Showing 33001 words to 36000 words out of 180592 words

Chapter 12 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1176

hade da lumshe ido, yafi minti goma a haka can ya mike jiki a sanyaye ya fita xuwa main house, sosai gabansa ya fadi ganin yakumbo, sae dae ya fuske ya xauna ya gaisheta tace "Sae yanxu ka ga dama kenan" ya shafa kai yace "A'a" Mami dae sae kallonsa take, Yakumbo tace "Toh ya maganar mu ta ranan, kasan dae kai ake jira ko?" Ta gefen ido ya kalleta yace "Ni ake jira kuma?" Yakumbo ta kalli Mami a fusace tace "Ki fa gaya masa don ya raina ku ni bai isa ba ne... Ni xae dinga ma tambayar walakanci?" Abuturrab yace "No ban gane xancen bane yakumbo." Buda baki tayi tana kallonsa, ita dai Mami uffan bata ce ba, Can ya mike yace "Kar ki damu Yakumbo xan kawo maki ita har gida ta gaishe ki, shknn dai koh?"
Washegari lahadi da yamma Abuturrab ya shirya don wucewa gun aiki, Yana rufe gate ya dawo xai shiga motarsa ya hangota tana tahowa, tsayawa yayi har ta karaso sanye take da Abayarta dake ta sheki tsabar iron, tayi Islam is peace da veil din abayar, bbu make up fuskarta sai eye pencil dake idonta da lip balm da ta shafa a pink lips dinta, amma ba karamin kyau tayi ba, tayi murmushi tace "Ina yini?" Yana kallonta yace "Lafiya! Ina xa ki?" Tace "Catechism yau Sunday!" Yace "Ohk shigo in yi dropping din ki" tace "Thought clinic xaka?" Yace "Yeah" ta langwabar da kai tace "Toh ae ba hanyar bane" yace "Idan xa ki shigo malama ki shigo" a hankali ta karasa ta bude motar ta shiga, shi ma ya shiga ya ja motar suka dau hanyar titi, ganin hanyar da ya dauka ta kallesa sai dai bata ce komai ba, tafiyar kusan minti ashirin suka yi ganin har sun wuce hanyar asibitin ta kallesa tace "Ina xaka kai ni Doctor?" Ba tare da ya dauke idonsa daga kan titi ba yace "Sayar da ki xan je in yi" bata ce komai ba, haka ya dinga tafiyarsa, ji yayi ta fashe da kuka, ya d'an saci kallonta yayi murmushi yace "Toh ae ba kuka ya kamata kiyi ba, you are supposed to be reciting ur last prayer...." Cikin muryar kuka tace "Ni dai ba wasa nake ba ka ajiye ni in koma gidanmu" yace "Ke da gidan ku kuma har abada..." Ta kuma fashewa da kuka, wani anguwa suka shigo basu wani shiga ciki ba yayi horn a bakin wani gate ba a dau lkci ba mai gadi ya leko ya bude gate din snn ya shigar da motar compound din, yana gama parking, ya kamo hannunta ta fixge, yayi murmushi yace "Yanxu kin yadda xan sayar da ki" hararansa tayi tace "Baka yi kama da wanda xai iya saida Bird ba bare ka saida mutum just that you didn't tell me you are taking me this far nayi xaton asibiti xa mu je" sai kuma ta fashe da kuka sosai, jawota yayi jikinsa yace "Ohk am sorry plsss, ba jimawa xa muyi ba, gidan mum dita ne nan...." Turasa tayi da mamaki tana kallonsa tace "Mum?" Yace "Yeah, my mum sister" ta fashe da wani sabon kukan tace "Ni dai ba ruwana ka kai ni titi in hau tricycle in koma gida" yace "Ohh she's nyc, and she will love seeing you, bata da matsala" bai jira cewarta ba ya ciro handki ya fara share mata hawayen idonta, daga haka ya bude motar ya fita ya xaga ya bude mata kofar ya fito da ita. Bbu kowa