Showing 30001 words to 33000 words out of 138998 words

Chapter 11 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

734

dai-dai lokacin da ya faka napep ɗinsa bakin ƙofar emergency,idonsa cike da ƙwalla ya ce

“Ta mutu ne?”

Sai ta ɗaga masa kai.

“Juya mu koma gida daman ta ce karna kawo ta asibiti”

“Da kin bari an dubata ko dogon suma ta yi”

“Jikina ya bani ƴata ta tafi har a bada, sai idan na iskota”

Shi ne ya matsa har aka fita da ita aka shiga da gawarta emergency, likitoci biyu suka dubata suka tabbatar mana da cewar ta mutu, sannan suka saka mana ita a motar ɗaukar gawa na asibiti saboda tausayin halin da suka ga muna ciki, mai Napep ɗin kuma ya ƙi karɓar kuɗinsa sai kuka yake kamar ƴar'uwarshi ce ta mutu. Ni dai bana iya aikin komai sai na kuka har muka iso gida. Jiniyar motar asibitin ce ta ɗago hankali kowa izuwa gidanmu, kan kace kwabo maza da yawa sun taru ƙofar gidanmu cikin har family Babanmu na babban gida, sai kuma family Inna maza da mata wanɗanda suke unguwar da kuma waɗanda bama da wata tazara mai nisa tsakanin unguwarmu da ta su.

“Miyasa ta? Tun yaushe ne bata da lafiya?”

Shine abunda kowa yake ta tambaya, masu kuka na yi, ciki har da kawayenta na makarantar islamiya da boko, tsakanin Sakina da Jamila bana iya banbance waye ya fi kuka a tsakaninsu, babu abunda ya fi bani tsoro kamar Noor da ya koma gefe ɗaya ya zauna ya natsu sosai ya kasa ko da guntun hawaye. Jidda ce ta shigo gidan da gudu tana ihu kamar zata tashi gidan, kuka take sosai tana kiran sunan Habiba kamar zata dawo da ita. Inna kan hawaye kawai take iya yi kamar yadda nima nake. Can kuma sai muka ji muryar Noor ya saka kuka ya yi waje da gudu yana kiran sunanta.

“Wayyo Mama Habiba-”

Ɗana ƙarami ne amman yasan mutuwa, yasan duk wanda ya tafi baya taɓa dawowa yasan ya yi rashin uwa har abada...!
Ƙanwar Bilal ta biyu ce Zulaihatu ta shigo tana kuka sai ta kama hannuna.

“Taso muje gida Bilal ya ce na zo da ke”

Bana iya uh bale uh uh tana jan hannuna na bita kamar babba da yaro ina ƙwalla ita kuma tana kuka, har muka isa gidansu. Gidansu Bilal irin babban gidan nan ne mai yalwa amman ba sosai ba, ba kuma irin na masu kuɗi ba na masu rufi asiri dai-dai gwagwado, gidane da ke cike da ƴan mata daga ƙanensa da kuma cousins ɗinsa da ake riƙo gida wasu saboda suna makaranta a sokoto wasu kuma zaman ne kawai, sai kuma Mahaifiyarsa da kishiyar mahaifiyarsa, da ƙanwar babansu wato Gwaggo Rabi.

Sun tausaya min sosai sun nuna kulawarsu a kaina, daga iyayen har ƴan matan da suke gida, a falon kishiyar mamansu aka fara shiga da ni na zauna sai kuma wata cousin ɗinsa ta shigo ta fita da ni zuwa ɗakin Bilal dake can gefen ɗakunan mazan gidan kuma a farkon shigowa gidan.
Kamshin turarene ya fara yi mana murhbun sai kuma lallausan carpet, ya gyara ɗakin kamar na mata komai akan tsari kamar na wani babban mai kuɗi. Wutar daƙin da kunna duk da kasancewar ɗaya da rabi na rana ya yi.
A saman gadonsa ta zaunar da ni har ta juya sai kuma ta juyo ta dawo ta kwantar da ni saman gadon kaina akan matashin kai, sannan ta ce

“Ya Bilal ya ce a kawo ki nan saboda gudun hayaniya”

Ta juya ta fice. Ƙaton hoton Bilal da ya yi da Noor nake kallo, a zahiri hoton na ke kallo amman hankalina yana can gurin Habiba da Inna. Zuwa can na lumshe ido bachin wahala ya yi gaba da ni.

