Showing 3001 words to 6000 words out of 138998 words

Chapter 2 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

726

babin kwaliyana ne na iƴa fito kamar matar minister.

“Inna zan tafi”

Na faɗa ina tsaye daga jikin ƙofa, kai na jingine da ƙofar ina kallon Baba da ke unƙurin tashi.

“Tau Allah ya kiyaye”

Inna ta faɗa, Baba kuma sai ya ce

“Ni ma bari na shiga kasuwa na ga abunda Allah zai yi”

Salamar Maniru muka ji wato almajirin Hajiya Murja, maƙociyarmu masu babban gida, matar babban soja wacce bata taimako sai idan da dalili. Ni da Inna muka haɗa baki gurin amsa masa, Baban kan ya amsa masa da.

“Bata nan taje makaranta”

Domin yasan Jamila take nema, takan aiko kiranta a duk lokacin da wani aiki ya sha gabanta, domin kawai ta taya ta aikin sai ta sammata wani abu daga abincin rana ko dare da aka yi a gidan.
  Bayan Maniru ya fita Baba ya haɗe fuskarsa saboda mu ɗauki zancensa da muhimmanci, ya saba mana a duk lokacin da yake hanin mu kan aikata wani abu ko kuma ba mu umarni.

“Bana son zuwan da Jamila take a gidan Manjo Faruku, kowa ya tsaya inda Allah ya aje shi”

“Ni kaima bana son zuwanta a gidan domin yaron gidan nan ba shi da tarbiya, sannan yunwa babu abunda bata sawa musamman ga waɗannan da suke yara”

Na faɗa cike da jin zafin tuna irin satar da ta taɓa ɗorawa Sakina a kwanakin baya.
Inna dai bata ce komai ba bayan ajiyar zuciya da ta sauke.

“Na tafi nidai ayi min addu'ah”

“Tau Allah ya bada sa'a karki daɗe dai, kuma ki kula.da irin mutanen da zaki yi hulɗa da su”

Cewar Inna ni kuma na amsa da tau na kama hanya ina addu'ar fita daga gida wato.  _Bismillaahi, tawakkaltu 'alallaahi, wa laa hawla wa laa quwwata ‘ illaa billaah._
_بِسْمِ اللَّهِ تَوَكَّلْـتُ عَلَى اللَّهِ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُـوَّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ_

Babu ko ƙwandala a hannuna ƙasa na kama hanya duk kuwa da kasancewar unguwar akwai ɗan nisa da ta mu. A bakin ti-ti na haɗu da Bilal wato abokina ko kuma na ce mutumen da muke mutunci da shi sosai har mutane suke raɗin-raɗin wai akwai soyayya a tsakanin mu.

“Nawancy”

“Bilal ya gida?”

“Lafiya ƙalau Wallahi Ina zaki je haka?”

Bana son faɗa masa ainahin inda zanje, ba kasafai nake son mutane su san ina zuwa aiki ba nafi son aji na samu aikin kawai, musamman Bilal da yake yawan nuna min baya son neman aikin da na ke.

“Nan zan je gawon nama gidansu wata ƙawata Zinatu”

Ya matso da mashin ɗinsa Honda

“Hau na sauke ki”

“A'a na gode”

Na faɗa ba dan bana son hawan ba sai dai bana son yasan gurin da zanje.

“Dan Allah ki hau mana, t-t ne balle ki ce kina jin kunya an mun fito cikin unguwar”

Bana da wata dabara ta da wuce na hau ɗin, babu tantanma idan har na zaɓi zuwa a ƙafa zan wahala sosai.
   Abun ka da mai nema sai kawai na gyara zane na na haye mashin kamar na yayana ko kuma na ce na Ubana. Bilal ba baƙona ba ne hakan yasa na sake da shi sosai muna fira har muka isa bakin ƙofar gidansu Zinatu. Na sauka ina masa godiya.

