Showing 57001 words to 60000 words out of 184554 words

Chapter 20 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1907

da murmushi kan fuskanshi yayi inda Hawwa take dake bacci anmata allurai da dama, Ammi na zaune ta buga tagumi ganninshi yasa Ammi takalleshi da damuwa akan fuskanta, Baba yajuyo yaja kujeran plastic chair ya zauna cikeda farin ciki yace “kidena damuwa Zainabu kiyi addu’a inhar Ibrahima rabon Hawwa ne kuma mijinta ne yau za’a daura mata aure” dasauri Ammi ta kalleshi tace “waye kuma Ibrahima Malam”? Labarin Khaleel yashiga bata all abubuwan daya sani, tai shiru Allah yasani yanda taga Khaleel yayi da Baba taji ya burgeta, banda haka Ni’ima said some disturbing about Hawwa, ita mace ce, sannan ita uwace, ko yara irin su Ramla sunsan sha’awa yanzu, Hawwa ba yarinya bace, babu bawa da baida sha’awa, tanaso Hawwa tai aure ta sami natsuwa da kwanciyan hankali, ba maza Hawwa kebi ba, bata iskanci so dole ne a irin shekarunta taji yana bukatan namiji, tabbas Hawwa na bukatan natsuwa, abun yamata, 50/50 Ammi keji azuciyanta, one side na zuciyanta ya goyi bayan auren sabida abubuwan da Ni’ima tafada especially bukatun Hawwa kafin yarsu tafada halaka, kota kauce hanya amata auren, zuciya ba kashi bane tsokace duk yanda takai da karfin imani shedan zai iyacin galaba akanta wata rana idan takasa hadiye sha’awar, another bangaren zuciyanta kuma zaiso ayi bincike akan koma waye Ibrahiman but idan aka tsaya bincike kafin agama yaron yagudu ko yace yafasa fa? Cus abinda ke faruwa kenan dazaran sunzo su gudu, yagudu yaushe Hawwa zata kara samin wani yafito ga Ni’ima ta tasata agaba? Sotake tai aure tai nisa da anguwan ta huta da bakin cikin Niima, she kind of reason with Baba sabida yanda samari ke guduwa gwara su kama Khaleel dinnan as earlier as possible, zata taya Hawwa addu’a Allah ya albarkaci auren ya kauda fitina su sami fahimtan juna, amman dai tai auren Hawwa na bukutan natsuwa kafin tafada wani hali, ganin tai shiru tana tunani yasa Baba yace “kin yarda Zainab? Dan banso mukara fada yanzu komi yawuce, ni da kene iyayen Hawwa, banda mu batada kowa, ada nai kuskure dana dinga bala’i dake, gayamin abinda ke ranki dan hukuncin nan tare zamu yankewa yarmu” murmushi Ammi tayi jin yanda Baba ya girmamata yabata matsayi yakuma karramata, anatse tace “na yarda Malam, nakuma aminta idan Alkhairi ne Allah yasa su dawo adaura idan ba alkhairi bane kuma Allah ya musanya mana yabata miji da gaggawa” Baba yace “Ameen Ameen” yana murmushi suka cigaba da hira, abinci aka kawo musu akace an riga an biya kudin abincin duk sukaci Ammi takira Ramla tace kartai girki, tabama Baba wayan Hawwa tace “Malam kira wajen aikinta ka sanar dasu tayi hatsari” Baba yace “nemomin number kaman DIG naji tana kiran Ogan nata duba kiciromin number” Ammi ta karba tana ciromai.

WAIWAYE BAYA KADAN..!

Ana fitar dasu waje har parking space aka kaisu aka tsaitsaya akansu kaman barayi, Salman yace “you have 10secs to leave this hospital else we hand you over to police and press charges against the both of you, we have cctv camera in every corner of this hospital starting from patient room” kallonta Baban Yaseer yayi yanda take kallonshi tana haki, ranshi ya baci iya baci da abinda tamai, baitaba sannin this is who Ni’ima is ba sai yau, cikin kakkausan murya yace “daganan kiwuce gidanku, namiki iyaka da gidana zankira mai gadi na shaidamai kada ki shiga gidan nan, kije na sakeki saki daya!” Faduwa gabanta yayi sosai zatai magana kawai yabude motan yashiga yawuce tabishi da kallo kirjinta na bugawa, Salman yadaka mata tsawa. “Madam leave our hospital!” Jikinta har rawa yake ta wuce ta shiga tata motar ta kunna tabar asibitin.

