Showing 66001 words to 69000 words out of 180592 words

Chapter 23 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1142

ido ya rike kai yana tunanin mafita, dago kai yayi bayan kusan minti goma jin fitowar Samha daga kitchen, kallonta yake har ta karaso parlor ta xauna, ya sakar mata murmushi yace "Weldone" jin bata ce komai ba yace "Dear!" Ta kallesa ya ce "An fara Reg din Jamb, gobe sae mu je ki yi koh?" Kallonsa kawai take bata ce komai ba, yace "Yeah gobe da safe in shaa Allah" daga haka ya mike ya shiga daki. Suna breakfast the next day ya sa ta shirya suka fita reg din Jamb din, sae kusan da rana suka dawo gida, bae bari tayi girki ba ya fita ya siyo masu abinci, daren ranan ya dinga tunanin ko dae ya kira small mum dinsa yyi mata maganar CV dinsa ne, yanke shawarar yin hakan yayi daga karshe, washegari lahadi yana xaune balcony ya hango Hajiya Hajarah xaune daga nata Balconyn da laptop gabanta, ganin ta kallo inda yake ya mike ya nufi gun ta, ya d'an dukar da kai yace "Ina kwana Mami?" Tana murmushi tace "Lafiya lau Boy, ya gidan?" Yace "Alhmdllh..." Tace "Ina Samha?" Yace "Tana ciki Mami" tace "Alryt wai in tambaye ka boy..." Kallonta yayi da sauri yace "Ina ji Mami" ta ajiye pen din hannunta ta nuna masa kujerar gabanta tace "To xauna" Ba musu ya xauna tace "Transfer aka yi maka xuwa garin nan?" Ya sunkuyar da kai yace "A'a Mami" tace "Ohk, naga kuma har yanxu baka koma aikin ba ko hutun mai yawa ka dauka, or rather let me put it this way...." Shiru ya d'an yi sai kuma yyi murmushi yace "Mami bana aiki yanzu" da mamaki tace "Baka aiki kuma?" Shiru yayi nan ma, ta sauke ajiyar xuciya tace "It's ohk Boy kar in shiga rayuwar ka koh!" Yar dariya yayi yace "Noo Mami ba haka ba, laifi nayi ma Abbana ya amshe CV dina and everything, that was why i left kano" kallon mamaki take masa, can ta girgixa kai tace "Duk a dalilin auren da kayi knn?" Ya gyada mata kai yana murmushi, tace "Toh ba a son yarinyar ne a gidan ku" nan ma ya gyada mata kai, tayi shiru tana kallonsa, sosai ta ji tausayinsa, can tace "But me yasa ka xabi aurenta da kayi ma iyayenka biyayya" A hankali yace "Mami haka Allah ya so" tace "Toh iyayenta fa?" Yace "Su ba ruwansu" Tace "Satin ku nawa da auren yau?" Yyi shiru kamar mai nazari sai kuma yace "Sati biyu da kwanaki" girgixa kai tayi tana kallonsa tace "Ur field?" Dago kai yayi ya kalleta yayi d'an murmushi yace "Am a Medical Doctor" kallonsa kawai take kafin tace "A doctor?" Yace "Yes Ma'am" ta cire glass din idonta tace "Where did you schl?" Yace "Uk nayi karatu Mami!" Tace "Ina matakin karatun naka?" Yace "Nayi degree, snn nayi masters duk a fannin medicine..." takardar dake gabanta ta dauka da pen ta mika masa tace "Am ur patient suffering from Malaria Typhoid, prescribe me drugs and injections...." Yar dariya yayi ya karbi takardar yace "Alryt Ma'am" ya gama rubuce rubucensa bayan kusan minti shidda sannan ya mika mata takardar ta karba ta sa glass dinta tana kallo, gyada kai ta shiga yi, sai kuma ta mika masa wani takardan tace "Prescribe for someone suffering from chronic stomach ulcer!" Karba yayi ya kuma rubuce rubucensa ya mika mata, ta karba tana dubawa tace "Um! Yayi kyau, kana