Showing 111001 words to 114000 words out of 138998 words

Chapter 38 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

754

fadawa Jibril cewar Siraj yana masa Zagon kasa ba, sai dai na kan yi kokarin nuna masa haka ta hanyar wasu abubuwan da Siraj yake yi, tare da Rabi muke komai ita take sanar da ni duk wani kudiri na Siraj ni kuma sai na yi kokarin Jibril aikatawa, Jibril bw taba yarda da ni sosai ba kamar lokacin da na daukeshi muka je bypass da kansa ya ga kamfanin da Siraj yake ginawa wanda be taba fada masa ba, hakan yasa shi ma na ya fara ja baya da shi har suka soma samun sabani saboda rashin fahimta da ta shiga tsakaninsu Jibril yana ganin be kamata ace Siraj ya boye masa abu mai muhimmanci kamar haka ba, shi kuma Siraj yana ganin Jibril ya dauki amana ya bani har ina shiga tsakaninsu.

Jibril ya sake shiga rayuwata a karo na biyu, na sake jiki da shi irin sakewar da ban taba tsammanin zan iya yinta ba, ya canjawa Noor da Jamila makaranta daga makarantar gwanati zuwa Imam international school, da school bus ake kawo su kuma a dauke su da safe, shakuwar data shiga tsakanin Noor da Jibril a yanzu har mamaki take bani lallai na yarda da aka ce yara sun fi sabawa da iyayensu maza. Sakina kuma ya maida Khalifa International School wace ke can kusa da Polytechnic bypass, dukan wani abu da za'a ci a gidan daga aljihun Jibril yake zuwa, idan na yi magana yace dansa yake yi ma, ni kuma na kan bashi damar hakan ne saboda nima na samu damar shiga cikin tasa rayuwar, ni ce na yi ruwa na yi tsaki a rayuwar mutumen da na fi tsana a duniya, bana da matsala a yanzu sai ta mutum biyu Bilal da kuma Siraj, na rasa yadda zan yi na fito kai tsaye na nunawa Jibril irin kudirin da Siraj yake da shi akansa, ina son nayi masa yadda zai fahimta ne kuma ya kamashi dumudumu amman na rasa yadda zan fahimtar da shi.

Sai Bilal da ya kasa fahimta ya kasai daina zargina duk kuwa da kasancesar an saka ranar aurenmu a yanzu, zuciyarsa ba raya masa kamar ina son Jibril ne, ga kuma ta bangaren Familynsa har yanzu mahaifiyarsa fushi take dashi ta kasa sakewa da ni saboda bata son auren, gashi tana ganin kamar saboda ni aka kore shi aiki daman mahaifinsa ne ya tsaya kai da fata akan maganar har aka saka ranar auren.
  Ko ranar da aka kawo tufafin sakawata sai sa yan'uwansa mata suka yi ta Maganganun kamar na habaici, ni dai ko kadan hakan be dame ni domin iya abunda na sani Bilal yana so na ni ma kuma ina son shi so kiyayyar yan'uwansa ba zata dame ni ba, domin ina jin a jikina zan iya canja musu rayuwa su soni ta hanyar kyautata musu da kuma yi musu biyayya.
  Ban tsammaci Bilal zai zuba min lefe kamar haka ba, domin kala talatin da biyu ya yi min kamar wata budurwa babu abunda be saka ba a cikin lefen, da na masa magana sai ya ce wai daman ya dade da siye ya aje ba a yanzu ya siya ba, baya aikin komai a yanzu sai tsaron wani shagon computers suna biyanshi kullum, amman ya yi applying a cbn da kuma aikin kaki har guda biyu, sai dai aikin naija sai a hankali za ka yi applying dauka sai na manta ma, baya son komawa kamfanin Jibril aiki kamar yadda nima bana so saboda kar Jibril ya dauka cewar Bilal da kamfaninsa kawai ya dogara. Ban taba sanin cewar Bilal yana da zafin kishi ba sai a yanzu, domin ko kallona ya yi sunan Jibril yake kira wai ai daman yasan ina son shi ni kuma wani lokacin har dariya yake bani domin idan ya bata rai abun baya masa kyau.

