Showing 105001 words to 108000 words out of 138998 words
yar iskace ko kuma marar tarbiya.
Some will say ya zata kawo mana wannan dogon sharhin nan ko? đ Wallahi abun yana ci damuna ne sosai kuma wannan ce kadai damar da na ke da ita wanjen yin wannan bayanin. Wanda na batawa rai ya yafe min Allah ya shirya mu gaba daya.
See you next page i can't wait na ji labarin da Rabi zata bawa Nawwara đidan Nawwata ta ji za tayi wani abu kuwan? Anya Iayayen Bilal zasu bari ya auri Nawwara kuwa? Duka zai zo a next page Inshallah. đ
[11/8, 9:37 PM] +234 703 352 5246: *RAI BIYU...â„đ€*
Wattpad @KhadeejaCandy
_This Chapter is yours Auntie Sisâ„_
5âŁ0âŁ
âLafiya?â
Inna ta tambaya.
âLafiya kalau magana ce kawai mukeâ
âKin tabbata?â
âBa komai Innaâ
Ba dan ta yarda ta juya ta koma waje, ni kuma na gyara zamana na kalli Aysha na ce
âBa ni kika cuta ba Aysha kan ki kika yi ma, daman duk mai cutar wani yana jin dadi kansa yake cuta domin alhaki zai dawo akansa wata rana, idan ma hakkina ne yake bibiyarki Wallahi na yafe miki daga yau ba zai sake binki baâ
Dagowa ta tu ta kalleni da idanuwanta da take faman kuka da su bakinta na rawa ta ce
âWallahi Nawwara ke ta daban ce ban tsammaci zaki yafe min da wuri haka ba, na gode sosai Allah ya saka miki da Alheriâ
âAmin, amman dan Allah ina son ki fada min taya aka yi kika gane gidanmu?â
Sai da ta share hawayenta ta koma saman kujerar ta zauna daidai sannan ta kalleni
âSiraj ne ya kwatanta minâ
âSiraj kuma? Waye hakaâ
Na mata kamar ban san waye shi ba.
âWani abokin Jibril ne, shi kadai ne wanda Jibril ya aminta da shi a yanzu, shine kadai mutumen da yake karfafa min guiwar cewar zai yi duk yadda zai yi wajen ganin Jibril ya aure niâ
âYanzu kina nan akan bakarki cewar Jibril rai aureki duk bayan yaudarar da ya yi miki?â
âBana jiransa shi kadai, idan wanda zai aureni da gaske ya zo zan aureshi, na dade da yafe masa abunda ya yi min saboda na san tun farko laifina ne ba nasa ba, kuma har gobe ina son Jibrilâ
Na sauke numfashi a hankali ina mamakin karfin hali irin nata son wanda baya son ka, ko da yake ya so ta da farko,amman ai ya cuce dan me zata wahalar da kanta gurin son sa. Kamar ta san abunda ke raina sai kawai ta ce
âNa san za ki yi mamakin jin har yanzu ina son Jibril, ke ma da ace kina son shi tun farko ko kuma rabo ya shiga tsakaninku da za ki kula shi, ko da yake Siraj ya fada min yanzu matsalar rashin haihuwa take damunsa shiyasa babu ruwansa da ko wace maceâ
âHaka ya ce miki? Yaushe rabon da ki yi magana da shi?â
âKo jiya mun yi waya da shiâ
âAmman har yanzu be fada miki Jibril na da da ba?â
âHaka ya ce min Jibril ba shi da da kuma ya lalata rayuwarsa da shayeshaye hakan yasa mahaifinsa ya koreshi daga kamfanin da yake ya dora Sirajâ
âAmman gaskiya Jibril be kyautawa rayuwarsaâ
âNi ma da na ji ban jidadi ba, amman Siraj ya ce zai yi iya kokarinsa wajen ganin ya dawo da shi hanyaâ
âAllah ya bashi ikoâ
âAminâ
Sai da ta shafe fuskarta ta gyara Hijabinta sannan ta dauki jakarta ta rayata ta mike tsaye.
