Showing 81001 words to 84000 words out of 184554 words
“go to your Nanny tamiki wanka” dasauri Noor tawuce tana gudu shikuma yadauki kwallon cikeda iskanci ya wurgama Mom tai baya baya kaman zata fadi sannan tarike ball din da kyar tana haki tace “Khaleely banson iskanci fa, karyewa kakeso nayi?” Khaleel ya kwashe da dariya sannan yataho inda take yabata sidehug yana daura hannunshi akafadanta cikin sangarci yace “Mom tsoro kike zan aur'o miki yar sanda?” Hade fuska tayi hakan yasa ya kwashe da dariya again Mom ta tsaya tana kallonshi he’s so happy this days, Khaleel yace “Mom do you think she will stop me from living my life? And enjoying myself?” Cikeda damuwa Mom tace “eh mana Khaleely girls like her sunfi karfinka” dariya yayi yace “Mommy I’m man enough to control kowace kalan mace na aura your Son is not a boy” yasaketa yawuce saikuma yadawo ashagwabe yace “Moma we will be having wedding on 23rd get ready invite all your friends, I want my side furnitures change, sannan agayara my main flat” yanuna wani arnen flat dake dayan barayin gidan dasauri Mommy tace “no Khaleel you will never leave my sight gaskiya side dinka dake cikin flat dina zaka dinga zama not bangaren chan kaji ba” wucewa yayi abinsa batare daya kulata ba yatafi sama gym dinshi yashiga yashiga yin exercise kafin daga bisani yafada shower yayi wanka yafito Sam haryazo suka tafi party abinsu.
EPISODE
Ranan gabaki daya Hawwa jitayi batajin dadin komi, har Ramla saida taga Hawwa was not in good mood sabida yanda tai shiru batama iya magana da kyau, sai lissafi take how zata fita daga this mess? Idan yanuna video ko pictures yacema Baba tayi kokarin mai fyade duk zasu yarda ta ina kunya zai barta ta kallesu dagashi har Ammi that means everything Ni’ima said is true about her.
Washe gari tsaf ta shirya ta tafi aiki around 12 DIG yakirata tashigo office nashi murmushi yamata yace “okay Ogana gabaki daya yakirani yace nabaki leave sabida kiyi planning wedding naki da kyau an baki 60 days” zaro idanu Hawwa tayi tace “Innalillahi 60 days that’s 2month, mezanyi da all this time Sir”? Dan murmushi DIG yamata yace “Hawwa have you seen abinda nafada miki jiya? Imagine danaje wajen Babanki to, wannan da Ogana ne yakira yace abaki 2months wedding leave abinda 3weeks ake bayarwa but naki is different, so zaki iya tafiya, we will see you on the wedding day in sha Allah idan kinyi inviting namu, Hawwa May Allah bless your home, Allah miki albarka, nasanki da ibada da yawan azumi Allah shine maganin komi so call on to him shine yasan wats best for you” kuka taji yana zuwan mata amman tahadiye ta gyadamai kai ta tashi ahankali tafito tana tafiya zuwa office nata wani officer yace “Miss Hawwa kinada bakuwa bamu barta tashigo nan ba tana chan” yamata pointing waiting room nasu, da mamaki tadinga tunanin waye ko wacece zatazo wajenta, dudda Ammi na hanya dan yau zata dawo amman ai baici ta iso ba tace mata by 11 zatabar gida, why is she even thinking of Ammi? Ammi bazata taba zuwa wajen aikinta ba, hanyar waiting tayi ganin Ni’ima taci gayu cikin atampa mai kyau ta yafa dan gyale ta rike handbag a hannunta yasa ta tsaya turus Ni’ima tamata murmushi kawai ta taso da gudu tazo batai wata wata ba ta rungumeta tace “Best suprise” chak Hawwa ta tsaya without hugging her back harsaida Ni’ima tadago ta kalleta tace “are you not happy to see me?” Dan girgizamata kai Hawwa tayi tace “no is not like that” dasauri Niima tace “muje office naki anata kallonmu anan” kawai takama hannun Hawwa, ahankali Hawwa tabita har zuwa office nata suka shiga idanunta ne suka sauka akan iPhone 15 pro max na Hawwa dake kan table last she check Hawwa was using Samsung S10 harya chanza mata wayane? Lallai gayen nan, abu taji ya