Showing 18001 words to 21000 words out of 138998 words

Chapter 7 - Rai Biyu Book 1 Complete Hausa Novel

05 Feb 2025

732

ba musu na miƙawa Noor wayar, ban san mi suke tattaunawa ba kawai dai na ga Noor yana dariya yana ɗaga kai sai kuma ya wulgumin wayar ya tashi ya fita da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.

“Falfala da gudu ɗan gidan Bilal sai in be kiraka ba”

Cewar Habiba tana dariya. Nishaɗin dake fuskarta shine a fuskar Inna da Jamila har ma Sakina da kuma ni kaina.

“Bilal ɗin nan yana son Noor kuma na tabbatar son da yake miki ne ya shafe shi”

Na ɗago na kalli Inna da furucin da ta yi.

“Ba fa so na yake ba, mutunci ne kawai a tsakaninmu, be taɓa cewa yana so na ba”

Habiba ta watsa min harara.

“Ji matar nan muna-muna munafuka, Wallahi son junansu suke amman shi ba zai iya faɗa ba ita ba zata ba shi dama ba, ai da yanzu an wuce gurin, duk alamun da yake nunawa ai na son ki ne, ke kuma kina kauce masa”

Na yi dariya ina girgiza kai.

“To ya kike son na yi?”

“Ya dai kamata ki bashi dama, zama haka ba zai yiyu ba, Allah kaɗai yasan iya gulmar da ake muku a unguwarnan, kin kore kowa kin zauna a gida gashi har mahaifinki ya rasu be ga wani auren na ki ba”

Wannan karon Inna ce ta yi maganar, kuma maganar da ta yi ta ɗan taɓani, tabbas mutuncin ƴa mace da kuma darajarta a gidan aurenta ne, sai dai ba kowa ne zai maka son tsakani da Allah ba, wasu kan zo so na saboda sha'awata da sun gwasa sun gano ni ba ƴar iskar barawarar nan ba ce sai su gudu, wasu kuma su nuna maka ba zasu yarda da je da yaron ka ba, wasu kuma basa da wani sana'ar kirkin da za su iya riƙe sauran iyalansu ma balle kuma a haɗa da ni, kowa da irin matsalarsa. Bilal ɗin ma laƙe min ya yi da sunan abota, sai dai ko da wasa ban bashi alamun da zai iya nuna min so ba, saboda na san iyayensa ba zasu yarda ya auri mace da taɓa aure har biyu ba kuma har da ɗa ma.

Uffan ban ce ba, Inna da Habiba kawai ke ta nanata maganar. Muna nan zaune Noor ya shigo da ƙatuwar leda a hannunsa har biyu a hannunsa baki har kunne.

“Momy kalli abubuwan da siyo min, kuma ya ce Mama Habiba kawai zan bawa kar na sammi ki, kuma ya ce yana kiranki yana ƙofar gida”

Shi da Habiba suka riƙa kokuwar buɗe ledar, ni kuma na zari Hijabina na nufi ƙofar gida. Tsaye na sameshi yana kallon ƙofar gidanmu da alama dai yana jiran fitowata ne.

“Ina ta zuba ido na ganki yau a kamfaninmu ban ganki ba”

Ban bashi amsa ba sai da na yi masa sallama ina murmushi.

“Assalamu alaikum”

Sai ya amsa min da murmushi.

“Wa'alaikissalam Nawancy, na zo na taya ki murnar samun aiki, ai na faɗa miki zasu ɗauke ki”

“Ɗazu na samu saƙon, na jidaɗi sosai”

“Mutane na ta zuwa karɓar uniform amman ke ban ganki ba”

“Uniform kuma?”

“Yes ai Uniform zaku saka, tun safe ake zuwa ƙarɓa kin ga ɗaga yau zuwa gobe ne kawai ake bada uniform ɗin, on monday zaku fara zuwa aiki, kuma idan kunje karɓar uniform ɗin za a nuna muku irin aikin da zaku yi”

“Gobe zanje Inshallah, ai ban san ana zuwa yau ba”

“Sai dai matsala ɗaya, Nawancy bana son ki saka wando, ina ganin kamar ba be dace ba”

‘Musamman ga irina masu manyan mazaunai’

Na faɗa a raina. A fili kuma sai na ce.

