Showing 48001 words to 51000 words out of 184554 words

Chapter 17 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1887

hatsari amman baya shiga hakan yasa ya nemi number Baban Yaseer yakira ringing daya yadaga anatse yace “Baba barka da warhaka” cikeda damuwa Baba yace “Aliyu Hawwa tayi accident gatanan a asibiti rai a hannun Allah” yanda zuciyan Baban Yaseer yabuga yakusan fitowa yace “wat?! Baba Hawwa tayi hatsari!”?

EPISODE

Ni’ima na kwance adakinta dan tun rannan maganan kirki baya shiga tsakaninsu, shima Baban Yaseer ya tattarata ya ijiye a gefe dan baison wahala da hayaniya, idan yashigo dakin yazo daukan kayane, yanda ya tattarata ya watsar abin bakaramin cimata rai yakeba, duktai wani iri kaman ba itaba, batada aiki sai shan kayan matan da Mama ta aiko mata dashi sabida duk randa zasu shirya yadawo yaga chanji, tana kwance awajen taji muryan Baban Yaseer ya ambato sunnan Hawwa, mummunan faduwa gabanta yayi dasauri ta zabura tamike tsaye tasauka daga gadon tai wajen kofa tasa hannu tabude tafito tahaderai tai folding hannu a kirji tana kallonshi, daidai lokacin Baban Yaseer yana sauke wayan daga kunnenshi da bala’in damuwa yakalleta yama manta basa wani maganan kirki fada suke yace “Hawwa had an accident Wife, Innalillahi! Suna asibitin Leadway, je dauko mayafi lets quickly go, ya Allah please keep Hawwa safe for me, please please please, yi sauri wife dauko mayafi” yayi maganan duk yadamu baimasan meyake fita daga bakinshi ba, tunda Ni’ima ta ayrı Baban Yaseer bata tabajin bakin ciki kansa kaman na yanzu ba, yanda yakeyi wlh koda tana labour room zata haihu bataga kalan rudewan nan atattare dashi ba, kirjinta kaman ana sassake kitsen wajen sabida suyan dayake mata na azaba, azuciye tashigo cikin falon yana kallonta danya dauka akwai wani abu dazata dauka awajen, batai wata wata ba tasa hannu tadauki car key shi dake kan table tarike gam a hannunta, Baban Yaseer yakalleta dasauri, Ni’ima tace “we are not going” da mahaukacin damuwa akan muryan Baban Yaseer yace “me kikace?” Kallonshi tayi afadace ta matso dab dashi tana hucin kishin fitina ganin yanda baya hayyacinsa sabida kawarta tace “Hawwa ta mutu ma idan zata mutu is not my business tunda ba yar uwanmu bace ko munhada jini da ita ba, kuma bazaka ba wat is your business with her? Nagadai kawata ce ba taka ba? Kataba ganin ina shigema abokananka maza? Baruwanka da Hawwa” baki Baban Yaseer yabude zaiyi magana Ni’ima taci numfashinsa tace “Aliyu stay away from my friend! Hawwa kawata ce she has no business with you! Baruwanka da ita! Wayataba cewa dole sai miji yadauki responsibility kawar matansa? Get a hold of yourself kadaina bin kawata kuma ba zakaba!” Tun bayan abinda yafaru ranan yadan bata space cus yasan she’s not okay, amman yaudai no, damuwan daya ciki ma jin Hawwa tayi hatsari bazai taba iya tsayawa gardama da ita ba he just want to see kanshi gaban Hawwa, hannu yamika mata strictly yace “give me my car keys” faduwa gabanta yayi yanda yahade rai yana tabashi key bama ta maganganun datamai yakeba ta masoyiyarshi dake asibiti yake baidama lokacin biyemata suyi fada hakan yakara tunxurata cikeda karfin hali tace “bazan bayarba, nace bazaka je ba, uban me kahada da Hawwa? I’m tired of yanda every little thing you will be running to her rescue, rannan haka kafita tsakar dare without thinking twice Aliyu kabar ni da yaranka biyu cikin gidan nan katafi wajen wata, wat if mu wani abu yasame mu? Wat if barayi sun shigo? I’m your wife you know nikeda hakki akanka ba Hawwa ba, bakada wani business or what so ever da abokiyata, wlh bazan bada key nan ba” cikin kakkausan murya Baban Yaseer yace “this is the last time zan miki magana, hand over my car key! I don’t have time for argument ko bala’i dake, ruhina, zuciyata da kuruwata basa nan suna wajen Hawwa da gangan jikina kawai kike magana, give me the damn car key Ni’ima” yanda kalaman Aliyu ke samata bakinciki kaman ta hadiye zuciya ta mutu awajen, ita Aliyu ke gayama magana haka, jitayi koma mexai faru yafaru kaman zata haukace da bakin ciki tace “wlh saidai kome zakayi kayi bazakaje asibitin nan ba, bazakaje wajen Hawwa ba, ina matarka kana gayamin kuruwanka na wajenta da gangan jikinka nake magana” kawai tafashe da kuka mai ciwo tace “macuci, maciyi amana kawai, mayaudari, kawata zaka so har kana haukacewa akanta haka dame Hawwa tafini? Baban Yaseer kaci amanata wlh kaci amanta, Allah ya kashe Hawwa! Allah ka dauki ranta afito da gawanta daga asibitin na……n” hannu dayaga ya kaimata mari a fuska sai kuma ya tsaya chak hannun na gab da landing a fuskanta tareda sauke hannun kasa yana huci sosai jin addu’an datama Hawwa, hannunshi tabi da kallo daya dunkule da yanda yake huci tace “ni zaka mara sabida Hawwa eh Baban Yaseer? Ni matar ka? Ni Ni’ima zaka kusan daurama mari sabida kawata? Baban Yaseer ni”?.

