Showing 129001 words to 132000 words out of 138998 words

Chapter 44 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

759

mana rana ban taba daga waya na kira Jibril ba, shi ma kuma be kirani ba ko gaisawar da yake da Noor sai ya daina. Idan har zai yi wata magana da ta shafi auren sai dai ya kira Baba Sulaiman, idan kuma ya bukaci ganin Noor sai ya aiko da direbansa ya daukeshi a akai masa shi.

Bilal kuma ban sake saka shi a idona ba, duk da ba fita na ke ba tun lokacin da aka saka min rana, Mama Turai ce take zuwa tana bani shike-shike na itatuwa da wasu abubuwa wasu na kan sha saboda fadan da take min, wasu kuma da na kafaici idonta sai na zubar. Ni dai bana shirin komai duk wani shiri daya danganci auren Inna ce take yi tare da Sakina da Jidda sai kuma yan uwnata da kuma yan Babban gida.

Ina jin yadda suke shirya za su yi walima ni dai Uffan ban ce musu ba, a nan naji cewar Jibril ya ce ranar da aka daura auren zan tare, ji na yi kamar na rabe biyu saboda bakinciki. Kallo daya zaka min ka fahimci cewar bana son auren. Ana sauran kwana uku a daura auren familyn Jibril suka kawo danyin abinci kama daga shinkafa da duk wani abu da za a sarrafa a ranar bikin, sannan suka bada kudi mai yawa na hidima. Cikin kudin ne Inna ta diba ta gyara gidan aka cike inda duk da fashe aka shafe gidan sam kai bama ka ce gidan mu ba ne.

Yau ta kama Assabar ranar da aka saka dauren aurena da Bilal, yau na tashi cikin damuwa da tunani, tun bakwai da rabi na safe Bilal ya turo min sakon da ya hanani sukuni.

_I love you so much Nawwara, na yi abunda na yi ne saboda ki samu farinciki, ni san Mama ba zata taba bari ki samu farinciki a gidana ba ina miki fatar alheri_

Ina gama karanta sakon hawaye suka wanke min fuska, wani abu marar dadi ya zo ya tsaya min a zuciya.
Karfe Goma dai dai na safe aka daura aurena da Jibril, a lokacin ne na fara kuka kamar an min mutuwa a ranar sai da na fita ran kowa daga Inna har yan uwan babana da yan'uwanta duk suka kasa fahimtata, Mama turai ce ta yi min fada sosai hakan yasa na daina kukan na koma yin na zuci.

Da hudu na yamma aka yi walima a a Women development center, walimar da ta bawa kowa da mamaki saboda kayan da aka rana, ko da yake wasu sun riga sun ji cewar mai kudi zan aura, daman na san wasu gulma ce ta kaisu domin ni bana shiga mutane balle kuma biki amman aka taro sosai ga yan uwan Su Jibril suka yi nasu takeaway daban suka rabawa mutane. Malama Aisha ta yi nasiha sosai akan zamankewar aure da kuma hakuri da tsabta nidai duk abunda take fadi jinta kawai na ke dan ban shirya yi ma Jibril ko daya ba.

Misali takwas na dare ya aiko da motoci daukar amarya motocin har sun yi yawa, Jidda ce ta cilasta ni ta yi min kwalliya ba dan na so ba, ta dauko min wata farar farar atamfa na saka, bayan na saka Inners farare sannan na saka fararen takalmi da farin gyale, Inna na min nasiha tana kuka kamar yadda nima na ke yi, sai aka wuce da ni babban gida su Baba Sulaiman da Yakunbo suka min tasu nasihar sai aka saka ni a mota ina ji ina gani aka dauki hanyar Sama road da ni. Na yi zaton gidan kai tsaye za a wuce da ni ganin ni bazarawa ce amman sai da aka biya wani babban gida inda yan uwan Jibril suka sauka aka kaini gurin Step mother dinsa da wasu kanen mahaifiyarsa da gwaggonsa suka min nasiha sannan aka sake sani a mota. Ba mu yi tafiya mai nisa ba muka isa wani katon gida mai farin fentin da gate golden color, ko ina na gidan haskene kamar da rana.
Ana fitowa da ni daga mota na done kaina kasa ban sake dagawa ba har aka shiga da ni bedroom din gidan, da kafar dama na shiga kuma tare da bismillah. A tsayar gadon na zauna fuskata a bude hawaye kawai na ke ganin hakan yasa Jidda ta ja min mayafina ta rufe min fuska, yan uwansa suna ta daukata hoto wasu kuma na ta kokarin ganin fuskata sai Jidda ta hana.