“Am Nawancy na manta ban labarta miki wani abu ba, mun samu sabon shugaba a kamfaninmu kuma ya buƙaci sauye-sauye saboda yana da zafi sosai, kuma duk ya zubar da ma'aikatan gurin ya ce sabbi za a ɗauka, sai dai be faɗi rana ba, so ina fatar idan za a ɗauki wasu zaki yi applying”

“Kai ka ce kai ma kun tsallake rijiya da baya”

“Wallahi mun tsallake kan, domin mutumen akwai zafi sosai, gashi baya ganin kowa da mutuncin, ko dan yana kamfanin Mahaifinsa ban sani ba”

“Ai fa ka ji to mu da ba wani zurfin ilmi mukayi an ya zai ɗauke mu kuwa, Bilal kafa san SSCE ne kawai da ni”

“Abun sa'a ne Nawancy zaki iya shiga kuma ki yi sa'ar samu, ai kisan mataki mataki ne”

“Naga Babban kamfani ne Bilal”

Yayi wani abu da fuska yana matse hancin, irin yadda yake min a duk lokacin da zai zolayeni.

“Trust me girl zaki samu babu tantama”

Na yi murmushin da ya fitar da dimple ɗina, ina ƙara jan gyalena dan rufe jikina.

“Ni zan wuce aiki kar na yi latti ya kore, dan ya faɗa mana idan ka ƙara minti ɗaya zai koreka daga kamfanin”

“Tau Allah ya kiyaye na gode”

Hannunsa ya ɗaga min.

“Ina gaida abokina Noor”

Kai na ɗaga masa as respond na juya kamar zan shiga gidansu Zinatu, ina hango ya kama hanya, na juyo dan har ga Allah ba gidansu Zinatu zanje ba na san ma by this time bata gida, ko ma tana nan mi zanje na yi a gidansu yarinyar da bata ƙaunar zuwa gidanmu.

   Miƙe ti-tin gawon nama na yi har na ɓullo ta gurin gidan Alu, wato tsohon gonnan, na  miƙe na tsallaka babban titi na doshi Candy Restaurant.
   Restaurant ne mai kyau da tsari ga tsafta, ba laifi ma'aikatan gurin suna na'am-na'am da mutane tun a farkon zuwana na lura da hakan. Kai tsaye na nufi gurin wanda na ke zaton babbansu mai sanye da riga orange an rubuta mata Candy Restaurant da fafaren harufa.

“Assalamu Alaikum”

“Wa'alaikissalam”

“Sannu ko ka gane ni?”

“Gaskiya ban gane ki ba, abun da yawa”

“Ni ce wacce na zo kwanakin baya ka ce min Khadeeja Candy bata nan”

“Ayya Allah sarki, sai kuma kika ƙara rashin sa'a yau ma bata nan”

“Dan Allah ko kasan yadda za'ayi ma sameta?”

“Gaskiya bata garin nan tana Gusau kusan yanzu a can take zama, ko tana garin ma da wahala ta shigo nan”

“Dan Allah ko zaka taimaka min da numberta?”

“Gaskiya ba zan iya baki numberta ta saboda matsala ta tsaro, amman ke zaki iya barin Number idan ta shigo gari sai na sanar da ke”

A take na rubuta masa Number Jidda domin bana da waya, kuma Baba ko Inna babu mai waya a cikinsu.

“Idan ka kira ka ce Nawwara kake nema”

“Tau Inshallah”

“Na gode”

“Yauwa a sauka lafiya”

Jiki ba ƙwari na juya na fito. Har ga Allah ban jidaɗin rashin ta tararda mai restaurant ɗin ba, ga kuma uwar hanyar da zan miƙe duk da yaƙe rana be yi sosai ba, sai dai ina jin kamar zan wahalar da kaina tafiya a ƙafa har zuwa unguwarmu.

“Allah ƙa zame min gata”

Na furta a fili ina busar da iskar bakina. Dabarar na je gidansu Zinatu ne ya faɗo min a rai duk da ban yi niyar hakan ba.
   Haka na kama hanya na miƙe na koma ta inda na fito har na isa ƙofar gidansu Zinatu. Har na kai hannu zan buga ƙofar gate ɗin sai mai gaɗinsu ya wangale gate ɗin gaba ɗaya daga can ciki. Zinatu hakince a motarta ta kunno kai da alama fita zata yi, har ta yi kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ta sauke gilashin motarta tana kallona ta cikin baƙin gilashin da yake idonta.

“Khadija Musa Kafinta”

Ta kirani da sunan da nake amfani da shi a makaranta, nima kuma sai na kirata da nata.

“Zinatu Alhasan Hamshaƙi”

Ta yi wani shu'umin murmushi tana cire gilashin idonta.

“Nawwara ashe ana ganinki ko dai hanya ce ta biyo da ke?”

“A'a haka kawai yau na ce zan kawo miki ziyara”

Ta yi ƙis a ƙasan maƙoshinta wato ƙwafa na ƙasan maƙoshi.