Bai tankataba cus baiso fushi yadebeshi yayi wani abun dazaiyi nadama nan gaba, baiyi believing in hurting women ba, but harga Allah Ni’ima is pissing him off, baima fahimci this whole anger da fushi da wani tantrums nata ba akan zancen nan shi baice zai auri Hawwa ba out of goodwill bawai dan bazai iyaba no sabida kawai bayason yabata beautiful years of friendship nasu, and again bai sanar da Hawwan ba, Hawwa have no idea yana sonta so what is all this haukan da Ni’ima keyi? Hannunshi yasa yakamo nata azuciye zai karbi key din Ni’ima tashiga kokawa dashi tana kaimai duka da hannu daya tana haki. “Wlh bazan bayarba saidai ka kasheni ka amsa” murde hannunta Baban Yaseer yayi Ni’ima tai kara tace “Aliyu you’re hurting me sabida Hawwa, wannan rawan jikin da haukacewan sabida best friend dina kakeyi, Aliyu I hate you, how could you? Why will you fall in love with Hawwa? Meta fini dashi? Yarinyar datai kwnatai sabida bakin jini? Yarinyar da Babanta ke rokon mutane suzo su aureta, rawan jikin menene kakeyi dame Hawwa tafini”? Hannunta ya murde da karfi ya karbi key sannan yanunata da hannu amasifance yace “Hawwa tafikida komi! Tafiki hankali! Tafiki natsuwa! Tafiki ilimi! Tafiki kyau da iya murmushi! Tafiki kunya! Tafiki iya girki! Tafiki kwazo! Tafiki kwarjini da haiba! Daga ranan bikinmu rannan dana fara haduwa da Hawwa naji inama ita na aura bakeba! Haryau har gobe I wish inama Hawwa na fara sani not you! I wish itane matana! Hawwa will never act like this! Hawwa carry kanta with dignity! She respects kanta! She knows what she’s doing unlike ke, look at the way kike behaving kaman dakikiya! I explained something for you but brain dinki yakasa comprehending ko ascertaining duka abinda nace, bayan you forced me to speak cus kece kikaje kikamin bincike who sent you to check my phone? Kina bincikamin waya who do you think you’re? Kece ke aure na? Kinama Hawwa wishing mutuwa kawarki that did everything in her power for you! Kin dauka inda inaso na aureta bazan iyabane? Kira daya zanma Baba angama magana, I explained everything for you but still jibi yanda kikeyi? What is all this classless attitude? For wat exactly? I hate razz woman idan kika zama one I will terminate aurenmu cus ban iya ihu ko fada ba, bakina baida kyau, don’t push me, if you push me wlh wlh saina auri Hawwa kuma agidan nan zata zauna! Don’t push me to the wall Ni’imatullah!” Kadakai yayi yawuce yafita abinshi Ni’ima tafashe da kuka sosai awajen kaman ta kashe kanta yau tayi dana sanin sanin Hawwa, ita Baban Yaseer zai kira dakikiya Innalillahi, batun yau yafara son Hawwa ba?.