“Ai zan iya saka Hijabi ko abaya a sama”

“Amman baya son haka, sai idan kin tashi aikin ko kuma idan zaki shigo, shi be yarda ma ko hula a saka a gurin aikin ba balle kuma Hijabi”

Cike da mamaki na ce

“Ba musulmi ba ne hala?”

“Wallahi musulmi, amman mutumen sai a hankali, haka zaki ga tattoo a jikinsa, ina jin ya zauna waje ne”

Na taɓe baki cike da ƙyamar halin mutunen duk da ban san shi ba

“Allah ya kyauta amman abun baƙinciki ne ace musulmi ya rinjaya wani addini sama da nasa, ga shi ka ce ya cika tsanani”

“Yana da tsanani sosai, amman tsananinsa yana burge ni wani lokacin, kin ga dole kowa ya riƙe aikinsa da muhimmanci, kuma kin ga wacan da aka canja baya damuwa da duk waɗannan abubuwan shiyasa duk ƙarshen wata sai an siyo kayan abincin da cups da aikatan gurin suke aiki da su, amman zuwan wannan ya saka dokar duk wanda ya fasa masa cups za a cire cikin albashinsa, dole kowa ya riƙa taka tsantsan da abubuwan gurin”

“Amman daman ba a biyan kuɗin abincin ne?”

“No ana biya restaurant ɗin da ke cikin kamfanin ai nasa ne, amman idan ba restaurant ba kin ga ma'aikici zai buƙaci shan ruwa ko wani abun ko kuma tea musamman ga masu zuwa tun safe, ko kuma idan aka yi baƙi, to duk da wannan cups ɗin ake amfani. Bayan ma wannan kamfani suna da Sabuwar Asibiti da aka buɗe nan by pass, One-On-One Special Hospital, amman ance ta masu kuɗi ce dan katin ganin likita ma ɗari takwas da hasin ne”

Na jinjina kai ina faɗin.

“Kamfanin ma akwai girma, ni Allah yasa ma har na yi aikin na gama ba zan ganshi ba”

Sai kawai yasa min dariya.

“Kina tsoro ne Nawancy?”

“A'a ba tsoro ba ne, kawai ba zan iya jurar wulaƙanci ba ne, kaga ƙara ma ace bamu haɗu ba”

Mun daɗe muna fira yana ta labarta min kamfanin da kuma wasu abubuwa na cikinsa da kuma yadda aikinsa yake, kamin hirar siyasar ƙasar nan ta shigo ciki, sai tara da rabi muka yi sallama ya tafi ni koma na cikin gida.
Ko da na shiga su Habiba sun ci sun ciye an gutsura min ɗan tsiton cake da nama ƙwara ɗaya an aje min sai kuma ice cream a cibi.

“Yanzu wannan abun kawai zaku bar min?”

“Eh mana dan kin samu ma mun rage miki”

Cewar Habiba, tana bani amsar tambayar da nayi, sai Noor yasa dariya yana cin namansa ya ce

“Momy ƙyale Mama Habiba sai ta yi bachi zan ƙara miki karki kuka kinji?”

Sakin baki Habiba ta yi.

“Au ni zaka watsawa ƙasa a ido?”

Ta kai masa dudu. Inna tasa dariya, yau kan ba laifi muna cikin farinciki farincikin da muka daɗe ba mu yi ba tun bayan rasuwar Baba, sam ba zaka gan mu a yanzu ka ɗauka akwai wata damuwa a ranmu ba. Daman can talauci baya hana mu walwala ko kuma farinciki, idan ka ganmu a damuwa to muna jin yunwa ne, da kuma mun samu mun ci sai mu gode Allah da wannan ni'imar, mu kuma roƙi na anjima.


