Showing 102001 words to 105000 words out of 180592 words

Chapter 35 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1149

kawai yake, mai adai daitan na tsayawa kofar gidan ya kalli Samha, a hankali tace "Toh me xaka ce ma Ummi?" Fitowa yyi ya ba mai adai daitan kudinsa ita ma ta fito, murmushi yyi yana shafa kai yace "I don't know wht to say, ko xaki fadi min abinda xan ce" ta tabe baki tace "Ni ba ruwana" yar dariya yyi ya kama hannunta suka shiga compound din bayan ya amsa gaisuwar mai gadi, kamar ynda yyi tunanin hakan ne don Ummi na xaune balcony tana aiki, Samha ta xame hannunta daga nasa, a hankali yake tafiya har ya isa Balcony din, Ummi kam tun da tayi masa kallo daya dama ta ci gaba da abinda take, durkusawa yyi nan gabanta sai kuma ya rasa abun cewa, kallon Samha dake tsaye gefe tana wasa da yatsunta tayi ta girgixa kai ta mayar da dubanta kan laptop dinta, da kyar Abuturrab yyi gathering courage yace "Mami ina yini?" Kallonsa tayi kafin tace "Lafiya lau" Samha ta d'an risina ta gaisheta ita ma ta amsa snn ta ci gaba da abinda take, ganin ba magana Ummi xata yi ba ya mike, har xai bar gun tace ya dawo, dawowa yayi ta kalli Samha tace "Ki shiga bedroom dina akwai makulli a kan study table ki dauka" shiga parlon Samha tayi, Ummi na kallonsa tace "Sai da kaje ka lalata masu rayuwar ya snn ka dawo knn, i never knew takura ka nake Aliyu amma it's a promise am making now baxan sake shiga rayuwar ku ba" da sauri yace "Wllh ba haka bane Mami, gun kanwar Abbanta na kai ta kaduna, she's a muslim nd.... Mami basu bari muka bar garin ba sai da suka tabbatar na aureta, am saying nothing but d truth, kuma sai da naje kano gun Mum dina, I begged her for forgiveness, i knw i failed u Mami amma don Allah kiyi hakuri kar ki hukunta ni...." Ummi dake ta kallonsa tace "Did i deserve u going without telling me Aliyu, xan hanaka don kace min xa ku gun aunt dinta? Ni baxan hana ka ba sai dai ko in hada ku da wani ku je tare, haka kke abun ka bbu reasoning Ali?" Sunkuyar da kansa yyi kasa yace "Am so sorry Mami nasan ban kyauta ba ki yafe min" Samha na fitowa daga parlor rike da makullin Ummi tace mata taje ta bude kofa a can, tana barin gun ta girgixa kai tace "Idan ma kun tafi without knowledge dina baka da wayar da xaka kira ni daga baya?" Shiru yyi bai ce komai ba, can ta girgixa kai tace "Gaskiya i was so surprise at you, you failed my trust for you" a hankali yace "Kiyi hakuri Mami..." Tace "Anyway, tashi kaje, Allah rufa asiri, it's good she's now ur wife" bai iya ya mike ba, can ya ciro kudin aljihunsa ya mika mata yace "Aunt dinta tace in bata sadakinta, ko xa ki siya mata abu Mami" ba musu Ummi ta karbi kudin ta ajiye a gefenta, ya mike da kyar ya bar gun. Har Samha ta fara gyaran gidan kafin ya taho, yayi dusting kujera ya xauna yace "You need rest dear, drop that broom now" ba tare da ta kallesa ba tace "I can't endure resting in dirt..." Kallonta yyi sai kuma yayi murmushi yace "Toh baturiya, transform the house as you wish" kallonsa tayi ita ma tace "You watch nd see..." Kwankwasa kofa aka yi ya mike ya isa kofar ya bude, mai aikin Ummi ce tsaye ta gaishesa ya amsa snn tace "Madam tace in xo in taya ta gyaran gida" hanya ya bata yace "Alryt" bedroom ya wuce ya bar su parlon, yana sllh ya cire bedsheet yyi kwanciyarsa, kafin karfe biyar da rabi suka gyara ko ina na gidan ya rage dakin da yake ciki kawai, Samha tace "Nagode sosai xa ki iya wucewa Anty" daga haka mai aikin ta wuce ita ma ta shiga bedroom din da Abuturrab yake, karasawa tayi kansa ta ja pillon da yake kwance kai tace "You call ur self a doctor amma kuma xaka iya bacci peacefully cikin dusty room din nn?" Har lkcn bai bude ido ba, ta hade rai ta buga gadon tace "Ni ka tashi in gama gyara na, you can go to the other room and continue" bude ido yyi ya fixgota jikinsa yana kallonta yace "Ashe kin iya magana haka Samha?" Kwace kanta ta shiga yi yaki sake ta ya mike xaune yana murmushi yace "One thing about you is that, you can pretend for africa" kwace kanta tayi ta mike ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fice daga dakin snn ya mike ya bi bayanta. Da magrib mai aikin ce ta kawo masu abinci duk da ya riga ya siyo masu, yana xaune shi daya parlor yana danna laptop khadija tayi sallama ta shigo, durkusawa tayi nesa da shi tace "Uncle ashe kun dawo, ya hanya?" Yana murmushi yace "Lafiya lau khadija, ya karatu?" Tace "Alhmdllh, ina sis Samha fa?" Mikewa yayi yace "Let me check her tana ciki" daga haka ya nufi bedroom, yana shiga tana fitowa daga wanka daure da towel, tayi masa kallo daya ta wuce can karshen gado ta xauna, ya bi ta da ido, satan kallonsa tayi ganin kallonta yake ta bata fuska tace "I want to dress up..." Rufe kofar dakin yayi yace "You re free" mikewa tayi xata koma bayin ya rikota, ta wani hade rai tace "Bna so, bana son haka doctor...." Shi ma ya hade giran sama da ta kasa yace "Baki son me?" Fashewa tayi da kuka, ya buda ido yace "Ehenn, me nayi maki" ganin da gaske take ya xauna gefen gado ya xaunar da ita gefensa yace "Khadija fa na jin ki a parlor, daga magana sai ki fara min kuka?" Kallon kofar dakin tayi tana share idonta, lumshe ido yyi ya rungumeta yana shafa gashinta ya kai bakinsa kunnenta yace "Hope anjima dai baxa ki ce min baki so ba don ko kukan jini xa ki yi ba wannan xancen yau..." Shiru tayi bata ce komai ba, ya saketa yana murmushi yace "Ki shirya tana jiran ki a parlor" ta gefen ido ta hararesa ta mike ta nufi press din kayanta, ya gyada kai yana murmushi har lkcn ya fita.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
63.....

