yace “one! Two! Thr…..” fita daga jikinshi tayi da sauri tana komawa baya wlh wani tsoron Khaleel take! Baki tabude zatai magana tana sheshekan kuka Khaleel yawani daka mata tsawa. “I said go back to your room!” Harwani gudu baya Hawwa tayi tana kallonshi sabida tsoro saikuma tajuya dasauri takoma side dinta kirjin Khaleel na tafarfasa ganin yanda tabar kirjinta awaje ga maza a compound nasu tako’ina mtsswww yajuyo yakalli Salamn da kanshi ke kasa yace “all of this security I don’t want them here anymore su dinga tsayawa a second gate, I don’t want men here that includes you unless na bukaci wani abu or i want to see someone” dasauri Salman yace “yes Sir” Khaleel yawuce flat nasu ranshi duk abace fuuu yashiga ciki Noor tazo da gudu tawani rungumeshi tace “Dady” daukanta yayi yace “my princess have you eaten? I’m taking you to islamiyya by 4” dasauri Mom tace “islamiyya kuma Khaleel? Batai karama da yawa ba she’s just 4 fa kasan islamiyun nan dukan yara suke fa” babu joy akan muryanshi yace “idan she’s not too to start school she’s not too small to start islamiyya, babu wanda zai dakanmin yarinya, princess kinason Islamiya?” Dasauri Noor tace “yes even Mommy FAA once said zata tell Dady na yasani a islamiyya so I love islamiyya” mommy ta harari Noor, Khaleel yadan kwanta akan kujera Mom tace muje kaci abinci girgiza mata kai yayi ahankali, cikeda damuwa sosai yace “Noor come here” dasauri yarinyar tazo tanamai murmushi daukanta yayi yasa akirjinshi yarinyar ta kwanta ajikinshi lamooo murya chan kasa yace “Dady loves Noor so much”murmushi tamai tace “Noor loves Dady too alot, and I love Momy FAA” shiru Khaleel yayi wlh he’s missing matarshi sosai kaman zai zare yana rikeda ita har saida Mom tace “saketa taje taci abinci Leely” wucewa sukayi itada Mom sukaje dinning Mom na feeding nata, he’s very very angry with Hawwa but he’s missing her, he can’t eat properly, ba daman ya zauna Tuna’nın ta ya addabeshi, this few days fight from dai ranan dayaje party nan feels like kaman yayi 100yrs suna fada, he’s so lonely, he’s so horny! He lost his sanity, but yama kanshi alkawarin nan kozai mutu bazai nemeta ba. Yana wajajen har lokacin asır yatashi yatafi mosque yana dawowa yaga Noor zaune tasa hijabi murmushi yayi yakama hannunta yace “muje” tabishi suka fice.
Wani babban makarantan islamiyya yakai Noor da kanshi na yaran yan gayu yabiya mata islamiyya da haddansu da akeyi Saturdays and Sundays 8-6 na yamma sannan yabarota awajen suka dawo gida driver ta will bring her by 6.
EPISODE
Hawwa duk tana tsaye wajen window taga dawowan Khaleel yawuce side nasu, ahankali tasaki labule ta zauna, she’s angry da kanta, she hates kanta, gawani mahaukacin son Khaleel datakeji da bata tabajin kalansa ada ba, like every single thing reminds her of him agidan nan nasu, tagumi tayi saikuma ta dauko Al Qur’ani takaranta har isha’i, ta tashi taje tayi wanka tafito ta shirya cikin wani short gown na bacci, tadauki wani vintage scarf blue ta daura dayamata wani shegen kyau, tazo tasake zama ita kadai, kawai rayuwa yamata zafi, duniya yamata zafi, wayan Ammi takira harya katse no answer, takira Baba shima yaki dauka kawai saita ijiye wayan hawaye suka gangaro mata daga idanu ta share da sauri, tashi tayi taje dakin Khaleel ta zauna tai shiru har shadaya tabuga tagumi sai kawai ta tashi tadawo dakinta wani navy blue hijab tadauka mai hula tasaka har kasa ta dauki wayanta kawai tasauko kasa tafito tawuce flat na Mommy, kaman barauniya tabude kofan gabanta na faduwa kar Mom takara kadota, luckily babu kowa a falon sai tv dake aiki ko’ina a gyare tsaf tsaf, maida kofan tayi tarufe tashigo tana kallon ko’ina wlh bama tasan inane dakin Noor ba, wani kalan gini ne ga sama ga kasa, ga bangare bangare, wajen kujera taje ahankali ta zauna tareda sauke ijiyan zuciya sanin akwai mutane anan sai taji hankalinta ya kwanta, ta kishingida a dogon kujera before kace me bacci yayi awon gaba da ita.
Mommy na cikin video call da Excellency awaya wuraren 12 nadare akai knocking, daukan wayan tayi a hannu tace “common in” bude kofa PA Mommy tayi tace “sorry to disturb you Ma” Mom tace “No problem lafiya? Noor