*** *** ***

Kamar yadda muka kwana cikin farinciki haka muka tashi da shi, abun ka da sabon shiga su Noor na wucewa makaranta nima na shirya muka fita tare da Habiba ita ta wuce tata makarantar ni kuma na ɗauki hanyar gurin mu a Napep.
Yau ma da na isa ban shiga ba sai da na ƙira Bilal na sanar masa ina bakin gate, shi ya fito ya shiga da ni, sai mita yake wai ya kamata ace na shigo ciki da kaina tun da Monday zan fara aiki, ni kuma ina taka tsantsan ne gudun ƙar na yi wani abun da ba daidai ba, shugaban ya ce zai hukunta tun ban fara aikin ba.
Ciki ya shiga da ni har muka isa cikin wani ƙaton haɗi inda na faɗa musu sunana suka duba sannan suka ɗauko uniform ɗin dake cikin leda suka ba ni, sai kuma wasu takalmi masu kama ta da malaman lafiya na asibiti, suka miƙa min wasu takardun na saka hannu sai suka buƙaci idan zan dawo na zo da ƙaramin hoto na guda biyu, wai zasu saka a file ɗayan kuma a kuma na saka a catin zan rayata a wuya na shedar aikina.
Ɗaya daga cikinsu ne ya yi min ja gaba har gurin da zan yi aikin nawa, kitchen zan riƙa gogewa da kuma da ake aje files kusan ɗaki biyar, sai dai ba ni zan yi sharar ba aikina Mopping ne kawai, kuma idan zamu yi mopping ɗin sai mun saka safar hannu idan mun gama mu jefar, sai kuma goge kofuna da jerasu a muhallinsu, shi ma sai mun saka safa, tsarin kamfanin kamar na turawa, lallai sai a yanzu na tabbatar da zancen Bilal na cewa Kamfanin yana takara da kamfanonin duniya. Mai nuna min aikina ya jaddada min kamin na jera kofunan sai na ƙirga ko guda nawane na rubuta a file ɗin gurin da kuma time da na fara da time ɗin da na gama, da kuma ko kofi nawa na tarar, daga ƙarshe Bilal ya kai ni reception ya nuna min gurin da zan saka sunana da kuma lokacin da na shigo, idan kuma na gama sai na saka sunana da kuma lokacin da na fita, ƙarfe bakwai zan fara aikin na ƙare tara, hakan na nufin bakwai ta yi min a can kenan.

Irin yadda tsari da dokokin kamfanin suke sai duk na ji aikin ya fara fita raina kamar ba zan iya ba, sai dai babu yadda na iya tun da nema na ke yi kuma ba anan zan dauwamaba. Har bakin titi Bilal ya rakoni, muna tsaye da shi na hango motar Zinatu ta shiga kamfanin, na tabbatar da ita ɗin ce saboda hangota da na yi ta gilashin motar da ke sauke. Bilal ya tara min Napep na hau sannan ya koma ni kuma na kama hanyar gida ciki da mamakin tsare-tsaren wannan kamfani, gaskiya ba dan ina son aikin ba da na haƙura da yinsa, a gurin da na saba sauka na ce mai Napep ɗin ya aje, sai na karɓi ragowar canjin kuɗin da Bilal ya bashi na nufi cikin unguwarmu.

A hanya na haɗu da mai gidan da muke haya, wata irin kunyace ta mamaye mu nasan yayi mana karamcin tun da be mana magana tun baya rasuwar Baba ga shi har Inna zata gama wanka takaɓan ta cikin wannan satin. Sun-sun-sun na gaisheshi ya amsa min yana murmushi tare da tambayar ya haƙuri.

“Mun gode Allah dan Allah ka yi haƙuri akan maganar kuɗin nan, inshallah za a kawo”

“Kuɗin me? Ai Bilal ya biya be faɗa muku ba ne? Tun Margayi be yi sati da rasuwa ba ya kawo kuɗin dubu arba'in cif”

Na saki baki ina mamakin ikon Allah.

“Wallahi ba mu sani ba”

“Wallahi ya biya sai dai ayi masa godiya”