âNa gode sosai Nawwara zan wuceâ
Har bakin kofa na rakata sai zuciyata na ta tunani akan abokinsa Siraj, miyasa be fada mata cewar yana da da ba? Haka ma yasan lokacin da na fara aiki a kamfanin amman be sanar da Jibril bayan yasan Jibril yana neman ganina, amman kuma miye damuwata da shi ai abokinsa ne babu ruwana a ciki, maganganun Rabi ne suka fado min a rai kan na ankaro Inna ta jefo min wata tambayar.
âWacece wannan yarinyar? Kamin nan miye shigo da ke kina kuka?â
Sai a lokacin na tuna da cewar na shigo ina kuka, sai wacan bacin rai ya dawo min na soma jin tsanar Jibril sosai a raina. Kusa da ita na zauna.
âInna wannan Aysha wacce ta yi soyayya da Jibril ce lokacin da ya aureni, ita ce wacce ya ce yana so, shine yanzu take neman gafarataâ
Haka na kwashe firarmu gaba daya na fada mata irin halin rayuwar da ta ce ta shiga bayan rabuwarsu da Jibril, sai kuma na dora mata da bayanin abunda Jibril ya yi min kamin ya fada mata cewar ya ansallami Noor daga asibiti.
âJibril be kyauta ba, be da ce ya yi miki haka ba, ina tunanin ya yi haka ne saboda ya bata ki a gurin iyayen Bilal kuma suma ya saka musu fargabar wani abu zai iya faruwa da dansu matukar ya aurekiâ
âNi Inna na tsane Jibril bakin mugu ne Wallahi ni ya dawo min da yarona ba zan barshi ya kwana a can baâ
Na fada ina shirin fashewa da kuka.
âAi kara ki kyale Noor ya shaku da Ubansa tun wuri domin kin san dai Jibril ba zai ta ba bari ki je masa agolanci da dansa ba, ke ma kuma ba za ki ji dadin zaman auren ba matukar kika je da Noor domin Mahaifinsa zai rika amfani da wannan damar yana cin zarafinki da mijin da zaki aura, idan kuma mijin da kika aura ya nuna baya son zaman Noor ki ce baya son kiâ
âAllah ka min mafitaâ
Na fada a fili a zuci kuma na ce Jibril din nan yabi ya tare min ko ina bana da wani sakewa. Muna nan zaune su Sakina suka dawo daga islamiya sai muka dauko wata firar har take fada mana wai malaminsu ya ce satin saman za a kawo kudin da zasu ba iyayensu domin su cigaba da daukar nauyin karatunsu.
âWai Inna ba zamu koma sabon gidan nan ba?â
Ta tambaya, ni har na manta da maganar gida domin ban taba zuwa ma ganinsa ba.
âBa zamu koma ba, ko kudin nan ba zamu karba ba duk Jibril ne yake shirya wannan abun, saboda ya siye mu da dukiyarsaâ
âYa fada miki shine?â
Inna ta tambaya.
âA a amman na san shi kadai zai iya wannan abun, idan ba shi ba ne waye neâ
âNima na yi wannan tunaniâ
âDan Allah Inna karku sake karba komai na sa idan ya baku, Wallahi mutumen ya raina mana hankali sosai ma saboda ya maida mu talakawa, ai da masu kudi ne mu be isa ya taka mu baâ
âKin dai ce kin yafe masa, bana son wata rigima kuma bamu je muka rokeshi ya bamu ba bana son wata fitanar kumaâ
âBa zan yi komai ba ai, amman kawai abun yana ci na sosai Wallahi ya ci amanata sosai, kuma ya raina min da wayo da har zai ce ya wai yana neman ya sake aureni, Wallahi aurena da be so da Bilal sai an yi sai dai ya mutu azzalumi kawaiâ
Na fada cikin daga murya hawaye na zuba a ido, ji nake kamar ace Jibril yana kusa da ni yanzu na shakeshi ya mutu. Bayan mun yi sallah magariba na kira Bilal a waya sai ya dauka, na yi tsammanin zan ji shi a cikin wani yanayi marar dadi ko makamancin haka amman sai ya zo a kasin tunanina na jishi cikin farinciki da walwala
âYar halak kin kirani daidai lokacin da zan kiraki na ce ki fito waje gani nanâ
âBilal kai neâ
âNi ne mana, wani kika je kira ne kika kirani?â
âAa kawai na ji na cikin farincikiâ
Ya yi dariya
âCikin bakinciki kike son jinaâ
âAa kawai na dauka zaka ji haushi na ne kai da Abbahâ
âAkan me zan ji haushinki Nawwara, abunda kika aikata be kara min komai ba sai kaunarki, yanzu dai fito gani nan kofar gidaâ
Daga haka ya kashe wayar ni kuma na lumshe ido cike da jindadi na sauke ajiyar zuciya, sannan na fadawa Inna na dauki Hijabi na saka na fito kofar gida, jingine da ginin gidan na sameshi kamar kullum yana jiran fitowa.
