Showing 6001 words to 9000 words out of 138998 words

Chapter 3 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

728

zo muje”

Abunda ta faɗa kenan tana shigowa. Inna ce ta rigani fitowa tana gaisawa da Jidda. Sannan na fito sanye da hijabi.


“Jidda sai yanzu?”

“Yi haƙuri dan Allah taliya na tsaya dafa masa”

Ta faɗa cike da damuwa. Jidda ƙawar arzikice dukan abunda ya dame ni kamar ya sameta ne, tana damuwa sosai da duk abunda ya shafi rayuwarta, shiyasa bana da ƙawa a duniyar nan da ta wuce Jidda.
Tare muka fita tana min bita kan haƙuri da yarda da ƙaddara, ni ko bana iya cewa komai sai hawaye da ke min zuba, ganin haka yasa ta daina maganar domin tana ƙara min ƙarsashin abun ne kawai.

Tun da muka shiga Napep har muka fita ni da ita babu wanda ya ce Uffan, gabana ya faɗi sosai lokacin da muka doshi station ɗin wata ƙila saboda ban saba ba ne ko kuma ina fargabar ganin halin da Baba yake ciki ne.

Jidda ta lura da hakan shiyasa ta wuce gaba ta bar ni a baya saboda kawai ta ƙarfafamin guiwa. Ƴan sanda da yawa muka tarar a gurin, ta kuma ɗai-ɗaikun jama'a waɗanda nake sa ran suma sun zo kan nasu matsalar ne, muna shirin tambayar sai na hango Baba Sulaiman wato ƙanen mahaifina da kuma yayyunsa. Cikin rashin kuzari da raunin zuciya na ƙarasa kusa da su idona na zubar da ƙwalla.
Baba na zaune saman tebur fuskarsa a buge jini har ya dasƙare masa saman kai da alama tun jiya suka dake shi ko kuma da dare. Ƙasa na zauna kusa da shi na riƙe masa ƙafafu kasancewar shi yana zaune saman banci ne tare da ƴan'uwansa.
Kasa kallona yayi wannan baya rasa nasaba da kukan da na ke wata ƙila baya son kuka a gaban jama'a ne. Kwanon ɗumame na gefen da na zauna nasan su Baba Sulaiman ne suka zo da shi.

Tsawar da Baba Ayuba ya katsa min ne yasa ni tsagaita kukan da nake har na dawo hayyacina.

“Ai yanzu sun yarda za su bada belinsa amman wai sai an bada dubu ashiri”

Cewar Baba Salisu yayan Baba. Ni ko na dafe kai ina sauke ajiyar zuciya, ko yanzu tsugune bata ƙare ba, ina zamu samu wannan dubu ashirin ɗin.

‘Oh Allah mun gode maka’

Na faɗa a raina ina ta ƙoƙarin tare kukana. A nan Baba Sulaiman yake faɗa mana yadda matar take son a je kotu, wai ashe dpo ɗin station ɗin ne ƙanen wacce aka yi ma satar.
Bamu ƙara minti goma a gurin ba, wani ɗan sanda ya zo yana faɗa mana lokaci yayi.

Duk miƙewa muka yi tsaye a nan na samu kallon bayan mahaifina kasancewar ba shi da riga ne, babu komai sai kwancin sanduna, yanayin yadda baya son motsa jikinsa kaɗai ya isa ya karantar da kai jikin na masa zafi da ciwo ne.

Ban san lokacin da kuka ya zo min ba, na rumgume bayansa ina mai jin kamar na yi tsuntsuwa ni da shi mu ɓace daga gurin gaba ɗaya.

“Mahaifinku be yi sata ba Nawwara, kuma be taɓa yi, ki gamsar da ƴan'uwanki da wannan”

Abunda Baba ya faɗa min kenan, ni kuma na ƙara ƙanƙanme shi. Hankalin duk wanda ke gurin sai da ya dawo kaina saboda kukan da nake, babu tausayi haka ɗan sanda nan ya tisa ƙetar Baba gaba suka wuce da shi ciki. Ni kuma Jidda ta rumgume muka riƙa kuka tare.

“Haba Nawwara akan ki farau? Miyr haka wuce kuje gida, mu zamu koma can zamu san yadda za mu”

Cewar Baba Sulaiman.
Ƙarfin hali na yi na riƙa hannun Jidda muka fito tare, a nan Baba ya Ayuba yake faɗa min wai a tura Sakina ko Jamila ta karɓo mana ɗumame.

