Showing 138001 words to 138998 words out of 138998 words
yarda da wannan ba shiyasa kullum cikin kwaliyata na ke da yin duk wani abun da zai daukewa Jibril hankali, ban yarda akwai wata mace da zata iya daukewa hankalin mijina ba, sai dai ni na dauke masa hankali daga wasu matan, idan yana gida ina makkale da shi, domin yarana sun bude ido sun ganni tare da Abbasu so na abun mamaki bane idan na kwanta a jikinsa kamar yadda dukansu wani lokacin suke zuwa mu kwanta tare
mu tausheshi muna dariya.
Idan kuma baya gida to waya tana kunnena ina jin labarin duk wani abu da ya gani a waje, kamar yadda nima nake labarta masa dukan abunda na aikata a gidan matukar ba aiki yake ba. Sakwannin barka da safiya kan sun zame min kamar jiki dole ne kullum sai na tura masa a waya, ko kuma na rubuta masa a paper ma aje masa.
Goodnight massage kuma kullum sai na tura masa kamar yadda shi ma yake turo min, wa zai ga rayuwarmu a yanzu ya ce mune a wacan lokacin? Lallai na yarda Kaddara ta riga fata!
Kamar yadda aka rubuta a iv yau ce ta kama 23 ga watan November, yau ake daura auren Sakina da angonta wato Mahmoud, hakan yasa na tashi da wuri na yi duka aikina amman hakan be hanani yin latti zuwa gida ba domin Jibril ya yi rantsuwa ba zan bar gidan ba sai na gyara masa ko ina kuma sai na tafi da yara kamar yadda yake min a duk lokacin daya fuskanci bana son zuwa da yara gida. Ko da tara tayi na gama komai na yi ma yara wanka ni ma na yi. Aai dai ba mu shirya ba domin bana son au bata atamfar ankonsu tun yanzu kara su kara wasu tufafin da aka dinka musu na cin biki kamin mu isa can.
Muma tsaye harabar gidan gurin mota muna jiran fitowarsa ya aje mu gida domin direbansa baya nan yana can ana hidima da shi ni kuma ya ki yarje min na toka motata wai a ganinsa ban gwari yadda ya kamata ba, hakan yasa indai da yaransa zan je yawo baya bari na yi driving sai idan ni kadaice ko kuma ni da shi. Farar shadda ce a jikinsa ta karbeshi sosai kai ka ce ma shine angon, fuskarsa sai annuri take, yana ta kamshin turare. Kallo daya na yi masa na ji kaunarsa ta kara shiga zuciyata, hakan yasa na kasa dauke idona akansa har ya shiga motar ya yi mata keys.
โWannan irin kallo haka barakkala Masha-Allah karki cinye niโ
Sai duk muka sa dariya har yara da suke bayan mota. Ni dai ban ce masa komai ba har muka isa gida yana aje mu ya wuce gurin daure aure da aka ce goma na safe za ayi. Mun yi biki lafiya mun kare aka kai Sakina Birnin Kebbi gurin da Mijinta yake aiki, kasancewar mai mata ne ta aura sai dai asalinsa shi ma dan sokoto.
Ranar data zagoyo Assabar babu kowa gidan sai ni da Jibril, a ranar muka sha soyayyar kamar wasu sabbin ma'aurata, washe gari shi ya girka mana abun karyawa domin ni ban tashi ba sai da rana ta fito. Haka muke a duk lokacin da yara basa nan sai abunda muka manta ne kawai bama yi amman ko wace irin kulawa da soyayyar na yi kokarin nunawa mijina kamar yadda shi ma yake muna min, muna jindadin zama da junanmu sama da yadda duk wani mai tsammani yake tsammani, ba mu da wata fargaba ko tunani a zama da muke da juna,muna karan junanmu da sunan da yayi mana dadi, idan kuma yana fushi da ni nasan irin sunan da yake min ka kaka da kakkani, ko ya kira da wani suna a cikin kayan girki, nima kuma na akan masa wannan lakanin kamar yadda yake min.
Al-hamdulillah a ko yaushe na kan yi ma Allah godiya da ya bani miji kamar Jibril domin ni da shi RAI BIYU ne bayan RAI BIYU da na rasa wato Habiba da kuma mahaifina. A yauzu a kullum ni nawa godiya ne a garin Allah.
___________________________
Al-hamdulillah nima na gode Allah daya nani ikon gama RAI BIYU Lafiya, duk da kasan ba kuso ya kare a haka ba ko kuma na ce a yanzu ba, ku gafarci idan akwai idan na bata musu rai tun farkom fara rubutun nan zuwa yau, ma gode da irin goyan bayan da kuka bani da kuma juriyar karanta lattafin da ba ayi editing ba.
Mu tara a littafi na gaba mai suna HAFSATU MANGA yarinyar kauye kuma labarin kauye kuma labarin sarauta mai sarkakiya da ban dariya da kuma tausayi, sai dai shi ba Free ba ne kamar wannan, HAFSATU MANGA na kudi ne, kuma ina fatar zaku bani hadin kai kamar yadda kuka ba ni a wannan, da ma sauran da zasu zo a gaba.
Godiya ta musamman gareku Whatsapp people baki ba zai iya gode musu akan irin soyayyar da kuka nuna min a littafin nan, sunanyenku ba zai lisafu ba amman ina son ku san cewa Khadeeja Candy tana son ku so na hakika. Gaisuwa da yabo gareku Wattpad readers I really appreciate your votes your comments your support, thank you so much, I love you All fisabilillah.
Littafin nan Sadaukarwa ne gareki Asma'u My Asmee Allah ya bar kauna da zumunci mai dorewa har Aljanna.
Ga Mai son siyen Littafin Hasfatu manga wanda zaizo nan da one month Insha-Allah ba wato 2020 zai iya nemana ta wannan line 08036126660, ta layin zaku iya turo min gyara ko kuma shawara akan littafin RAI BIYU da ma wasu littafan da suka gabata ko kuma masu zuwa nan gaba, I thank you so much my fans without you guys there's no Khadeeja Candy ๐
LTTAFAINA MASU ZUWA
HAFSATU MANGA (Labarin kauye)
KILAKI (Karuwa)
HASKEN ANNURI (the light and darkness)
And many more....
Best regards ๐
Khadeeja Candy
One heart
One love.
#Don't forget to follow me and also add Hafsatu manga to your library, thank you all stay bless ๐ช๐