Showing 69001 words to 72000 words out of 184554 words

Chapter 24 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1892

see you soon! Babu wacce nakeso da bazan iya samu ba, bakinta har rawa rawa yake tace “Pops Boy?” Dasauri Baba da Ammi suka kalleta basu gane metake cewa ba arude tace “Baba wannan mutumin daya kawo yarsa jiya da daddare asibiti? Ammi likitan daya kawomu gida? Shi wai kuke cewa kun auramin?” Dasauri duk sukace eh Baba yace “ai yagayamin kusan juna kece kika ceto Noor da aka sace” hannu Hawwa tadaura saman kirjinta dake bugawa kaman zai fito dasauri, Baba yace “Hawwa” cikeda fushi Hawwa tace “Baba kasan waye Khaleel kuwa? Kunsan wakuka auramin? Eh Baba” shiru daga Baba har Ammi sukayi suna kallonta, zuciya ba dadi tace “Baba auri saki Khaleel yakeyi fa, dan shaye shaye ne Baba wlh, dan giya ne Baba” tsayawa Ammi da Baba sukayi suna kallonta ganin basuce komiba yasa dasauri ta matso kusada Ammi dake kallonta tace “Ammi wlh dan shaye shaye ne babu abinda bayasha, banda haka ga auri saki ya maida mata kaman riguna yacire wannan yagaji yasaka sabuwa, Baba ni koshine namijin karshe aduniyan nan bazan aureshi ba na tsaneshi, bantaba haduwa da wanda na irinsa ba, ko kadan baimin ba, kucemai banyin auren, Baba bazan zauna dashi ba” kallon Ammi Baba yayi, Ammi ma takalli Baba hankali tashe Baba yace “Zainabu anya Hawwa ita kadaine?” Dasauri Hawwa tace “Baba nataba maka karya ne? Baba wlh Khaleel dan giya ne ga auri saki ni bazan taba yarda da auren nan ba gaskiya cus shi ba mijin aure bane” sosai Ammi ke kallonta saikuma ta kalli Baba tace “Malam gobe muje wajen malamin dakamin magana muma Hawwa ruqiya” turus Hawwa ta tsaya tana kallon Ammi jin maganan datayi wai basuji metake fada musu bane?