tsaya mata arai dasauri tasaki hannun Hawwa tai wajen wayan tadauka tace “wow kin chanza waya Hawwa? Kin koma iPhone? Ni fa banson iPhone ance basu rike charge duk application saika saya? Baka iya downloading movies anyhow, komi kudi, Ke kika siya ko mijinki ya saya miki”? Karasowa Hawwa tayi ciki tazauna ahankali tace “shi ne” wani irin murmushi Ni’ima tana danne bakin ciki da zafi datakeji aranta tayi tace “awwwn lovebirds, ohh my my, Hawwa I’m happy for you Allah yaga how patient you are yabaki mai sonki, wai yaushe kuka hadu ne baki taba bani labarinsa ba, eh yaushe kuka hadu?” Baki Hawwa tabude zatai magana akai knocking kofan da sauri dukansu suka kalli kofan Abraham ne ganin Ni’ima yasa ya tsaya yace “can I see you Miss Hawwa”? Gyadamai kai tayi tace “sure” ta mike suka fice tarufe kofan dawani irin sauri Ni’ima ta danna screen din wayan ganin babu password yasa tashiga cikin wayan dasauri tace “calls” call log tashiga d only number datai magana dashi for long batai saving ba saina Ammi datai saving da Ammi hakan yasa tashiga kwashe number da she’s sure Khaleel ne dan ya kikkirata bata dagawa daidai tana gama kwasa tanaji ana taba kofan da sauri tafita tarufe wayan ta ijiye kan table Hawwa ta shigo rike da Maltina ta ijiye gaban Niima, Ni’ima tace “thank you Best” Hawwa ta zauna Ni’ima tace “gist me Best ya shirye shirye? Kayan daki kayan kitchen? Na kaiki wajen wanda yamin na dakina?” Ahankali Hawwa tace “Baba da Ammi are in charge of everything bansan mesuke ba” gyadamata kai Ni’ima tayi saikuma tace “wai har yanzu kin rikeni azuciye ne? Best I’m really sorry wlh ina sonki you mean the world word to me kinji” dan lumshe idanu Hawwa tayi saita gyadamata kai tareda bude idon, Ni’ima tace “anko fa? Nafitar miki da anko?” Shiru Hawwa tayi saikuma ta gyada mata kai, murmushi Ni’ima tayi tace “thank you, can you call Baban Yaseer for me yanzu da wayan naki”? Shiru Hawwa tayi all maganganun Ammi nadawo mata ahankali tace “Ni’ima banso nakara shiga lamarinki da Baban Yaseer I promise kaina that, for licence naki nayi magana za’a samu nasara in sha Allah” murmushin karfin hali Ni’ima tayi tana danne abinda takeji azuciyanta tace “shikenan hakan ma I’m grateful after kalan abinda namiki not everyone will even help me that much, kinada zuciya mai kyau Hawwa, thank you” gyadamata kai Hawwa tayi, daidai nan wayan Hawwa yahau ringing Ni’ima ta saci kallon screen din ganin number data kwashe ne kaman Hawwa bazata dauka ba, but ganin Ni’ima and tanaso tanunama Ni’ima she’s cool with Khaleel kodan tacire tunanin Baban Yaseer da ita aranta yasa gently tadauka takai kunnenta, murya chan kasa Khaleel yace “I sent a delivery guy what’s your office number”? Shiru tayi chan tace “baza’abarshi ya shigoba” dan murmushi yayi yace “no one can stop my delivery, office number Kulu” murya chan kasa tace “0040” katse wayan yayi almost 1min saiga knocking anatse Hawwa tace “come in” bude kofan akayi wani delivery guy ne rike da flowers na red roses da akai wrapping katon gaske, saikuma platter na yan gayu na different intercontinental dishes da note ajikin both of them delivery guy din yace “I’m looking for Mrs Hawwa Alhassan Ibrahim Khaleel” Ni’ima jitayi yawun bakinta yayi daci da kyar tahadiye, ahankali Hawwa ta mike ta nunamai table din zuwa yayi yafara mika mata flowers din dake kamshi sosai like Khaleel plus kamshin roses again, office din yacika da kamshi, karba tayi ta ijiye sannan yabata platter na abincin shima ta ijiye yabata note nashi tai signing sannan ya tafi, kafin Hawwa ta zauna har Ni’ima tasa hannu tadauki card dayayi note ajiki tace “love bird bari muga meya rubuta miki” dasauri kafin Hawwa tace wani abu, tace “_I know you haven’t had breakfast banson matana looking skinny you are too light for my liking, eat and get chubby, cheers to starting your leave today! Sowie about yesterday with love Mijin Kulu