EPISODE

Khaleel na zaune a premises na asibitin kan wani hadadden kujera dake under wani shade na flowers yana jiran suzo su daukeshi dan sunce sun kusa akwai traffic a hanyan school na Noor sabida accident din nan, kuma hakanan baiso yakoma ciki sabida Baba tunda yagane Baban Hawwa ne yakejin nauyinsa hakanan, motan Baban Yaseer daya danno kai cikin hospital din Khaleel yabi da kallo, wanda kallo daya yama motan yagane motan sabida plate number shi kanshi baisan how come ba but yatuna rannan yakalli plate number motan kuma yazauna akanshi baimasan me dalilin da plate number wani random mutum zai zauna akansa without permission ba, haderai yayi tamau yabi motan da kallo, parking Baban Yaseer yayi nesada inda Khaleel yake zaune yakashe motan yafito yana sanye da riga da wando na shadda mai ruwan goro dayamai kyau, yakafa hula akanshi, haskenshi yafito bau ga bakin glass akan idanunshi, zagawa yayi zuwa bayan motan yabude yafito da manya manyan ledojin for you supermarket yayi shopping yarufe motan yawuce yana tafiya anatse, abu Khaleel yaji ya tsayamai a wuya sai kawai yatashi da hannu yakira security asibitin yazo da gudu yace “Yallabai gani” cikeda isa yanuna Baban Yaseer yace “seize ledojin da mutumin chan yazo dasu” dasauri security yakalli Baban Yaseer saikuma yakalli Khaleel daya haderai sosai yadan rage murya yace “Oga mezan gayamai? I can’t seize abinshi” ihu Khaleel yamai ranshi abace yace “tell him we give our patients food, we don’t accept akawo musu anything daga waje it’s a law daga yanzu go!” Khaleel yafadi aharzuke security yajuya yatafi da sauri shikuma ya tsaya awajen yana kallonsu dudda baiji meyake fadiba but dan bacin rai daya gani akan fuskan Baban Yaseer yamai dadi dan murmushi yayi yana tsaye awajen saiga Baban Yaseer yajuyo, dauke kai Khaleel yayi abinshi haushin sa yakeji kawai yaciro waya ma abinshi, haka Baban Yaseer yabude mota yadawo da komi ya ijiye sannan yawuce Khaleel yajuyo ya watsamai kallo mara kyau daidai motanshi na shigowa wucewa kawai yayi yashiga ya zauna sukabar hospital din sai alokacin hannunshi yafaramai zafi ya kalli hannun, dan tsaki yayi ya yarfe hannun yadan kishingida da kujera bacci yakeji sosai, yau kwata kwata bai sami baccin da ranshi keso ba.