School nasu Yaseer yawuce direct ranshi na suya ya daukosu yace zasu danyi tafiya na 2week, sukaje gida yahada kayansu tundaga kansu Ipad yasasu a mota kawai sukai Kano gidan iyayenshi sukaje yakaima mahaifiyarshi yaran sunata murna yace suyi kwana biyu yasayo musu komi washe gari yabar Kano da sassafe danso yake yaje yaga Baba he made up his mind zai auri Hawwa yanzu, he wants to make her his wife.

****

EPISODE 

Sundanyi nisa ahanya yasa hannu yadauki wayanshi yayi dialing number Babanshi, Musbahu PA Excellency ya dauka yace “Khaleely Babanka na kan chamber” cikeda isa yace “I don’t care kaimai waya” cikeda lallashi Musbahu yace “Allah huci zuciyan yallabai bari na kaimai” Khaleel na kan layin kusan 5min sannan yaji muryan Babanshi a speaker yana excuse me sai chan Excellency yayi magana cikin so da kewa yace “Khaleely na ya akayi? Ina tsaka da meeting? Meya faru bakada lafiya ne”? Dan kishingida yayi murya chan kasa yace “I will send you address na wani anguwa kasameni awajen by 6, kazo da trust friends naka” dasauri Excellency yace “angama yarona zanzo, but meke faruwa lemme know wat I’m coming there for” shiru Khaleel yayi kaman bazaice wani abuba chan yace “I want to marry someone Pops” dasauri Excellency yace “aure? Aure Son? Ba mamanka is the one handling all of that for you ba, an mata screening ne ita wacce kakeson auren? Why do I have to come our lawyers da Malamai can take care of the aure for you, is my presence necessary”? Kai tsaye Khaleel yace “ai nasan dasu nace kazo Pops” dan tausasa murya Excellency yayi yace “I know, I know, karka bata rai I didn’t mean to hurt you, zanzo kawai nayi mamaki ne this is the first person dakake neman aure da kanka batare da Mom naka ta zaba maka ba ta auro maka ba, wacece yarinyar?” Kai tsaye yace “that police girl” dan zaro idanu Excellency yayi yace “you mean officer Hawwa wacce ta ceto Noor? That criminologist”? Murya chan kasa Khaleel yace “uhmm” dan shiru Excellency yayi sai chan yace “Khaleely are you sure about this decision? Cus naga yarinyar is hot tempered, bakaga yanda kuketa fada rannan ba, and you guys are almost age mate fa dan ba karaman yarinya bace, banson wacce zatazo tana baka ciwon kai ba tana wahalar da d’ana fa, I dislike stubborn girls” ahankali Khaleel yace “I can handle her Pops, I just wanna have fun with her Pops don’t worry” dan murmushi Excellency yayi cikeda kaunar yaron nashi yace “you know I will always give you kome kakeso ko? You have my support, see you by 6, I love you yarona Khaleelyn Babanshi” dan smiling kadan Khaleel yayi ya katse wayan ya yar agefe yadago kanshi yakalli Salman yace “I want every info akan mahaukaciyan nan and that photo boy of hers” gyadamai kai Salman yayi yace “yes sir” kallon driver yayi yace “Sam’s house”.

Wani tamkeken estate suka wuce suna zuwa gaban gidansu gate yayi scanning motansu kawai yabude musu suka shiga, budemai kofa Salman yayi Khaleel ya sauko yawuce ya shiga flat din Sam dayake bangare daban aka budemai kofa, tundaga falo yake jiyo ihun Sam din tareda na mace, tsaki yayi yawuce wajen dinning inda yaga wine, wine cup yadauka yaje fridge yazuba ice sannan yazo ya tsiyaya wine din ya zauna yafara sipping yana jiyo ihunsu wlh sun isheshi, bacci yakeji, dan gajeren tsaki yayi ya ijiye wine glass din kawai yawuce sama kai tsaye yabude kofan dakin yashiga Sam yadago kanshi yana nishi kaman kwado yace “Hi cousin” mugun kallo Khaleel yama yarinyar dayake abun da ita yace “get out!” Dasauri yarinyar ta fixge jikinta ta duka tana kwasan kayanta ta wuce tafita Sam rai abace yace “wai kai mehaka ne eh? I’m not done fa Dan iska kawai mai bakin hali” tsaki Khaleel yayi yawuce abinshi ya shiga next dakin yafada gado yana lumshe idanu bacci yakeji sosai.