“Aiko kin kyauta gashi kuma zan fita, ki shigo na saukeki gida kawai”

Na ji wani sanyi a raina daman abunda nake nema kenan.

“Okay”

Na faɗa sannan na buɗe motar na shiga. Jefi-jefi muke firar makarantarmu wato Nana Girl's Secondary School, kamin na ɗauko mata zancen masters da naji ance ta fara yi.

“Wallahi ina nan ina yi yanzu haka kuma na samu aiki a wani babban kamfani this monday zan fara”

“Mashallah, Allah ya taimaka”

“Amin ai ke kin ƙi karatu ko?”

“Uhmm”

Na yi murmushi kawai ina danne abunda ke raina, yawancin mutane sukan faɗa min haka musamman abokaina wai na ƙi karatu bayan kuma karatun ne ya ƙi ni tun da komau sai da kuɗi, hawan napep zuwa da dawowa ma ai sai da kuɗi. Har ta sauke ni ƙofar gidanmu bata kalma bata sake fita daga bakinta, nima kuma ban sake ce mata wani abun ba.

“Na gaida Inna”

Ta faɗa lokacin da ta ga na buɗe mota zan fita.

“Inna zata ji na gode”

“Okay”

A bakin ƙofar gidanmu na tsaya ina kallonta cike da sha'awar rayuwarta, duk mutune da yayi karatu burgeni yake, balle ita da ta fara cin amfanin karatun a yanzu. Sai da na daina hangota kan kwanar gunguwarmu mai kwatannin sannan na shiga gida.

Inna na samu a tsakar gida tana shara, gyale na kawai na yaye ya karɓi tsintsinyar dake hannunta na cigaba da shara.

“Allah yasa dai an yi sa'a”

“Wallahi ba'ayi ba Inna wacce na je nema bata nan, amman na bada number wayata aje mata”

“Allah yasa mu da ce,  amman dai daga yau karki saki zuwa wani gurin ki haƙura idan ”

“Amin, inshallah nima zan haƙura indai da rabon na samu zan samu”

“Allah ya miƙi albarka”

“Amin”

Ta shinfiɗa tabarma ta zauna ni kuma na cigaba da sharar ina labarta mata cewar Zinatu ce ta kawo ni gida. Bayan na gam sharar na tattara na kwashe, muka ji ana sallama a ƙofar gida. Inna ce ta amsa ni kuma na nufi ƙofar dan duba ko wanene. Ganin mutun sanye da kakin ƴan sanda yasa gabana faɗuwa sosai.

“Nan ne gidan Musa Kafinta?”

“Eh Nan ne”

Na amsa murya na rawa.

“Musa Kafinta yana police station na guiwa locos, ana son a sanar da iyalansa ne kuma baya da waya shiyasa na zo”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, miya faru?”

“Idan kika je can zaki ji”

Ya juya yayi tafiyarsa, ni kuma na juyo cikin gida idona na zubar da ƙwalla.



MAI KUKE TSAMANI A PAGE NA GABA?
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


4⃣

Inna ta doso inda na ke a yayinda da juyo cikin gida hawaye na bin fuskata.

“Nawwara lafiya?”

Ban san ta ya zan faɗa mata ba, sai dai babu wata damar ɓoye mata dole na faɗa mata gaskiya.

“Wai Baba aka kama, yana station ɗin ƴan sanda”

“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un”

Ta faɗa tana dafe kanta fuskarta na bayyana tashin hankalin da ke zuciyarta.

“Mi yayi musu?”

“Nima ban sani ba, na tambaya ya ce idan na je can zan sani”

“Mun shiga uku muna cikin wannan halin kuma wani za mu shiga”

“Ina ganin sharar fage ne ga wata sabuwar rayuwa”

Na faɗa ina hawaye. Bata kula zance ba ta shiga ɗaki ta ɗauko tsohon Hijabinta ta saka tana ce min.