Baba ya jinjina kai yace “ba shakka” saikuma yakalli Hawwa dake kallonsu yace “Hawwa bakiso kiyi aure ne kin fiso kiyita zaman gida kawayenki na cimiki mutunci akan mazajensu”? Dafekai Hawwa tayi ganin Baba da Ammi basu fahimcetaba sun dauko magana daban, kaman zata fashe da kuka tace “Baba baku fahimce ni ba, bawai auren ne banaso ba, wanda kuka auramin ne ba mijin aure ba, Baba bakuyi bincike akanshi ba” da dan masifa Baba yace “ke kinyi bincike akan shi ne?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta girgiza kai alamun a’a, cikeda da dan masifa Baba yace “sau nawa duka duka kikaje gidansu aikin Noor da aka kiraku?” Ahankali tace “sau biyu” dadan masifa Baba yace “mutumin da sau biyu kika hadu dashi shine zaki dingamai kazafi haka kinsan menene dan giya kuwa?” Yakalli Ammi yace “Zainabu tsakaninki da Allah zaki fadi badan ni ba bakuma dan Hawwa ba, kifadi iyakan gaskiyan ki har zuciya Khaleel yamiki kama da dan giya?” Anatse Ammi ta girgizakai tace “Hawwa ko kadan Ibrahim baiyi kama da dan giya ba, muna ganin yara masu shaye shaye munsani, tundaga kan halayyansu, mu’amalan su, yanayin magana da yanayin bakinsu ana ganewa Khaleel ba dan giya bane” dafe goshi Hawwa tayi ranta yayi masifan baci, Baba yace “kikace yana auri saki Ibrahima yasanar dani tun yana yaro dan shekara ashirin da hudu mahaifiyarshi kemai aure, duk yasaki matan ciki harda mahaifiyar Noor, baitaba neman aure da kanshi ba sai akanki daya ganki yaji kuma yanaso, sabida yayi auri saki ada baya nufin zaiyi dake ke zakiyi abinda za’a sakeki ne? Ga mahaifiyarki anan zata koyardake yanda ake tattalin miji da sauransu”baki Hawwa tasaki idanunta na tsatso hawaye tana kallon Baba dake kare Khaleel kaman irin yayi shekara da shekaru dayasan shi yace “na natsu da natsuwar Ibrahima! Na yaba da hankalinsa da kyauta da sauransu, abinda na lura akan yaron shine yaro ne mai shagwaba wanda daga gani iyayensa sun sangartasa koda kin aureshi abarayin ne zaki iya samin matsala dashi sabida yasaba kome yakeso yana samu, wanda rayuwan nan babu wani bawa da baida aibu, inada nawa kinada naki mamanki nada nata bature yace nobody is perfect” Ammi tace “kwarai” Baba yakalleta sai kuma ya tausasa murya yace “Hawwa agabana aka cimiki mutunci aka zageki aka goranta miki sabida bakida aure kin zaci ina farin ciki da hakan?” Yayi shiru yanuna Ammi yace “an zageta, an zageni, an zagi tarbiyan damuka miki, aka goranta mini, aka kira diyata da tai kwantai, aka miki kazafi, kin dauka ina farinciki da hakan?” Jikin Hawwa sanyi yafara yi, anatse Baba yace “danabar dakin nan jiri ya debeni zan fadi Ibrahima yatareni” Baba yawani kalli saman dakin hawaye na gangaromai daga idanu kaman mai tuna abubuwa da dama yace “Ibrahima ya kamani, yarikeni ajikinsa kaman daman ya sanni daga wani waje, yakaini daki yabani kulawa da agaji na gaggawa, cikin tattausan lafazi yace Baba kadena damuwa zan auri Hawwa!” Sai kawai Baba yafashe da kuka sosai yace “ko yaran cikina basu tabamin hallaccin da Ibrahima yayimini ba, ya fitar dani kunya, yanunamin soyyaya haka yanunama yata, yakawo iyayensa aka daura aure, wani awaje ya sharemin hawaye sai kene yanzu Ina sanar dake namiki aure zaki watsamin kasa a idanu” Baba yafashe da kuka sosai Ammi ta taso ganin da gaske Baba kuka yake tace “Malam dan Allah kayakuri abin baikai ga hakaba ya isa ya isa” Hawwa Baba yanuna yace “Zainab yarinyar nan tasan yanda nake sonta kuwa? Ita kadai nake gani natuna Aisha matata ita kadai, amman maisa Hawwa ke wahalar dani tana bani ciwon kai” wlh at first Ammi tadauka Baba just lie lie cry yake but sosai Baba ke kuka, Hawwa tazo bakin gadon ahankali tadafa kafan Baba tace “Baba dan Allah kayakuri bahaka nake nufi ba dan Allah”Fashewa da kuka Baba yayi yace “Zainab kinsan shekara nawa rabona danai bacci? Wlh tunda Hawwa takai shekara ashirin da biyar batai aure ba daga ranan har zuwa ana gobe zatai hatsari bantaba kwana gari yawaye ban tashi inyi salla inama yarinyar nan addu’a tayi aure tasami miji nagani ba, bana bacci bana iya runtsawa tunanin Hawwa nake, sai ranan da aka daura mata aure shekaran jiya shine nai bacci sai asuba natashi da jiya dakuma yau in 4yrs ina abu daya sai ranaku ukun nan na iya bacci sabida na aurar da ita” dasauri Ammi itama tace “Malam meyayi zafi haka? Dan Allah kayakuri ya isa” takalli Hawwa dake kukan bakin ciki ganin abinda Baba keyi sabida dan iskan Khaleel tace “Hawwa I know concerns naki, tunda ba kisan kai Ibrahim yake ba, ko saida yara, ko fashi, ke kaddarama yana shaye shayen ke ba matarsa bace? Ai mata Allah yabasu power da suna iya gyara mazajensu from bad to good, banda haka bayan Baba yazo damaganan na jera kwana biyu a asibiti ina alwala nayi raka’a biyu nayi du’aul istikhara wlh naji na natsu da Khaleel and it’s a sign auren ku zaiyi albarka, Hawwa koma meke damunki dake hanaki aure fight it this time, karki bari shedan yayi nasara akanki, auren nan yanda aka daura an daura kenan har abada kibar zancen rabawa” baki Hawwa tabude zatai magana Baba yadaga mata hannu.