Ko da na farka dishi-dishi na fara gani kamin na ga dai-dai, Bilal ne zaune gurin kaina idonsa na kaina Noor kuma na bayana yana bachi sai faman sauke ajiyar zuciya yake yana wani ɗaukar numfashi, da alama ya yi kukan ne har ya gaji.

Kallo kallo muka riƙa yi ni da Bilal ni na kasa tashi daga kwance da nake, shi kuma ya gagara motsawa har sai da yaga idona ya fara zubar da ƙwalla.
Sai ya yi saurin kai hannunsa for the first time ya riƙa ya tayar da ni zaune, babu wani kuzari a jikina ko ƙire ji na ke kamar ba ni ce ba, fashewa na yi da kuka sai ya yi min masauki a ƙirjinsa ya rungume tsantsan.

“Shiiiiiiiii”

Rarrashina ya ke amman ji nake kamar yana ƙara min ƙarfin kuka, ban lura da shafa baya da yake alamar rarrashi ba sai da kukan ya tsagaita min, sai na yi saurin barin jikinsa na miƙe tsaye, shi ma ya miƙe tsaye yana kallona.

“Ina zaki je?”

Ban iya amsa masa ba na juya ina kuka, sai ya y hanzarin kai hannu ya juyo da ni ya rumgume a karo na biyu, a nan na rushe da kuka muka durƙushe da a ƙasa tare ni ina kuka shi kuma yana hawaye suna sauka saman kaina.
Wata irin natsuwa da kwanciyar hankaline suka ziyarce ni, na ji daɗin rumgumar da ya yi daman i need some shoulder to cry, har ga Allah na san ba dan wani abun Bilal ya rungume ni ba sai dan rarrashi da kuma tausayi, hakan yasa na sake jiki na yi kuka iya yadda zan iya sannan yasa handkerchief ɗinsa ya goge min fuska yana shafa saman kaina kamar wata yarinya.

“Shiiiiiii karki tashi Noor, daker na samu ya yi bachi”

Gunɗe bakina na yi na lumshe ido ina sauraren bugun zuciyata, yanayin Bilal yana min kamar na tsohon mijina wato Margayi Faruk, yau a bayar tafiyarsa wani namiji mai natsuwa da kamala ya rumgume da har na samu natsuwar da na kasa samu a farkon aurena, sai dai wannan ba da ijiya uku ya rumgume ni ba. Tuna wannan yasa na yi hanzarin barin jikinsa, duk yadda ya so ya tsayar da ni sai na ƙi a dole ya biyo bayana yana min magana amman ban kula shi ba har na bar gidan.


JUMMA'AT MUBARAK...😘
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


2⃣0⃣

I dedicated this chapter to each and every RAI BIYU fan's, especially RAI BIYU CONVERSATION and RAI BIYU FAN'S GROUP together with KHADEEJA CANDY NOVELS. Thank you so much for your lovely and meaningful Comments. Son So Fisabilillah 😘


•••~•••

Ko da na isa gida na tarar ƴan'uwa da masu karɓar gaisuwa suna Sallah la'asar, ashe huɗu ta yi ni ban ma sani ba kasancewar na kwanta ne a lokacin da ba a fara zuwa masallaci ba. Ba zan iya kwatantan yawan mutane da na tarar a gidanmu ba, daga ɗakinmu har ɗakin Inna da tsakar gida cike ya ke da ɗan adam, hakan ya tabbatar min da an kaita gidanta na gaskiya kenan. Duk yadda na so na danne kukana sai na kasa saboda raunin zuciyata, kuka na ke haƙuri ake ba ni amman kamar wuta da fetur na zama, haƙuri na ƙara min kuka, daker mutaneɓ suka rarrasheni har wasu suka samu damar yi min gaisuwa, da yawa na ji suna faɗar dole zan yi kuka saboda shaƙuwar da ke tsakaninmu da Habiba.