“Zan je na faɗawa Dahiru muje tare, ke kije ki faɗa a babban gida”

Bata ko tsaya jiran abunda zan faɗa ba ta fita hankalinta a tashe. A take nima na saɓi mayafina, na ja ƙofar gidan na nufi babban gida wato gidan kakaninmu.
Babban gida ne mai ginin ƙasa da laka irin gidan nan da ake a zamanin baya wanda a yanzu ake kira da family house, ba kasafai na ke son zuwa gidan ba saboda mutanen da ke ganin mutunci na da na ubana basa a raye a yanzu, wato kakanin na kenan waɗanda suka haifi ubana, sai dai ƙanen da ƴaƴansu da suke ganin kamar Baba yayi mana gata dan ya ware mu daban, duk laifin duniya da ganin kamar mu munfi kowa sai suka ɗauka suka ɗora mana har wasu na cewa wai dan Tsoho ba shi da rai ne tasa Baba yin haka.
Alhalin ba haka ne kawai Baba baya son rigima ne da ƙaƙanan maganganu da yawan anyi an'ce kamar ya kashesu.

Sashensu Yakumbo na fara shiga wato gwaggo Babana, tana ganin hawaye a fuskata tasan ba lafiya.

“Tsohuwa Lafiya?”

“Baba aka kama”

“Kama kamar ya? Kamu na ƴan sanda ko mi?”

A take ya zayyana mata komai ina hawaye. Miƙewa ta yi tsaye ta fita tsakar gida duk da jikin nata babu wani dogon ƙwari saboda tsufa. Kan ka ce kwabo har ƙofarta ta cika da ƴan cikin gida kowa na tambayar ba'asi, abunda na faɗa mata shi na faɗa musu, sai tasa aka kira ƙannen Babana wanɗanda basa nan a waya ta sanar musu.

Ban baro gidan ba sai da aka kira sallah azahar kuma har lokacin Inna bata dawo ba. Sakina da Jamila kan suna tsakar gida zaune, Noor ne kawai yake sha'aninsa, ina shiga suka yo kaina da tambaya.

“Anty ina kika je?”

“Baban gida na je”

“Me kika je yi, ina Inna?”

Yara ne ƙanana a tunani be kamata na sanar su wannan maganar yanzu ba.

“Na riga Inna fita ban san inda taje ba, ni na je gaishe su ne kawai”

Noor ya zo ya riƙe min hannu.

“Momy yunwa na ke ji, kunon da na sha ya ƙare”

Hannu da ke cikin nasa na sunce na nufi ɗaki dan bana son yaga ƙwalla da suka cika min ido. Ɗan kuka na yi kaɗan a ɗakin domin idan na yi da yawa zai tona asirin abunda na ke ɓoyewa Sakina da Jamila ne, fito na yi waje na yi alwala na koma ɗakin na shinfiɗa ɗankwalina na yi sallah azahar, babu irin addu'ar da ban yi am Baba ba duk ya ke ban san halin da yake ciki ba ko kuma dalilin kama ɗin shi ɗin ba, na roƙar masa mafita da sauƙi ga Allah, tun a cikin sujudar ƙarshe har a cikin zaman tahiya zuwa addu'ar da ake bayan sallamewa.

Ƙarfe biyu da kwata Habiba ta dawo gida cikin uniform ɗinta na makaranta. Tun da ta yi sallama na kasa amsa mata ta fahimci akwai matsala. Hijabi ne kawai ya zame mata dole ta cire ta nufo inda na ke zaune ta dafa ni.

“Nawwara mi ya faru”

Idan na ce zan ɓoye mata hawayena to zan yaudareta ne kawai, domin ta riga ta ga yadda hawayen ya ke sauƙowa daga idona, bakina kuma a gumɗe ina gintse kuka da ke son fito.

“Ki faɗa min mana ina Inna?”

Ta sake tambaya idonta na cika da ƙwalla.

“Habiba ƴan sanda sun kama Baba, tun safe Inna ta je har yanzu bata dawo ba”

Ta ɗora hannu saman kai.

“Mun shiga uku? Mi yayi musu?”

“Wallahi ni ma ban sani ba”

A gurin ta zauna ta fara kuka kamar an yi mana mutuwa, daman Habiba bata da taurin zuciya irina, zan iya ɓoye kukana ko kuma bayyanawa a duk lokacin da nake buƙatar hakan amman Habiba bata iya wannan, a duk lokacin da abun kukan ya sameta a take zaka gane.
Sakina da Jamila har da Noor suka shigo ɗakin a guje suna kallonta, nima kallonsu na ke hawaye na bin fuskata. Sallamar Inna da muka ji ne yasa muka ɗunguma gaba ɗaya muka fita waje, tana kallonmu sai ta fashe da kuka ta faɗi zaune.

