Showing 162001 words to 165000 words out of 184554 words

Chapter 55 - Gargadan So Book 2 Complete Hausa Novel

M SHAKUR   

31 Jan 2025

1901

na takurawa yaran wasu nasama yaran unguwa ido saida Allah yasa y’ata taki auriwa nazo na gyara kuskurena, Point din is ai nima ba mutumin arziki bane, banda aiki sai zama kofar gida na sama yaran mutane idanu ina Kai karansu wajen iyayensu ni maisa wasu yaran basu zageni ba? Iyayyenka ko bokayene babu wanda ya isa ya zagan maka su, Zainabu Hawwa ta kama yaron mutane taita bugu iyye? Lahaula fi sha’atillah! Hasbunallahu wa ni’imal Wakeel! Zainabu takama yaron mutane tanata bugu tana sharara masa mari? Zan iya rantsuwa iyayensa basu taba marinsa ba wai kinga yanda mahaifin Ibrahima ke sonshi kuwa? Ina ganin ko ihu baitamaba yaron nan ba balle har akaiga mari amman Hawwa taita zubamasa mari takama yaro tana bugu tana jibgansa? Zainabu idan na cemiki ban tsani Hawwa ba nai karya nayi karya!” Ammi ta runtse idanu ahankali, yace “Wlh wlh da Aminu zai auro yarinyar dake hali sak irin wanda Hawwa na tayi wlh sainasa ya rabu da yarinyar nan, ba matan aure bace amman yau Hawwa! Hawwa na fa danake gani tafi duka yarana hankali take abubuwan nan sabida taga yaron sangartacce kaman baida wayau dukya haukace a sonta shine take haka kome?” Baba ya tambayi Ammi ranshi abace yace “uban me zaimasa ta tsaya tama kula Baban Yaseer Aliyu da aurenta? Ai bayan gaisuwa bai kamata tama tsaya sauraransa ba kwata kwata kamata yayi ta tada mota tabar wajen” Baba ya girgiza kai yace “Zainabu na rantse miki banjin inada karfin dazan iya kallon idanun Ibrahima ba ko kadan diyata tariga ta tozarta ni nan nan kafin ta yardan masa su hada shimfida saida mukasa baki eh wani kalan zuciya ke ga Hawwa”? Baba yace “kinga kucemata tafito tabarmin gida billahilazi ko ruwan gidana aka bata tasha sai nahau sama na fado kasa da mutum tazo tabar gidana idan zaki tafi da ita zaria ne chan muku amman nidai Hawwa bazata zauna gidana ba!” Dasauri Ammi tace “Malam nasan ranka yabaci amman dan Allah ka fahimceni, na farko dai bazan taba daukan Hawwa na tafi da ita zaria ba yoo ai nama daure mata gindi kenan! Kawai so nake ka kira Khaleel yanzu yasa abarmu mu shigo idan mun kaita abada hakuri asa tabashi hakuri tunda bai riga yasaketa ba” Baba yace “naje nabada hakuri gobe tasake marinsa? Gobe tasake bugunsa? Koko gobe tama harbesa gabaki daya”?.

WLH DUK WACCE KO WANDA YAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DAYA KO TA BIYABA BA BAN YAFEMATA BA HAR ABADA HAR ANADA!!!