Kusan 20min Sam yadauka dan saida yayi wanka sannan yafito yashiga dayan dakin yana kallon Khaleel dake lumshe idanu yace “ya akayi Lee”? Da muryan bacci yace “wake me before 6 zamuje daurin aure” Sam yace “wani daurin aure wazaiyi aure?” Yana kulle idanunshi yace “me”? Dasauri Sam yazauna bakin gadon yana kallonshi yace “yaushe aka fara daura maka auren gayyatan jama’a? I thought a seminar room na gidanku ake komi”? Hamma Khaleel yayi yace “this time is different” “wazaka aura”? Sam ya tambaya da kosawa, Idanun Khaleel a kulle yace “that Police gurl” fashewa da dariya sosai Sam yayi yace “Leee bakada mutunci shegen gari! Ai nasan after all that girl said you must find a way to show her who’s the boss, there’s nothing da zakaso da bazaka iya samun shi ba, and comfortably use it and dump it” murmushi kadan Khaleel yayi yace “starting tonight! She will belong to me!” Sam na annashuwa yace “use her kayi BDSM kamata lilis, 50shade of Lee zakai da ita” dan dariya kadan Khaleel yayi murya chan kasa da bata fita da kyau sabida bacci yace “she’s sick I don’t wanna hurt her now!” Da sauri Sam ya kalleshi jin maganan dayayi which sounds so unlike him yace “Lee mekace? Cousin? Kai Khaleel?” Yakai hannunshi yayi tapping nashi amman ina yayi bacci, dan murmushi Sam yayi yace “shegen yaro to ahaka zaka auren? Lemme call Balalau designer” kiran designer yayi aka turamai bespoke manyan kaya dayawa na gizna ya zabanma Khaleel milk shiya dauki ash yatura kudi around 4 aka kawo musu kayan wuraren 5:00PM wayan Khaleel yahau ringing ganin Pops ke kiranshi yasa Sam yashiga tadashi da kyar yatashi wayan Sam yabashi karba yayi yasa a kunne yana lumshe idanu yace “gamu a hanya already” gyadama Pops kai yayi yace “okay” Dasauri Excellency yace “bacci kake ne Khaleelu?” Ahankali yace “uhn” cikeda so yace “okay tashi kashirya sannu stop stressing yourself” katse wayan yayi yana kallon Sam dake shiryawa baiyi magana ba Sam yace “jekai wanka ga kayan ka nan my gift for ango” dan tsuki yayi kawai yatashi yafada bayi yayi wanka yafito jallabiya mai kyau yasa ya shimfida dadduma yayi la’asar yana idarwa Ga mamakin Sam saiyaga yawuce yana bude kayan without complain cus baison saka manyan kaya yafara sakawa Sam kawai ya tsaya yana kallonshi…….

Tun around 4 Baba yabar asibiti yakoma gida, yana kwalama Ramla dabata dawo hospital ba sabida Ammi tacemata yazauna kawai an basu abinci kira, dasauri tafito tace “gani Baba” murmushi yayi yace “dauko hijabi kibini kofar gida tabarmai zamu shimfida kaman zanyi baki da yamman nan” biyo Baba tayi har dakin Umma data hadarai Baba ko kallon inda take baiyiba yashiga kwaso tabarmai daga dakinshi yana bata taba karba sannan suka wuce waje tare tashiga shimfidawa yace “bari na leka gidan Malam Sama’ila Allah yasa yana nan” yawuce yana kallonshi yashiga sallama a gidan dake just 2 houses daga nasu.