Yau ta kama Friday ina dawowa aiki na zauna na shiryawa Bilal Snack saboda yana ciki favorite dinsa musamman ma idan ni nasa yana ci sosai, sai da magariba na gama sai na yi wanka na shirya cikin wata jar kamfala, ta karbeni sosai saboda jan abu yana fitar da farin mutum, sai na bi jikina na fashe da turare sai na dauki blue mayafi na saka, na dauki wayata na kirashi bugu biyu ya daga.

“Hubby ina nemanka yanzu”

“Me za ki ban?”

“Sai zan baka wani abu kawai na ke da ikon ganinka?”

Na fada kamar zan fasa masa kuka.

“Gani nan zuwa”

Yana fada ya kashe wayar, haka yake mina yanzu zuwa fira ma sai yaga dama saboda kawai yana fushi da ni wai ala dole ni soyayya na ke da Jibril, ko kadan bana ganin laifinsa domin na san ko a littafi ba za a samu namijin da zai yarda ya kyale matar da zai aura tayi aiki karkashin wani ba a
Wai dan kawai da taimaki rayuwar danta.
Ta bangaren yan uwansa ma nasan ba a rasa masu masa magana domin abokansa da yake zuwa da su wani lokacin sukan zolayeni da Maganganun marar dadi ko kuma na bugun ciki domin kawai su ji abunda zan ce, amman ya toshe kunnuwansa domin kawai ya bani damar cin ma kudirina har shi yake kokarin kare ni wani lokacin.

Bayan kamar mintuna talatin sai gashi ya aiko min sako wai na fito yana kofar gida, ni kuma na yi murmushi na dauki snack din na kira Noor ya rika min lemun kwakwa hadin gida da na yi masa muka fito tare fito Noor na aje jug din yaje da gudu suka rumgume juna.

“Uncle Bilal i miss you”

“I miss you too Noor”

“Wannan Saturday data wuce ka ce zaka zo kaje da ni yawo kuma baka zo ba”

“Mantawa na yi but dis weekend zamu je”

“Gobe ko? Gobe weekend fa”

Bilal ya dafe kansa.

“Oh na manta tau gobe za muje”

“Thank you”

Ya fada har da tsalle, sai kuma ya tsaya yana kallon bakina da shi yadda muke gaisawa, ganin hakan yasa na umarce shi da ya wuce cikin gida.

“Ga snack din da na maka”

Sai ya kawarda kai baya ma son kallon snack din.

“Bana jin cin komai a yau”

Hakan yasa ni jin babu dadi amman sai na daure na dauki daya na mika masa a hannu.

“Dan Allah ka ci da kaina na hada maka”

“No na koshi yanzu na gama cin indomie”

“To ga lemun kwakwa nan da kaina shi ma na hada”

“Ai ko baki fahimtar hausa ne?”

“Na fahimta dan Allah Bilal ka daina fushi da ni, na san ka yi hakuri ni kaina ba dan raina yana so nake aikin nan ba, kuma na yanke shawarar aje aikin a wannan week”

Ya kalleni

“Saboda mai?”

“Saboda ya kamata na aje, na yi iya kokarin da zan yi na taimakon Jibril, sai dai na bishi da addu'a kawai, kuma kaga aurenmu sauran wata uku a wannan lokacin ne ya kamata na aje aikin ai”

Murmushi ya yi ya soma wasa da yatsun hannunsa.

“Har yanzu kina son Jibril ko Nawwara?”

Kallonshi na yi jin tambayar banbaragwai da kuma yanayin yadda ya kira sunana kai tsaye ba kamar yadda ya saba kira ba.

“Wannan kuma wace irin tambaya ce Bilal?”