EPISODE 

Cikin bacin rai Baba yace “idan kalma mara kyau zaki fadi akan Ibrahima na kiyi shiru kada ki fada don yana sosamin rai” shiru Hawwa tayi batasan me Khaleel yamusu ba especially Baba imagine ma harda Ammi, dukansu biyun basu yarda da itaba, just for peace Baba yadena kukan nan zata yarda tai shiru amman tai alkawari saita nunama su Baba waye Khaleel she will bring evidence and everything dan kome za’ayi ayi she will never ever accept yaron Pops din nan amatsayin mijinta ba!. “Hawwa kinji abinda muke fada miki?” Kallon Ammi tayi fuskanta ta share tass da bayan hannu ta kalli Baba tareda kakalo murmushin dole tace “naji shikenan na yarda babu komi” wani kayataccen murmushi Baba yayi yana share fuskanshi sai kawai ya rungumeta kaman zai cinyeta yace “nagode Hawwa, banso na tursasaki kiyi abu, nagode dakika yarda” sakinta yayi yace “cikin kudin sadakin nawa kike bukata nabaki inaso naba Ammin ki sauran asayo miki kome kikeso Ibrahim yace sati uku on 24th ne taron biki” wani abu Hawwa taji ya tsayamata awuya amman dai ta gyadamusu kai Baba yace “zamu fara shirin biki wannan gwal din kuma nida Aminu zamuje banki gobe mu boyemiki, yanzu gayamin nawa kikeso a kudin?” Ahankali tace “banson komi Baba kuyi abinda yadace inada dan kudi ai ni” Baba yace “to shikenan zan dauki ko miliyan goma ne nasai miki filaye kisami kaddara sauran kudin ayi kayan aure dasu da gara” Ammi tace “zanje Zaria jibi nadan shiryo nadawo saimu fara shirye shirye bakama hannun yaro afito da anko sabida kowa yasami dinki tunda lokaci ya kuro” Hawwa kawai tai shiru tana kallon Baba da Ammi dake planning sosai zuciyanta na kuna tana durama Khaleel ashar kirjinta na radadi kaman zata kama da wuta cus tasan auren is nothing but a game.

Har tai bacci tabarsu awajen planning bikinta Ammi da Baba suke wlh ko Baba ne amaryan sai haka. wuraren 3 na dare ta farka tareda taba wayanta tadan haska Ramla ne ke kusada ita tana bacci, sai Ammi a bakin gadon ta dayan edge din, kankame jikinta Hawwa tayi abin yataso mata what is wrong with her? She’s on MP fa though tagama da asuban nan zatai wanka tafara salla, haushin kanta ta shiga ji sabida tunawa da yanda Ni’ima use this feelings against her, iska ta fuzar ahankali ta zame ta sauka kasa sai kawai ta sulale ta kwanta akasan tiles din dakeda sanyi, kusan 20mins tana ahaka kafin yasoma lafawa bacci ya kwasheta anan wajen, cikin bacci taji ana kiran sunanta da sauri tabude ido Ammi ce ta kunna wutan dakin tace “badai Ramla ta turoki kika fado kasa ba?” Danne kunyan datakeji tayi tace “Ammi nakan fado kasa haka wani zubin” Ammi tace “ahh lallai sannu iyayen bacci mara kan gado, idan zaki wanka yanzu nasa ruwa a wuta bayau zaki fara salla ba?” Gyadama Ammi kai tayi ta tashi tana cire kaya Ammi tahau dadduma ta kabbarta salla wucewa tayi tafice Ammi tajuyo wlh tunda ta farka Ammi ta farka sabida ijiyan zuciyan dataketa saukewa abinda yatasheta kenan, saikuma sauka datayi kasa aranta Ammi tace “kodai tama Baba magana ne ayi bikin next week akaita kawai”.

Dawowa dakin tayi tazauna gaban madubi tana kallon kanta dayayi tsufa ahankali tace “anjima zanje saloon” tuna zancen Baba ya auramata Khaleel sai kawai taji ranta yabaci kwafa tayi she has plan she will show Baba waye Khaleel she will get evidence, saita nunama yaron nan ita ba kalan sauran matan daya saba aure bane, she don’t want him so bazata taba zaman auren nan ba, 3weeks is morethan enough for her to show Baba evidence kan waye Khaleel even if it means nemo all matan daya aura adah.