Har muka iso gida kuka na ke, Jidda ce ta iya tsayawa ta zayyana ma Inna abunda ya faru. Ba laifi na ga farincikin Inna wata ƙiƙa saboda sun yarda zasu bada belinsa ne.

Bayan Jidda ta wuce Sakina ta je karɓo abincin, ni kuma na tashi na nufi ɗaki kaina na mugun ciwo, abincin da aka karɓo ma ban iya ci ba, kamar yadda Inna da Habiba suka kasa ci duk da kasancewar muna jin yunwa.

Ni dai ina cikin ɗakin har aka kira sallah azahar, bayan na yi sallah na nufi ɗakin Inna, a nan take tambayata Habiba.

“Bata ɗaki na ɗauka tana nan ma”

“Bata nan ƙila ta je baban gida”

Haka kawai gabana ya faɗi zuciya ta riƙa nasalta min kamar ba can ta je ba. Babu wani hirar kirki tsakani na da Inna saboda bana son labarta mata halin da na samu Baba duk da kasancewar idanuwana sun saka goge hoton abunda suka gani.

Misalin huɗu da rabi Baba Sulaiman ya shigo gida yana faɗar an haɗa dubu shida da ɗari takwas abun da ƴan'uwa masara son zumunci, taya za a ce duk yawan familyn Babban gida ace dubu shida kawai aka haɗa. Takaici da baƙinciki ya hanini cewa komai haka na koma cikin ƙarƙashin iccen dalbejiya na zauna.

Ɗari da hansi ya cire a cikin kuɗi ya miƙawa Sakina wai su saye wani abu su ci. Inna kuma ta saka Hijabinta suka fita tare wai zasu je station ɗin su kai musu ko zasu karɓa.
Ni dai nasan wahala ce kawai zasu yi, ƴan sanda da basa da imani, kuma sun ce dubu ashiri ya za'ayi su karɓi dubu shida. Noor ne ya zo ya zauna kusa da ni yasa hannunsa yana share min hawayen da ban san sun zubo ba.

“Momy ki daina kuka”

Murmushin ƙarfin hali na yi na shafa kansa. Kan Habiba na fara hangowa ta leƙo sai ta koma ta laɓe, hakan yasa ni miƙewa tsaye ni nufi ƙofar, ƙaton hijabinta ne na islamiya a jikinta, sam babu natsuwa a tare da ita idonta ya kumburo kamar ba nata ba.

“Ina kika je Habiba?”

A maimakon ta amsa ni sai kawai ta jefomin wata tambayar.

“Inna na nan tsakar gida?”

Kai na girgiza mata alamar a'a ina kallon yanyinta. Baya na yi hakan ya bata damar shigowa cikin gidan, hankalinta be kwanta ba sai kalle-kallen tsakar gidan take kamin da wuce ɗaki da sauri. Cikin rashin kuzari na rufa mata baya, ina shiga cikin ɗakin sai ta kama hannyena ta danƙa min sababin kuɗi ƴan dubu-dubu.

“Nawwara ga dubu ashirin ɗin nan kije ki kai su saki Baba, daga baya sai a biyata kuɗinta”

Wani jiri na ji ya kamani na kasa riƙe kuɗin, suka suɓuce daga hannuna suka watse ƙasa. Ita kanta ta tsorata da yanayi da sauri ta soma yin baya-baya tana fashewa da kuka.


COMMENT AND SHARE
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


6⃣

Faɗuwa na yi saman guiwoyina na kai hannu na taɓa kuɗi, kamin na tada kai na kalleta.

“Habiba ina kika samu wannan kuɗin?”

“Tsinta na yi”

Ta faɗa cikin kuka mai ƙarfi. Miƙewa na yi tsaye na matsa kusa da ita ina nunata da yatsa.

“Karki raina min hankali Habiba, ta ya zaki tsince dubu ashiri a wannan halin?”

Na faɗa ciki wata murya da ban san ina da ita ba. Sai ta rufe bakinta ta matsa baya.

“Kyauta aka ba ni”

Na watsa mata wani irin mahaukacin mari.

“Ba ƙaramar yarinya ba ce ni, karki yi wasa da hankalina”

“Mustapha ne ya ba ni”

Ta sake faɗa tana dafe fuskarta saboda zafin marin da na yi mata.