“Tambaya ce dai kamar ko wace tambaya amsarki kawai na ke so”

“Idan har baka so ba aikin nan Bilal ba zan yi ba”

“Na isa na hanaki? Ban riga na aureki ba Nawwara balle na gindaya miki wasu sharadodi, so ban isa na hanani aiki tare da Jibril ba, idan ma na yi kokarin hanaki sai Inna da ke sun ga laifina”

“Babu wanda zai ga kaifinka saboda kana da cikakken iko a kaina, be kamata ka zargeni ba Bilal”

“Mi zan yi bayan zarginki Nawwara? Jibril first love dinki kuma karya kike yanzu ki ce min babu son shi a cikin zuciyarki, na san yana son ki sosai kuma zai yi komai dan ya ga ya same ki, ya fini kudi na sani kuma ya kyautata musu da abunda ni ba zan iya ba”

Idanuwa sun cika da kwalla kalamansa sun ratsa zuciyata cikin rashin jindadi na hadeye yawun da ke bakina na ce

“Jibril ya fika kudi amman be fika karbuwa a zuciyata ba, Jibril ya wukanta ne Bilal irin wulakancin da wani da namiji be taba ma mace ba, kuma a yanzu kake zargin zan iya aurensa? Bayan an saka mana rana da kai mika dauki iyayena ne zasu canja magana ta da kai saboda kawai Jibril ya fika kudi?”

“Idan har baki son shi dan me za ki taimaki rayuwarsa? Har ku kuma kuna zama kamar wasu masoya, dan Allah Nawwara baki ji kunyar kanki ba?”

“Da ka nuna min baka so tun farko da ban yi ba, dukan abunda na ke ma Jibril ko kuma na yi masa na yi ne saboda Noor idan ya gyaru Noor zai amfana idan kuma ya lalace Noor ne zai tagaiyara miyasa ka kasa fahimtata ne?”

“Saboda Noor ko? Komai ma ai saboda Noor ne Nawwara i understand”

Yana fadar hakan ya saka hannayensa aljihu ya wucewarsa ya barni nan tsaye ina faman hawaye.



JIBRIL POV.

Daker yake numfashi saboda nauyin da zuciyarsa ta yi masa, daman yanzu abun ya zame masa kamar jiki idan yau be yi ba gobe sai ya yi, sai dai duk wannan abun be taba yarda ya yi gaban Nawwara ba, idan har suna tare abun ya taso masa sai ya kulle office dinsa ko kuma ya bar kamfanin ya dawo gida.
  Daker ya unkura ya tashi ya nufi bathroom yana shiga sai aman jini yau kan be yi shi da yawa ba kamar yadda ya saba, sai da ya wanke bakinsa sannan ya bude cabinet ya dauko wasu kwayoyi ya hade tare da ruwa sai ya juyo ya fito daga bathroom ya zauna saman kujera ya lumshe ido yana sauke numfashi a hankali.

Nawwara ce kadai macen da yake gani idan ya rumtse idonsa, duk da a yanzu ya sadakar ba zata taba zama tashi ba, yana ji a jikinsa kamar ba zata sake rabarsa, but he's happy da ta yi aiki da shi ta maida da shi cikakken namiji, dukan wani canji daya samu a rayuwarsa yasan ta dalilin Nawwara ne, domin be yi zaton zai iya daina shan cocaine ba amman gashi yanzu komai ya zama tarihi, and now he can read Quran duj da be yi nisa sosai a ciki ba amman ya san bakin domin kullum Malaminsa yana zuwa yana koya masa har ma da wasu littafan na daban da kuma bayani akan sallah da wasu abubuwan na addini, shi kansa a yanzu yana jin dadin rayuwarsa Saboda yana jin ya kara kusanci da Ubangijinsa hakan yasa ba janye dokan hana saka hijabi a kamfaninsa domin a yanzu ya fahimce babu komai a cikin addininsa sai rahama da jinka ga gata da addinin musuluncin yake ma ko wane musulmi, bashi da wata matsala ta rayuwa a yanzu sai tunanin Nawwara da ya zame masa kamar abinci, idan suna office har baya son su rabu saboda kewarta da yake komai ya zo masa kamar a mafarki ace Nawwara ce ta sake jiki da shi suna aiki haka, but a duk lokacin da ya tuna zancen aurenta da Bilal sai yaji kamar ya hade zuciya ya mutu, wannan tunanin ya yi tasiri a zuciyarsa da har ya zurfafa masa ciwon dake damunsa, a iya yanzu ya sadakar kuma ya yarda rayuwarsa ba mai tsawo ba ce a duniya, saboda matsala da cocaine ya haifar masa da kuma yawan tunanin da yake a baya ga kuma wanda yake a yanzu, wannan yasa shi yin saku saku da rayuwa. Wani lokacin yana kan kamar ya samu Nawwara ya fada mata hakan sai dai yasan ba zata fahimta ba kuma zata zargeshi da cewar saboda yana son bata alakarsu da Bilal ne, wannan yasa ya danne komai ya barwa zuciyarsa sai kuma mahaifinsa da Siraj da suka san da matsalar.

