Showing 21001 words to 24000 words out of 184554 words
bazaki taba ganin daidai ba” dan murmushi kadan Hawwa tayi kaman bazatace komiba saikuma tasa hannu tadauki cup tasha ruwan tass ta ijiye ta kalli Umma tace “Umma kenan ai ko azaban dakika azabtar dani yabiya koma wani kalan laifi Mamana tamiki, kibar tunanin dakikeyi, lokaci kawai baiyi bane, duk sanda lokaci yayi zanyi aure Umma, bakece dalilin ba” tayi maganan tana mikewa Umma tace “sai ayi mugani, mara kunya kwantai kawai”.
Fitowa Hawwa tayi daidai zataje dakinta taji Baba na kwalamata kira yana shigowa gidan da saurinshi. “Hawwa, Hawwa, Hawwa, Jiddah” tsayawa tayi chak tace “na’am Baba” cikeda farin ciki Baba yataho yace “maza shiga ki sanyo hijabi kifito munyi baki, Zainabu ke fito da tabarma ki shimfida anan tsakar gida” yana maganan ya shiga juyawa Hawwa ta bishi da kallo kirjinta na mata zafi saikuma tawuce tafada dakinta itakuma Umma tafito da tabarma ta shimfida musu shigowa Baba yayi ga Malam Sama’ila gakuma wani dan tsoho haka da akalla zaiyi 50 plus yana sanye da kaya masu dan mutunci da hula akanshi ga gemu kaganshi siriri kaman iska zai kwashesa, ga yar gemunsa siririya da gashin duk yayi fari fari Baba yace “bismillah ku bismillah ku” zama sukayi Baba ya kwalama Umma kira da katon murya yace “Zainabu kawo musu ruwa”Malam Sama’ila yayi gyaran murya yace “to Malam Hamisu bayan maganan damukayi dakai kwanakin baya nabada sanarwan kaman yanda kace sabida shi d’a dakake gani nakowa ne” Baba yace “kwarai!” Malam yace “Hawwa yarinya ce mai hankali datai boko tana aiki a matsayin yar sanda, maza da dama sun fito but gaskiya yawancinsu gajiyayyu ne ko matayensu na gida basu rike ba balle su kara da Hawwa, shi Kabiru daya zomin da maganan shi kadai na aminta dashi”
Yanuna mutumin yace “dudda Kabiru ba a unguwan nan yake ba but anan aka haifesa anan yataso marigayi mahaifinsa aminina ne, Matan Kabiru biyu yanada yara goma sha daya, Alhaji ne yasauke farali, yanada gonaki sannan shi principal ne a makarantan gwamnati ta cikin Bwari” Baba jikinsa har rawa yake yace “uhmm Masha Allah da kyau” Malam yace “yanada rufin asiri daidai gwargwado sannan yanada gidan kansa, danamai magana ya nunamini ai ya dade da kaunar Hawwa azuciyansa shi tsoronsa aikinta, baison mace mai aiki ballema irin nata aikin na yan sanda zaiso tabar aikin, sharadinsa kenan saiya kawo kudin aure, sati biyu zuwa uku inhar kun yarda yakeso adauka ayi auren ayi komi koba hakaba Alhaji Kabiru”? Anatse ya gyadakai yace “kwarai Allah gafarta Malam hakane” dariya Baba yayi irin na manya yace “indai aiki ne matsalan bakada matsala Kabiru kaman tabar aikin nan tagama, hana karya dai kasan irin aikin nasu dole kaje ka kai takardan barin aiki dan idan baka kaiba ana iya zuwa a kamaka koba hakaba Malam to zanso kabarta taje tabasu takardan ayi signing komi tarabu dasu lafiya koba hakaba”? Kabiru yace “hakane, indai wannan ne ba matsala Abba zata iya zuwa” washe baki Baba yayi kaman an basa kujeran makka Baba yace “Malam tashi muje waje shi saiya gana da Hawwa” ba musu Malam Sama’ila yatashi yayi hanyar zaure Baba yawuce jikin kofan Hawwa ya bubbuga yace “maza kifito kinada bako Hawwa” sannan yawuce waje yana murmushi sosai. Kusan duka abinda suka tattauna a kunnen Hawwa, dan koda bataji maganan kowaba zataji na Baba cus Baba akwai katuwar murya, she’s feeling so sad and so angry with Baba, like akanme zatabar aikinta bayan bawaima auren ya tabbata bane wat is wrong with Baba? Why is he so blind and obsess with tayi aure da he’s