07012181461 chat me up and pay is 3k Document

Telegram group inda zaki karanta complete is 1k

EPISODE

Dasauri Ammi trying to calm Baba that is extremely angry down tace “wlh bazata karaba, Malam Hawwa bata da hankali karmu mubiye mata, za’a mana dariya muka bari aurenta yamutu ko tadawo gida yan anguwa aka gane yaji tayi dariya za’a mana sosai” ahankali Ammi tace “koni inaso Ibrahim ya hukuntata amman dan Allah adakinta kaji Malam, dan Allah, yarinyar nan na son mijinta hauka ne ke damunta da sokonci but she will learn her lesson, kaima nasan bakaso aurenta ya mutu, kar zuciya yasa muyi dana sani, kafin ya aiko mata da takardan muje mu tare komi, da zafi zafi ake dukan bakin gatari mu ciccimata mutunci agabansa, kaji Malam” shiru Baba yayi yana kallon Ammi yabuga tagumi, Ammi tace “trust me bazata kara dukansa ba wlh namaka alkawarin nan tashiga taitayinta, Malam ko basu shiryaba yau yacimata mutunci adakinta, yamata kome zai mata, kawai dai karmubar Hawwa anan wannan shine halin iyaye na kwarai kaji dan Allah Malam nasan kana fushi” ijiyan zuciya Malam yasauke yace “toh!” Ahankali tace “kirasa saika samo mana wani cikin samarin anguwa dazai iya tuka motan Hawwa banjin zata iya tuki ba bari naje ciki” Ammi tawuce tashiga ciki, Malam yadade zaune sannan yaciro wayansa bala’in kunyan kiran Khaleel yake amman yadaure yayi dialing number harya katse ba’a daga ba, na biyuma haka ana uku wayan na gab da katsewa aka dauka Baba yaji muryan Khaleel chan ciki ciki yace “Baabaa!” Saikuma yaji muryan kaman mahaifiyar Khaleel tana mesa kake bashi wayan Salman? Kashemin d’a za’ayi, wani iri zuciyan Baba yayi, anatse Baba yace “Khaleel idan harna isa dakai kasa abarmu mu shigo gidanku gamunan zuwa da ni da Ammi da Hawwa kaji d’ana” shiruuu Khaleel yayi baiyi magana ba Baba yace “Ibrahima naaa” ahankali Khaleel yace “ohh kay” ya katse wayan tashi Baba yayi da kyar yana kakkabe jikinsa.

Tana shiga gidan Ammi taga Hawwa dake kuka sosai idanunta sun kumbura suntum tana mata fada wajenta tayi kawai Ammi ta dagata tace “tashi dan ubanki muje, Umma kema sako hijabi” Umam tace “waza’a barma gidan Zainabu? Kuje zan zauna” ahankali Ammi tace “okay” tadauki key motan Hawwa taja Hawwa dake binta luuuu babu karfi ajikinta, suna fita sukaga Baba dawani matashi tsaye kallo daya yama Hawwa ya dauke kai Ammi tabama yaron key tace “an gode” tabude baya tasa Hawwa ciki da kyar itama ta shiga Baba yashiga gaba yaron yashiga aka jasu har gidansu Hawwa suna zuwa ko bincika motansu ba’ayiba aka barsu suka shiga cikin gidan har wajen parking ga PA na Mom tsaye sanye da suit da Musbahu yana sanye da manyan kaya bude mota yayi Baba yasauko suka shiga gaisawa da Musbahu Ammi ta sauko tajuyo takalli Hawwa tace “sauko” ahankali Hawwa ta sauko kanta akasa, Musbahu yace “this way please” akai flat na Mom dasu Mom suka gani cikin shiga na alfarma a tsaye tasanya wani Bubu lace, ga Excellency shima a zaune amman wlh kana ganin fuskanshi kasan babu farin ciki cikinsa babu Khaleel awajen kafin su zauna ma Mom tace “me kuka kawota? Me kuka dawo da ita? So kuke takarasa kashemini d’a tukunna?” Excellency dudda ranshi abace amman yace “Madam atleast ki barsu su zauna tukunna common” yakalli Baba da Ammi dake tsaye Hawwa abayansu a tsaye kanta akasa yace “Bismillan ku”

Zama Baba yayi bayan yabama Excellency hannu sun gaisa Ammi ma tazauna Hawwa ta zauna akasa takifa kanta akan kafafu Mom tace “yarona zaki sama bindiga akai sabida saurayinki? Waye ke Hawwa? Me kike takama dashi? Dukanki guda nawa kike? Me akayi aka yiki? I can make one call yanzu agabanki ayi dismissing naki as a police saidai kiga wasu na aikin not you, an kawoki gidan nan bamu taba cutar dake ba, ko kuntata miki, amman kina kokarin daukan rayuwan danmu, me kukazo yi? D’ana yace baya auren? Zai aiko mata da saki dazaran ya sami kanshi, akan wani dalili zata kara shigo mana gıda, mesa ma Khaleel zaice abarku ku shigo”? Daidai lokacin aka bude kofan falon Khaleel yashigo da kyar Salman na rikeshi ga hannunshi da kanula muryanshi babu karfi yace “don’t be rude to my parents please Mom” dago kanta ahankali Hawwa tayi tana kuka takalli Khaleel Allahu Akbar! Dasauri Baba yadago kanshi ganin Khaleel sai kawai yatashi da sauri yayi wajen yana kama Khaleel cikeda usulin so yace “Ibrahima meya sameka?” Kafin yayi magana Mom tace “yarka taso kaishi lahira” kallon Momy Khaleel yayi hakan yasa tai shiru, idanun Baba suka shiga kukkullewa kuka na neman kufcemai