parlorn ya sa ta xauna kan kujera snn ya tafi dakin Mum, Hajiya Mariya dake gyaran kayanta a closet tana kallonsa da mamaki tace "Aliyu, daga ina haka?" Yace "Gida Mum" tace "Ikon Allah, sannu da xuwa ya hanya?" Yace "Alhmdllh, da bakuwa muke" bai jira cewarta ba ya fita, sai ga ta ta biyosa, tun bata iso parlon ba take kallon Samantha har ta iso, Samantha ta sunkuyar da kanta gabanta na faduwa, Murmushi dauke fuskar Hajiya Mariya tace "Sannu da xuwa bakuwa" Samantha bata iya ta kalleta ba ta xamo kasa a hankali tace "Ina yini Mumy" Hajiya Mariya tace "Lafiya lau, ya hanya?" Kasa cewa komai Samantha tayi, Hajiya Mariya ta xauna tana kallonta tace "To koma kan kujeran mana" bata dago ba bata kuma ce komai ba, Abuturrab yayi murmushi yace "Mum meet Samantha.... But I do call her Samha.." Hajiya Mariya tace "Ohh maa sha Allah, but this Samha is too shy, taki xama kan kujera" Yace "No she's comfortable there" Hajiya Mariya tace "A'a ni ba ruwana ta koma kan kujera" daga nan ta mike ta nufi fridge don dauko masu drink, kallonta yayi yace "tashi koma kan kujera" bata kallesa ba bata kuma tashi ba, ya mike yace "Toh bari in daga ki" da sauri ta koma baya tace "No bana so ka bari plss" kamar xata yi kuka tayi maganan, ya wara ido yace "Toh kuka xa ki min?" Kin cewa komai tayi, Hajiya Mariya ta dawo parlon da ruwa da lemo ta karasa kusa da ita ta ajiye tana kallonta tace "Yanxu baxa ki hau kujera ba bakuwata" girgixa kai kawai tayi, Haka kawai Hajiya Mariya taji ta burgeta a xuciyarta kuwa tunani take wnn din ce Christian din da Abuturrab ke fadi mata, kitchen ta koma ta xubo masu fried rice din da tayi, ganin ynda Samantha taki sakin jiki ta bar masu parlon, tana wucewa ta dago kamar xata yi kuka tace "Doctor plss mu wuce" ya hade rai yace "Gidan Mum dita ne nn fa" tayi shiru bata ce komai ba, ba karamin takurata yayi ba ta ci abincin shi ma kadan, hade rai yayi ya sauko kasa ya karbi spoon din ya debi abincin ya kai bakinta, kamar xata yi kuka tace "Doctor ka bari plss" dafa forehead dinta yayi ta bude bakin da sauri ya xuba mata ya kai sauran baki, sunkuyar da kanta tayi tana taunar abincin a hankali, can ta kallesa a hankali tace "Doctor wllh na koshi" yace "Me kika ci?" Tace "Pounded yam and vegetable" yace "Shine baki kawo min ba?" Ta wara ido tace "Kana so?" Yace "Ehh mana" ta langwabar da kai tace "Toh xan maka" mikewa tayi tace "Kitchen fah?" Ya nuna mata hanyar kitchen ta dau tray din abincin ta nufi can, mikewa yyi ya shiga bedroom din Hajiya Mariya. Tana shiga kitchen taga kayan wanke wanke a hade cikin sink, liquid soap ta dauka da sponge ta hada ruwan kumfa ta fara wanke su, cikin kankanin lkci ta gama don bai da wani yawa, ta tsaftace kitchen din ta goge har Gas snn ta dau sweeper ta fito parlor, Abuturrab ya xauna gefen Mum din sa dake waya har ta kare wayar snn ta kallesa tace "Ita ce yarinyar Aliyu?" Kai ya gyada mata, ta girgixa kai tace "She's cool and pretty, kuma bata yi shige da yare ba kamar bafulatana, and kamar ba Christian ba" murmushi yayi yace "Abbanta bafulatani ne ae...." Shiru Hajiya Mariya tayi, can tace "Allah sarki.... Toh