Sallama na masa na wuce zuciyata cike da hauƙin Bilal, bakina kuma har rawa yake naje gida na labartawa Inna wannan labarin. A hankali wata mota da ta fito ɗaga gidansu Manjo ta doso inda na ke, mai maotar na kawowa daidai ni sai ya sauke baƙin gilashin motarsa.
Ashe Mustapha ne, cikin shigar manyan kaya wato farar shadda da kuma barar hula sajensa na kwanta sai sheƙi yake, da alama jumma'a zai je tun da yau friday, fuskarsa cike da annuri, sai dai bana mutanen kirki ba, na kuɗi da kuma kyawun hallita da suka nuna isa a fuskarsa. Kallona yake ba ko ƙyafta ido, ni kuma na bawa banza ajiyarsa sam babu tsoro a tare da ni saboda na shirya tarbar ko minene daga gareshi.
Haka nasa kai na wuce na barshi a gurin zuciyata har wani zafi take min saboda da tsanarsa.
Da sallama na shiga gida, Inna da dpo suka haɗa baki gurin amsa min, hakan yasa naji kamar na janyo sallamar na mayar da ita a bakina, yau ma ya taki sa'a na sauke idona cikin nasa hakan yasa ni jin kamar na ƙarasa a inda yake zaune gaban Inna na shaƙe wuyansa.



THE GAME IS ABOUT TO START
.*RAI BIYU...♥️🖤*

Wattpad @Khadeeja_Candy


1⃣4⃣

Na ɗauke kaina kamar ban san da zaman mutun a gurin da Inna take ba.

“Har kin dawo?”

Inna ta tambaya, ni kuma na nufi ƙofar ɗakin mu ina amsa mata domin bana son na juyo idona ya haɗu da na azzalumin mutunen nan.

“Eh Inna”

Na ɗaga labulen ɗakin mu na shige zuciya cike da abubuwa guda biyu farincikin abunda Bilal ya yi mana da kuma baƙincikin ganin dpo a gidanmu. Kayan da ke hannuna ma saman katifa na jefasu, na zauna ƙasa raina a jagule.

Jidda ce ta faɗo min a rai, ya kamata ace na tabarta masa samun aikin nan da na yi, har na unƙura zan tashi na fita sai na tuna dpo yana tsakar gida, hakan yasa na koma na zauna, sai tunanin Bilal ya dawo min rai. Lokaci zuwa lokaci na kan samu kaina da murmushi tuna irin abubuwan alherin da Bilal yake mana, wanda na san har ƙasa ta naɗe ba zan taɓa saka masa da abunda ya yi min, ya sadaukarda abubuwa da dama saboda farincikina.

Kiran da Noor yake min a tsakar gida ne ya katse min tunani, ina unƙurin tashi na fita sai ya shigo ɗakin da gudu har yana ƙoƙarin faɗuwa.

“Momy duba aka raɓa mana sabon littafi a makaranta”

Na faɗaɗa fuskata da murmushi ina karɓar littafi tare da buɗewa ina dubawa, littafi rubutu ne mai hoton ciyaman, da alama ya kai musu ziyara ne, daman naji a rediyo ana cewar zai ziyarci makarantu.

“Momy da idona na ga Ciyaman yana jawabi har da godiya ya yi mana, sai aka raba mana littafai”

Na kai hannu na shafa fuskarsa ina dariya

“Amman Ciyaman ya kyauta da ya bari Noor ya ganshi”

Sai ya ƙyalƙyale da dariya ya rumgume ni. Haka ɗa na yake, masu kuɗi da ƴan siyasa suna burgeshi ko a mota ya ga mutun sai ya tsaya kallonsa har sai ya daina hangoshi sannan hankalinsa ya kwanta, a ranar kan labari sai abunda ya manta.
Zaunar da shi na yi saman jikina, na soma cire masa talkamin makaranta tare da safa, shi kuma yana duba littafin tare da karantawa. Habiba ce ta shigo ɗakin babu ko sallama, kana ganinta kasan a gajiye take jikar littafanta ma a bakin ƙofa ta sakesu ta kwanta kusa da ni tana ƙoƙarin cire hijabinta.

“Lafiya kike kuwa?”

Na tambaya ina kallonta, Noor kuma ya tashi da sauri ya fita waje. Ɗan guntun tsaki taja irin na wanda baya son magana kana ta ce

“Wallahi bana jindaɗi, amai na biyu makaranta kuma kaina ciwo yake sosai”

Dukan shida-shida gabana ya yi tsaɓanin uku-uku da na kowa keyi, a take nima na ji ciwon kan ya kamani, dafe kaina na yi na lumshe ido yana sauraren yadda zuciyata take bugawa. Ƙoƙarin kawarda abunda ke zuciyata nake, yes cikin zai iya nunawa a sati biyu amman ba ko wanne ba, cikin Noor ma a sati biyu aka gano ina da ciki balle kuma Habiba da ke da wata ɗaya har da sati ɗaya, tunda ranar litanin Inna zata cika wata ɗaya da sati biyu cikin taƙaba.