EPISODE 

Fitowa Malam Sama’ila yayi Baba suka gaisa sosai Baba yace “Malam Sama’ila kai kadai nake sanarma da maganan nan sabida koda abun baiyuba kar kunyan duniya yakamani” yadan sauke ijiyan zuciya yace “inasa ran wani yaro dake neman Hawwa zai kawo mahaifinshi da mangariban nan suna zuwa nakeso na daura musu aure shine nace bari nazo nafada maka tunda kaine Babban amintacce na kuma limamun masallacin mu” cikeda farin ciki yace “Alhamdulillah, Alhamdulilah ubangiji Allah ya tabbatar da alkhairi, matar mutum kabarinsa inji hausawa, bakada matsala ina nan ai duk sanda suka zo sai nabada sanarwa a masallacin a tsaya” gyadamai kai Baba yayi jikinshi narawa yace “akwai wani abun da ake bukata ne a masallaci kowani abu, kaga duk su test din nan ba matsala bace Hawwa wajen aikinta duk bayan rabin shekara 6month sukeyi, nasan AA ce Hawwa zata iya auren kowa, sannan Hawwa na batada wani cuta, banson tambayoyin nan suhanani auran da ita dan Allah kadama kayi Malam Sama’ila” murmushi Malam Sama’ila yayi yace “kada kadamu bazan yiba” Baba yace “yauwa bari nabaka kudade adan fefesa turare a masallacin asa yara su gyara” cikin kudaden daya dauka dazu dazaije asibiti yazare 20k yamikamai Malam Sama’ila ya karba Baba yawuce yatafi Malam Sama’ila yabishi da kallon tausayi yace “Ya Allah kadubi zuciyan tsohon nan ka aurar da yarshi kada ka kunyatashi” saikuma kawai yawuce masallacin nasu.

Zama Baba yayi a kofar gida sai kada kafafu yake itama Ramla tafito tazauna kusadashi dan cikin gidan ya isheta ganin yanda yakeyi yasa Ramla tace “Baba su waye zasuzo wajenka ne haka”? Dan kalle kalle Baba yayi saikuma yamata alamu da hannu datazo kusada shi dasauri Ramla tazo tana zama agabanshi akasa akan tabarma, dan dukowa yayi cikin whispering yace “Hawwa ce tayi miji sunanshi Ibrahima, bakiga yaron ba badai shiga rai ba, gashi kyakkyawa dan gayu tsaftsaf dashi son kowa kin wanda yarasa ga tausayi, inhar abun ya yuwa Kulu na tayi goshi” zaro idanu Ramla tayi cikeda farinciki dan bakaramin addu’a sukema Hawwa tasamu mijiba ba, Baba kaman yaro yace “banso asani, banson kowa yaji, daga Mamanki sai Malam Sama’ila sai kece mutum ta uku danike fadamawa, hadiye murnan” hadiye murnan kuwa Ramla tayi tana kallonshi kaman TV, Baba yace “nace suzo karfe shidda da mangariba dai kinga ana salla sai adaura auren kawai” kai kasa daurewa Ramla tayi kawai saita tashi tahau tsalle sosai tana bude bakin ihun murna amman bata bari ihun ya fito, Baba ya tuntsure da dariya sosai yana kallonta yanajin dadin dabai tabajiba yace “wai bacewa nayi kidena murna ba, wannan yarinya bakiji” yacigaba da dariya shima kaman yatayata tsallen, shi kanshi baisan murnan yakeba, zama Ramla tayi awajen sai hira suke da Baba farin cikin auren yama kore damuwan rashin lafiyan Hawwan dake asibiti akwance, wajajen 6:30 Ramla tawani zabura tace “Baba ga motocin yan sanda tare da wasu jeep suna shigowa, Baba wlh sune, sune Baba” Da Ramla da Baba yar tsere tseren leke ake yakama hannunta yana hamdala yace “zauna zauna Ramla kada aga mun kosa kokuma imaza je kiramin Malam Sama’ila maza” dasauri Ramla tawuce tana kallon motansu dake shigowa ahankali yaran anguwa na binsu daidai ana parking motoci a kofar gidan Baba, shima Malam Sama’ila tareda wasu dattawan unguwa da Ramla na zuwa wajen duk sukazo suka tsaya tareda Baba dudda maza ne Ramla jitayi bazata iya komawa ciki ba wlh agabanta za’ayi komi abunka da yarinya.

Gently aka bude motan Excellency yasauko yana sanye da Baban riga na gizna tareda Musbahu, aka bude second car din, Mahe ne Baban Sam kanin Excellency shima sanye da manyan kaya, sai third car, Nigerian chief of staff da attorney general wayanda shakikan Excellency ne sai fourth car wanda gently Khaleel ya sauko yana sanye da milk na Gizna dake sheki ya kafa hula ta kusan 8million akai tana sheki yana zuba kamshi fuskanshi yayi wani kwarjini da annurin haiba, Ramla ta taushe bakinta sabida ihu na neman fitowa ganin mijin Ya Hawwa tace “Ammi mijin Ya Hawwa na da kyau, wayyyoo wlh bantaba ganin mutum me kyanshi ba, Ammi yahadu, Ya Hamza, Asiya wayyooo” Sam shima yafito, anatse Malam Sama’ila yace “Bismillan ku” gaban Baba sai bugawa yake yaga Khaleel yasan dan masu kudi ne but bai dauka kudin yakai hakaba, duk zama sukai akasa Baba ne kadai zaune kan kujera dan zaman kasa namai wahala sabida kafanshi da guda daya ce.