“Mustapha”

Na maimaita sunan, tabbas Mustapha zai bata fiye da dubu ashiri, zai iya bata miliyan ma, amman idan ta ba shi mutuncinta.

“Ya taya mutuncinki ne ya baki kuɗin ko kuma kin riga kin siyar masa ne?”

Na tambaya gabana da dukan shida-shida, zuciyata kuma na ala-ala idan bata siyar ba.

“Na siyar... Nawwara idan ba haka na yi babu inda wannan kuɗin zai fito, ki duba halin da Baba yake ciki, babu ruwan kowa da mu”

Baya-baya na yi har sai da na jingina da ƙofar ɗakin.

“Habiba kin kashe mu, ya kike tunanin Inna zata yi idan ta ji wannan abun? Kina tunanin wannan abun da kika aikata zai burge Baba? Da wane ido zaki kallesu”

Da sauri ta ƙaraso kusa da ni ta riƙe hannuna tana kuka har muryarta na karkarwa.

“Dan Allah karki faɗa musu, saboda su na yi wannan abun idan suka yi fushi da ni Wallahi mutuwa zan yi”

“Kin san da wannan kika je kika siyar da mutuncinki? Allah da ya samu cikin wannan hali shi zai mana mafita, kina kunyar iyayenki amman baki kunyar Allah ki? yanzu ina kika son na ce mun samo wannan kuɗin?”

Risinawa ta yi a gurin da cigaba da kuka mai taɓa zuciya. Sallamar Jidda ce ta razanar da mu daga ni har Habiba ɗin. Da sauri na fita waje domin na tareta karta shigo, na manta da hawayen da ke fuskata har sai da Jidda ta min magana.

“Nawwara kuka kike yi?”

Nasa hannu na share hawayen yayinda wasu suke ƙara zubo min, kuka ya zama biyu a yanzu. Hannu ta kama ta danka min dubu uku.

“Ga dubu uku ku ƙara”

“Ke kuma ina kika samu wannan kuɗin?”

Na tambaya muryata na rawa.

“Wayata na siyar vivo”

A maimakon na yi mata godiya sai kawai na fashe da kuka, hakan ya karantar da ita ba wannan ne kawai damuwata ba, lallai da akwai wani abun a ƙasa.

“Nawwara ko dai wani abun ya faru ne?”

Ɗurƙushewa na yi a gurin na fashe da wani sabon kuka, har su Sakina suka yo kaina. Hakan yasa na katse kukan na miƙe tsaye na kama hannun Jidda muka shiga ɗaki.

“Jidda Habiba ta siyar da mutuncinta ta kawo dubu ashirin”

Na faɗa ina nuna mata kuɗin. Ita kuma ta ɗora hannu saman kai tana faɗin

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Inna ta ji? ”

“Bata sani ba, amman yanzu dole zata sani idan ta ga wannan kuɗin”

“Habiba miyasa kika yi haka?”

Jidda ta tambaya hawaye na bin fuskarta. Habiba kan aikin kuka kawai take, ta ma kasa ɗaga ido ta kalli Jidda.

“Ina zaku ce kun samo wannan kuɗin Nawwara?”

“Nima ban sani ba”

“Karki faɗawa Inna, bari na je da kuɗin ni nasan yadda zan yi”

Duƙawa ta yi ƙasa ta tsince kuɗin ta fita. Har na cira ƙafa zan bita sai Habiba ta kirani cikin muryar kuka.

“Nawwara”

Juyowa na yi na dawo. Sai ta tashi zaune

“Dan Allah karki faɗawa Inna”

“Ba zan faɗa ba”

“Idan na yi tafiya ba zata ga ne ba?”

“Ba zaki ita tafiya ba ne ba?”

“Gurin zafi ya ke min sosai, bana iya haɗe ƙafafuna da kyau”

Wani ƙololon bakin ciƙi na ji ya ratsa zuciyata. Cikin rashin ƙwarin jiki na fita waje na kunna wuta na ɗora mata ruwan zafi, Sakina kuma na ce su je su siye wani abu su ci da kuɗin da Baba Sulaiman ya basu. Sai da na cika mata roba da ruwan zafi sannan na zuba mata wasu a bota, da kaina na kai mata banɗaki, naje na riƙo ta kaita banɗakin.

Tana gurin wankan Inna na ta dawo, fuskarta da alamun damuwa tun daga yanayin sallamarta na lura da hakan balle ma lokacin da ta zauna kusa da ni.