Khaleel yabashi tausayi hawayen zasu fito dasauri Khaleel yace “noo Baba nooo, I had headache aka samin drip” Mommy tace “bakin cikin yarku yasa ya sume Salman yakawoshi gida unconscious likitoci biyu sukai reviving nashi, menene abin so a wajen yar sandan nan? Yarinya na son halakaka wannan wani irin GARGADAN SO ne?” Cikin murya mai rauni Baba yace “Ibrahima banda bakin baka hakuri dakai da iyayenka, ka yakuri Ibrahima ka gafarci Hawwa namaka alkawari zata chanza hali give her second chance” Mom tace “nifa dana yagama auren yarku kome zakuyi!” Zeenatu! Excellency yakirata azafafe hakan yasa tayi shiruuuu tace “hmmm” kowa ya kalli Excellency, mikewa yayi ransa abace yace “Hawwa” ba karamin bugawa gaban Hawwa yayi ba ta dago kanta idanunta sunyi jajur sun kumbura, babu wasa kan fuskan Excellency yace “come with me” yashiga tafiya ahankali Hawwa tafara kokarin tashi tsaye wlh takasa Khaleel takalla dayaki kallo inda take magana yake da Baba he looks very sick Ammi ta tayata tashi.

Mommy ta zuba mata harara tace “muguwa mara kirki, mai bakin hali” sauke kanta Hawwa tayi kasa fresh hawaye na zubomata Excellency yace “come with me” ahankali Hawwa tafara tafiya da kyar Baba dake magana da Khaleel but saida ya lura da yanda Khaleel yadan juya yabi Hawwa da kallo wlh saiyaji Khaleel yakara bashi tausayi, how can you love mata dake maka rashin mutunci haka? How? Kamashi yayi da kanshi yace “muje ka zauna”.