Bayan kamar minti arba'in Jibril ya shigo tare da abokansa sai zolayarsa suke, a gafe gado ya zauna, sannan wasu daga cikin abokansa suka shiga yi mana nasiha daga karshe suka rufe da addu'a. Ina jin lokacin da suka fita tare da nawa yan uwan da kuma Jidda, suka bar mu mu kadai a cikin dakin. Mun kusa minti talatin daga ni har shi babu wanda ya ce da wani uffan, baka jin komai sai shesshekar kukana.
A hankali na ji ya kai hannunsa ya yaye mayafina ya dago fuskata, hawaye yake kamar yadda nima na ke yi.


“Ki yi hakuri Nawwara na san ba ni kike so ba, na san na yi miki kutsu a rayuwarki, amman ina da tabbaci zaki auri Bilal nan da wani dan lokaci kadan, da shi zaki yi rayuwa dawwamamma irin wacce kike so”

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya cigaba.

“Ada na yi tunanin idan an aureki zan kasance a cikin farinciki, amman wannan hawayen da na gani a idonki ya sani jin babu dadi kuma ya sani jin nadamar cilasta miki aurena”

“Ba zan taba son ka ba Jibril, ka rabani da komai nawa, idan har kana da kunya a idonka ba zaka taba kai hannunka ka taba jikina ba, jikin macen da ka hada hotonta da wani ka ce karuwa ce mai neman maza da aurenta, ka rabani da mutumen da yake so tsakani da Allah saboda kawai ka samu farinciki, to bari na fada maka, ka kara matsowa da mutuwarka da bakinciki da damuwa da nadama a kusa da kai”

Na fada ciki kuka. Sai ya yi saurin dauke kansa ya sauke wani numfashi da alama maganata bata masa dadi ba. Tashi ya yi tsaye ya cire Babbar rigarsa ya aje.

“Taso mu yi sallah”

Ya fada cikin muryar da ke nuna rashin jindadin da ke cikin ransa. Ban masa musu ba a nan na sauko saman gadon sai ya wuce gaba ya nuna min inda bandaki yake ya bude min, na shiga ciki na yi alwala ko da na fito ya shinfida carpet da alama shi da alwalar ya shigo.
Wardrobe ya bude ya dauko Hijabi ya miko min na saka sannan ya yi gaba ni kuma ina baya ya kabbatar sallah nafila.
Bayan mun gama ya yi addu'a nima na yi tawa addu'ar sai juyo ya rika goshina ya soma karanta addu'ar da annabi ya koyar da mu wacce miji yake rika goshin matarsa ya karanta saboda niman tsarin da zaman lafiya.

اللَّهُمَّ إِنِّي أَسْأَلُكَ خَيْرَهَا وَخَيْرَ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ، وَأَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّهَا وَشَرِّ مَا جَبَلْتَهَا عَلَيْهِ

Allaahumma 'innee 'as'aluka khayrahaa wa khayra
majabaltahaa 'alayhi wa 'a'oothu bika min sharrihaa wa sharri maajabaltahaa 'alayhi.

Na yi mamakin jin wannan addu'ar daga bakin Jibril lallai ba da wasa ya riki karatun qur'ane ba tun da har ya iya maida hankali ga yin addu'o'i ma. Bayan ya gama ya tashi ya dauko manyan ledoji ya aje a gabana tare da plate da cups. Ni kuma na mike tsaye na nufi hanyar da aka shigo da ni wato falo.