“Kin dawo”

Na tambaya ina ƙoƙarin ɓoye hawayena.

“Eh mun kai musu kuɗin amman sun ce sai an cika sauran, ba su bar mu mun ganshi ba”

“Allah yayi mana mafita”

Na faɗa ina sauƙe ajiyar zuciya. Yayinda idona ke kallon Habiba ta tsaya tana leƙon. Na san tsoronta ɗaya kar Inna ta gane halin da take ciki, ina baƙin cikin halin da Habiba ta faɗa da ƙananan shekarunta ni kaina mai shekara ashirin da huɗu mutane kan kirani da ƙaramar yarinya balle ita mai sheƙaru goma sha bakwai.

Tunanin dabarar da zan yi ma Inna ya ɗaukr hankalinta har Habiba ta samu ta wuce na ke, sai ga Jidda ta shigo kamar ta san ina nemanta. Saman tabarma ta zauna tana gaishe da Inna, ko da wasa Jidda bata kalli inda na ke ba, sai kawai ta fara jerawa Inna irin ƙaryar da data tsara.

“Inna ga dubu ashirin na kawo, na siyar da kayan Kitchen ɗina ne, Maman Nura ma bata sani ba kuma idan ta ji zata min faɗa, dan Allah karku faɗa mata, inyaso idan Allah ya kawo sai ku biyani”

Ya ƙarasa tana danƙawa Inna dubu ashirin ɗin, Inna ta saki baki.

“Haba Jidda ayi haka?”

“Zan iya muku komai Inna ni dai ki rufa min asiri karki faɗawa Maman Nura”

“Ba zan faɗa ba, Allah ya saka miki da alheri ya biyaki da aljanna, ya baki miji na ƙwarai”

Da ido na yi ma Habiba magana akan ta zo ta wuce saboda hankalin Inna ya ɗauko kan kuɗin, sannan na amsa da

“Amin Jidda mun gode Allah ya bar zaman tare”

“Ba komai ai yi ma kaine”

Inna ta kalleni.

“Ai ban ga ta zama ba ni kan, bari na je na samu Sulaiman mu kai musu cikon kuɗin ko?”

“Inna ana kiran magariba kuma? Da dai kin haƙura har a jima ko gobe”

Cewar Jidda.

“A'a Jidda tun da har Allah yayi mana mafita ƙara muje mu kai musu kuɗin, baki san halin da bawan Allah ya ke ciki ba”

Na kalli Inna zuciyarta cike da tausayinta da kuma tausayin kaina da na Jidda, na san tun safe bata ci komai ba ga rashin kwanciyar hankali da ke damunta. Hijabinta da ke gabanta ta ɗauka ta saka ta miƙe jikinta har rawa yake ta saka talkaminta ta kama hanya. Na kalli ƙawata Jidda tare da yi mata godiya.

“Na gode sosai Jidda”

“Ba komai, ki yi magana da ƴar'uwarki Nawwara ki kwantar mata da hankali karta sake shiga wani hali, ni zanje gida kar Abbah ya dawo”

“Na gode sosai Jidda”

Tashi ta yi ta fita, ni kuma na tashi nayi alwala na yi sallah, shiru-shiru Inna bata dawo ba har bayan Isha'i, sai dai hakan be sani tsoro ba a tunani ko zasu ɓullo da wani abun ne na daban. Takwas da rabi Inna ta dawo ita kadai cikin yanayin damuwa. Sai dai ban tambayeta komai ba har sai da ta yi alwalah ta rama sallah magariba ta yi isha'i bayan ta sallame na matso kusa da ita na ce

“Inna ya kuka yi da su”

“Lamarin ƴan sanda nan yana ba ni tsoro Nawwara, basu bar mun ganshi ba, amman sun karɓi kuɗin wai zasu zo anjima su kawo shi da kansu, ni ban taɓa jin inda aka yi haka”

“Ko dai ba zasu bada belin nasa ba ne?”

“Ni ya zan sani, an ce dpo gurin ƙanen wacce aka yi satar ne, kin san kuwa sai yadda Allah yayi”

“Baba Sulaiman be ce komai ba?”

“Babu irin roƙon da ba mu musu ba Nawwara, Har Salisu da Dahiru duk sunje, amman sun ce ba zasu ba da shi ba sai dai su kawo shi da dare, shine su suka wuce gida ni kuma na dawo”

“To ko wasu kuɗin zasu ce a ƙara musu kuma?”