yanxu ta yarda xata yi converting din ne?" Xaro ido yayi yace "Mumy ni fa bamu taba magana irin wanda nake maki da ita ba...." Da mamaki tace "Kana nufin bata san kana sonta ba?" Shiru yyi sai kuma ya girgixa kai a hankali yace "Ko ma ta sani bata taba nuna ta sani ba" Hajiya Mariya tace "Toh fah, then it's better ka fadi mata soon as possible kaji ra'ayinta" ya lumshe ido yace "Ohk mum" 'yan shawarwari ta basa sannan tace ya tafi parlor ya bar ta ita kadai, mikewa yayi ya fita, xaune ya sameta idonta na kan tv, ya karaso ya xauna kusa da ita yana kallonta yace "Sae bayan magrib xa mu tafi koh?" Ta dago da sauri ta kallesa xata yi magana sai ga Hajiya Mariya wanda hakan yasa tayi shiru, Hajiya Mariya tace "Sannu my daughter, mun bar ki ke daya koh?" Murmushi Samantha tayi bata ce komai ba, ya kalli agogo yace "Mumy xa mu wuce...." Tace "So early?" Yace "Mun dade fa Mumy" tace "A'a ba wani dadewa" daki ta koma ba a dau lkci ba ta fito rike da leda ta mika ma Samantha tace "kiyi hakuri bbu yawa kin ji...." Da sauri ta girgixa kai tace "A'a nagode Mumy" Mumy ta mika ma Abuturrab tace "Toh gashi ka bata tunda kunya ta take" har mota ta rakasu sai da suka fita sannan ta koma ciki, a hankali yake driving din, can ya juya ya kalleta, idonta na waje tana kallon titi, kamo hannunta yayi ta juyo tana kallonsa, ya murza fingers dinta yace "Kin san me?" Janye hannunta take son yi ya ki saketa, murya can kasa yace "My mum.... Kinsan me tace?" Kallonsa ta sake yi snn tace "A'a" murmushi yayi murya can kasa tace "Wai tana son ki, she likes you, how she wish you were a Muslim sai ki xama in-law dinta" murmushi tayi ta kwace hannunta bata ce komai ba, yace "Kin yi shiru" wara ido tayi tace "Uhm and unfortunately am not a Muslim"

*Haske Writers Asso*=???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

18.....

Murya can kasa yace "And you can't become one koh?" Wani kallo tayi masa ta gefen ido tace "as in?" Shiru yayi bai ce komai ba, can yayi murmushi yace "Gaya min me ya burge ki a Christianity!" Ta girgixa kai tace "I don't want to talk about that now!" Bai sake ce mata komai ba har suka iso layinsu, tace "Kayi dropping dina kawai in karasa da kafa" bai tanka ta ba ya isa har gate dinsu ya tsaya snn ya juya yana kallonta, ta bude motar ta fita hade da daga masa hannu, dauke idonsa yyi ya ja motor ya bar wajen, ta bi sa da kallo har yayi nisa snn ta juya ta shiga cikin gida. Mumy ce xaune parlor da wata bakuwa, ta durkusa ta gaishesu xa ta wuce Mumy tace "Ina bible din naki?" Shiru tayi tana kallonta, lkci daya ta tuna ta bar shi a motar Abuturrab, rasa abinda xata ce tayi, uwar ta watsa mata wani kallo tace "Ba kya ji ne?" Wayar Mumyn ne ya dau kara ta dau wayar tare da dagawa, Bakuwarta da ke xaune ta kalli Samantha tace "Tashi kije" mikewa Samantha tayi da sauri ta bar wajen don in har Mumy ta ci gaba da tambayar xata iya fadi mata gaskiyar daga inda take. Karfe tara saura tana xaune da Mathematics gabanta tana solving don Tuesday suke da maths, gaba daya ta kasa ci gaba don ta manta calculation din, bude kofar dakin aka yi Mumy ta shigo tace "Daughter xan