Daga ni har Habiba kasa tambaya mukayi kowa da abunda yake saƙawa a zuciyarsa, musamman ni da nake zargin ko sun kashe she ni. Jamila da Sakina ne suka ƙarasa inda take suna tambayarta.

“Sata ake zargin mahaifinku yayi ta kimanin dubu ɗari biyu da saba'in”

Tana faɗar haka ta ƙara fashewa da kuka, Habiba ta faɗi zaune irin jikinta ya mutu sosai, ni kuma na lumshe ido wasu zafafan hawaye suka zubo min.
*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


5⃣

Haƙiƙa mahaifina talaka ne, amman bana tunanin wannan talaucin zai saka Baba sata, sai idan wani tsautsayin ne ko ma zai sata ba zai saci kuɗi har naira dubu dari biyu da saba'in ba, tau ina zai kaisu?

“Miya ɗauka har na dubu ɗari biyu saba'in?”

Habiba ta yi tambayar da na ke da niyar yi ma Inna.

“Dako ya je yi kasuwa, wacce yaje yi ma dakon wayoyinta da ɗankunenta na zinari ya ɓata, ta ce wayoyinta na dubu ɗari da ashirin ne, ɗankunen zinarinta kuma dubu ɗari da hansi”

Sulalewa na yi ƙasa hawaye na min zuba, babu zancen da nake tunawa kamar maganar mu ta ɗazu da safe, yadda na ke nanata masa kar yaje dakon nan kamar na san abunda zai faru.

“Babu irin roƙon da ba'ayi mata ba ta ce ita ba zata haƙura sai an biyata”

Inna ta faɗa cikin kuka. Sai duk muka saka kuka har su Sakina da Jamila, daman Habiba bakinta a buɗe yake tana aikin kukan.

“Ku daina mana kuka tun da ba mutuwa aka yi ba”

Cewar Inna tana share hawayenta. Bayan Inna ta bar gurin na miƙe tsaye na koma cikin ɗakin na zauna ina aikin kuka. Haka muna yi sallah isha'i cikin zullumi da tunanin makomar Baba har ma da tamu gaba ɗaya, bayan an yi sallah isha'i ne maƙota suƙa riƙa shigowa suna mana jaje.
Ban taɓa yarda tashin hankali na hana bachi ba sai a wannan karon ina ji ina gani bachi ya ƙaurace daga idona. Alwala na fara gabatarwa kamin sallar nafila, har aka kira sallah asuba ina zaune saman ɗankwalina ina tasbihi, bayan na gama na yi ma Baba addu'a sannan na gabatar da sallah asuba.

Tun da dungu-dungun safiya muka ji an buga mana ƙofa, Habiba ce ya je ta buɗe yayinda ni nake zaune ina karatun ƙur'ane. Ina jin lokacin da ta zauna kusa da ni sai dai ban kalleta ba har sai da na kai ƙarshen ayar da na ke karantawa, sannan na rufe ƙur'anen ina ambatar sunanta

“Jidda”

“Na'am Nawwara, jiya cikin dare na ke jin abunda ya faru kuma kin san Abba baya bari mu fita da dare, da gaske ne?”

Na ɗaga mata kai hawaye na bin fuskata.

“Baba ba zai yi sata ba, sai dai idan wani sheri ne aka masa”

Cikin kuka na zayyana mata abunda Inna ta faɗa mana. A take ta fashe da kuka.

“Nawwara ki yi haƙuri jaka ƙaddara take zuwa wani lokacin, yanzu bari na je na shirya sai muje mu ganshi”

“Babu ko naira hannuna Jidda”

“Ina da ɗari uku zasu ishemu”

“Tau Jidda na gode”

Miƙewa ta yi tsaye ta fice, ni kuma na tashi na nufi ɗakin Inna, gaisheta na fara yi sannan na faɗa mata yadda muka yi da Jidda.

“Tau bari na jira har ku dawo sannan muje”

Tashi na yi na koma ɗakinmu na cire tufafin jikina na ɗaura zane na ɗibi ruwa a robar da muke wanka na shiga banɗaki na yi wanka da ruwan sanyi.

Tufafin jiya na ɗauka na saka ban damu da shafa mai ba, domin ba kwaliyarce a gabana ba, sai takwas har da ƴan mintuna sannan Jidda ta dawo, baƙar abaya ce jikinta sai jan mayafi, hannunta ɗauke da kular abincin.

“Nawwara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login