_”
Murmushin dole Ni’ima tayi ta ijiye card din, taja platter box na abincin tana budewa tace “eat mana” wow tafadi ahankali lafiyayen abinci ne aciki dat are very hot, mash potatoes da chicken wings, samosas, Pasta sai Mandi rice, ga salad ga fruits juice very cold ga sweet da cingum na mentos, kallon abincin itama Hawwa take, deep down she feels happy but then she don’t wanna feel d happiness ahankali tace “ke kici idan zakici” dasauri Niima ta girgiza kai tace “a’a inacin abinci nafito” gyadamata kai Hawwa tayi saita rufe platter ta matsar gefe idanunta suka sake saika akan rose din kawai ta tsaresu da idanu Niima duk na kallonta, aranta tace “munafukar mugun son mijinta take amman tana bobboyewa, hala ma sun riga sun sadu” wayan Hawwa ya shiga ringing dasauri ta waigo ganin Khaleel ne yasa ahankali tadauki wayan takai kunne murya chan kasa Khaleel yace “have you eaten? Is the food good? Kona chanza mana Chef? Shizai dinga mana girki bayan auren mu, abincin yayi”? Shiru Hawwa tayi murya ciki ciki tace “mesa baka dafa da kanka ba”? Dan zaro idanu Khaleel yayi yace “Momy bata barina in kitchen I don’t know me akayi a kitchen” murya chan kasa Hawwa tace “uhnn Moms boy” murmushi kadan Khaleel yayi yace “do you like the rose?” Kin magana Hawwa tayi, ahankali Khaleel yace “but I said sowie about yesterday” murya chan kasa Hawwa tace “sowie is not sorry” dan dariya kadan Khaleel yayi ahankali yace “wa akace tana tareda ke a office?”
EPISODE
Faduwa gabanta yayi jin tambayan daya mata, hakanan sai takasa magana, “answer me” yafadi da kakkausan murya still kin magana tayi sai kawai ta zare wayan daga kunnenta takatse ta ijiye takalli Ni’ima ahankali tace “zan tafi gida natashi” tashi Ni’ima tayi tace “toh nima bari natafi, bari natayaki daukan rose din saike ki dauki platter” wani iri Hawwa taji amman saita daure ta mike tashiga hada abubuwanta tadauki car key suka fito tare ita tana rikeda platter Ni’ima na rike da rose din har zuwa inda motar Hawwa yake, Ni’ima sai kallon motar take tanaji kaman tahadiye zuciya ta mutu idanunta harsun kada sun chanza, abayan motan sukasa komi Ni’ima na kallon motan irin wannan fa ba tokunbo car Hawwa ke dashi ba no, asalin sabuwa gal ce, komi na motan ba ariga an daye mata ledaba, maida kofan bayan Hawwa tayi tarufe tace “bye” tawuce ta shiga gaba Ni’ima na tsaye tana kallonta, Hawwa taja mota tabar wajen abinta, da kyar Ni’ima ta iya wucewa zuwa wajen tata motar zuciyanta kaman an barbada busheshen barkono da danye tsabagen azaban radadi dayake mata, sai kawai ta tsaya tana kallon motan ta, motar Hawwa tada Toyota Camry ce 2006/2007 ita lokacin da Baban Yaseer yabata Camry nan na 2014 kaman zata haukace dan tafi na Hawwa kyau da tsada gata latest, but yanzu dataga motan da Hawwa keja benz datakai irin 150M sai taji ta tsani tata motar, saitaji ta rainata, wai tayaya ma rana daya Allah zai dauki miji mai bala’in kudi yabama Hawwa ne? Eh? Within a blink of an eye rayuwan Hawwa ya chanza kakap, big phone iPhone 15 pro max, ita tana fama da Samsung S21 dinta da ada takejin dadi yafi na Hawwa S10, Hawwa ce big car, ga sadaki mai tsoka, ga gwalagwalai, Hawwa ko sisi taki bata, da dane da hala yanzu Hawwa tabata like 20M from that sadaki wlh dan Hawwa bata kyashin bata abu, Hawwa is going to big house now and yaron seems to love her alot, jibi yanda yake bata gifts, ranan su diamond agogo dasu turare yau abinci da flowers masu tsinannen kamshin dadi, he’s so romantic, she thought babu miji that will be as sweet and romantic as Baban Yaseer yanzu taga wanda yafisa.