âPearlâ
Na kalleshi fuskarta da murmushi.
âWallahi ban tsamaci haka ba ko kadan, na yi tsamanin Abbah zai maka fada neâ
âNawancy kenan, ya yi min fada sosai amman akan rashin kunyar da na yi ma Hajiyar Mustapha ba wai akan abunda ya faru ba, kuma ko da yayi min fada akan ai ba zan dora laifin akanki ba, shine ma ya bani shawarar karna fadawa Mama cewar kin je station domin ya fahimci muna son junan kuma idan Mama ta ji zata yi fadaâ
âNa gode Allah da Abbah ya fahimtaâ
âKuma ya ce na fada miki cewar Assabar din nan mai zuwa zai zo ya ga su Baba Sulaimanâ
Na rufe idona da sauri saboda dadi da kunya da suka rufe ni lokaci daya.
âDa gaske?â
âAa da karyaâ
Ya fada da fuskar zolaya, sai na sa dariya.
âMama fa mi ta ce?â
âMe kike tsammanin zata ce?Addu'a kawai ta yi mana da fatar Allah ya sa alheri a cikiâ
Na san yace haka ne kawai dan ya kareta amman ba zata so aurena da danta saboda tana ganin kamar kwaruwace xan yi ma danta bayan na yi aure biyu har da kuma yanzu na ce zan auri danta. Mun sha fira sosai a wannan daren sai da aka fara kiran sallah isha'i sannan muka yi sallama ba dan ran mu ya so ba ya tafi ni kuma na dawo cikin gida. Inna ta yi murna sosai kuma ta nuna jindadinta akan maganar har ma ta yi mana addu'a, daga baya kuma ta tambaya abunda iyayensa suka ce kan abunda ya faru yau, ni kuma na labarta mata kamar yadda ya labarta min.
Bayan mun gama sallah isha'i wayata ta yi ringing ko da na duba sai na ga number Rabi na yi mamakin kiranta a wannan lokacin sai dai hakan be hanani dauka ba.
âAssalamu alaikumâ
âWa'alaikissalam Nawwara kina gida?â
âIna gida lafiya dai?â
âLafiya kalau akan maganar nan ne, bana son na yi shigowar rana wani ya gan ne, alhalin kuma ba Oga Jibril ba ne ya aiko niâ
âYanzu zaki zo kenanâ
âIdan zan samu dama baâ
âAllah ya kawo ki lafiyaâ
Daga haka na kashe wayar sai ga kiran Jibril ya shigo wayata, da gangan na ki dauka saboda ina tunanin wata maganar zai min ta daban, har sai da ya yi min kira fiye da uku sai kuma ya aiko min da sako karta kwana wato sms cewar Noor ne yake son magana da ni, da ya sake kira sai na dauka cikin rashin walwalah saboda tsanarsa da na ke ji cikin raina.
âHelloâ
âBabe-Naj ga Noor zai yi magana ina fatar kina lafiyaâ
âZan bashi but ki amsa min mana ko sanyi na jiâ
âZan kashe wayar idan baka ba shi baâ
âAllah ya huci zuciyarki, ya dorani akan ki Najâ
Yana fadar haka ya mikawa Noor wayar.