‘No ba ciki ba ne, maleriya ce inshallah ba ciki ba ne’

Zancen da nake a zuci shi Habiba take a zahiri.

“Nawwara na ce ƙila maleriya ce, saboda idona har nauyi yake”

Na buɗe ido na kalleta tare da ɗaga mata kai alamar ‘Eh’

“Ita ce, bari na aika Sakina ta siyo miki Anti-Malaria shago”

“Tau”

Ta juyo min baya tana dafe da kai, hakan ya bawa hawayen da ke maƙƙale a idona saukowa zuwa kumatuna, ban taɓa tabbatar da hawaye na da zafi ba sai a wannan lokacin, gumi ne ya soma keto min ta ko ina kamar wacce ta yi rashin gaskiya. Cikin hanzari na kai hannu na share hawayena saboda motsin Sakina da na ji zata shigo ɗakin, sai na miƙe tsaye na nufi ƙofar fita. Ashe magana take min ban ji ba har sai da ta riƙoni.

“Anty Nawwara, wai ɗan sanda nan yana kiranki a waje”

Da kai na iya amsa mata, daman Hijabin da na shigo da shi yana jikina sai kawai na zarce ƙofar gida, har ga Allah ba dan ina cikin ruɗu ba babu abunda zai sa dpo nan ya kirani kuma har na tafi. Tsaye na yi masa idona a ƙasa ina ta tunanin makomarmu, idan har ta tabbata Habiba na da ciki mun shiga uku, lallai mutane zasu gasgata cewar Mahaifinmu ya yi sata, tun da ga ƴar'uwata da cikin shege, duk wani yabo da ganin mutuncinmu da ake a unguwarnan zai zube, ya Inna zata yi idan ta ji Habiba na da ciki? Ita kanta kanta Habiba ya zata kasance? Ni kaina da suka san na yi aure lokacin da na haifi Noor sai da suka kira shi shege balle kuma Habiba.

“Nawwara”

Kiran sunana da dpo ya yi na yasa na dawo hayyacina har na kalleshi, ashe tun da na zo gurin magana yake min amman ban fahimtaba saboda tashin hankalin da ke zuciyata.

“Ki yi haƙuri dan Allah, ki share hawayenki, duk abunda na faɗa miki zanyi ki yarda da ni”

Sai a lokacin na kula da hawayen da ke ta zuba a idona, cikin sauri na sa Hijabina na gogesu ina jan magina. Sai ya ɗora da zancen da ban gane masa ba, ba dan kuma yana min wani yaren ba sai dan hankalina baya gurin, babu komai a zuciyata sai fargaba tunani da kuma zullumin abunda zai je ya dawo, na tabbatar da za'a auna jinina a lokacin za a tarar ya haura ɗari uku da wani abu bama ɗari biyu ba.
A gurin na barshi tsaye na shige gida ba tare da hawayen sun tsaya min ba, haɗa ido da muka yi da Inna yasa idona ƙara cika da ƙwalla, tausayinsa ne ya kamani tabbas Mahaifiyata ba zata iya ɗaukar wannan ba, duka-duka yaushe ta rasa mahaifina kuma yanzu ta ji Habiba na da ciki.

“Lafiya?”

Tambayar da ta yi min ne yasa na share hawayena ina ƙoƙarin ƙirƙiro ƙaryar da zan mata.

“Ba komai kawai mun yi magana kan Baba ne”

“Nawwara ki yi haƙuri idan ma a duniya ba a yi komai ba, lahira za'ayi domin Allah baya zalumci kuma zai ƙwatar mana haƙƙinmu”

“Haka ne, Inna kina da kuɗi a siyowa Habiba maganin Malaria?”

“Duba a cikin jakata ba za'a rasa ba, tace kanta ke ciwo”

Ban iya tsayawa amsa mata ba, na nufi ɗakin na ɗauko kuɗin na aiki Sakina ta je siyo mata,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login