not seeing clearly, she’s regretting abinda yasa bataje aiki bama yau dan dataje da bazama a sameta a gidan ba balle amata wannan maganan kusan 15mins tabata aciki kawai babu yanda zatayi mahaifi mahaifine hakan yasa tadauki wani nude color hijab tasaka dayamata bala’in kyau tazo wajen kofa tadan daga labule ta leko compound din, amai taji yazo mata wuya cus this is not the man datai imagining living life with, he’s too old for her! He’s not handsome at all, he’s too slim kaman ana dibanshi ayi miya, gawani dogon baki dayake dashi kaman na fish, yawani zauna akan tabarman kaman wanda yazo wa’azi, itafa tanada taste, she loves fine classy men dasuka iya gayu not this types, ijiyan zuciya tasauke tace “Hawwa calm down” lumshe ido tayi tabude sannan ta fuzar da iska daga baki kafin tasa hannunta tabude net, karan bude net din yaji dasauri Alhaji Kabiru yajuyo yazuba mata wasu mayun idanu azuciyansa yace “mace har mace wayyoo Allah, na sameta bakaramin hutawa zanyi da itaba, Allah ne ya taimakeni Babanta yabada sanarwan nan daban isa na tunkareta da zancen soyayya ba” in reality yahade fuska cus bayason ta rainashi wannan da har sanarwa ake ana nema mata miji tayi kwantai dole yanuna mata shi mai tsada ne infact she’s lucky ma yazo, jahadi yazoyi sabida tadinga binshi sau da kafa sabida karya gudu shima, duk yanda yaso yajaye idanunshi karya kalleta yakasa tundaga kan kafafunta yake kallo har ka, kallon dayake mata kaman zai tashi ya lasheta, abin yakara tunxura Hawwa ta dauke kai har takai gaban tabarman taja ta dakata ta tsaya dan jitayi bazama ta iya zama kusada shi ba, agogon hannunshi yashiga kallo yace “da fitan Babanki zuwa yanzu kimanin minti sha biyar, haka kikaga babar ki na batama Babanki lokaci”? Dasauri Hawwa ta zubamai shegun idanunta da saida yaji gabanshi ya yanke ya fadi rasss dahar hakan yasa bakinshi ya shiga rawa yabasar yamike tsaye da sauri yace “nan da kwana uku zan kawo kudin aurenki dan haka ki tabbatar kinyi resigning daga aikin nan kafin nazo, and kuskuren dakikai na yau kada ki saka gwada kwatankwacin irinsa” yashiga saka takalmansa zai wuce Hawwa ta mike hannunta daya ta taresa kaman irin ta tare dan cikinta dinnan da kakkausan murya tace “Kai!”.
Bala’in faduwa gaban Alhaji Kabiru yayi yabi hannunta dake dab da tabashi a saitin kirjinta da kallo that’s so milky yana shinning da fararen kumbanta dasuke nan dogaye a gyare sosai yadai daure da kyar dan hakanan yaji kawai yana shakkanta wlh tsoro ma yaji tana bashi, sauke hanunta Hawwa tayi tadan tako ta tsaya agabanshi daidai kusan tsawonsu daya dan Hawwa nada tsayi, cikin wata kalan sansanyar lalatacciyar voice na cikakkiyan mara kunya tace “kasan what I do to men like you a office dina?” Tayi maganan slowly tana kallon kwayar idanunshi kaman yanda yake kallon nata, yatsanta ta daga tayi pointing goshinsa sannan tashiga sauke yatsan kasa yana bin yatsan da idanunshi hartakai yatsan wajen gefen gabansa tace “i thrash men like you!” Dum dum dum gabanshi ke fadi yana kallonta dan she could see fear a idanunsa batasan wani kalan baiwa Allah yamata ba but maza na dan tsoronta saidai idan bata zuba musu idanu ba, dan duko da fuskanta tayi takawo dan da nashi tace “Idan you don’t want to end up akan table dina nayi thrashing naka! Avoid Hawwa! Bazan taba aurenka ba! Ka kama kanka da sharadinka kabar gidan nan” dan komawa baya tayi tana kallonshi sannan tajuya abinta yabita da kallo zuciyanshi na bugawa dum dum dum har lokacin kaman zai fito sannan yayi hanyar zaure da sauri.