Har wajen study Excellency sukayi yabude kofan ya tsaya yana jiran Hawwa dake tafiya da kyar saida takaraso wajen ta tsaya strictly yace “shiga” wucewa tayi ta shige ciki Excellency ma yashigo tareda maida kofan yarufe yasaka key karma Mommy tazo takara bashi takaici, yawuce Hawwa yaje ya zauna kan chair dake officer din ga table agabansa, ahankali Hawwa ta shiga tsugunnawa gabanta fadi kawai yake Excellency yadan fuzar da iska fuuuuu sannan yace “Mrs Hawwa from the first ever day dana ganki I liked you, I sees you as a responsible girl mai hankali natsuwa and hikima, there’s nothing da Madam batace akanki game da auren nan ba naki sauraronta, yar sanda is stubborn, Khaleely can’t manage you, zakifi karfinsa menene menene duk naki yarda da ita but why did you prove her right? Why did you disappoint me Hawwa? Eh!” Excellency yadakama Hawwa tsawa dan ranshi abala’in bace yake his very angry da Hawwa, the only dayasa he’s even doing something sabida yaga how deep Khaleely ke son Hawwa, despite everything ya kasa sakinta, bazai iya bari aurensu yamutu ba something might happen to yaronshi, yanda Hawwa ke kuka Excellency ya kalla yace “I just have couple of questions for you karki kuskura kimin karya, when did you started seeing your ex? Har yanzu kina sonshi ne?” Girgizama Excellebcy kai Hawwa tayi da sauri tana shesheka tace “Abba wlh he was never my ex, mijin kawata ne bantaba sonshi ba bamu taba soyayya ba, ina cikin mota naji anyi knocking kawai na ganshi, same thing this morning naje KFC nafito zan shiga mota na ganshi, Abba I find out he has been stalking me tunda nayi aure wai yana street din nan yana wuni that’s how he even find out rannan nafita haryabini court, Abba wlh he is not my ex na rantse” Har kasan ranshi Excellency yaji ya yarda da abinda Hawwa tace, anatse yace “rannan da kikaje kika dauko Khaleel daga wajen party nan drunk I was inside this office ina kallonku Hawwa I felt proud of you then, nobody has ever done that for d’ana saike I was happy finally someone na Khaleely’s life dazata chanza shi” Excellency ya fuzar da iska sosai yana runtse idanu cus this part pains him the most yace “why would you maaka d’ana a kotu Hawwa? Meyayi zafi dazaki bar gıda kije kotu? D’ana yataba abusing naki ne? Is Khaleel hitting you? Molesting you? Raping you? Starving you? Wani babban abu Khaleely yamiki dazaki dauki d’ana ki maka a kotu eh?” Excellency yadaga murya dayasa jikin Hawwa har kyarma yake bata tabajin ta tsani kanta irin yauba, Khaleel baitaba raping nata ba, baitaba dukanta ba, baitaba molesting ko abusing koma verbal abusing nata ba, bata tabajin yunwa agidansa ba da gaske ne maganan da Abba yayi meyayi zafi dahar zata shigar da danshi court? Wlh saita kasa magana kawai ta daura hannayenta akan fuska tana ma Excellency kuka, Excellency muryanshi ba dadi yace “Hawwa you put a gun to my Son’s head kinsan shekara nawa muka nemi haihuwa bamu samu ba kafin nasami yaron nan dakike kokarin harbi?” Yayi shiru yace “I know Khaleel, wlh yarona is not a violence person, I know he loves you deep there’s no way zai ganki da wani da bazaiyi reacting ba, I know fear of karyayi kissan kai yasa kikai reacting just the way you did but Hawwa did you have any idea wat message you sent to your husband with that one single action naki?” Excellency yace “Kin gayama Khaleel nan gaba if something should happens that will warrant you to take his life you will not hesitate zaki dauka!” Hawwa ta shiga girgiza kai takasa magana, Excellency yace “koni bazan iya zama da matan da others comes first for her ba before ni mijinta, in that situation you should look at how hurt my son is not how hurt that other man is, believe me at that moment ciwon da Khaleely na yakeji a zuciyanshi yafi ciwon dayake jima shi dan bura’uba yaron that caused all this wahala ajiki” Kai! Maganganun Excellency wani kalan shiga Hawwa suke for the first time she’s seeing this from another perspective he’s saying nothing but the truth, Abba is right, Excellency yayi shiru yana kallon Hawwa da he’s very very angry with her but then tabashi tausayi dan adam ajizine, No body is above mistake shima dan nashi yayi kuskure, Ijiyan zuciya ya fuzar yace “I have last question for you as mahaifin Khaleel you need to tell me the truth trust me bazan taba yarda d’ana yayi keeping naki in this house against your will ba ko sonki zai kashesa, Hawwa bamu taba cutar da kowa ba wlh ask duka matayen nan, kowacce da iyayenta da yardanta zasuzo nan, suke turo hotunan su da kansu, babu wacce ta taba shigowa gidan nan forcefully, we don’t ruin life of the girls we make it better! Auren aure ne da suma sunyi for one or two selfish interest nasu, check all matayen da yataba aure they’re doing far better than before, wat i am saying is bamu wulakanta su sauran matan da ga kalan auransu ba bazamu taba wulakanta ki ba, idan bakison auren ko Khaleel zai mutu da sonki wlh saiya barki Hawwa ba’a dole arayuwan nan dan haka tell me this is between me and you KINASON D’ANA KO BAKISON KHALEELY NA?!”.

