Showing 39001 words to 42000 words out of 184554 words
Bata taba kawo Baban Yaseer ba cus tadauka Ni’ima ta turoshi yabiyota hanya, tai tunani tai tunani duka amsan da brain dinta ke bata is takama tashiga hanya da daddare batare dataje wajen Ni’iman ba abinda yasa take fushi kenan, ko abinci bata nema ba tunda tashigo garin nan cus bamata da apatite na ci haka tai bacci da yunwa.
Around 5 ta farka sabida aiki wayanta tadauka ta danna abinda tafara gani is text message from Ni’ima dasauri tawani zabura ta tashi ta zauna bacci nafita daga idanunta tabude message din da sauri.
“Inada magana dake Hawwa, let’s meet a Dims Eatery by 4:30 na yamma today” harwani ijiyan zuciya Hawwa ta sauke tamata reply okay good morning, saikuma ta kalli time da Ni’ima ta tura mata sakon around 2nadare, Ni’ima datasani lokacin nan bacci take Allah sa she’s fine babu wani abu dake damunta, kokuma is Ni’ima sick? Shine take boyemata cus bataso ta damu? Or is she pregnant? Dan cute murmushi Hawwa tayi kadan tace “ai kinsha miya da yawa is good kiyi ciki ama su Yaseer kanni” ta ijiye wayan dan damuwanta yaragu sosai tafito taje tai wanka tai brush da alwala tadawo daki simple riga tasa tai salla tana kan dadduma har 7 sannan ta tashi tafara shiryawa.
Riga da wando tasaka, navy blue wando ne palazo da riganta shima navy blue but mai designs na flowers daya saukanmata har cinya ta makala botura rigan yamata kyau cus ita tadinga da kanta zaka dauka wasu expensive kaya ne nan ko yadi ne tasayo a wajen yan material a kasuwa tadinka abinta, sky blue veil tadauka tai rolling tai pinning tasa links na hannun rigan masu shegen kyau tashafa lip gloss lips nata na shinning sosai, hada yan abubuwan datake bukata tayi a jakanta tadauka tasa cover shoe mai dan tsini kadan mai shegen kyau na zara, tasaka agogo tafesa turare tai wani kalan calm kyau kaman ka sace tana sassanyan feminine scent, tafito ta kulle kofa tana kamshi tayi waje, Baba baya waje maybe yana masallaci har yanzu, motanta tawuce tai warming ta chanza ruwa ta maida bonnet din tarufe sannan tashiga mota tabar anguwan saida tasha mai agidan mai sannan tawuce office by 8 tana ciki.
Rannan sunsha aiki kan wasu victims da akai kidnapping sai around 4:20 sannan ta iya fitowa, salla tayi a mosque nasu da gudu gudu tawuce mota ta shiga taja tabar premises nasu tanama Ni’ima text tace “yanzu aka banni nafito I’m driving already you will see me nan da 20min” ijiye wayan tayi tana kallon hanya tana murmushi yau zasu shirya da Best, dadan holdup a hanya saida ta bata 30min around 5:00 takai resturant din tai parking, babban restaurant ne hadadde, Ni’ima na zaune asaman terrace dan wajen tabiya kudi tamusu booking, shiru tayi bata ko motsi kallon Hawwa takeyi dataga tana sauri sauri tafito daga mota sannan ta rufe kofan, kallonta Ni’ima take batako kyaftawa yau for the first time tana ganin some things da bata taba luradasu da ba, Hawwa nada kyau sosai tafita kyau sosai, bazama ka kwatanta ba, yanda take saurin nan her boobs are shaking haka jikinta ma, babu wani abu da Hawwa bata fita dashi ba, ga diri danma bata taba saka kayan da ake gane shape nata, Hawwa akwai boobs manya masu kyau a tsaye ga shape, itako nata sun soma kwantawa kai sunma kwanta yara biyu to sun sha yanbiyu wasa ne ba dole Baban Yaseer yace yanasonta ba, gata doguwa