“Zo ki ci abinci mana”

“Bana jin yunwa”

Ita ce kawai amsar da na bashi na nufo falo na zauna, sai kuma na kasa yin kukan da na fito yi, haka na zauna a saman manyan kujerun alfamar ina ta kallon yadda aka tsara falon, ba dan ina ganin sha'awa ba sai dan na rasa abun yi zuciyata cike da tunanin Bilal. Har sha biyu ina zaune falon ni kadai kuma Jibril be fito ba. Jin na yi na tsallawa da kayan dake jikina kasancewar atamfar ta matseni sosai hakan yasa na tashi na koma dakin dan dauka wasu tufafin domin Jidda ta fada min inda ta aje min kayan da zan canja idan zan kwanta.

Aabunda na tarar ya tashi hankalina sosai, Jibril ne kwance kamar matacce ga jini nan gefensa da alama amai ya yi. A firgice na kai hannu na taba shi amman be motsa ba.

“Na shiga uku Jibril Jibril Jibril”

Shiru be amsa ba balle ya motsa, tun ina girgizashi kadan har na fara yi da karfi ina kuka, hannu na kai daidai hancinsa sai na ji baya numfashi hakan yasa ni fasa ihu na fito a firgice falo ban san lokacin da na fito harabar gidan ina ihu ba. Ban san da akwai mai gadi ba har sai da ya taso ya nufoni yana tambayar lafiya.

“Jibril ne ya suma ya ya ya mutu”

Na fada cikin Matsainancin kuka da tashin hankali. Tare muka dawo dakin da shi babu abunda ke fita bakinsa sai Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, yana girgiza Jibril tare da fadin

“Mai gida Mai gida”

Amman Jibril be motsa ba.

“Mi ya same shi”

Ya tambaya yana cigaba da girgiza shi cikin tashin hankali na ce

“Wallahi ban sani ba, ni ma ina falo ko da na shigo na ganshi haka”

Wayarsa ya ciro ya kira wani wanda ban san ko wanene ba, cikin kankanen lokaci mutumen ya iso a nan na gane direban da Jibril yake aikawa a gidanmu ne. Tare da taimakonsa suka saka Jibril a mota nima na shiga muka dauki hanyar asibitin One On One Special Hospital.
Muna isa aka karbeshi aka shiga dashi wani dakin suka shiga bashi taimakon gaggawa, sai direban ya dawo yana cewa na kira iyayensa na fada musu.

“Babu waya hannuna tana hannun Mamana”

“To ki kira line sai ki sanar musu idan kina da number a kai”

Ya fada yana mika min wayarsa. Cikin hanzari na karba na saka numberta na kira, sai da tayi ta ringing har ta katse na sake kira sai a na uku Inna ta dauka cikin muryar bachi.

“Assalamu Alaikum”

“Inna Nawwara ce ni ce, muna asibiti Jibril ba lafiya ya suma ko ya mutu”

“Wani abun kika masa ko?”

Na yi shiru na kasa amsawa sai kuka nake.

“To kin kyauta, kuma bari kiji na fada miki ko mutuwa ya yi karki kuskura ki dawo inda na ke, ki nemi wata uwar can ba ni ba fitsararriyar yarinya”

Tana fadar hakan ta kashe wayar. Sai na mika masa ina kuka kamar zan hadiye zuciya na mutu.

“Ki kira mahaifinsa ki fada masa”

Kuka da nake ya hanani fadin bani da numbersa numfashina har gargada yake. Shi da kasan ya kira Abbah ya fada masa, kusan a tare suka iso da Inna da wasu yan uwan Inna.