theatre ne?" Yace "Ina yi Mami" ta basa wani takardan tace "Rubuta min procedure din yanda xa ayi operating din patient that's suffering from Appendix...." Karba yyi cikin yan mintuna ya gama ya mika mata ta karba tana kallo, murmushi tayi tace "Alryt Doctor, am offering you work at my clinic daga gobe, sai ka shirya da safe mu fita tare..." Ya buda ido yace "Am soo grateful Mamina" tace "My pleasure, but try to reconcile with ur parent kaji boy, kar mace ta hadaka da iyayenka" a hankali yace "In shaa Allah Mami" aikin da take yi a laptop ta juya masa gabansa tace "Idan baxan takura ka ba pls go on with this it's understandable, am already exhausted dama..." Yace "Alryt Mami" daga haka ya fara duba abinda take yi, duk abun nn da suke Fatima na lekensu don tun da taji muryarsa ta taho da sauri ta labe, tana ganin uwarta ta mike ta bar gun da sauri, Hajiyar na kallonsa tace "Xaka iya tafiya da shi boy, idan ka gama sae ka kawo min" yace "Alryt Mami," daga haka ya dau system din da takardun dake ajiye yayi mata sallama ya wuce, ita kuma ta shiga ciki, shara ya tadda samha tana yi a parlor ya girgixa kai ya xauna yace "Kin san me?" Ta kallesa ta ce "Mene?" Yace "Three things you never get tired of are, bathing, cooking and sweeping i notice" dariya ya bata sae dai bata yi ba tayi murmushi ta xauna tace "Toh sae ka tashi kayi" ya wara ido yace "Haba in tashi in yi" ta hararesa tace "Ehh" mikewa yayi ya nufi gun da ta ajiye broom din ta dauke da sauri kafin ya isa, karba yake son yi taki sake masa tace "Nooo, ka kyaleni...."

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
_Hafsat Ummu Ilham, i don't dedicate pages but here is a whole page for you dear sis, Am so grateful for the visit Allah ya bar xumunci sis ya raya su Ilham da Annur, Khaleesat heart you sisto_ =?
?

36.....

A can kano kuwa har gobe neman Abuturrab Abba yake, har imagining irin hukuncin da xae masa yake, Sosai Mami ta damu ganin har kusan sati bbu labari, to ina Aliyu xae kai yar mutane, kullum Hajiya Mariya sai ta xo gidan yayar tata tana kwantar mata da hankali amma ko kadan bata nuna tasan idan Aliyu yake ba duk da ta lura xargin ta yayarta take, Mahaifiyar Samantha kuwa ba don mai gidanta da ya hanata ba kotu dama tayi niyar kai karan, bata da aiki sae kuka da tsine ma Abuturrab ta kuma dau kudirin ko da ya dawo da Samantha kasheta kawai xata yi kowa ya huta don bata san mugun abinda yaje yyi mata, da dai ace ta xama musulma gwara ta kasheta a cewarta, bbu bata lkci ta shiga shirin tafiya Jerusalem don yin addu'an Allah ya dawo da Samantha tayi masa sacrifice dinta, mahaifin Samantha kam mutum ne mai saukin kai da boye damuwa baxa ka taba cewa abun na damunsa ba. Ranar Asabar Samha na kitchen tana kkrin daura girki da yamma shi kuma Abuturrab na xaune balcony rike da sabon system din da ya siya don bai iya rayuwa bbu shi, d'aga kai yyi ganin shadow din mutum, ya ga fatima tsaye daga bakin balcony din tace "Mum tace matar ka ta xo" daga haka ta juya ya bi ta da ido, haushin ta ya ji har cikin ransa, ko kadan yarinyar bata yi masa ba, ya ga alamar bata dau hali irin na mahaifiyarta ba sai girman kai, ya tabe baki ya mike ya shiga