and naturally dogayen mata nada farin jini da grabbing attention da maza ko ita tana tareda Hawwa ansha complementing tsayin Hawwa maza na admiring hakan, gata da gashi ga dadin murya na fitina ga iya turenci ga iya magana ga natsuwa ga wayau with lot of maturity, bazaka taba kama Hawwa na murmushi anyhow ba ako’ina dan tafi Hawwa fara’a sosai, gata da ilimi, ga Allah yamata gata she’s so bright and she’s a lucky mutum, imagine she’s no body but Allah supported her tasa kanta a makaranta da kudin dinki, tana fara aikin police akai promoting nata sabida sunga how intelligent and smart she’s ba dole Baban Yaseer yasota ba, Hawwa tahadu in every aspect wlh boko da islamiyya ga wayau ga hankali ga jarumta ga hazaka, ga addini yawan salla da azumi kai ga komima, idan Hawwa tasami miji kowaye yanzu saita kamashi with her charming and seductive nature, kai ko ayawan addu’a da salla sai Hawwa ta kwacemata Baban Yaseer, banda haka Hawwa zatai everything possible not to live marriage idan tai aure dan tadade bataiba, how can she allow Baban Yaseer ya aureta? Bayan tasan Hawwa tafita komi cus tafi kowa sannin qualities na Hawwa, Hawwa is desperate for a Man idan tai grabbing Baban Yaseer ai tata takade, kwace mata miji zatayi ya manta dasu, gatada karfin sha’awa Aliyu yasami haka ai shikenan kuma takade tana cikin tunane tunanen nan taji ringing a wayanta firgigit ta farga daga tunanin ganin Hawwa ke kiranta yasa ta katse wayan tamata text kizo terrace ina sama.
Tana zaune awajen Hawwa ta shigo bayan an bude mata kofan shigowa terrace din hada ido tayi da Ni’ima data kafeta da idanu tana zaune kan kujera tana sanye da black abaya saitaga Ni’iman ma dukta rame tai wani iri kaman mara lafiya, dawani sauri tai wajen jakanta ta ijiye kan table da wayanta kai tsaye tai hugging Ni’ima tace “Besttttt” ijiyan zuciya Hawwa ta sauke kusan 2min amman Ni’ima batasa hannunta tai hugging nata back ba, sakinta ahankali Hawwa tayi takalli fuskanta tace “are you sick? Face naki gabaki daya ya chanza, what is wrong with you?” Dan gajeren murmushi Ni’ima tamata ta nuna mata kujera tace “sit please” dan jimmm Hawwa tayi tana kallonta kafin tawuce tazauna kan kujeran, Ni’ima tadan kalleta dan hakanan bamatason tana kallon Hawwan yanzu cus is making her feel insecure and so little tace “mezakici order?” Girgiza mata kai Hawwa tayi tace “kin manta yau Monday ina azumi” gyadamata kai Ni’ima tayi batace komiba tana kallon gefe, wani iri Hawwa taji tanaji ganin yanda Ni’ima is acting wired ko kallonta ma batason yi kaman ta tsaneta, no let them iron koma menene she hates fight, ahankali tace “Ni’ima wat is wrong? Dan Allah kifadamin? Why don’t you want to look at me? Fushi kike dani”? Dago kanta Ni’ima tayi takalli Hawwa adake tace “Hauwa’u!” Faduwa gaban Hawwa yayi dan yau ne rana na farko da Ni’ima zata kira sunanta haka amman tadaure tace “na’am Best” murmushi Ni’ima tayi wanda is so obvious you can see how hurt she’s, da kyar take murmushin ma tana kallon Hawwa ido cikin ido tace “Baban Yaseer na sonki Hawwa!” Dooom!!! Haka Hawwa taji gabanta yabuga, still cikin karfin hali Ni’ima tace “nasan bai sanar dake ba saisa ni nake sanar dake, inaso na tayashi tambayanki hand naki in marriage” tai dan shiru takara murmushin da da kyar take murmusashi tace “zaki aure Baban Yaseer Hawwa!?”.
