Showing 12001 words to 15000 words out of 138998 words
ina tsayuwa da shi ba, saboda ƴan sa idon unguwa. Shi kansa ya lura da hakan sai yayi min sallama ya tafi ni kuma na dawo cikin gida.
Bayan Sallah isha'i nake labarwatawa Inna maganar aikin har ma na nuna mata wayar da Bilal ya bani.
“Allah ya bada sa'a”
Kawai tace min ta jingina da gini tana jan carbi, wanda hakan san be min daɗi ba, Habiba ce kawai ta zo ta zauna kusa da ni tana tambayar yadda aikin yake. A cikin dare na ɗauko tsohon layina na saka a wayar da Bilal ya ba ni.
Washe gari ta kama ranar alhamis, ranar na tashi da azumi, daman duk litanin da alhasmis na kan yi azumi wani lokaci, musamman yanzu da ya zama ba komai na ke ci ba idana ban yi azuminba zan wuni da yunwa ne kawai.
Misalin bakwai na safe na ɗumama su Jamila tuwon shinkafar da na yi musu jiya miyar kuka, Inna kuma na dama mata kunu ita da Habiba saboda shi kaɗai suke iya sha ko da rana da dare kuma ruwan tea. Bayaɓ na gama na je yani wanka na shirya ciki wata farar atamfa na saka baƙin Hijabi sai kuma tsofi takalmi waɗanda suka kasance baƙaƙe sannan na sake dawowa ɗakin Inna na same ta har lokacin tana shan kunu.
Jaƙar da muke ajiye kayan karatu na buɗe na ɗauki takarduna na makaranta na buɗe ina duba tare da tunatar da Habiba maganar zuwa makaranta.
“Ya kamata ace kin je makaranta gobe ko kuma monday nan mai zuwa, yau kusan kwana nawa baki je ba, kuma jarabawa kuke fa, gashi rashin zuwanki ya haddasa har su Sakina sun daina zuwa”
Ta turo baki.
“Ni ba zan sake zuwa ba, karanta mo zai tsinana min, ko na yi karatu ba zan wuce babbar makaranta ba, kema da kike da ssce min kika amfana da shi”
Murmushi na yi, nasan tana tunanin babu wanda zai iya ɗaukar ɗawainiyarta ne da har zata yi babbar makarantar gaba da secondry, tun da karatun ya zama sai da kuɗi.
“Na miki alƙawari zan ɗauki nauyin karatun ki, ke dai ki dage ki cigaba da wannan ki kammala sai kije babbar makaranta”
“Ta yaya?”
Ta tambaya tana hararata irin bata yarda ɗin nan ba.
“Wannan aikin idan na samu zan riƙa aje wani abu daga albashina saboda ke Habiba”
“To Hajiya bari har ki samu”
Ta faɗa tana ɗaukar Noor ta ɗora saman ƙafafunta. Ni kuma na yi murmushi na kalli Inna na ce
“Ni zan ta fi Inna”
Fillo ta ɗaga ta ɗauko ɗari biyu ta miƙa min.
“Ki hau Napep, karki manta da nasihar da mahaifinki yake miki akan mutuncinki Nawwara”
“In'sha Allahu”
Na tashi cikin jiki ba ƙwari na fita. Yau kan sai da na yi nisa sosai sannan na samu Napep, kai tsaye na kwatanta masa inda zai kaini wato koko road.
Nesa da Company ya sauke ni na bashi kuɗinsa, sannan na aikawa Bilal please call me kasancewar babu ko na flashing a wayar, sai ga shi ya kirani cikin ƴan mituna, na sanar masa ina kusa da gurin.
“Ki ƙaraso mana gani nan fitowa”
Bayan na amsa masa da okay na doshi company gaba sai dukan uku-uku yake, wata ƙila ko dan ban taɓa zuwa babban kamfani kamar wannan ba oho..
*ONE-ON-ONE LIMITLESS*
_One of the Largest Metal Companies in the world_
A hankali na karanta, ina ƙara faɗaɗa ido ga kallon ƙofar gate ɗin company ma da ta kasancewa ƙatuwa.
‘Anya za su ɗauke ni aiki kuwa’
Na tambayi kaina ina kallon securities da ke bakin gate ɗin sanye da uniform kamar na ƴan police sai dai na su farar rigace sai baƙin wando. A ƴar ƙaramar ƙofar da ke gefen gate ɗin na hango Bilal ya fito sai sauri yake ya doso inda na ke.