Kalaman da ta yi masa yau a office na cewar zata aje aikinta a wannan satin mai zuwa ne suka haddasa masa ciwon kai har ya abun ya sauko a zuciyarsa, kullum sai ya kirga kwanakin da suka rage na aurenta da Bilal kamar da shi za a daura auren. Ji yayi yana da bukatar ganin dansa domin a yanzu shine kawai farincikisa, a duk lokacin da Noor yake kusa da shi yana jin dadi sai ya dinga jin kamar Nawwara ce a kusa da shi.

Unkurawa ya yi ya tashi cikin karfin hali ya koma bathroom ya yi wanka ya fito ya shirya cikin kananan kaya ya feshe jikinsa da turare sannan ya dauki wayarsa da car keys ya fice daga dakin.

Har ya fito harabar gidan be daina jin zafin da zuciyarsa take masa ba. Haka ya shiga motar ya dauki hanyar da zata kaishi gidansu Nawwara. A kofar gidan ya yi parking sannan ya dauki wayarsa ya kira Nawwara, bata dauka ba har ta katse sai ya sake kira haka ya jera mata kira hudu ba tayi picking sai ya fita daga motar ya je kofar gidan ya buga, sai gata ta fito hawaye shabe shabe a fuskarta.

“Dan Allah dan girman Allah karka sake zuwa kofar gidan nan Jibril da sunan ganina, yanzu yanzu Bilal ya bar gurin nan da ya tararda kai ai ba zai ji dadi ba, saboda kai yau na fada min magana marar dadi, kuma na fada maka cewar komai ya kare a yanzu, tun da zaka iya komai da kanka shiyasa nima zan aje aikin saboda na samu damar kula da Bilal da kuma kaina”

“Ina son ganin Noor ne shiyasa na zo”

“Idan kana son ganinsa ka sanar da ni zan sa a kawo maka shi har gidanka, amman a i zuwa yanzu ka daina zuwa nan sai na yi aure”

“Okay Nawwara ba zan sake ba, and ki bawa Bilal hakuri akan abubuwan da suka faru, na san mun shiga hakkinsa but yanzu komai ya wuce”

Ba tare da ta sake cewa komai ba ta juya ta koma ciki, shi kuma ya cikama bakinsa iska ya busar sai ga Noor ya zo da gudu, sai Jibril ya risina kasa ya shafa fuskar dansa sai kuma ya rumgume shi ya lumshe ido.

‘Ni na jawa kaina komai saboda haka dole na yarda da rashinki’

Ya fada a ransa, a fili kuma sai ya dago fuskar dansa ya kalleshi ya ce.