ciki, kallonsa Samha tayi jin abinda yace, can tace "Toh girkin fa!" Yace "Don't worry ki sa hijab ki tafi" ba musu tayi yanda yace ta fita xuwa part din Hajiya, tana parlor da duk 'yan matan nata uku sai wata dake xaune tare da fatima alamar kawarta ce, Samha ta risina ta gaisheta ta amsa da fara'a tace "Kadaici bai damun ki Samha, ki dinga shigowa nan ku saba da su fatima mana" murmushi Samha tayi tana wasa da fingers dinta tace "Toh" Hajiya tace "yauwa ko ke fa, xama ke dayan nn bbu dadi, ki dinga shigowa cikin mutane" kai samha ta gyada mata, Hajiya tace "Kar fa ki daura girki xa a kai maku idan an gama a nan kin ji" murmushi Samha tayi bata ce komai ba, Mami tace "Gobe su fatima xa su saloon sai ki bi su ki ga gari idan mijin ki ya amince, ke ma sai kiyi gyaran gashin daga can" Samha tace "Uhm to Mami" Fatima ta mike ta dalilin wayarta da yayi kara ta kalli kawarta Bilkisu tace "Gashi sun kira Billy" daga haka suka fita balcony, a waje Billy tace "Teemah new tenant din gidan nan ne yarinyar nn?" Fatima ta kalleta sae ta fasa d'aga wayar tace "Ehh" Billy tace "Kai amma yarinyar is pretty... Amarya ce koh?" Fatima tayi wani murmushi tace "Sai ma kin ga mijin xa ki san she is nt pretty...." Billy ta wara ido tace "Haba dai??" Fatima tace "Uhn He is more than cute, kin san Allah gabana faduwa yake idan muka hada ido da shi, but sai in wani daure fuska ko gaishesa bana yi" Billy tace "Waoww xan so in gansa kuwa" Fatima xata yi magana sai ga Samha ta fito ta sa takalmanta ganin yanda suke kallonta tace "Sannun ku" Billy tace "Yauwa!" Daga haka tayi wucewarta xuwa part dinsu duk suka bi ta da ido. Abuturrab yace "Har kin dawo?" Kai ta gyada masa tace "Tace xa mu je saloon gobe da yaranta" Shiru yyi yana kallonta sai kuma yayi murmushi yace "Allah ya kai mu" ciki ta shiga tayi kwanciyarta tun da tace kar tayi girki, fatima ce ta kawo masu abinci kusan Magrib bbu sallama ta shigo parlon, Abuturrab na xaune yana kallo a system Samha na gefensa ta jinginar da kanta jikin shoulder dinsa idonta a kan system din ita ma, a tare suka daga kai suna kallonta, ko kunya taji sai kuma ta sunkuyar da kai tace "Assalamu alaikum" Samha ce kawai ta amsa ta karaso ta ajiye abincin tace "Mum tace a kawo" Samha tace "Mun gode" daga haka ta juya ta fice. D'an tsaki Abuturrab ya ja can ciki, Samha ta kallesa tayi murmushi bata ce komai ba. Washegari khadija ce ta taho Balcony tana kallon Abuturrab dake duba newspaper da ya siya daxu da ya fita karo masu kaya a boutique, gaishesa tayi ya amsa tace "Wae Ummin mu in kira Anty Samha idan ta shirya" Abuturrab yace "Toh ga ta nan xuwa, ya sunan ki?" Tayi murmushi tace "Sunana khadija" yace "Alryt xan fadi mata Khadija" juyawa tayi ta wuce ya bi ta da kallo ganin banbancinta da yayarta, baxa ta wuce shekaru sha bakwai ba amma tafi yayar hankali, yana xaune parlor samha ta fito da hijab har kasa tana kallonsa, murmushi yyi yace "Cute" murmushin ita ma tayi, yace "Sae kun dawo but kar ki bari a dinga kalle min ke fa" dariya tayi yace "Yeah nikab ma xan siyo maki" kofa ta nufa ya bi ta da ido har ta fita, jiranta ta samu su Fatima na yi, Hajiya Hajarah tace "Toh sae kun dawo, Allah ya tsare hanya" driver