“Miya sameshi”

Shine abunda mahaifin Nawwara yake ta tambaya, ni kuma na kasa magana saboda kuka, Inna kan ban da hararata babu abunda take. Bayan likitoci sun gama bincikensu daya daga cikinsu ya zo yana ma Abbah bayanin cewar Jibril yana da heart attack kuma da alama an bata masa rai ne shiyasa wannan dogon suma.

“Zuciyarsa ta buga a yanzu, kuma an barshi ya dade ba a kawo shi asibiti ba, ban da Allah ya masa tsawon rai da yanzu ya mutu, da alama an bata masa rai ne ko kuma be samu wani abu da yake so ba ko ya rasa wani abu, so shawarar da zan baku ku yi kokarin kawarda duk wani abu da zai bata masa rai saboda in ta sake bugawa gaskiya zaku rasa shi yanzu ma sa'a ce kawai da kuma rabon shan ruwa a gaba”

“Mun gode likita zamu kiyaye”

Shine abunda Abbah ya fada, kallo daya ya yi min ya dauke kansa, ya nufi dakin da Jibril ya ke ya shiga, har su Inna suka shiga aka barni nan ni kadai tsaye kamar marar gata. Su Inna ne suka fara fitowa ban san ko karfe nawa a wannan lokacin amman tabbas dare ya yi sosai amman hakan be hana Inna da yan'uwanta bin daren au koma gida ba. Bayan Abbah da yayan Jibril sun fito tare da wasu yan uwansa mata na shiga, sai na tararda wasu yan uwansa a cikin dakin, sai dai ina shiga duk suka fita waje aka bar ni ni kadai.

Zaunawa na yi saman kujerar dake kusa da gadon ina hawaye, sai na dora kaina saman gadon da yake kwance ina kallon fuskarsa. Oxygen ne a bakinsa sensor na nuna yadda numfashinsa ke tafiya, tausayinsa ne ya fara kamani da kuma tausayin kaina a lokaci daya...
[11/19, 1:12 PM] Farar Mace...: *RAI BIYU...♥🖤*

Wattpad @KhadeejaCandy


5⃣9⃣

Ina biyu aka yi sallah asuba, sai na shiga bandakin da ke dakin na yi alwala da na fito sai na shimfida dankwalina already ina da Hijabi a jikina wanda na yi sallah da shi a daren jiya, sai kawai na kabbatar sallah. Dukanin addu'a ta ta nemawa Jibril lafiya, na tsorata sosai da yanayinsa ina tsoron na zama ajalinsa gashi mahaifiyata ta soma fushi da ni mahaifinsa kuma ba zai taba yafe min ba, duniyarta zata sake rikice har ma ta fi ta baya.

Idan har ban yi hakuri zama da Jibril ba duk abunda ya same shi a yanxu ni za a zarga, kuma nasan Bilal ba zai aureni a yanxu ba, ko da kuwa na kashe auren ne na fito. Saboda bakin jinina kowa ni zai dorawa laifi, addu'ah nake hawaye suna min xuba, mafita kawai na ke nema a gurin Ubangijina, ina rokon ya sassauta min zuciyata ya bani ikon mantawa da komai. Bayan na gama na dawo saman kujera na zauna ina ta kallon fuskarsa tashin hankali da zullumi cike a zuciyata. Misalin bakwai da rabi Mahaifinsa ya shigo ina ganinsa na sauka daga kan kujerar na duka har kasa na gaisheshi amman abun mamaki sai ya ki kallon inda na ke balle ma ya amsawa. Ban tashi daga duken da nake ba likita ya shigo ya kara duba jikinsa ya yi musu bayanin cewar jikinsa da sauki kuma zai farka nan da wasu yan awoyi.
Likitan na fita sai Step mother din Jibril ta shigo tare da wasu yan uwansa, su kan da na gaishesu sun amsa min har ma suka tambayeni mai jiki na ce da sauki.

“Hajiya kuje waje likita ya ce a barshi ya samu isasshen bachi, kuma akwai maganar da nake son mu yi da matarsa”

Shine Abbah ya fada abunda ya fadarmin da gaba, ba musu suka fice suna Allah ya sauwake, bayan fitarsu Abbah ya kalleni irin kallon nan na tsana ya ce.