EPISODE 17
Fadawa dakinta tayi tacire hijabinta ta yarda ta zauna kan gadon tayi tsaki, ba’a wani jimaba Baba yayi sallama yana bude kofan abinda baicika yiba da wuya yazo dakinta saidai ya aiko akirata da sauri ta tashi zaune shigowa yayi yana murmushi sosai kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki yace “Hawwa kinga Alhaji Kabiru ko ai sai yanzu Malam kemin kwatancen mahaifinsa da kyau wlh nima naganesa aminin mu ne” yayi maganan yanajan kujeran wajen kayan kwalliyanta ya zauna yana ijiye crutches nasa a gefe dasauri Hawwa ta tasauka kasa ta zauna Baba yace “Alhamdulillah nagode ma Allah Hawwa, to yanzu yace yanason kibar aikin jibi zai aiko da magabatansa da kudin aure kinji”Abu tahadiye daya tsaya mata awuya she respects Babanta so much and she loves him alot sabida ko ba komi duk wuya duk runtse yariketa ta taso a hannunshi ai bai bari Umma ta azabtar da itaba, sai dai wanda bada saninsa ba, yayi makesure tai makaranta yabiya mata WAEC dudda anan ya tsaya da biyan komi ita tasa kanta a university da kudin dinki datakeyi tun tana yar 3yrs ta taso taga Mamanta na dinki wlh bata taba koyan dinki ba samin kanta tayi ta iyawa dan Baba yabata keken dinkin Mamanta as shine gadonta ahaka tayi school, Baba supported school nata tunda babu miji while sauran kanninta daga sunyi WAEC Baba ya aurar dasu, bayan tagama criminologist kawai taji tanaso tashiga police nan fa saida aukai fada da Baba but daga baya ya yarda taje police school a Kano tafito tafara masters kafin ta sami aiki, she loves Baba and tanaso tarabu dashi lafiya, but this she can’t do, tabar aiki wazai rike gidan bataso suyi fada hakan yasa tace “shikenan Baba amman bansan sanda zasuyi approving resignation later na ba” Baba sosai yayita murmushi ganin batamai gardama ba yasa yace “inhar sunyi signing kafin auren da sauki zan iyama Kabiru magana ya barki kicigaba da zuwa ai naganshi mutumin arziki ne mai saukin kai, Allah miki Albarka kinji Mamana” gyadama Baba kai tayi takalleshi jin sunan daya kirata dashi, Kafin yatashi yafita yana kwalama Umma kira dan yabata labari.
Lumshe idanu tayi, aduk fadin duniyan nan da Baba da Umma kawai take tolerating itama Umma darajan Baba takeci forget suna fadansu but Baba he deeply cares for her, batason wani abu dazai dagamai hankali tariga ta girma yanzu tundadai ba dukanta Umma zata iyayiba tariga ta shafe chapter ta cus she’s her least problem.