*RAI BIYU...♥️🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣0⃣
Na ɗan faɗaɗa fuskata da murmushi kaɗan na kuma gyara tsuwata. Shi ko haƙoransa a watse har ya ƙaraso kusa da ni.
“Miyasa baki shiga ciki?”
“Waɗannan jibgin securities ai ba za su bar ni na wuce ba”
“Haka zuciyarki ta nuna miki, ai su aikinsu tsaro ba hana mutane shiga ba, kin tsorata ne?”
“Sosai ma”
Sai kawai yasa min dariya har da tintsirawa.
“Haba sai ka ce wacce bata zauna ƙasashen turawa ba, ai zaki saba da su ne, amman fa zan yi fama da kishi dan suna sakewa da mata sosai”
“Kishi?”
Na tambaya cike da mamakin kalaminsa, haka wani lokacin ya ke sakar min magana kamar mai suɓul da baka.
Sai kawai ya shafa fuskarsa be bani amsa ba ya zuma hannayensa aljihu ya kama hanya.
“Mu je”
Kai kawai na kaɗa, na bi bayansa yana gaba. Faɗuwar gabana ne ya ƙaru yayinda da muka doshi ƙaton gate ɗin nan, yana isa suka buɗe masa ƙofar da biyo ɗazu ya wuce suna zolayarsa ni kuma ina bayansa.
Tafiya mika mai nisa sosai sannan muka isa katafaren kamfanin, hakan ya bani damar kallon gurare da dama a harabar gurin, daga dama wani ɗan madaidaicin guri ne mai kamar ma'aikata an rubuta masa RESTAURANT, sai kuma wani ƙaranin gate dake can hagu an rubuta masa PARKING SPACE, a can gefen gurin kuma an wani gate ne mai zagaye da falawoyi an rubuta masa GARDEN GROVE. Duka cikin manyan harufa masu ƙyali da burgewa.
“Gurin nan na da girma sosai Bilal”
Na faɗa ina kallon gaban kamfanin da duk madubi har takalminka kana gani a ciki da duk wanda zai zo bayanka, gida sama ne mai hawa biyar, na gane haka ne ta windows ɗin dana ƙira, hawa-hawa har biyar.
“Yeah kin ga can gurin cin abinci ne, can kuma duk wani mai abun hawa can zai aje shi, garden kuma gurin hutawa ne ko kuma fira ko meeting haka, kamar idan wanda ba ɗan kamfaninba ya zo ganinka zaku iya tsayawa a can ku yi firarku”
Ya ƙarasa yana nunnuna min guraren, ni kan sai bawa idona abincin na ke, gaba ɗaya na zama baƙauya sam ba zaka taɓa cewa Nawwara ce wacce ta taɓa zama a London ba, ko da yake shekaru da yawa yanzu na zama baƙauya. Ƙofa biyu ce a gurin ko wacce ƙatowa, ɗaya a dama ɗaya a hagu mutane na ga suna ta shiga da damar masu fitowa kuma na fita ta hagun, muna ƙarasawa sai ƙofar ta buɗe mana da kanta a ƙasan gurin inda mutun zai ɗora ƙafarsa an rubuta WELCOME ɗa manyan haruffa masu ƙyali. Tsaye na yi ina kallon yadda mutane ke zirga-zirga ba dan ina tare da Bilal ba dan zan iya rantsewa wata ƙaramar duniya ce na shigo, kamin ka shigo fuskar kamfanin duk madubi ce cikinsa kuma komai kamar zinari yake, ga wasu manya-manyan plasma da ke tallata abubuwan da kamfanin ke yi.
Reception ne ke facing ɗin duk wanda ya shigo, ma'aikatan gurin na sanye da suit maza da mata. a dama da Reception ɗin manya lifted ne guda huɗu, a hagu kuma Excavator ne babban guda biyu na hawa da kuma na sauka, a can gefe kuma wani ƙaton guri ne mai kamar falo an jera ƙasaitatun kujeru ga plasma a gurin, ko ina security camera ne a gurin, ac ta ko'ina ratsa jikin mutum ya ke.
“Nawancy...”