Gida suka wuce ana parking yafito yayi flat dinsu yabude kofa Momy yagani zaune tareda Momy Sam matar kanin Excellency wacce take baturiyan bahaushiya, mahaifiyar ta yar Nigeria ce yar kano bature ta aura ta haifesu saisa duk sukai kaman da baturen but hausa rass abakinsu, suna magana yashigo wajen Mommy yawuce ashagwabe yazauna kusada ita babu batun gaidasu yamika mata hannunshi kaman dan yaro yace “Moma zafi” duk randa shagwaban shi yatashi Moma yake kiran Mommy, dasauri Momy tace “Subhanallahi, Khaleely tayaya kaji ciwo haka? Menene amfanin guards dinka dazasu barka kaji ciwo haka? Why are they getting paid”? Afusace Mommy Sam dan duk jirgi daya ya kwasosu tace “fire them they don’t know their job, Khaleely ne zai kulada da kanshi? They’re very useless, Sorry Son” tai maganan tana kallon Khaleel dake abu kaman yaro yana kallon ciwon dakemai zafi, duk Mommy tarude ta tashi da sauri ta dauko first aid kit tazauna kusadashi spirit tadauka da sauri tana gutsuran auduga tasa aciki takai zatasa a hannun wlh kaman dan yaro, kaman Noor karama ya fizge hannun yace “Momy ni banson spirit zafi yakeyi” kaman Mom zata fashe da kuka dukta susuce tace “yakuri ka daure nasa maka kaji Khaleely, wai yama akayi kaji ciwo eh? All this workers namu sunsan babu abinda na tsana irin naga mistakenly kaji ciwo? Ya akayi kaji ciwo haka”? Turo baki yayi batare dayayi magana ba, Mom Sam ta taso itama tazo wajen tadafa kadanshi tace “muga hannun” nunamata hannun yayi ahankali cikeda dabara tace “toka daure give your Mom to treat it kaga yanda ta damu” kallon Mom yayi datai kaman zatai kuka kaman wani babban abine ya sameshi tsabagen yanda take sonshi, ahankali yace “small zakisa Mom” dasauri tace “eh naji, kadan zan sama” bata hannun yayi tasa kadan Khaleel yayi ihuu zokaga yanda suke lallashin sa ohh ikon Allah kaman kwai, sannan tashafa healing balm yamike ahankali, Mom tace “zokai breakfast” ahankali yace “I want to sleep I’m sleepy Mom” bangarenshi yayi Mom ta kwalama PA kira, dasauri PA tazo tana sanye da suit baki, Mom tace “cikin 3 girls din nan dasuka rage akaimai daya” Gyadamata kai tayi PA tayi tace “yes Ma” tajuya itakuma Mom suka cigaba da hira, fitowa PA tayi da Zainab dasai murna take cus bata dauka zai kara nemanta nabiyu ba aka kaita side nashi har zuwa sama, knocking PA tayi gaban dakinshi shiru hakan yasa tabude kofa takalli zainab tace “shiga” shiga ciki Zainab tayi itakuma PA tawuce.

Fitowa Khaleel yayi daga wanka daure da towel a waist ruwa na bin chest nashi yakalli Zainab dake tsakiyan dakin tsaye, suna hada ido ta sauke kanta kasa dasauri jikinta har bari yake sabida dadi, awulakance yadauke kai wucewa closet yayi dan yaji sanda ake knocking bai wani jimaba yafito sanye da boxer yana kamshi yagaji bacci kawai yakeso fadawa gado yayi yana sauke ijiyan zuciya yana kallon sama hakanan kawai deep down he’s wishing ta farka yanzu, yadan lumshe idanu gaban boxer dinshi a mike idanunshi a lumshe har lokacin yace “ke come here” dasauri Zainab tai wajen gadon kaman tana magana da sarki tace “g….ga…..gan….gani” dan lallataccen tsaki yayi batare daya bude idanunshi ba yace “ride me” jikinta har rawa yake ta shiga cire kaya tazo tahau kanshi har lokacin idanunshi a lumshe, har cikin ranshi ya furta “don’t die i still have business with you” riding dinshi Zainab keyi amman he’s not even feeling anything kawai yayi shiru kaman matacce kusan 10min kawai ya kifar da ita yafara he don’t even know why yaketa gannin that accident mara kunyan yarinyar nan consistently……

Su Momy na zaune a falo suka fara juyoshi yana ihu, Mom tai murmushi tace “muje falo na kinsan Khaleel baisan menene shiru ba shikuma arayuwansa” tabe baki Mom Sam tayi tace “idan da sabo ai nasaba hakama Sameer duk ubanninsu suka gado ai” dariya sukayi daga Mom har ita tace “yara ace this is just wat is making them happy, zamaninmu is not like that ooo” dariya Mom tayi tace “is from abincin dasuke ci, see en let’s give them happiness” Mom Sam tace “sonake Sam yayi aure kaman Khaleel banson matan banza, shikuma matan banza yafiso” Mommy tace “samowa zakiyi kimai da yaronka yayi iskanci awaje gwara yayi agida, look at abun kaman irin ragon layya ko nama, danka na son wannan tinkiyar I don’t mind konawa ne wlh zansa kudi na sayo na kawomai yacisu ya koshi koyayar koya zubar idan yagama ci duk ba matsala ta bace haka nake kallon duka matayen Khaleel kaman tumakai danasa kudi na sayo nabashi yayi bukatanshi da su idan baiso ya zubar ko ya yasar Safara” tasauke ijiyan zuciya tace “all this shaye shaye is time zasu dena yarane, last month Khaleel yayi 32yrs birthday nashi fa, he’s still a child, at the age of 24 nafaramai aure cus I caught him watching all this videos na banza, I give d’ana freedom yayi anything dayakeso agaba saisa me and Khaleel share a deep bond sosai I understands him sosai sama da babanshi, idan lokaci yayi zakiga da kansu zasubar shaye shayen kuruciyane wlh, kinga Khaleel babu wani abu nashi daban sani ba, I choose the gurls all of them for him , I’m his everything” gyadama Mom kai tayi tace “wlh zanma Sam auren nan shima” Kusan 1hour suna juyo ihun Khaleel ko ajikinsu chan suka jishi shiru PA tawuce dan dauko yarinyar dan baya kwana da kowa agadonshi, knocking tayi gaban kofan batare data budeba tace “kifito” tashi Zainab tayi daga kasa tana kallon Khaleel dayayi rub da ciki abinshi, kasanta har zafi yake mata ya kumbura sabida yanda shi babu yi ahankali a lamarinshi tawuce tafita. ‎<This message was edited>