Hawwa ta hadu da irin gayen kan taki fadamata har sai bayan tayi hauka? The way suke soyayya hakan nan she can swear Hawwa tadan jima da sannin gayen? Wannan dayaketa bata gifts sunyi sex ne? Hawwa is so happy she wants her to be sad, tafison taga hawaye da bakin ciki da bacin rai da damuwa akan fuskanta, wannan gayen ya shigo rayuwanta yasa Hawwa ta chanza bata damu da itaba yanzu, imagine wai ita Hawwa ke shama kamshi, what will she do yanzu? Da kyar ta lallaba tashiga motan ta tada tabar wajen tana tana tafiya akan titi tazo ta wajajen banex ta kalli masu bara dake wajen, sai kawai tayi parking motan tafito taje wajensu tace “zan baku kyautan kudi sosai amman saikun bani wayanku na tura wani sako” har rige rigen bata wayan ake, kakkarba tayi marasa kati har tana samusu ta bank dinta, sako tashiga turama number Khaleel da kusan duka number su sannan ta basu 5k suraba tawuce takoma mota tana murmushi taja abinta zuwa gida.
**
Khaleel na cikin mota tareda Sam wayanshi yayi kara daukan wayan yayi yaga messages guda 5 from different numbers hardly unknown ke kiranshi ma talk more of sako, kaman bazai budeba saikuma yabude daya.
“_Hawwa is a whore! Tsohuwan karuwa ce she sleeps with everyman dayake zuwa yace yana sonta saisa suke guduwa basa aurenta sabida tabasu abinda suke nema_”
Chak Khaleel ya tsaya yana kallon messege din to be very very honest he doesn’t care idan Hawwa sleeps around or not cus yasan tun zamanin da wato old days aka daina samin virgins, konji is real babu yanda za’ayi yataso maka baka nemi wanda you will sleep with ba so what ai d’ane tayi, baida right to judge her life is not easy takai this years 29 without a man, shi tun yana 24 yafara ai, but dudda haka saiyaji still zuciyanshi namai wani iri sai kawai ya ijiye wayan da sauri without opening sauran messages din ahankali yace “park the car” Dasauri Sam yace “lafiya? We are not there yet” dan murmushi Khaleel yamai yace “just give me a moment” fita yayi daga motan yafara tafiya zuwa chan gefen titi baitaba sani akwai randa za’a gayamai wata yar iska ce harma yaji abun yadameshi ba, ko yadingajin ciwo aransa ba, duk sai yaji wani iri, who even send the message? What if is Hawwa? He don’t think she will ever defame kanta dudda yasan batason auren su but Hawwa is someone that value self respect and image nata, ko kadan batason compromising self respect and imagine nata saisa he even use that picture and threaten her with it, cus yasan she will not want him to expose that koda ba gaskiya bane dan she values her self respect, juyowa yayi yakalli Salman daya fito daga motan yana kallonsa da hannu yama Salman alamu daya daukomai wayansa amota daukowa yayi yazo wajen yakawomai dasauri ya karba yabude second message din.