Yan anguwa aka taru kaman ana wani abu but babu wanda ya iya zuwa wajen sabida jami’an tsaro dasuka tare wajen da bindogoginsu a hannu.

Malam Sama’ila cikeda natsuwa yabude taron da addu’a yace “ina muku maraba da zuwa” faram faram su Excellency suka amsasu, anatse Excelllncy yace “to Masha Allah da farko dai sunana Alhassan Mangal senate president na Nigeria” kaman ruwa ya cinye su Baba yana kallonsu yayi shiru, yanuna Mahe yace “ga kanina Uwa daya uba daya Mahe, ga yarona Ibrahim Khaleel, ga dan kanina Sameer, gakuma shakikai na” yanuna kowa yace “d’ana ya samemu da maganan yaga yarku mai suna Hauwa’u yanaso, sun hadu ta sanadiyan kwato mana yarmu datayi daga hannun yan kidnapping Noor, munzo neman aurenta dafatan za’a bamu” murmushi sosai Baba yayi he’s overwhelmed baisan cewa yaune rannan da zaiga auren Hawwa ba, today started so bad for him, ciwon Hawwa saikuma hatsarinta, saikuma Ni’ima da abubuwan datayi, baitaba tsammanin ending na yau will be this good ba, lallai bahaushe yayi gaskiya dayace idan kasan mafitar rana bakasan mafadan ta ba. Gyaran murya yayi yanuna kirjinshi yace “harga Allah na yarda da Ibrahima! Na aminta da Ibrahima! Nakuma natsu da Ibrahima, danhaka ni mahaifin Hawwa nabawa Ibrahima auren y’ata Hauwa’u dayazo nema ayau!” Malam Sama’ila yace “Allahu Akbar” duk akai Kabbara awajen, Malam Sama’ila yace “idan ba damuwa ga masallacin mu nan, muyi sallan magriba tunda lokaci yayi sai adaura auren” kai tsaye Excellency yace “bismillan mu” duk aka tashi aka wuce out of respect Excellency ya jera da Baba dake dogara sanda suna zance freely kaman sunsan juna babu wani zancen nuna kaskanci, hakanan abin yama Khaleel dadi inda Pops yafi Mom kenan, yanada saurin accepting mutane unless baice yana sonsu ba, hakama yanuna bayason abu to wlh Pops shima zai nuna bayaso kodako menene abin.

Alwala akayi yau masallaci ya cika makil har gaban layi akai salla aka bada Sanarwa za’a daura auren Hawwa, dumbannin jama’an unguwa suka sheda aure tsakanin IBRAHIM KHALEEL DA HAUWA’U AKAN SADAKI MILIYAN HAMSIN DA DARHAMIN GWAL DARI!

Zokaga yanda mutanen anguwa suka haukace news na flying kaman kite Hawwa tayi aure, ashe wani jinkirin alkhairi ne, ta auri dan masu kudi, ai shi Khaleel din shine d’a daya tilo wajen mutumin the richest man a Nigeria menene menene, tashi Excellency yayi ya karbi speaker ya sanar yama masallacin nan donating miliyan dari! Saikuma yabama mutanen ungunwan matar dansa tundaga kan yaro da babba, tsoho da tsohuwa Miliyan dari arabama kowani household, haukacewa Umma tayi acikin gidan dan tanajin announcement daga speaker tace “ina matarsa zai aurar da diyarsa banda darajan dazai fadamin saidai naji a speaker? A inama tasami mijin? Kodai hada baki akayine? Ta ina Hawwa zatasan yaron Alhaji Mangal damuke gani a TV ta ina? Kai karyane da wata akasa auren nan bazai taba lasting ba” kaman mahaukaciya takasa rike bakin cikin tashiga kiran yaranta mata wanda all of them are happy for yayarsu suna cewa zamasu zo gobe kawai ta katse wayan tana zage zage har Ammi dake waya da Ramla dake bata labari saida tajuyo ta Ammi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login