EPISODE

Shiga cikin hospital din Baban Yaseer yayi anan reception yaga Baba zaune dasauri yayi wajenshi adan rude yace “Baba” dasauri Baba yajuyo jin muryan Baban Yaseer yace “na’am Aliyu harkazo? Ga dakin nan likitoci na ciki cewa sukai na fito, ina Ni’ima”? Boye komi yayi yace “tana asibiti, nariga na gayamata zatazo da zaran tasami chance” Baba yace “Allah sarki Ni’ima nasan tashiga cikin tashin hankali” Baban Yaseer yace “Baba an ina tayi hatsarin”? Tagumi Baba yayi ahankali yace “wlh bansani ba ko inda motanta yake ma bansani ba ta lafiyanta nake yanzu, kwananta biyu batada lafiya tun ranan litinin da yamma, yauma cewa tayı bari taje asibitin su Ni’ima adubata saidai aka kira su Ammi wai me waya tayi hatsari nikuma suka kirani su Ammin suka sanar dani” anatse Baban Yaseer yace “kada kadamu Baba zan kira wani Abokina dake aiki da road safety naji idan zan sami any details na hatsarin da inda motarta yake” Baba yasauke ijiyan zuciya yace “tom shikenan” Baban Yaseer yadaga wayanshi yakira yadan matsa daga inda Baba yake kusan 20min yayi sannan yadawo yace “Baba ance motoci biyar ta deba ta hada da trailer amman Alhamdulillah babu any casualty babu wanda yarasu saidai sunji ciwo, ance wanda yakawota asibiti yasa agent ne ko PA wani dai nasa yasaka yabiya duka masu motocin har trailer kudin gyara motan su da kudin zuwa asibiti” Baba yakama baki da mamaki yace “iyye awannan zamanin abiya kalan kudin nan? Wannan bawan Allah akwai kyan zuciya da imani dakuma adalci da taimako” Baban Yaseer yace “ba shakka, kowaye gaskiya yayi kokari Allah sakamai da Alhairi”.

Duk suna zauna awajen dan an hanasu shiga dakinta har around 12 na rana saiga Ammi tashigo reception din tareda Ramla dake goye da katuwar jaka abayanta dukansu idanunsu ja, Baba na ganinta yashiga kokarin mikewa hakama Baban Yaseer Ammi ta taho wajen dasauri Baba yayi wajenta hankalin Ammi atashe tace “ina Hawwan Malam? Ina Hawwa na? Ina tak….” Sai kuka kaman ba Baba ba yace “ya isa ya isa, gatachan adaki ance kar adameta kar a shiga saita farka, zauna, Ramla kema zauna” ahankali Baban Yaseer yace “ina yini Ammi” gyadamai kai tayi tana goge fuskanta da bakin hijabi tace “lafiya lau Aliyu sannu, bazakaje aiki ba ka zauna anan” adan hankali yace “bari mugani zuwa ta farka yanzu banda natsuwan yin aiki” ijiyan zuciya Ammi tasauke wlh har ranta batason zamanshi anan, cikeda hikima tace “to dan Allah tayani kai Ramla gida ta ijiye kayanmu tadafo wani abu takawo incase

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login