Wani simple riga da skirt tasaka tadauki dadduma ya shimfida itama tai salla suka idar ta gaida Ammi, Ammi tace “yajikin?” Ahankali tace “lpy lau” murmushi tamata “zanje zaria nataho damai gyaran jiki, dakin chan da akasa tarkace Baba yace yau duk zaisa afitar dasu a gyara tsaf anan za’a dinga tara abubuwan ki da za’a siyo mai gyaran ta sauka anan, saikuma inaso ki gayamin wani kalan kayan kitchen kikeso?”

Ita abinma dariya yadan bata sai kawai ta tashi tace “duk wanda kika saya Ammi, bari nai aikin office yau zani saloon gobe nakeso nakoma aiki” Ammi tabita da kallo tace “okay”

Wuraren 11 Baba yashigo yana kwalamata kira tana cikin shiryawa itada Ramla datace zata bita dasauri ta taho kofa, wani key mai kyau na benz yace “gashi mijinki ya aiko miki da motansa wai kidinga hawa naki har yanzu ba’a gama gyarawa ba tai condemn” key tadan harara kadan tace “da keke zamu ai Baba ba nisa saloon din” sarai yasan halin yarsa watsamata mugun kallo yayi yace “mijinki yabada umarni kihau tasa motar ke kice keke zaki hau? Hawwa kinsan hukuncin wacce batama mijinta biyayya tarbiyan dana miki kenan? Wlh zan cimiki mutunci fa” Kaman zata kurma ihu ta hadiye abu awuya tasa hannu ta amsa tace “yakuri” murmushi Baba yamata yace “ko Kefa yar albarka yanada kyau mata tadinga bin umarnin miji tafi ganin haske arayuwanta” komawa ciki Hawwa tayi ta zauna turus akan gado ranta dukya baci Ammi tace “uwarfada tashi kuwuce kutafi kafin na sabamiki” mikewa tayi ahankali tadauki black veil na abaya dake jikinta dogo mai kyau ta daura aka tadauki wayanta da handbag Ramla ta fesa turare sannan suka fito, motar na kofar gida wata mahaukaciyan 2024 Benz ce grey, ga ledojin duk ajikin car seats din daga gani kasan sabuwa ce motar har kyalli take, Baba yace “kunfito wuce kutafi” sake hadiye abu tayi awuyanta tawuce Ramla tabita taje zata bude motan tasake tsayawa turus tadan kalli Baba ganin ita yake kallo yasa ahankali tabude motan ta shiga ahankali kaman bataso ta zauna Ramla ka tashigo tace “wowwww Ya Hawwa sabuwar mota ce kal wlh Ya Ibrahim naji dake” mugun kallon da Hawwa tamata yasa taja bakinta tai gum, ganin taki tada motar yasa Baba yadaga murya yace “kuna jiran wani ne? Ko injin ya mutu ne azo aturaku”? Ahankali Hawwa ta tadamotan kaman bataso sannan taja motan ahankali sukabar anguwan motan dadi Ya Allah! Wato better thing money kill am, steering wheel din kaman oil sabida yanda yake juyuwa ta dadi ba irin nataba da kaman tana dambe ba, wayanta ne yashiga ringing tahau kan hanya batare tadauka idanunta kan hanya takai wayan takai kunnenta batare data kallaba cikin murya mai dadi tace “hello” strictly taji muryanshi that sounds kaman yanzu yake farkawa daga bacci yace “da permission din waye kika fita?” Dawani irin sauri Hawwa tazare wayan daga kunnenta number ne kuma Truecaller ta bai fadamata waye ba kashe wayan tayi taidan tsaki ta ijiye Ramla ta kalleta ringing wayan yashiga yi taki kallon wayan ma Ramla tace “Ya Hawwa ana kiranki” ahankali tace “share” har sukakai saloon din kiranta yake, kashema wayan tayi daga baya gabaki daya suka shiga saloon din batason tai kitso kar kanta yayi ciwo kawai tsifa da wanke kan da blow drying shiko aka mata cikin 1hour aka gama tabiya kudi suka fito Khaleel tagani zaune kan bonnet na motanta yadaura kafa daya kan daya dagashi sai short na rick owens nude more like milk, da armani polo mai kyau maroon ga pcap akanshi milk shima dayamai kyau crocs ne akafanshi duk wanda zaiga Khaleel saiya juyo yakara kallonshi cus baimayi kama da Nigerians