“_Hawwa babe din boss dinta ne DIG she slept with him in order ya dauketa yasata a task force din nan dan she was an ordinary police girl before without any star_”
Sai another message. “_Officer Hawwa sleep with yaran office example Abraham data girmeshi da shekaru slept with Hawwa countless times_”,
Yanda zuciyan Khaleel ke bugawa kasa cigaba da bude sauran messages din yayi ya manna ma Salman wayan a kirjinshi yace “track those numbers all of them for me, track them! I need information uuughhhhh!” Ya dunkule hannu yayi punching air yawuce fiuuuu yatafi mota ya shiga da kanshi yarufo da mahaukacin karfi akaja motan Sam yace “lafiya are you okay”? Lumshe idanu yayi yaki magana har sukakai party saukowa yana shiga yadauki about 5 shots na tequila yana sha Sam yace “Lee are you okay? Why are you drinking like that” ko kallonshi baiyiba shaye shayen dayahau yi saida yabama duka abokanshi tsoro saida yayı total out sannan Sam da Moh suka kaishi sama aka kwantar dashi agado Moh yace “kasan what’s wrong with him”? Girgixamai kai yayi suka wuce suka fita daga dakin aka barshi warwas agado.
EPISODE
Washegari Khaleel yafarka adakinsa da kyar ya lallaba yaje yayi salla wuraren 9, ko wanka baiyiba yafito yasauko kasa Mommy na falo tace “good morning Son” ko kallonta baiyiba Noor ta taho wajenshi da gudu tace “Daddy” kanta yashafa kadan yace “go to grandma I’m coming Noor” yafice idanunshi sunyi ja duk sun nuna alamun bacci, yayi waje yana kallon Salman daya taho da sauri Khaleel yace “ya?” Salman yace “we tracked the numbers duka numbers din beggars ne dake hanyar banex, da kyar bayan nabasu kudi suka iya sanar dani wata mace ce tazo tabasu 5k tayi amfani da wayansu” dasauri Khaleel yace “did you ask them description nata?” Salman yace “yeah wai batada tsawo sosai she’s very fair and da Toyota tazo” shiru Khaleel yayi kaman mai tunani, kawai yawuce wajen motar sa Salman yabiyosa ya shiga driver ma yashiga sukabar gidan, ahankali cikin muryan gajiya da bacin rai yace “my wife’s house” jan motan sukayi har zuwa unguwan su Hawwa.
Baba na kofar gida azaune da aswaki a bakinsa ya hango mota yasan Khaleel ne kawai sai yafara murmushi kafin ma abudemai Khaleel yabude da kanshi yafito Baba ya tsareshi da idanu ganin idanunshi adan kumbure hakama fuskanshi dasauri Baba yataso shima Khaleel yawuce wajen Baba kafin yayi magana har Baba yakai hannunsa kan fuskanshi cikeda so yace “bakada lafiya ne Ibrahima”?Baba Khaleel ya kalla dan ranshi abace yake yayi shiru yakasa magana sai dan huci da yasauke Baba sai kawai hankalinsa yatashi yace “meya sameka? Tell me”? Dan ijiyan zuciya yasauke yajuyo yakalli Salman da hannu yamai alamu yakawomai wayanshi wayan aka kawomai muryan Khaleel ba dadi yanunama Baba wayanshi yace “Baba wasu sakonni aka turamin marasa dadi bazan iya karanta maka ba kaima, nasa ammin tracking number” yadanyi shiru Baba da gabanshi ke faduwa yace “ina jinka gayamin menene ke faruwa”? Cikeda jin zafi Khaleel yace “Baba matana ta batamin rai sosai, ina kyautata zaton har yanzu tana tareda mahaukaciyan nan, so nazo na ganta ne”
Dudda Baba baiga sakon ba but ayanda yaga Khaleel yasan Ni’ima tayi wani abu ranshi inyayi dubu yabaci tsabagen bacin rai yace “muje ka shiga gidan kacimata mutunci ba anan waje zan