Wayanta ta dauka dan kiran Ni’ima taga Alert 1.5Million ya shigo account dinta dasauri tashiga taga DIG ne yatura musu da sauri ta kunna data taga yayi magana a group din dasuke just su hudu yace “the vice president appreciate efforts namu with some token, i sent kowa his share, Weldone guys get some rest i will see you tomorrow at work” taga su Hayatu da Abraham sunyi godiya itama tai typing thank you Sir, she’s happy with the money, bude account nata tayi tasama Ni’ima 100k, ta turama Aminu 50k, Asiya 50k, Rahma 50k sai Nanah 50k, ahankali tace “I will keep 50k for Mims” tadanyi murmushi daidai kiran na shigowa wayanta datai saving da Aminu Bro, katse wayan tayi dan she always act like the big sis to kanninta takirashi back, ringing daya yadaga da so much excitement yace “Ya Hawwa you are the best big Sis ever thank you” murmushi tayi tace “ya school din? Ya project kagama?” Da murna akan muryansa yace “yau zankai chapter 4” gyadakai tayi tace “okay” adan natse yace “hope you’re fine ko Baba da Umma basu damunki, hope you are okay?” Dan murmushi tayi tace “I’m very okay babu mai damuna just study well if you need anything ka kira” gyadamata kai yayi yanda Ya Hawwa ke kulada su ko Umma mahaifiyarsu bata kula dasu haka, ahankali yace “thank you Ya Hawwa” anatse tace “bye” tana katse wayan kiran Asiya na shigowa ta katse ta kirata dasauri Asiya tace “Ya Hawwa naga sako nagode nagode Allah amfana” batason ana mata godiya hakan yasa dasauri tace “Ya Akram yana cin abinci yanzu”? “Eh yafara ci, har tuwo ina bashi but da miyan yauki yakeci” murmushi tayi tace “okay a gaida Baban su bye” bye all sisters nata saida suka kirata, dudda duk sunsan mahaifiyarsu batason Hawwa su suna kaunanta cus she takes care of them, tanada very good and matured relationship da siblings dinta, tana gama wayan saiga na Ni’ima ta daga, tana dagawa Ni’ima tace “wai dawa kike waya haka?” Murmushi tayi tace “kishi kike nayi sabuwan kawa ne”? Dariya Ni’ima tayi tace “akwai invincible name dina a goshinki babu wacce ta isa tai kawance da kawata, naga kinsamin kudi I’m refunding it right now” kai tsaye Hawwa tace “ba naki bane Hajiyata calm down na Yaseer ne da Yasmeen, an bani bonus na aikin damukayi, so I wanted to spoil them idan ke ba evil spirits bane kidawo da kudin mugani” dan shiruuu Ni’ima tayi chan tabude baki zatai magana cikeda tsokana Hawwa tace “toh Mamana zata faramin wa’azi kan kashe kudi yanzu zatace kayan daki yakamata nadinga siya ina tari” dan murmushi Ni’ima tayi da dan damuwa tace “Hawwa idan aka tashi aurenki bakida mai miki, Baba bayida karfi shima adan albashin naki yake surviving, u will be the one to do everything ga gyaran jiki so many things” dan tabe baki Hawwa tayi tajuya idanu alamun tagaji da zancen tace “zanhau keke nayi dinki anjima zanje kasuwa nadan sayo kayan abinci bye” Ni’ima zatai magana Hawwa ta katse wayan da sauri chan saiga messege tace “thank u Best, I love you, yaranki suma sunce Allah amfana”.
Murmushi Hawwa tayi batare datayi replying message dinba ta tashi tawuce wajen basket din tabude tana ciro wasu materials datariga ta yanka ta warwaresu akasa sannan tadauki wani ta hau kan keken tana saita zare tahau dinki, yawanci dinki yanasa tana mantawa da damuwanta, tana cikin dinkin akai sallama wani yaro yakawo mata makullin mota inji Baba ta leko ta amsa.
Sai bayan tayi la’asar sannan ta shirya cikin wani black abaya mai kyau sosai ta daura gyalen asaman kanta batare datai rolling ba, tadauki handbag da wayanta da car key tafito kaganta zaka dauka yar mai kudi ce tanada expensive body, fitowa waje tayi Baba yace “ina zaki”? Ahankali tace “zandan karo kayan abincin gidan ne Baba an biyani bonus, zan kuma siyo landing da zaren dinki ina dinka wasu kaya ne banda abubuwan dinki” jinjina mata kai yayi yace “to saikin dawo Baban Yaseer ya aiko da motan ki dazu” gyadamai kai tayi tawuce wajen motan nata dataga an wanke har ciki yayi tsaf tsaf yana kyalli tabude ta shiga tanabin motan da kallo dataga an samata turarukan mota masu bala’in kamshi harda wani expensive car diffuser, murmushi tasakeyi ta shiga tada motan yan anguwa sai kallonta suke inda sabo ta saba tai reverse ta juyo sannan tafice daga anguwan kasuwa tafara shiga tasayo buhun abinci dasu jarkan mai akasa mata a boot sannan taja motan zuwa wani super market dake wuse 2 mai shegen kyau yawanci anan take samin wani botura masu kyau foreign datake sawa gaban shirts dinta na zuwa office.