Bana iya kwatanta yawan mutane da ke ta zuwa gaisuwa ba, tsakanin ita da Baba bana iya banbance waya fi yawan jama'a, tun daga maza har mata, ta samu addu'ah da yabo sosai, kowa ya ji mutuwar Habiba har ma da waɗanda basu danta ba gani ko kuna jin ta rasu haka kawai babu wani ciwo. Ban tabbatar da na yi rashin ƴar'uwa ba sai da dare ya yi naga inda take kwantawa babu kowa sai matashin kanta, da kuma komatsan kayanta a gefe, ban san lokacin da na fashe da kuka ba sai kuma dariya ta biyo baya, wata ƙanwar Inna ce ta shigo ɗakin ta fita da ni zuwa ɗakin Inna, amman har lokacin ban bar kuka da dariya ba, ni kaina zan iya cewa na kusa na haukace ne a wannan lokacin.
Addu'ah suka riƙa min suna tofa min har sai na dawo ina kukan kawai babu dariya, kuka ne ya saka Inna kuka, ni da ita aka rasa mai rarrashin wani. Ni da Inna ba mu runtsa ba sai dai ƙannenta ne suka samu suka yi bachi, ni kuma na tashi na raya dare ina tayi ma Habiba da Baba addu'ah da kuma Faruk, sai mutuwar ta dawo min ta yi min tsaye, duk mutanen da suka da muhimmanci a rayuwata ina ta rasa su.
Ka rasa mahaifina sai kuma na ƴar'uwata, na rasa RAI BIYU masu muhimmanci a rayuwata, kuma duk a cikin shekara ɗaya.


Har aka yi kwana ukun Habiba aka gama bana aikin komai sai kuka, bana iya cin komai sai ruwa, a wannan babin kan na yarda Inna ta fini tawwakkali domin da kanta tana kan zauna na bani haƙuri tana min maganganu masu tausasa zuciya, amman na kasa jurewa wannan ƙaddarar kan na saka ɗaukarta, a kowa ne dare gani nake kamar Habiba zata dawo, bana da mafarki sai nata, da naja numfashi na sauke addu'ah nake mata, ƙiriƙiri bachi ya gagareni duk dare bana iya bachi har garin Allah ya waye, wani lokacin Bilal ya kan shigo har cikin gidan saboda bana fita ya riƙa min nasiha yana jana da hira wai ko zan sake amman ina na kasa kai zuciya nesa, Jidda ma ta yi iya yinta har ta gaji ta sa min ido.

Haka na kwashe sati biyu babu wani canji tsakanin ni da Noor domin shi ma idan yana bachi kiran sunanta yake, idan zai ci abinci sai ya ambaci sunanta saboda mun saba cin abinci tare, da an taɓa shi ya buɗe baki yana kiran Mama Habiba. Ranar da ta cika kwana goma shabiyar a ƙabarinta ina zaune waje ina karatun ƙur'ane Noor ya kwanto jikina yana kuka.

“Momy miyasa idan aka mutu ba a dawowa?”

Kallonsa na yi, da farko rasa na yi mi zaɓ ce masa sai kuma na yi ƙarfin halin ba shi amsa.

“Haka Allah yaso, kuma duk wanda ya samu lahira baya ƙaunar dawowa duniyar nan, sai dai mu iskeshi”

“Momy nima ina son na mutu naje inda Mama Habiba, kullum ina mafarkinta bana jindaɗi idan bata nan”