Kiran da Bilal ya yi min ne ya dawo da ni hankalina, har na kalli inda ya dosa, na rufa masa baya da sauri. lifted da ke farko ya danna, sai da muka yi tsayin minti biyu zuwa uku sannan ta buɗe mutun uku daga cikin lifted suka fito sannan muka shiga, bayan mun shiga muka juyo muna fuskantar ƙofar sai ya kai hannunsa a maɓallan da ke gurin ya danna number four, sai lifted ta rufe.
“Wow...”
Na furta ina lumshe ido. Sai kawai Bilal yasa min dariya, har da ciro wayarsa yana ƙoƙarin min video. Lokacin da lifted ta buɗe mun tarar wasu na jiran mu fito ta su shiga. A nan na ma ashe wata duniyar ce, da komai na ta na glass ne, mutane sun kasu kashi-kashi, wasu na ta aikin akan documents wasu na gaban computer.
“Haka aikin na ku ya ke?”
“Yeah nan na masu diploma ne, kin san mu NCE ne da mu muna hawa na biyu”
Yana min maganar muna cigaba da tafiya har muka isa wani ƙofar wacce kana tsinkayar wanda ke ciki shi ma kuma yana tsinkayarka. Buɗe min yayi na shiga sannan shi ma ya shiga ya nuna min gurin zama, yana mikawa wanda ke gaban conputer hannu su gaisa.
“Manir”
“Ya Bil ya aikin?”
“Ba daɗi, ga baƙuwar da na ce maka zata kawo takardunta”
Wanda aka kira da Manir ɗin ya juyo yana min wani kallo baki a sake.
“Wow Welcome Ma'am, gaskiya tana da kyau sosai gata fara mashallah”
Bilal ya shafa yancinsa yana satar kallona fuskarsa ɗauke da murmushi, yanayin yadda Manir ɗin ya yi min ya karantar da ni kamar akwai abunda Bilal ɗin ya ce masa a kaina.
“Sannu ya aiki?”
“Hooooo i beg see golden eyes”
Ya furta yana ba Bilal hannu su taɓe. Na yi ma Bilal wani kallo da shi kansa ya san ba na lafiya ba ne, sai kawai ya miƙa hannu ya karɓi takardun hannuna ya miƙa masa.
“Gashi ka shigar da bayanan mu zamu wuce”
Ya miƙa hannu ya karɓa yana dariya.
“Okay ba matsala, Allah ya sanya alheri ya tsare, perfect match”
Har na buɗe baki na ce wani abu sai Bilal ya yi saurin buɗe ƙofar.
“Muje Nawancy”
A dole tasa na miƙe tsaye na nufi ƙofa, ƙamin na ƙarasa sai yayi saurin tare ni.
“Sorry Nawancy bari Oga ya wuce”
“Wane Oga?”
“Mai kamfanin”
Jin hakan yasa ni miƙa wuya dan na hango mai tarin wannan dukiyar, sai dai ban yi sa'ar ba dan har ya shige Lifted. A nan Bilal ya ba ni hanya na fito muka jera muka nufi lifted da muka shigo ɗazu, ƙashim turaren da na ji ya sani faɗuwar gaban da har ya haddasa min ciwon kai a take, saboda na tsani wannan ƙamshin kamar yadda na tsani mutuwa, jin sunan turaren kaɗai zai iya haddasa min hawan jini saboda tunawa da mai shi.
“Wannan da ya wuce ogan mu ne, mahaifinsa ne ke da wannan kamfanin, shi baya son idan na zo a lifted kai ma ka zo, sai dai kowa ya ja baya har sai ya zaɓi wacce zai shiga idan ya shiga sannan kowa ya shiga, kuma baya son yaga mutun ba a gurin aikinsa ba, abu kaɗan kan iya sakawa ya ƙoreka aiki, ba shi baya ɗaukar ƙaddara idan kika fasa masa kofi sai an cire cikin albashinki, ba a latti zuwa gurin aiki, minti ɗaya kika ƙara daga lokacin da kike zuwa aiki sai an rubuta, da kin yi haka sau goma sha biyu zai koreki, idan wata matsalar ta same ki sai kin faɗi dan wuri ki rubuta takardarki ki aika idan ba haka ba zai koreki”
“Kai amman ya cika tsauri, sai kace turai”
“Gashi ba shi da dariya, kuma baya son kallo”
Na haɗe yawu ina jijina lamarinsa, domin nima kaina bana son kallo. Ya cigaba da ba ni labarin kamfanin da kuma yadda suke abubuwansu har muka iso bakin ti-ti.