ne xae kai su saloon din, fatima ta shiga gaban mota, Khadija da Rabi'ah suka xauna baya tare da Samha, su kadae suke mata hira har suka iso saloon din, fatima ta bude mota ta fita su ma suka fita suka bi bayanta xuwa cikin babban saloon din, khadija na kallon fatima tace "Big sis a fara yi ma Anty Samha koh?" Fatima ta kalli Samha ganin kallonsu take bbu yabo bbu fallasa tace "Alryt" daga haka taje tayi xamanta kan daya daga kujerun Saloon din sae dae can kasar xuciyarta ji take kamar ta shake yar uwar tata, Samha da Rabia aka fara ma gyaran gashin don akwae mutane saloon din, tun da aka bude kan Samha Fatima da duk yan saloon din ke kallo, matar mai gyara mata gashin sae cewa take "Maa sha Allah you've got a very fine long hair" Samha ta kirkiri murmushi bata ce komai ba sai dai duk a takure take ganin yanda ake kallonta, cikin minti ashirin aka gama mata ta mayar da hijab dinta da sauri, aka kama kan fatima sae dai ita kitso tace xata yi, ita din ma ba baya ba gun gashi, mai saloon din na kallonta tace "Baxa kuyi lalle ba Madam?" Khadija tace "Xa muyi" wani kallo Fatima ta watsa mata tace "ke da wa, waye xae jira kuyi lalle?" Khadija tace "Ae na tambayi Ummi tace mu yi" dauke kai fatima tayi bata ce komai ba, khadija aka fara yi ma snn Samha da taki yarda da farko har sae da Khadija da Rabi'a suka tilastata, suna saloon din har aka kira azahar, Khadija ta kalli Samha tace "Mu shiga daga ciki mu yi sllh Anty Samha" shiru Samha tayi sai kuma ta mike kamar mara laka ta bi bayanta, Khadija ce ta fara alwala a toilet ta fito snn Samha ta shiga, tsura ma tap din ruwan ido tayi, lkci daya xamanta gidan kanwar Abbanta ya fado mata, a hankali ta bude ruwan ta shiga alwalan kamar yanda take yi a kaduna da yaran Aunt dinta, tana gamawa ta fito ta ga Khadija ta shimfida mata wani darduma ta saka hijab dinta ta hau kan darduman babu abinda ta mance a ynda ake sllhn sae d'an abinda baka rasa ba, har hakan ya bata mamaki, tana idarwa Khadija tace "Me xa a karbo maki?" Murmushi Samha tayi tace "Bana jin yunwa..." Khadija bata ce komai ba ta fita, samha ta mike ta bi bayanta, snacks da drinks Khadija ta sa driver ya karbo masu, bbu yanda samha ta iya haka ta karba, ba su suka bar saloon din ba sai kusan karfe uku, part din su suka tafi gaba daya, Hajiya ta yi masu sannu da xuwa tana kallon Samha tace "Har kun dawo?" Samha ta gyada mata kai, tace "Toh sannun ku daughter, bari a xubo maku abinci" Samha tace "Ae mun ci" Hajiya bata saurareta ba tasa mai aiki ta xubo masu abinci gaba daya, har aka yi la'asar tana parlon, Hajiya tace "Khadija ku shiga ciki ku yi sllh" Khadija ta kalli Samha tace "Muje daki muyi sllh" ba musu Samha ta mike ta bi bayanta xuwa bedroom dinsu, kamar daxu haka tayi sllhn suka fito bayan sun idar, nan Hajiya tasa mai aiki ta xuba mata abinci ta kai ma Abuturrab, ta karbi abincin tayi godiya ta fita, Kwance ta samesa parlor yana bacci, ta ajiye abincin hannunta ta durkusa kusa da shi tana kallonsa tace "Doctor!" Bude ido yayi a hankali, ta langwabar da kai tace "Anyi sllh fa" ya mike xaune yana shafa fuskarsa, tace "Are you okay?" Girgixa mata kai yayi yace "Am having headache..." Tace "Toh kayi sllh sai