Ya faɗa yana kuka, sai na rufe ƙur'ane na aje gefe na kwantar da kansa saman cinyata ina shafa kansa, shi kuka ni kuka.
Na yi kuka sosai har sai dai na jawa kaina ciwon kan da ban taɓa irinsa ba, domin har cikin ƙashin bayana yaƙe sauko min, a ranar bana iya ko da motsin kirki har sai da aka kira wani nurse ya duba ni ya bani magani. Wasa wasa ciwo ya fara min yawa yau ciwo gobe lafiya tun abun be kama Inna ba har ya soma bata tsoro, sau biyar ana min ƙarin ruwa amman kamar zubarwa ake, duk nabi na rame na lalace farar fatata ta soma ɗuhu, gashi bana iya cin komai.
Haka Inna zata saka ni a gaba tana kuka tana cewa ni ma rasa ni zata yi, damuwar da nake ganin tana ciki ne yasa na ragewa kaina tunani ta yadda zan samu na riƙa cin abinci ko da kaɗan ne, domin nurse ɗin ya faɗa min matuƙar ban daina tunani ba ba zan taɓa jin sauƙi ba, kuma ba zan taɓa iya cin komai ba, idan zan kwanta sai na shimfiɗa zanen da Habiba take shinfiɗawa na yi matashin kai da fillonta hakan yasa sai ma ji kamar tana kusa da ni.

Da addu'o'i da ƙarfin hali na fara samun sauƙi, cikin sati ɗaya na koma normal sai dai ban iya maida jikina ba, lafiyata ma bata dawo gaba ɗaya ba, amman Alhamdulillah na dawo cikin hayyacina ma miƙa lamarina ga Ubangijina, har na kan fita naje gidansu Jidda saboda rage kewa, Bilal kuma ya yi min sallama na fita mu gaisa na tattara komai na adana a zuciyata, na tabbatar da ace ana buɗe zuciya da tawa zuciyar idan aka buɗe ba za a tarar da komai ba sai damuwa, baƙincikin, tunani, da kuma hudu na rashin RAI BIYU da na yi.

Walwalar da nake tasa Noor ma ya sake har yana sawarsa da yara, sai dai duk da haka idana ka masa wani abu sai ya shigo yana kuka ko ya ce da Mama Habiba na nan da yanzu ta rama masa, Sakina ce ta ɗauke halin Habiba a gidanmu duk wani aiki da Habiba take Sakina ce take yinsa a yanzu, Noor ma idan aka masa wani abun itace kan gaba wajen magana, sosai take ɗauke min kewar Habiba daman suna kama sosai da Habiba ta fuska da kuma ta magana, inda suke da banbanci Habiba tana da tsawo ya yinda Sakina take gajeruwa sai dai ba can sosai ba.

A kwana a tashi hasarar mai rai! Wasa-wasa kwanaki suka soma ja, har Habiba ta haura wata ɗaya da rasuwa, a zuwa yanzu kan mun fara sabawa da rashinta, sai dai duk da hakan kewarta bata bari na bachi har sai na kwantar akan shinfiɗarta. Ranar da Inna ta fita wanka, wato ta gama taƙaba sai mutuwar Habiba da ta Baba ta dawo mana sabuwa. Mutane da dama kama daga ƴan'uwa, maƙota abokan arziki suyi ta shigowa suna mana barka da fita wanka da Inna ta yi lafiya. Sai dai babu Family Bilal ko ɗaya da ya zo mana barka da fita wanka, hakan be bani mamaki ba daman can na san ƴan gidansu ba son alaƙar dake tsakanin mu suke ba.
Bilal kan sai dare ya zo, ya kawo ma Inna atamfa vilisco ta dubu biyar da kuma wax ita ta dubu biyar da Hijab mai kyau yadi huɗu, sai turaruka da man shafawa da kuma kayan ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, abunda yan uwan Babanmu suka kasa yi, ko atamfar roba ka rasa wanda zai siyo ya kawo ma Inna da suna ta saka na fitar wanka saboda rashin haɗin kai da kuma halin ko'in kula nasu.

Duk yadda Inna ta so ta rage kaya sai Bilal yaƙi yarda wai idan har ta mayar masa hakan na nufin bata ɗauke shi ɗa ba. A bakin ƙofar gida muka tsaya muna fira da shi, a nan yake min zancen aikina wanda ni har na watsar da lamarin.