âHello Momy ina wuni? Momy i miss youâ
âI miss you too miyasa ka bi Daddynka ba ka zo nan ba?â
âDaddy ne ya zo da ni, kuma ya ce ke ma za ki zo gobe, Momy ki zo yanzu mu kwana nan dan Allahâ
âBa zan zo ba Noor, gobe ma ba zan zo ba har abada ba zan zo ba, idan kana son zama da ni ka ce ya dawo da kai gidanmuâ
âSaboda me ba za ki zo ba?â
âSaboda nan ne gidanmu ni ba zan zauna ko ina ba sai gidanmuâ
âMomy gidan yana da kyau fa, har ya fi na su Sadiq kyau dan Allah ki zoâ
âBa zan zo ba Noor, idan kana son zama tare da mu ka ce ya dawo da kai gida gurin muâ
âMomy zan yi kukaâ
Ya fada cikin muryarsa mai nuna yana shirin yin kuka da gaske. Sai na ji muryar Jibril yana fadin
âNo no don't cry Noor tana maka wasa ne kawai zata zoâ
Ni kuma na katse wayar na kalli Inna.
âInna rabi zata zo yanzu, akwai maganar da zamuyi da itaâ
âWace magana ce?â
âWallahi nima ban sani ba, amman dai ta ce tana da muhimmanci sosaiâ
âDa wa kike waya yanzuâ
âNoor neâ
âAmman shine kike fada masa wannan maganar kamar wani babba? Kina son ki saka danki a damuwa ko? Ki raba masa hankali gida biyuâ
âAmman Inna ai kara na fada masa gaskiya saboda yasan ba zan taba zama da mahaifinsa ba tun yanzuâ
âAmman be kamata ki masa magana ta wannan hanyar ba, ki daina sauke masa haushin mahaifinsa akansaâ
âInshallah Inna ba zan kara baâ
âAllah ya kyauta gabaâ
Sai da na amsa da Amin sannan na tashi na soma duba dakin inda be kintsu ba kimtsa saboda kar Rabi ta zo ta tarar da dakin ba a natse ba.
Tara saura kwata ta Rabi ta shigo gidanmu da lullubinta na katon gyale kai baka ma ce ita ba ce, duka muka hada baki gurin amsa mata sai na fita na shigo da ita cikin dakin ta gaisa da Inna sannan Inna da su Sakina da Jamila suka fita waje suka bar mu mu kadai.
âIna tunanin babu wani gurin da ya kamata mu yi maganar nan sama da gidanku shiyasa na zabi na tarar da ke a gida, kuma idan da dare ba kowa zai gan ni ba balle har a tsammaci wani abuâ
âMe kike so mu tattauna mai muhimmanci har haka?â
âNa fada miki akan ki da kuma dan ki da kuma Noorâ
âMe muka yi?â
âBa ku yi komai ba sai dai wanda ake shirin yi mukuâ
âBan fahimta baâ
Ta sauke ajiyar zuciya.
âNawwara ke kadai ce mace da zata iya tsamo Jibril daga tarkon Siraj a yanzu, ke kadaice zaki iya raba alakar da ke tsakaninsa da Siraj a yanzuâ
âMiye nawa a ciki da har zan shiga na raba alakarsu? Babu komai fa tsanina da Jibrilâ
âNa san babu komai a tsakaninku a yanzu, amman ai akwai yaro tsakaninku, iya abunda na fahimta Oga Jibril yana son ki sosai, ke ce kadai zaki iya anrar da shi daga ramen da yake kokarin fadawaâ
âNi fa ban gane wannan bayanin na ke baâ
âNawwara Siraj ba abokin kwarai ba ne, kokarin zamewa Oga jibril kafafu yake ya dilmiyar da shi, kokarin kwace duk wani abu da Jibril ya mallaka yake kokarin ganin ya zama na sa.