kaci abinci then you take drugs" tana magana amma ido da hankalinsa na kan kunshin hannunta, ta bata rai tace "Ina maka magana" kamo hannunta yayi murya can kasa yace "Waow, baby kunshin yayi kyau sosai, i like it" ta kwace hannunta tace "Thanks" ya d'an marairaice mata yace "Toh baxan ga gyaran gashin ba?" Murmushi tayi ta cire Hijab din jikinta tana kallonsa, ya lumshe ido underneath his breathe yace "I have always loved you from the very first day i saw you Samha!" Kallonsa kawae take, ya bude ido a hankali yace "Tell me daga ina kike that very Night?" Murmushi tayi xata mike ya jawota jikinsa yace "Noo, talk to me baby" murmushin ita ma tayi tace "I don't want to talk about that now!" Yace "Noo plss baby..." Ganin yanda ya zuba mata manyan idanuwansa ta sauke kanta kasa a hankali tace "My frnd forced me to her birthday party, ni ban san it's an indecent party ba, shine na gudu na bar wajen..." Bude kofar parlon aka yi ta xame jikinta da sauri dai dai lkcn da fatima ta shigo, ta sunkuyar da kai ta karaso parlon, Samha ta xamo kasa a hankali ta xauna, takardun hannunta ta mika ma Abuturrab tana kallonsa tace "Ummi tace in baka wannan..." Mikewa yyi bbu yabo bbu fallasa yace "Drop it!" Daga haka ya shiga bedroom, ta bi sa da ido, Samha ta kirkiri murmushi da kyar ta karba tace "Bari in ajiye" sake mata fatima tayi ta juya ta fice daga parlon. Samha ta mike a sanyaye rike da takardun ta shiga dakin da ya shiga, xaune ta gansa gefen gado ta durkusa kusa da shi tace "Me yasa kayi mata haka?"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
_Tohm ya na iya tunda Ummu Ilham na da 'yan adawa irinsu Chamo, Zaarah, Teemahluv, Deezoh... Gasu nn dai=?D? su ma kuma sun ce sai fa an masu baxa su yarda ba, toh ina ku ke gashi nan sai ku kacalcala shi bbu ruwana naku ne_ =??

37

Dagota yayi ya xaunar da ita gefensa yace "Kinsan me Baby?" Ta girgixa kai yace "Hajiya ta ban aiki...." Samha tace "Aiki kuma?" Yyi murmushi yace "Yeah she's also a medical doc...." Tace "Uhm hw did she know you re a doc?" Yar dariya yyi yace "Taga bana xuwa aiki shine ta tambaya nd i told her nayi ma Abbana laifi shi yasa na bar kano..." Xaro ido tayi tace "You told her everything??" Kamo hannunta yayi yace "No i didn't love!" Sunkuyar da kanta tayi, ya daura hannunsa kan dogon gashinta murya can kasa yace "Haka xa ki haifa min yara masu irin gashin nn kin ji" da sauri ta fara kkrin sauka daga kan gadon yaki saketa, kmr xata yi kuka tace "Doctor baka yi sllh ba fa..." Dariya yayi yace "Sai in tare xa mu yi bby" ta kallesa tace "Uhm ae yau na yi!" Yace "Dagaske?" Tayi murmushi tace "Yeah nayi Zuhur a saloon, nayi Asr a gun su Ummi" ya wara ido yace "Don Allah da gaske Baby, toh me da me kika ce a sllhn" wara ido tayi tace "Na fa ce maka ina yi a kaduna, rayuwar da nayi a kd a da yafi wanda nayi a kano da parent dina, am still missing my aunt, amma Mum dita ta rabamu wai she's putting me in the islamic way..." Abuturrab da ke ta kallonta yace "Toh me Abba yace?" Ta wara ido tace "Toh me xai ce? He said nothing, for the past 3yrs aunt dina bata xo gun mu ba..." Abuturrab yyi murmushi yace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login