EPISODE

Kallon Excellency Hawwa tayi Excellency yace “idan bakison Khaeely I personally zan karba miki saki a hannun Khaleely yarabu dake for ever it’s your fundamental human right ki zauna in a marraige da kikeso not wanda bakiso, tell me DO YOU AT ALL LOVE MY SON HAWWA KOKUMA YOU HATE HIM?” Shiruuu Hawwa tayi rayuwanta da Khaleel from beginning of haduwansu kawowa yau na flashing right before her eyes, babu wanda yataba making nata special like Khaleel! Like he always makes everything about her! He loves her kaman itane alkibilan rayuwanshi, dazu dayace su rabu was the darkest moment of her life, she felt this fear of loosing him forever! She felt this urge na she can’t even go a day without Khaleel arayuwanta! Right now she’s feeling Khaleel in her heart, her tissues! Her organs and blood, she’s feeling Khaleel in her mind and soul ahankali tace “Abba inason mijina!” Tayi shiruuuu chan tace “I am afraid of loosing him!” Hawaye suka gangaro daga idanunta tace “Abba I love Ibrahim Khaleel with everything in me! Abba wlh ina bala’in son mijina kaman zan mutu!” Excellency yayi shiru yana kallonta, ahankali tace “I know I messed up! Nayi kuskure da dama, I disappointed you, Baba na, Mahaifiyata and mijina ma!” Muryanta yafara rawa tace “Abba just give me second chance I will make everything right! I will show Khaleel he was never wrong to love me! I will show him I am the only girl made for him!” Dan murmushi kadan Excellency yayi saikuma ya gyara fuskanshi yace “okay I will give you second chance! Khaleel is extremely angry with you! All explanations din nan dakikamin find a way make him listen to you sabida you guys have lot of misunderstanding na each other, don’t worry bazan taba bari ya rabu da ke ba aurenku mutu karaba but don’t ever make this kind of mistake kinji” gyadamai kai Hawwa tayi ahankali tana share hawaye,

Excellency yace “all of this dake faruwa are just OBSTACLES OF LOVE! find a way and overcome it! Everything is going to be okay alright”? Gyadamai kai Hawwa tayi sai kawai Excellency yataso yadauki tissue yazagayo da kanshi yasa hannu yadago Hawwa ta mike da kyar yakai tissue kan fuskanta yana sharemata hawaye yana kallon lips dinta da akwai jini yace “meya sami lips dinki?” Girgixamai kai tayi tace “bakomi” dasauri yace “did your parent hit you?” Sunnar da kanta kasa Hawwa tayi, cikeda masifa Excellency yace “Ha’a why will they hit you eh? An gayamusu ana dukan yarana you are just a child you made mistake okay shi Khaleely ai he’s not entirely innocent, shima he provoked you banson abu hakafa, No banson ana tabamin yarinyana fa” Wayyooo Allah kai! Maganan yataba Hawwa kawai saitaji she’s regretting cema Khaleel datayi iyayenshi basu bashi tarbiya ba iyayen Khaleel are very nice wlh! Abinda mahaifinshi yamata today ko mahaifinta bai mata shi ba, he gave her a listening ear, ya saurareta, corrected her and yagoge mata hawaye, kawai sai Hawwa ta zube tai kneeling agabanshi tafashe da kuka sosai tace “Abba dan Allah kayafe mini I was very wrong I’m sorry Abba I am so sorry Abba dan Allah” kallonta Abba yayi sai kawai yaduka yadagota wani kyakkyawan side hug yabama Hawwa yace “shuuu shiiiii shuuuuu! It’s okay, I forgive you no need to be this hard on yourself okay, ya isa kukan, you’re just a girl! Akwai wanda baya mistake ne, dena kuka don’t worry everyone will forgive you har Khaleel, ya isa hakanan okay” yakai tissue yana sharemata fuska Hawwa tai lamo a shoulder shi feeling that fatherly love daga wajenshi, Ahankali Excellency yace “it’s okay karki damu da duk wani abu da Madam zatace that one dama tacika masifa but she’s also a good person like me, and she’s not wicked trust me she will come around and she will love you also kinji, just work on giving me GrandBabies!” Dasauri Hawwa tasakeshi tajuya da fuska tana jawo gyalenta tana rufe fuskanta kunya kaman zata shige kasa Excellency ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login