“Dukan abunda Nawwara ta yi da wanda na yi mun yi ne saboda kai Noor, ina son ko da bana raye ka kasance mai alfahari da ni a matsayin ubanka”

“Ni ban gane abunda kake cewa ba”

“Zaka gane wata rana, ina son ka zama mai biyayya ga Mahaifiyarka ita ce zata rayu da kai har ka girma, na yi farincikin da na rayu da kai Noor ina son ka sosai”

Ya rumgume shi idanuwansa cike da kwalla, sosai da sosai yake shakar kamshin jikin Noor, domin haka na masa dadi yana jin kusan da dansa sosai.

“Noor zamu je yau ka yi weekend gidana ko?”

“Ee amman Uncle Bilal ya ce zai je da ni yawo gobe Saturday”

“Yaushe ya zo?”

“Dazu”

“Okay, idan kun dawo sai na aiko a dauko min kai ka ji”

“Okay Daddy Momy har da cake ta yi ma Uncle Bilal”

Wani irin daga kai ya yi ya sauke numfashi saboda yadda maganar ta sokeshi.

“Okay je cikin gida ni zanje gida kar dare ya yi”

Ya sumbanci goshinsa.

“Goodnight”

“Goodnight”

Noor ya fada yana daga masa hannu sannan ya shige cikin gida, shi kuma ga mike tsaye ya jingina da motarsa ya lumshe ido yana sauke ajiyar zuciya. Ya samu thirty minutes a gurin sannan ya bude motaraa ya shiga cikin rashin dadin rai.



*** *** ***
NAWWARA POV.

Na farka yau cikin rashin dadi rai saboda abunda ya faru jiya, sam ban jidadin yadda Bilal ya kasa fahimta ta ba, duk da nasan kowa waye dole ya zargi wani abu a tsakaninmu, amman komai ya kare a yanzu ba zan sake bari wata alaka ta shiga tsakanina da Jibril ba da har zata sa Bilal ya zargeni.

Na dade a kwance kasancewar yau weekend har su Noor da Jamila suka dawo daga islamiyar safe ban tashi ba ba dan kuma ina bachi ba sai dan ina jin jikina da rayuwata babu dadi, ina son na labartawa Inna sai wata zuciyar ta hanani saboda na san ba komai ya kamata ace iyaye sun sani ba musamman a abunda ya shafi fada a tsakanin ma'aurata ko kuma masoya, har sai idan ya kai ya akwo mun kasa shawo kan abun. Wayata na dauka na aika masa da sakon barka da safiya amman be maido min da amsa ba, hakan yasa na kirashi sai be yi picking ba.

Tashi na yi na fita tsakar gida na gyara ko ina sannan na shiga na yi wanka na shirya cikin bakar abaya, Inna ma ta kula da yanayin da na ke cikin na rashin dadin rai, sai dai bata min magana ba, wata kila ta fahimci akwai abunda ya shiga tsakaninmu da Bilal jiya da dare saboda na dawo ina kuka duk da kasancewar ta tambaye dalilin kuka na ki fada mata.

Misalin sha daya da rabi Bilal ya kira ni ina picking ya ce

“Ki shirya ma Noor gani nan zuwa”

“Tau, har yanzu fushi kake da ni ko?”

Sai kawai ya kashe wayar, ni kuma na ja dogon numfashi na sauke na tashi na fita. Ko da sha biyu ta yi da kwata Bilal na kofar gidanmu yana jiran Noor, ban san miyasa ba na samu kaina da rashin jindadin fitar shi tare da Noor duk da sun saba fita amman yau ina jin daban gashi gabana sai faduwa yake, wata kila saboda bana cikin dadin rai ne ko kuma wani abun ne daban oho. Da kaina na riko hannunsa na kaiwo shi kofar gida, saiga wayar da ke hannuna ta yi ringing Jibril ya kira, daman yakan kira da safe ya yi waya da dansa haka ma da dare idan zai kwanta sai dai yau yayi ranar kira domin har sha biyu ta gota ko da yake yasan yau weekend ne Noor baya suwa school. A nan na mika masa wayar ya gaisa da Jibril sannan Bilal ya rika hannunsa ba tare da yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login