tafi church yanxu akwai prayer da muke yi ma wata...." Da sauri Samantha tace "Yaushe xa ki dawo Mumy" Mumy tace "At dawn, Blessing na nan ai, take care of ur self" daga haka ta juya ta fita, Samantha tayi tagumi, it's always church ta fadi a xuciyarta, shi kuma Abba alwayz politics..... Tabe baki tayi ta ci gaba da kallon math din gabanta, Abuturrab ne ya fado mata ta Kalli agogo, dai dai nn ta ji fitar motar Mumy, mikewa tayi sai kuma ta kalli jikinta ta ga 'yar rigar bacci ne iya gwiwa, ta bude press ta fiddo da kimono mai d'an kauri ta daura kan kayan ta dau veil ta rufe kanta snn ta dau textbook dinta da note book tare da pen sai calc, a hankali ta bude kofar ta ta fita ta leka dakin da mai aikinsu take taga har ta kwanta, a hankali ta sauka kasa ta nufi kofa taga a rufe, ta bude ta fita, sai da ta ganta kofar gida gabanta ya shiga faduwa, tafiya take da sauri da sauri har ta iso kofar gidansu Abuturrab, ta tsaya kusa da gate kamar munafuka, tura gate din tayi ta ji a bude ma yake, ta tura a hankali ta shiga sannan ta rufe, da sauri ta nufi balcony tana lekan parlon ta gansa xaune a kan carpet yana danna laptop yyi backing kofar, cikin dubara ta murda kofar yanda baxai ji ba sbda k'aran Tv, tana shiga parlorn bata rufe kofar ba cikin sanda ta nufesa, ta durkushe bayansa tayi wani k'ara, juyowa yayi da sauri lkci daya ya jawota jikinsa ya matse ta, xaro ido tayi, ya buga goshinsa da nata yana wani murmushi yace "See you! Tun da kika bude gate naji shigowar ki malama" boye fuskarta tayi tace "Ohhh," ya dago kanta yace "yan gidanku sun tafi church kenan" kwace kanta take son yi yaki saketa kamar xata yi kuka tace "Pls ka sake ni mana" kallon kafarta yayi don kimonon ya d'age daga kasa yace "Baki sa kaya ba knn.." Bai kai karshe ba ya dage kimonon, sai ga long legs dinta a waje, ta wani hade rai tana kkrin kwace kanta tace "What's this" ya buda ido yace "Ohh sorry, i never knew you were naked" wani kallo ta watsa masa tace "Am not naked" ya fashe da dariya, ta samu ta kwace kanta ta mike ta dau litattafenta ta nufi kofa, ya tashi da sauri ya isa gun kofar ya rufe, kallonsa take kamar xata yi kuka, ya langwabar da kai yace "Wasa fa nake" tace "Yeah na sani, bude min kofa in wuce" yace "Nooo baby i was only joking" bata ankara ba sai ji tayi ya wani sureta ta runtse ido tace "Doctor....." Kan kujera ya direta yace "Ki hakura plss" da sauri tace "Nayiii" ya ja hancinta yace "Troublesome girl" kallonsa kawai take, ya hura mata iska ta rufe idon da sauri yana murmushi yace "Irin wnn kallo" turo baki tayi tace "I brought my mathematics, put me through pls" daga haka ta bude textbook din tana nuna masa ya karba, k'asa ya sauka ta bi sa, nan ya shiga nuna mata solution din question din, sai kusan goma suka gama, mikewa tayi tace "Ka raka ni plss dare yayi" yace "Spend the night here tunda dare yayi" ta hade rai tace "No, why shud i??" kamo hannunta yayi ya tsare ta da ido yace "Cinye ki xan yi idan kin kwana?" Kallon manyan idanuwan nasa take, murya can ciki yace "Plss dear" a hankali kamar xata yi kuka tace "but it's not decent, it's not proper....." Da sauri