“Kamfani da ke saffara duk wani abu da shafi ƙarfe, kuma kamfani da ke siye da sai da hannu jari, ga kwangiloli kala-kala kamfanin yana yi, kuma akwai wasu ƙananan kamfaninni da suke ƙarƙashin kulawarsa”
“Ayyah za su ɗauke ni aiki kuwa?”
“Za su ɗauke ki kan, amman sai kin yi haƙuri da kuma kin jure ba a makara ba a ɗauke ƙafa, kuma ba a kuskure”
“I will try”
Sama-sama yake ta labarta min abubuwan akan kamfanin, kamin ya tarar min Napep, ya faɗa masa inda zai kai ni, ya miƙa masa dari biyar ya ce ya bani ragowar canji.
Ni kan jikina har rawa yake na isa gida na labartawa Habiba abunda idanuwana suka gani da kuma ji.
My page is depend on your comments, ku da kuke cewa ina short page don't blame me, blame your comments 😂
Idan an gama karatu sai ku zo ki siya garin ɗan wake, da kuma ƙwaryar kwaliyar ɗaki ko falo da faifai duk domin ƙawata ɗakinki. Ga mai sha'awa sai a ku nemi number nan 08036126660 muna aikawa ko'ina a arewa cin ƙasar nan.
Tau Lemme come and be going 🚶....
*RAI BIYU...♥️🖤*
Wattpad @Khadeeja_Candy
1⃣1⃣
Tun da na baro kamfanin sai komai na titi ya riƙa burgeni, idanuwana har yanzu kallon komai suke kamar kamfanin wata ƙila saboda labarin da ke ƙumshe a bakina ina son na labarta musu Habiba da Inna yadda gurin ya ke da kuma aikin shi kansa.
Tunawa da zancen Bilal ya sani dariya tare da furta sunansa a fili.
“Bilal kenan wai zan sha fama da kishi”
Ajiya zuciya na sauke ina tuna irin kallon da Mutune yake min ɗazu, lallai da akwai abunda Bilal ya faɗa masa akaina.
“Sauke ni a nan”
Na faɗa ganin Mai Napep ɗin yana ƙoƙari wucewa ta har cikin unguwarmu, ba kasafai na ke son napep ko achaɓa ya sauke ni ƙofar gida ba.
“Ba ni canjin”
Ya buɗe akwatinsa na kuɗi dake cikin napep ɗin ya ɗauko ɗari uku ya miƙa min, ni ko na ƙi karɓa.
“Haba Malam ya zaka ɗauko ni daga Koko road ka kawo nan kawo nan arƙila kuma ka ce zaka cire har ɗari biyu”
“Haba Hajiya kuɗin nan fa Mai gidane ya bada su ba ke ba, miyasa ku mata kuke son tauye mu ne wai”
Hannu ya kai ya ɗauko naira hansin ya miƙa min, ina ƙoƙarin karɓa na ji takun mutun a bayana yana katsawa mai napep ɗin tsawa.
“Kai wane irin mahaukaci ne zaka kawo mashin ɗinka a nan ka tarewa mutane hanya nonsense mtssssss”
Juyowar da zan yi sai idanuwana suka yi arba da Mustapha, mutun na biyu da na tsana a duniya, ba da ni yake maganar ba amman sai na ji kamar da ni yake saboda tsanar da na yi masa da kuma sanin yadda baya ɗaukar kowa da mutuncin a unguwarmu.
Tassss na wanke masa fuska da mari sannan na katsa mashi tsawa kamar wata uwarshi.
“Haka kuke ba ku ganin kowa da mutuncin, kowa a gurinku wulaƙantaccene, uban kowa baka ganin mutuncinsa a unguwarnan, sha-sha-sha marar tarbiya”
Mamaki da al'ajab ya kafe shi a gurin ya kasa ko da motsa idonsa balle ya yi wani motsi. Ni ko a zuciyata tsoro fal marata har ta cika da fitsari, amman a zahiri kallonshi na ke kamar yadda shi ma yake kallona sam ba zaka kalli fuskata ka gano akwai alamar tsoro a tare da ni ba.