EPISODE
Mikewa da bala’in sauri Hawwa tayi tana kallon Ni’ima cus yanzu take understanding the whole reason na shareta da Ni’ima tayi tama kasa magana sai kallon Ni’ima take dake kallonta itama idanunta sun kada sunyi ja tace “kibani amsa I want to know zaki aure Baban Yaseer ohh zaki aure Aliyu ko bazaki taba aure ba”? Kai tsaye Hawwa adan zafafe tace “da yanzu this instant Allah zai karbi duka ran mazan duniyan nan yarage Baban Yaseer tal kuma kwal aduniya bazan taba auren sa ba saidai nakoma ga Allah haka!” Tafadi da zafi sabida tambayan ya bata mata rai barinma data gane it has something to do with fushin da Ni’ima keyi, with so much sincerity tace “bantabama Baban Yaseer kallon abinda zan aura ba saidai kallon Babban Yaya agareni, mijin kawata kuma” sosai Ni’ima ke kallonta batako kyafta idanu, Hawwa tace “I will never, ever, marry mijinki koda ranki ko ba ranki cus I consider it cin amanan kawance! Ni’ima kada ki karamin irin maganan nan, bazan taba auren mijinki ba” dan tuntsurewa da dariya Ni’ima tayi kaman mahaukaciya mai ciwo tana kallon Hawwa saikuma tai shiru cikin wani kalan siga da ita kanta Hawwa bata gane ba Ni’ima tace “nima bazan taba so naraba mijina dake ba Hawwa!” Takalli Hawwa sosai tace “namiki tambayan nan ne kawai sabida na sauke hakkin ki da hakkin Aliyu” tasauke ijiyan zuciya kafin ahankali tamike tsaye itama tana kallon Hawwa kaman yanda Hawwa ke tsaye tana kallonta tace “I have few things to say to you Hawwa” ta sauke ijiyan zuciya tace “Hawwa mun taso tare, no one knows me better than you do, I am always honest with my feelings kinsani” tai dan shiru sannan tace “Hawwa ke babban kawata ce, haka mijina ma mijina ne! Mijina daban yake akan kowa da komi! Thinking of sharing him with you ma is shattering me, Hawwa bazan iya baki aron Aliyu kona kwana daya ba ballema na ana maganan rayuwa har mutuwa that’s aure, I can’t ke I don’t even wanna picture you as matar Aliyu, matar mijina!” tasakeyin shiru sannan tasauke kanta kasa kafin chan tadago takalli Hawwa dake kallonta looking confuse and scared and everything ma, Ni’ima tace “ni da ke ba yara bane, we are not more teenagers, I don’t wanna end up fighting you over man, ni da ke munsan wats good for us, inhar Baban Yaseer yayi developing feelings for you relationship dina dake have to come to an end!” Dasauri Hawwa ta kalleta kirjinta na girgiza lips nata narawa magana ma baya fitowa sabida yanda maganganun Ni’ima ke dakan kunnenta abazata, gyadamata kai Ni’ima tayi tace “Hawwa stay away from me kifita daga rayuwana dan Allah!” Bugawa kirjin Hawwa yafara kaman zai fashe, Ni’ima tace “baki bani Hawwa!” Sake bugawa zuciyan Hawwa tayi, Ni’ima tace “karki kara tako kafanki zuwa gidana!” Shaking at this point zuciyan Hawwa yafara, Ni’ima tace “kada ki kara zuwa nemana a asibiti!” Hawaye fara tsatsowa daga idanun Hawwa sukayi, Ni’ima tace “delete number mijina daga wayanki, koda wasa kada ki sake ki kira mijina for anything, delete my number also!” Ni’ima tace “don’t ever call me again or watsapp me ko message me, I’m blocking you anyway!” Tasauke ijiyan zuciya tace “amutunce nakeso muyi parting ways with dignity and honor like the matured girls we are saisa ma harna kiraki to tell you to your face” Ni’ima tai shiru tace “Allah baice dole sai anyi kawance har karshen duniya ba, haduwan school, ba dangin iya bare na kaka, kawancen mu muka daurama kanmu ba wani yadaura mana ba mumukaga zamu iya, yanzu kuma naga bazan iyaba is that simple Hawwa, dan haka stay away from me! It’s OVER!”
Yanda kalaman Ni’ima ke hitting kan Hawwa kaman ana daukan guduma ana bugamata aka, she’s feeling like she’s dreaming this is not real, ba Ni’ima ke mata all this maganganu ba, Ni’iman ta dake sonta, Ni’ima dake tayata kuka idan she’s sad, Ni’ima dake lallashinta, Ni’ima dake kula da ita, is this Ni’ima ko watace tasaka facemask takoma Ni’ima? Best dinta ke cewa su rabu?