Sunana Rabi'at Abdulrazak, ni ba bahaushiya ba ce ni ibira ce asalina ni yar jihar kogi ce, ina zaman gurin Antyna ne a Abuja bayan na gama karatu na, daga baya na samu aiki a kamfanin One on One limitless company da ke Abuja, da sannu na fara aikina kwarewata da kuma jajircewa ta a akan aiki yasa mahaifin Jibril wato Alhaji Baahir yake yaba min sosai kuma ya dauki yarda ya bani, lokacin da zai turo Jibril aiki a nan sokoto sai ya sa muka zo tare akan na rika kula da duk wani abu da Jibril yake yi saboda yana ganin kamar Jibril ba zai iya kula da kamfanin yadda ya kamata ba, da muka dawo nan sai Jibril yasa aka yi ma Siraj transfer daga Abuja zuwa nan, ban san cewa Siraj abokin Jibril ba ne sai a wannan lokacin, ba zan iya fada miki dalilin alakarsu ba domin ni ma ban sani ba, amman da aka dawo da shi nan sai Jibril ya dauki yarda da amana ya mika masa, idan be samu zuwa meeting ba Siraj yake turawa, komai za ayi sai ya ce a a nemi Sirajâ
Ta gyara zamanta kana ta yi dariya.
âBa ina kishin Siraj ba ne Nawwara, sai dai akwai abubuwan da na lura da su akan Siraj, ina tunanin kamar shi ya koya masa shan cocaine saboda ua haukarta shi ko kuma ya juyar da hankalinsa zuwa wani gurin ba dan damuwar Jibril kawai ba, idan har dan damuwa ce shi Siraj baya da ita? Miyasa baya sha sai Jibril yake bawa? Abu na biyu ni yake sa na kira mahaifinsa na fada masa dukan abunda yake gudana a kamfanin marar kyau, Siraj ne yayi kokarin kashe Noor saboda yana tunanin idan har Jibril ya san yana da da zai sashi ya daina abunda yake kuma ya natsu, wanda ba haka Siraj ke so ba kuma yana ganin kamar idan Noor yana raye dole wata alakar zata sake kulluwa tsakaninki da Jibril wanda baya son haka shi be ki ma Jibril ya mutu ya mamaye dukiyarsa ba, da hadarin ya faru sai ya dorawa Bilal laifin ta hanyar sanar da Jibril cewar wani ya fada masa cewar Bilal ne ya yi kokarin kashe Noor saboda yana bakinciki Jibril, wannan yasa Jibril ya koreshi daga aiki har ma yayi kokarin kai kararsa kotu amman sai Siraj ya hana a cewar su wai basu da hujja su jira har sai an samu wani abun na daban wanda zasu rike su yi hujja da shi, ke kanki rayuwarki tana cikin hadari domin Siraj zai iya sawa a kasheki kuma a kashe Noor saboda Noor ya ga fuskarsa lokacin da ya yi kokarin kadeshi da mota, ya yi nadanar hakan kuma ya ji bakinciki sosai da Noor be mutuba, daga baya kuma sai ya wani tunanin ya zo masa cewar miyasa be sa wani ya aikata ba sai shi ya aikata? Wannan ya tabbatar da cewar nan gaba ba da kansa zai je kashe ki ko Noor ba wani ko wasu zai sa su yi, yana tunanin idan ya yi haka shikenan ya gama da rayuwar Jibril sai kuma ya yi amfani da cocaine ya karasa halaka shi.
Na san zaki yi mamakin jin haka ko kuma ki yi mamakin a ina na san duk wannan ko? Na sani ne saboda Siraj ya fada min, yana amfani da ni ne a matsayin wacce mahaifin Jibril ya yarda da ni, ya ce min zai aureni kuma duk abunda ya samu zai raba rabi ya bani rabi abunda yake kokarin yi yanzu ya mallaki nasa kamfanin ta karshin wannan kamfanin, a yanzu haka mahaifin Jibril ya sauke Jibril ya dorashi akan kamfanin kin ga ya fara samun dama kenan, ni kaina rayuwata tana cikin hadari domin mugun mutum baya yarda da kowa, ni kaina xai iya cutar da ni idan ya samu abunda yake so, saboda yana ganina kamar ba bahaushiya ba yasa yake son ya yi amfani da wannan damar ya cilla burinsa saboda yana ganin kamar muna da son kudi kuma idanuwana a bude suke, na masa na amince ne saboda na san idan har na ki amincewa zai iya kashe ko ya kulla min wani