“Bari kiji na fada miki duk da na ya mutu sanadiyarki kema sai kin mutu, ko wane ango aka kai masa amarya farinciki yake yana zumudi balle ma Jibril da yake jin kamar ya hadiyeki, amman daren da aka kai shi daren aka kwasoshi zuwa asibiti yan biki ko watsewa ba su yi ba, Wace irin macece ke wani irin kallo kike so duniya ta miki? Jaruma ko hajirtacciya? Duniya zata miki kallo wawuya ne marar hankali wacce ilmimta be amfaneta da komai ba.
Da kin san irin son da da na yake miki da ko ko da baki bari ya taba shi ba balle har ki bata masa rai, ban taba sanin cewar dana yana da heart attack ba sai yau, kuma na san saboda ke ne, idan kika kashe Jibril da wane ido zaki kalli Noor? Anya Nawwara akwai imani a zuciyarki kuwa?”

Zubewa na yi kasan guiwoyina ina kukan da ban san ta ina yake fito min, kukan da ya hanani cewa komai har su Inna suka shigo sai Abbah ya juya ya fita bayan ya gaisa da su. Inna kamar jira take ya fita sai ta hau ni da masifa ranta a bace

“Karkar kuka kike Nawwara, da kukan jini zaki yi, ba sakike kike so ba? Bari Allah ya bashi lafiya zan sa ya sakeki kije ki auri Bilal din mahaifiyarsa ta yi ta gasa miki garwashi a hannu ba ma gida ba, mutumiyar banza marar hankali wannan hakin naki ba haline na mutanen kirki ba, kuma duk mai irin rayuwarki ba zai taba jindadin zama duniya ba, ke baki ma Allah laifi ya yafe miki ne ko ke kin fi uban kowa ne, Jahila kawai ilminki ba shi da amfani Nawwara kin yi hasara jindadin zama da mutane indai haka zaki cigaba da rayuwa”

Babu bakar maganar da Inna bata fada min ba, ita da Mama Turai mutuwa ce kawai ban yi a gurin saboda kuka, amman har numfashina kokarin fita ya rikayi. Hakan be sa Inna ta tausaya min ba sai ma haushina da take ina kokarin rike mata zane ta buge min hannu ta fice a fusace, babu wanda ya tsaya ya saurari ni. Kuka na yi a gurin har sai da na gode Allah sannan na tashi na koma saman kujerar na zauna ba dan hawaye sun daina min zuba ba. Wata yar uwar Jibril ce ta shigo da kayan abinci ta aje sai ta dafani

“Adda Nawwara ki yi hakuri Yaya zai tashi Insha-Allah”

Uffan ban ce mata ba har ta fice, sai na maida kaina na kwantar jikin gadon na lumshe ido kaina na mugun ciwo kamar zai tsage.


JIBRIL POV.

Misalin goma da rabi na safe ya bude idonsa, ya dade yana gani dishi² sannan ya soma gani dai dai har ya gane asibiti aka kawo shi. A hankali ya maida dubansa gurin Nawwara da kanta ke kwance saman gadon idanuwanta a lumshe da alama bachi take amman sai shesshekar kuka take. Hannu ya kai ya shafa saman kanta, ya lumshe ido. Sai kuma ya kai dayan hannunsa ya cire oxygen din da ke bakinsa ya unkura cike da karfi hali ya tashi zaune, yana jin zuciyarsa kamar zata rabe biyu.
Hakan ne ya farkarda Nawwara daga bachin da take suna hada ido sai taga abun kamar mafarki saurin mikewa tsaye ta yi sai ta rumgume shi tsabar jindadin ya farka be mutu ba, sai ta fashe da kuka.

“Ka yi hakuri Jibril ba zan sake ba, ban zata abun ya kai har haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login