“Ban sani ba”

Ta faɗa tana fashewa da kuka. Iya ƙoƙarin da nayi na danne kukana sai na kasa saboda ganin hawayen mahaifiyata yana zuba. Shiru-shiru har goma na dare babu wani labari, daga ni har Habiba da Inna muna cikin tashin hankali da zullumi, dukanmu hankalin sai ya tattara ya koma gurin ƙofa ko iska ya kaɗa sai muga kamar Baba ne za a shigo da shi.

Sha ɗaya da rabi na dare na tashi zan rufe gida, izuwa yanzu kan mun sadaƙar ba zasu kawo shi. Ina kaiwa bakin ƙofa sai na hango motar ƴan sanda ta faka a ƙofar gidanmu ahankali, ta yadda ba za a ji ƙarar motar ba, fitar motar ma a kashe take. Ban ƙara tabbatar da ƴan sanda bane har sai da naga sun fara fito daga cikin motar. Da gudu na juya na koma cikin gida dan faɗawa Inna.

“Inna Inna ga su can sun zo”

Ba Inna kawai ba, har Sakina da Jamila da ke bachi sai da suka farka duk muka ɗunguma muka fito waje da gudu.
Sai dai abunda muka yi karo da shi ya faɗar da gabanmu dukanmu.

Baba ne suka aje gefen icce sai wasu ƴan sanda uku kusa da shi ɗayansu ya ƙaraso kusa da mu yana mana bayanin da ban gane kansa ba.

“Zuciyarsa ce ta buga, ku kai shi asibiti da safe”

Yana faɗar hakan ya juya da sauri suka fice daga gidan. Mu kuma muka ƙarasa gurin da Baba yake kwance, hannu na kai na girgiza shi be motsa ba, na kira sunansa be amsa ba, na jijjiga amman be yi wata alama ta mai rai ba. Firgice na nasa hannu na yaga rigar yadin da ke jikinsa, sai ga ƙirjinsa da dukan jikinsa da jini, tashin hankali ya mantar da ni cewar dare ban san lokacin da na kwala ihu ba, na yi tsalle na dire na faɗi ƙasa na mulmula na mulmulo ina kuka, Habiba kuma ta faɗo kaina sumammiya.



YAWAN COMMENTS YAWAN TYPING. 🙌
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


7⃣

Cikin tashin hankali na kwantar da Habiba da ta faɗo kaina, na nufi Inna da ke baya-baya tana nuna Baba da yatsa. Ina riƙata sai ta cafki hannayena jikinta na karkarwa.

“Gawa suka kawo mana Nawwara, sun kasheshi, miya musu? Basu yarda zamu biya kuɗin ba? Ko dan sun maida mu talakawa? Saboda ba mu da galihu? Akan ƴan kunnen zinari da wayoyi suka ɗauki rai? Miyasa za su kawo mana shi? Saboda muma mu taru mu mutu ko? Sun maida mu mahaukata...”

Daga kalaman da take na fahimcin ƙoƙarin fita hayyacinta take. Riƙata na yi na zaunar, Sakina da Jamila da ke kuka na tura su ɗaki. Sai kuma na dawo tsakar gidan na yi tsaye ina kallon Baba, kana na kalli Habiba da ke sume, sai kuma Inna da ke zaune tana kallona, neman kukana na yi na rasa ashe akwai ranar da zaka buƙaci kukan ya ƙi zuwa maka, idona gaba ɗaya na ƙafe kamar hawaye be taɓa taruwa a ciki ba, yawun bakina na bushe kaina kuma yayi mugun nauyi kamar an ɗora min dala.

Ban damu da rashin mayafi da babu a jikina ba da kuma takalmi na fita da gudu zuwa babban gida. Gudu na ke amman gani nake kamar ƙara maida ni baya ake, tsakaninmu da su babu nisa amman yau sai ya koma min kamar gari da gari.

“Keeeeeeee”

Na ji an kirani sai dai hakan be sani tsayawa ba, har sai da na ji an harba bindigar mahalba. A firgice na juyo ina ɗaga hannuna sama yayinda su kuma suka tunkaroni suna nuna ni da bindigar, ɗaya daga cikinta da dalla min fitila mai tsananin haske da kashe ido.

“Nawwara miya fito da ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login