ba kaman irin black black American people din nan ma har yanda yake dressing, Ramla ta washe baki ganinshi tama wuce Ya Hawwa ta taho wajenshi da gudu tace “Ya Ibrahim ina yini kazo” murmushi kadan yamata yace “Hi Ramla kema kinyi saloon da wanchan yarinyar nan ne”? Yanuna Hawwa dake tahowa sarai tajishi takuma shaka but ta daure sabida Ramla, akunyace Ramla tace “ni yau kwanan kitsona uku saisa banyiba, Ya Hawwa na rako kawai” zuwa wajen Hawwa tayi azuciye zata wucesu tabude mota karaf taji an rike mata hannu kafin tai magana kawai Khaleel ya fizgota jikinshi da shegen zafin nama, kafin tasake magana taji hannunshi cikin nata ya karbe key motan ya wurgama Salman ya chabe yace “take Ramla shopping then home Salam, I want to talk to my wife privately!” Kawai ya kankame Hawwa ajikinshi yana turata baya kunya kawai yarufe Hawwa na masifa, ga Ramla data saki ido baki hanci tana kallon abinda Khaleel kemata, ga jama’a, ga su securities dinshi, she had no choice haka ya dinga turuwanmai har jikin motanshi yakaita yabude kofa yamata rumfa agabanta kaman zaiyi hugging nata yakalleta yace “get in” zatai magana yace “i will kiss and touch you all over kikamin gardama!” Runtse idanu Hawwa tayi ta tabbatar Ramla taji maganan wlh harsu Salman da kowama, kaman zata shige kasa, da kyar tabude idanunta Ramla tadan kalla dahar ta shige gaba abinta tana mata bye tana washe baki na murna da farinciki, da sauri kawai ta juya ta shige without saying a word, shima yashige yana rufo kofan motan yace “let’s go” Aharzuke Hawwa ta kalleshi tace “wai is something wrong with you? How dare you touch me like that a public?” Hannu yasa yazare pcap na kanshi yakalleta babu wasa kan fuskanshi yace “duk randa kika kara fita without kin sanar dani sai ranki yabaci I forgive this one but next one I won’t” tsayawa Hawwa tayi tana kallon ikon Allah abinma sai yasa tai dariyan takaici tace “ikon Rabbi! Auren da Baba yamin dakaine yasa kake wani takama kana feeling kaman u own me?” Kallonta Khaleel yayi baice komiba hakan yasake pushing Hawwa to the wall, tace “guess wat nariga nama kaina alkawari before this 3weeks I will expose who you are to my family! I trust Baba da kanshi zai raba auren nan daya mana I will prove to them cewa you are nothing but a womanizer sai aure aure kaman ayu ga shaye shaye da party BfF din dujal, I’m Hawwa! I can never settle for less! I want a man dayaci sunanshi man not yaro! I want a responsible man not Pops boy! I want a man that shoulder responsibilities not wanda ake shouldering responsibility shi! Ni da kai are two world apart trust me you need plenty years to get to world din danake, so forget kayi abin nan waishi daurin aure but Hawwa can never ever be yours” wani juya idanu Khaleel yamata kaman zaiyi bacci yayi shiru chan yace “feel free! Do whatever you want! Khaleel yariga ya sameki! Dudda kina chan world dinki but without stress na mika hannu na ciroki daga world din nakawoki my own world dakika tsana so much Kululuwa, matar dujal bff” dasauri tawani yunkuro kaman zata dakeshi tace “nace kadaina kirana sunannan!” Murmushi kadan yamata yace “to Yar Sanda!” Wani irin runtse idanu tayi kaman zata dakeshi cus he’s pushing her yayi murmushi kadan baice mata komi ba, afadace tace “ina zaka kaini? Ba hanyan gidanmu bane nan ba?” Dan kanshi ya sosa yana kallonta kaman yanda take kallonshi murya chan ciki yace “we are going to hotel!” Mummunan gaban Hawwa yayi.

EPISODE

Gidan Mama Jin parking mota a kofar gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login