Juyawa Ni’ima tayi tasa hannu tadauki jakanta tace “kinfi kowa sanin yanda nakeson Aliyu, mijina is a no no! Akan Aliyu zan iya jama kowa layi!” Tai shiru sannan tace “Hawwa najamiki layi kema yau get out of my life” daukan jakan tayi tajuyo takalli Hawwa da idanunta suka cika tap da hawaye da basu riga sun zuboba tasa tace “Ma’assalam Hauwa’u” tajuya tayi tafiya one two zata wuce tafita Hawwa tasha gabanta daidai hawayen na zubowa daga idanunta tasa hannu ta gogesu da sauri, asanyaye tace “Ni’ima!” Haderai Ni’ima tayi idanunta sunyi jajir hakanan kawai yau for the first time saitaji tafin hannun Hawwan ma taushin tsiya kaman na Baby so that means har taushin hannu Hawwa tafita, kishi ne ya turnuke Ni’ima sosai sai kawai take ganin so many many things da Hawwa kedashi that are better than hers, kabar da hannun Hawwa tayi daga jikinta da sauri dan har zafi taji kaman Hawwa tasamata garwashi ajiki Ni’ima tace “karki sake tabani” tabi ta gefenta ta wuce tsayuwa Hawwa tayi kaman gunki idanunta sun cika da hawaye bazata iya decribing yanda takeji ba yanzu, juyawa tayi da sauri gudu gudu tashiga sauka daga bene hawaye na fitowa daga idanunta tayi waje tana kallon Ni’ima dahar takai parking space dasauri tafito wajen bata damu da manya manyan motocin dake wajen ba dan manyan mutane na zuwa restaurant din sosai Ni’ima na kokarin ciro key a handbag dinta tabude mota Hawwa tazo wajen da gudu ta rungume Ni’ima tabaya tabude baki tana kokarin magana kawai emotions got her wlh tafashe da kuka! She can’t describe it but tanason Ni’ima so sosai! Bawai irin son da akema namiji ba dan some people think maza kawai akeso no, tanama Ni’ima wani so da kauna na jini dan Ni’ima ta taka rawan gani arayuwanta sosai.
Tama kasa magana sabida kuka she’s not even thinking of inda suke, ko mutane ko jam’an wajen, she’s strong, she’s hard, kowama yasani but akan Ni’ima she’s not, she even forgot wat strong is dataji Ni’ima nacewa zata rabu da ita, kusan 30seconds tayi abayanta tariketa tana kuka, yau kawai kaman Allah nabama Ni’ima revelation kan Hawwa dan kawai jitayi komi na jikin Hawwa taushi kaman ba jikin yar 30yrs ba kaman jikin new born baby haka taji fatanta, juyowa Ni’ima tayi a fusace ta hankadeta saida Hawwa tai flying ta bugu da wani mota dake wajen next to na Ni’ima, tai kara awahale ta kalli Ni’ima idanunta sunyi jajur tana kokarin tashi daga jikin motan dan kaman bayanta ya karye haka taji, Ni’ima tanunata da yatsa da zafi sosai kan tone nata tace “Hawwa ke na tsaneki yanzu don’t you get it? Narike inata holding nashi in banaso na gayamiki but kin nace, I hate you Hawwa! I hate you! Jikinki da hannunki feels like garwashin wuta ajikina, karki kara tabani” daidai lokacin taga key motanta ta ciro tajuya tabude motan zata shiga Hawwa ta tashi daga jikin motan da kyar bata damu da ciwon da jikinta keyi ba kawai saitai kneeling tareda rike rigan Ni’ima muryanta na rawa same thing da jikinta rawa suke sosai tana kuka wiwi tace “Ni’ima I don’t know ta yanda zanzo na fara rayuwana without you, ke kadai gareni, rayuwana yariga yasaba dake, ke kadai gareni, I have no one to talk to, I will never ever betray you Ni’ima, I’m not ready to let go of our friendship, Best remember our lives, we’ve come a long way don’t abandon me, dan Allah kiji tausayina Ni’ima don’t abandon me, you’re my