Parking tayi tabude motan tafito tana rike jakanta a hannu tanajan gyalen gaba sabida yanda gashinta ke fitowa gashi kitson yadanyi tsufa, maida kofan tayi tarufe tama motan key sannan tai ciki tana tafiya ahankali one step at a time harta shiga tafara duba wajen supplies din kayan dinki duk abinda take bukata saida ta dauka sannan tabar wajen tana tafiya ahankali rikeda basket din datasa abinda tasayo ciki, wajen shelves na books ta tsaya tana daukan novels tana duba authors din cus tana karanta English novels sosai kamshi mai bala’in dadi ne ya daki hancinta daidai ta dauki wani novel abin har saida yasa takai novel din hancinta cus she was curious an fara scented novels ne? Jin ba novel din ke kamshi ba yasa ta janyeshi daga hancinta, she don’t want to look stupid but wlh kaman tajuya ta nemi mai kamshin and ask sunan turaren cus she loves the scent, tana tsaye awajen kaman daga sama taji an rungumeta ta baya. “FAA yayyyy!” Adan tsorace Hawwa ta juyo dan har saida gabanta yafadi jin yanda muryan little girl an kuma riketa atare, da sauri ta juyo daidai Noor ta saketa tana dagowa tana wani irin murmushi tana kallonta, kyakkyawan yarinya ce tana sanye dawani half gown, kallon yarinya Hawwa tayi sosai from facial expression dinta kasan bata ganeta ba saikuma tabi gabanta da kallon ko zataga iyayen yarinyar, ganin maza tayi su hudu wanda tana ganinsu tasan bodyguards ne, hannunta taji an kama dasauri Hawwa tadauke kanta daga kallon bodyguards din takalli yarinyar dake murmushi sosai tana washe baki tace “I can never ever and ever forget your face Anty, Anty you don’t remember my face”? Ahankali Hawwa ta duka tana kallon yarinyar that is so beautiful and the way she talks is so adorable tace “Hi cutie” still trying tagane yarinyar dasauri Noor takai hannunta goshi tace “oh noo, I’m Noor Ibrahim Khaleel Mangal, and you saved me, your are my fairy angel Anty FAA” zaro daradaran idanunta Hawwa tayi tace “Ohhh Noor I’m sorr……” bata karasa magana ba Noor ta matso tareda manna mata peck a goshi tace “Noor loves Fairy Angel Anty, come and see my Dady” yarinyar tayi maganan tana kama hannun Hawwa data tashi da sauri awkwardly tace “uhm Noor, no….” jan hannunta da karfi Noor tayi tace “please, please please FAA, yanzun nan Dady na yafita yayi waya” yanda bodyguards din suka wani bude musu hanya yasa ba yanda ta iya tabar basket na abubuwan dazata saya awajen tabiyota suka fito waje Noor tarike hannunta gam gam kaman za’a kwace zuwa wajen wata arniyan customize Maybach dake pake a tsakiyan motocin mopol guda biyu gawani lafiyayyen bodyguard tsaye gaban motan dayana ganin Noor yabude bayan motan, tana zuwa wajen motan batai wata wata ba tasaki hannun Hawwa data tsaya awkwardly tana kallon yanda yarinyar tashiga motan ko 1min batayiba tafito tana jawo black hand waje da karfinta kaman yanda taja Hawwa dazu tace “Dadyyyy” rasa yanda zatayi Hawwa tayi Noor tajuyo tana kallon Hawwa tana dariya sosai kaman mara lafiya nan ko tsabagen murna ne tace “Dady see my Fairy Angel Anty she saved me that day from those bad people, Dady comeeeee” tai maganan ashagwabe kaman zata fashe da kuka dayasa gently ya sauko da kafafunshi kasa hakanan Hawwa taji gabanta yafadi dayasa dasauri tace “Noor Dear, Dady don’t have to see……” Kasa karasa maganan Hawwa tayi sabida yanda Khaleel yafito daga motan yana sanye da 3quater wando daya tsayamai a knee, yasaka wani black sneakers na givency mai tsinannen kyau, yana sanye da shirt lilac color shirt da butura ukun sama duka a bude kana