Matsowa ya yi kusa da ni ya ɗaga yatsansa ya nuna kamar zai yi magana sai kuma ya cige bakinsa ya yi ƙwafa ya juya koma cikin motarsa, ribas ya yi ya koma inda ya fito da alama ya fasa shiga unguwar ma.
Sai a lokacin na samu sa'idar sauke ajiyar zuciya na juyo gurin mai Napep ɗin na karɓi hansin ɗin da yake miƙa min.
“Kai amman ke wannan ƴar bala'i ce, Allah ya raba mu lafiya”
Ba shi kaɗai ba ko mutanen da ke kusa da mu sun yi mamakin yadda na wanke mutun kamar Mustapha da mari, ni ba mafaɗaciya ba, kuma kowa yasan halin Mustapha a unguwarmu, ni kaina sai a yanzu na ke jin kamar ba ni ce na mareshi ba, wata ƙila kuma saboda na tsane shi ne shiyasa har idona ya rufe haka.
Sai dai mamakina yadda ya ƙyale ni be rama ba, yaron da harararsa ma baka isa ka yi ba saboda yana taƙama ubansa wani ne a cikin garin sokoto. Da wannan tunanin da kuma mamakin dalilin ƙyaleni da ya yi na iso gida, duk wani ɗuki da na ke na labartawa su Inna gurin aikin sai ya kau saboda wannan abun da ya faru tsakanina da Mustapha ya tsaya min a rai.
Ko da na shiga na samu Habiba tana da fa shimkafa da wake, Sakina na daka barkono (Yaji) Inna kuma na ɗaki kamar kullum.
“Har kin dawo ashe ba a daɗewa”
Cewar Habiba tana ƙara tura itacen murhu.
“Eh kin san da yake ba aikin ba ne, takardun ne kawai za a kai”
“Allah ya baki sa'a ya sa su ɗauke ki”
“Amman Babban Kamfanine Habiba, ba lallai ne su ɗauke ni aiki ba”
“Zan riƙa tufa musu fatiha a tsakar dare”
Na yi murmushi, kana na doshi ɗakinmu dan cire mayafina. Bayan na fito na doshi ɗakin Inna, ita na fara labartawa yadda kamfanin yake kamin Habiba ta shigo mana da abinci mu soma ci gaba ɗayanmu, ko lokacin da Baba na dai baya ƙwanar ya ga mun raba abinci daga manyan mu har ƙanana, sai dai kowa ya wanke hannunsa a ci a guri ɗaya, yana yawan faɗa mana cin abinci tare yana saka zumuncin da nishaɗi da kuma son juna, kuma ta nan zaka iya karantar halin mutun da lurar shi irin cin abincin da ya dace ya yi. Hakan yasa suka muka saba bama iya raba abinci inda wanda za a ci ne, ko da ɗayan mu baya nan sai mun jira ya zo ko da kuwa Jamila ce ita da ta kasance ƙaramarmu, balle kuma Noor da ko ina muka je baya cin abinci sai da ni matuƙar ina gurin.
Na bijiro musu da zancen marin da na yi ma Mustapha, a take hankali Inna da Habiba ya tashi har ma da Sakina
“Ina ruwanki Nawwara ai ba da ke yake ba, kuma ko da ke yake ai kya shafa kanki lafiya ki bashi haƙuri, yanzu wannan abun da ya faru da mahaifinku be isheki ishara ba? So kike ki ƙara jawo min wani?”
Cewar Inna. Habiba kuma ta ɗora da cewar
“Da ma ba ki mareshi ba Nawwara, kar ya ce kuma zai miki wani abun, kin san halinsa idan ma ya ƙyale iyayensa ba za su ƙyale ba”
Ganin yadda hankalin Inna ya tashi ƴasa ni yin ƙarya.
“Ke wasa na ke daman kawai ina son naga yadda zaku yi ne, ban mare shi ba kuma da ya zo yana faɗa da mai Napep ɗin ma na bashi haƙuri”
“Da Gaske?”
Na gyaɗawa Inna kai ina dariya saboda ta yarda. Sai dai na lura da Habiba kamar bata yarda da ni ba, har muka gama cin abincin ban ga yanayin Inna ya dawo dai-dai ba.
Bayan sallah la'asar Jidda ta shigo gidanmu, a lokacin ina zaune waje ni da Habiba Inna kuma tana ɗaki, Sakina da Noor da Jamila suna islamiya. Kusa da ni