yace "Naga dare yayi ne fa..." Xata yi magana yayi mata wani kallo ta kasa cewa komai tana kallonsa, sake hannunta yayi ya nufi kofa ya bude yace "Alryt, you can go sai da safe" ta sauke idonta kasa, ya karasa kujera ya xauna, kallonsa tayi snn ta nufi inda yake ta durkusa tace "Ohk am sorry, i will spend the nyt here sai in tafi da sassafe kamin mumy ta dawo" yace "No, am not forcing, kar ki fara wani tunani fah, you can go...." Hade rai tayi tace "Toh am not going" ya shafa beard dinsa hade da tabe baki yace "Da wani katon idonta a wajen, i guess her thought will be like what is this guy up to da yake son in kwana yau" xaro ido tayi ya fixgota kusa da shi yana murmushi yana kallon kwayar idonta yace "ko ba
Haka ba? Babu abinda xan maki har sai ran da Allah ya mallaka min ke a matsayin matata" buda ido tayi tana kallonsa tace "Matar ka kuma" ya kai fuskarsa dab da nata yace "Ko baxa ki iya aurena ba" xaro ido tayi da mamaki xata yi magana ya rufe bakinta yana murmushi yace "Yesss" daga haka ya mike ya fita ya rufe gate snn ya dawo ciki ya rufe kofa ta bi sa da kallo har ya xauna yace "Za kiyi wanka?" Ta girgixa kai yace "Alryt shiga ki gyara inda xa ki kwana ni parlor xan kwanta before then bari inyi wanka" binsa tayi da ido har ya shiga dakin sai kuma ta bi bayansa, taga har ya shige bathroom, kallon gadon tayi taga it's tidy except from the bedsheet wanda hakan ya nuna alaman yayi bacci a kai, ta karasa ta shiga gyarawa tana gamawa ta dau wayarsa dake gaban mirror ta fara game, har ya fito bata sani ba, sai jin kamshi me dadi hade da ruwa da ya diga a jikinta, da sauri ta dago suka ci karo, ta mike tace "Ohhh sorry" yace "Uhm ohk" sauke idonta tayi ta mayar ga wayar ya nufi gaban mirror, har ya gama shiryawa bata kalli inda yake ba, sai bayan da ya gama ya dawo ya xauna kusa da ita yace "Kina da paper gobe?" Ta girgixa kai tace "Sae Tuesday" kallon game din da take yayi tayi, can ta mika masa wayar tace "Za kayi amfani da shi?" Ya girgixa kai yace "No, i just want you to tell me a story, may be a bible story, i like them, No! Ko kuma mu ci gaba da wanda nake baki ranan" ta kallesa tace "Toh barin in fara baka sae ka ci mim gaba, wani iri kake so?" yace "ko wanne" ta langwabar da kai tace "Ohk let me tell you the story of Joseph you will like it" yace "Tohm" hawa gadon yayi ya nuna mata kusa da shi ta turo baki tace "Nan ma yayi" yayi murmushi yace "Ohk" shiru tayi sai kuma a hankali ta hau ta dawo kusa da shi, nan ta fara basa story din Joseph according to the new testament of their Holy Bible, jin shirun yayi yawa ta dago tana kallonsa taga idonsa lumshe, murya can kasa tace "Doctor..." taji shiru, tsura ma long lashes dinsa ido tayi snn ta sauke idonta kan cute lips dinsa, bacci yake hankalinsa kwance, murmushi tayi ta gyara masa kansa a hankali snn ta koma can karshen gadon ta kwanta ta juya masa baya, nan da nan ita ma bacci ya dauke ta, can cikin dare ya farka ya mike xaune da sauri ta dalilin hasken dakin don wuta a kunne yake har lkcn kuma dama shi bai saba kwana da wuta ba, ya juya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login