special thing, Ni’ima kiyakuri kiyafemin, don’t abandon me, I’m your friend Ni’ima” juyowa Ni’ima tayi aharzuke tace “friendship din banza da wofi what is friendship? Uban friendship! Ke uwar friendship, durun uwan best friend, tare aka haifemu da bazan rabu dake ba? Ke ki kyaleni we are not related, dole ne? Better accept that weren’t not friends anymore, let it sink in your head move on, I’ve move on too” tashiga fizge riganta zata shiga mota Hawwa taki saki tana girgiza ma Ni’ima kai hawaye na fitowa daga idanunta sosai jikinta na rawa like a little gurl, tana kuka tace ““Ni’ima you are the only person I have, Sisters dina are not close to me duk na girmesu, ko sunaso suzo kusadani Umma bata barinsu, banda Mama, there’s no one arayuwana banda ke, you’re the reason I’m not lonely nor depressed, kika barni Ni’ima yazanyi? Who will look after me? Who will love me like you? Wazaimin fada idan naji ciwo? Wazai bani magani? Wazai kirani? Ni’ima I’m sorryyy” ahaukace Ni’ima tace “au bazaki sakeni ba Malama”? Gyadamata kai Hawwa tayi tama kasa magana sabida kuka, idanun Ni’ima sun rufe tasa kafanta tashiga tattake hannun Hawwa da takalminta Ganin taki saki yasa tasa wajen heels na takalmin ta take hannun Hawwa da karfi hakan yasa dasauri Hawwa ta saketa sabida zafin da hannunta yamata tana kuka ta shiga mota tai reverse tabar wajen Hawwa tabi motan da kallo zuciyanta nawani kalan tsinkewa tana yarfe hannunta dake jini.
FRIENDSHIP BREAKUP HURT
KISHI IS REAL! BAKOWA KEDA KARFIN CONTROL KISHI BA
ABINDA NI’IMA TAYI TA KYAUTA???
WAI IS IT THIS EASY AYI BREAKING UP???
SHIKENAN NO MORE HAWWA AND NI’IMA SABIDA NAMIJI??
KAI MAZA BAKUYIBA BABAN YASEER SINGLE HANDEDLY RUINED THIS BEAUTIFUL FRIENDSHIP
BUT BABAN YASEER KO NI’IMA KO HAWWA WAYE KEDA LAIFI???
EPISODE
Sosai take yarfe hannunta sabida yanda yake mata zafi jini na diddiga takasa motsi daga wajen tana kuka har saida security guard sukazo wajen daya rikeda bag nata da phone yace “Ma’am is everything okay your hand is bleeding we believe this is your own” yamika mata jakanta da wayanta, hannunta mai lafiya takai ta goge fuskanta tass but dudda haka idanunta sunyi jazur alamun kuka sannan takai hannun daman kasa tana kokarin mikewa dan bayanta ciwo yake mata da dabara ta iya mikewa tsaye but tsabagen yanda batada karfi kawai ta luuuuu tai baya runtse idanunta tayi gam kawai ta sadakar tafadi charab taji an tareta tafada kan hannun dataji daya a waist nata daya a shoulder ta, ga kamshi mai bala’in dadi dake ratsa hancinta, almost 10secs tayi batai motsi ba kuma ba’a saketa ba kafin gently tafara bude idanunta dahar yaji yaji suke mata sabida kuka ta sauke rinannun idanun nata acikin na Khaleel dake kallonta awkwardly gadan toothpick abakisa tana iya hango kirjinshi sabida yanda baisa boturan gaban shirt nashi ba as usual, wani irin zabura tayi tafita daga jikinshi cikeda tsana tajuya ta karbi wayan nata da bag daga hannun security zata wuce cikin yar iskan voice yace “so you’re into gurls? I see no wonder kike tsani maza” tsayawa tayi tana kallon gefenta zuciyanta namata radadi, Khaleel yazo gefenta yakai hannu yana zare toothpick daga bakinshi cikeda neman tsokana irin na yan iskan yara yakai hannunshi gaban fuskanta yana waving yace “I feel sad she shatter your heart” yamata wani dan iskan kallo yanadan murmushi, Hawwa kawai