“Ya kamata ki koma kin ga idan kina fita zaki fi sakewa, kuma ita kanta Inna zata ji daɗi”

“Amman Bilal ni aikin ya fita daga raina ma”

“Aiko yanzu ne ya kamata aiki ya shiga kanki domin Sakina da Jamila da Noor suna da buƙatar taimakonki, ga kuma Inna”

Gaskiya ya faɗa tun da bamu da wasu ƴan'uwa masu son taimako dole ne mu tashi mu nemi namu, daman hausawa na cewa ‘indan ma ɗan'uwa nemi naka’

Ajiyar zuciya na sauke na kalleshi duk da kasancewar ba zan iya ganinsa ba saboda babu hasken farin wata, ita kan wutar nepa na manta rabon dana ganta a gidanmu domin an daɗe da yanketa, sai dai idan maƙota sun kunna wuta hasken gulob ɗinsu na haska gidanmu musamman masu gidan samman nan dake kusa da mu, sai dai yau basu kunna ba sakamakon babu wutar gaba ɗaya a unguwa.

“Amman basu kore ni ba? Na daɗe ban zo ba”

“Na basu rahoton cewar baki da lafiya, dan haka idan kin shirya zuwa kije kawai”

“I will try”

Na faɗa ina tsotsa lips ɗina. Bayan zancen aiki sai kuma muka ɗora da wani zancen na daban, ba laifi na saki jiki mun yi fira har da dariyata kamar ba ni ba, da wannan na yarda cewar zuciyata ta fara zaurancin son Bilal domin ina jin nishaɗi a duk lokacin da muke tare da juna, ko sunansa na tuna sai na samu kaina cikin hauƙi da murmushi.

Bayan kwana biyu da faruwar hakan na shawarci Inna akan maganar aikina, na yi zaton zata hanani ne ko tace wani abu sai naga ta nuna farinciki sosai har tana ce min wai na fara dawowa a mutun ɗinta, farincikin dana gani a tattare da ita ne ya ƙarfafa min guiwa na yi jimmar wanke uniform ɗina na zuwa aiki.

Washe gari na shirya tsaf na ɗauki Hijabina na saka, sai kuma na buɗe jakar da nake aje tarkace na na ɗauko ƙaramin hoton Habiba na saka a aljihu, hakan zai kwantar min da hankali kuma zai ƙarfafamin guiwa domin a duk lokacin da nake kusa da wani abu da ya danganceta ina jin kamar ƴar'uwata tana kusa da ni.

Sai da na yi ma Inna sallama sannan na fita bayan na yi addu'ar fita daga gida. Bana baƙinciki ba farinciki na isa gurin aikin, kamar yadda nake a baya, sai da na fara zuwa na rubuta sunana da lokaci na aje hijabina da wayata a inda aka tanada domin aje irin waɗandanan abubuwan sannan na domin sai sannan na nufi gurin aikina, ina cikin aiki na ji muryar wani namijin yana faɗin

“Khadija Musa Kafinta you're fired”

Da sauri na juyo na kalli mai maganar yana sanye da black suit hannunsa riƙe da file.

“Saboda me?”

Na tambaya cike da mamaki.

“Saboda rashin zuwa da kika yi, shugaba baya son haka, kuma ya ce be yarda da rahoton da aka bada cewar baki da lafiya ba”

A take raina ya ɓace sosai, taya zai ce be yarda ba shi beda uzurine hala! Sai da na fara aiki za a ce an koreni, ni ko ba zan yafe haƙƙina na kwana biyu da na yi ina aiki ba.

“Na ji an koreni amman a bani kuɗina na aikin da na yi na kwana biyu da rabi”

“Kwana biyu da rabi?”

Ya maimaita fuskarsa a haɗe.

“Ee ai na yi aiki sau biyu a wannan kamfanin kuma yanzu na yi rabin aikin, dan haka a biyani haƙƙina”

Ta yadda na yi masa maganar ya fahimci ina cikin zafin raine, domin a hasale nake ina katsa masa tsawa, yasan duk ya yi wasan sake ce min wani abu zan haukace masa ne.

“Kije hawa na biyar bi faɗawa mai kamfanin, ba ni zaki faɗawa ba”

Ya faɗa yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login