Tana gama shirinta ta fita parlorn, xaune ta tadda khadija har lkcn, ta karasa tana murmushi tace "Maimakon ki shigo ciki" khadija dake kallonta ita ma tana murmushin tace "Yanxu Ummi ke ce min kun dawo sister, ya hanya" Samha ta xauna gefenta tace "Alhmdllh, ya makaranta?" Khadija tace "Lafiya lau" fruits dake cikin wani bowl Samha ta mike ta kawo ta ajiye mata tace "Rabi'ah fa?" Khadija tace "Ae har yanxu bata dawo gida ba" Samha tace "Ayya, sis fatima fah?" Khadija tace "Tana cikin gida" Apple kawai khadija ta dauka ta mike tace "Bari in je dare yyi sis Samha sai gobe" Samha ta kalli agogo tace "Da wuri haka" dariya kawai khadija tayi tace "Xan goge hijabs dina kafin in kwanta ne" daga haka ta kalli Abuturrab dake ta danna laptop tace "Uncle sai da safe" ya kalleta yace "So early Dija" murmushi tayi ta nufi kofa yace "Toh ki gayar da Mami, Yusuf na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Yana Egypt" yace "Alryt" har balcony Samha ta rakata suka yi sallama sannan ta dawo parlor ta dau bowl din sauran fruits din ta ajiye a fridge, yace "Ke baxa ki sha ba?" Girgixa kai tayi tace "Na koshi" daga haka ta wuce daki, hijab din jikinta ta cire tayi kwanciyarta ta rufa da blanket. Sai kusan karfe sha daya Abuturrab ya gama abinda yake ya mike ya rufe gidan snn ya kashe wutan parlon ya dau laptop dinsa ya wuce daki, ajiye laptop din yyi gaban mirror ya kunna ac din dakin ya shiga bathroom don yin wanka, yana shiga bayin ta mike don dama ba bacci take ba ta dau hijab dinta ta fice daga dakin ta koma daya dakin ta shiga ta rufe tayi kwanciyarta, ko da ya fito murmushi yayi da bai ganta a dakin ba, ya gama shirinsa har da ya kwanta sai kuma ya mike ya nufi dakin da ta shiga, ta wani rufe ido kmr me bacci ya karasa kan gadon yace "Why did you leave the room" bata bude idon ba bare ta basa amsa, ya kafa mata ido yana kallo, hannu ya daura forehead dinta yace "I kiss you now idan baki bude ido ba" bude idon tayi ta mike xaune ta hade rai tace "Doctor ni fa ina ce maka bna son irin haka," kallonta ya tsaya yi can ya fixgo shoulders dinta yana mata wani kallo yace "Baki son me knn?" Ja baya tayi ta kauda kai ta tsuke baki, yace "But me yasa lkcn da kike xuwa wajena can gida bakya cewa baki son ina taba ki, you like it then koh?" Ta kallesa da sauri sai dai bata ce komai ba, ya daga kafada yace "Yeah, ynxu ne baki so but you like it then i notice" Sauka ta shiga kkrin yi daga kan gadon ya fixgota ta fashe da kuka, ji yyi ransa ya baci ya fixge hijab din jikinta yace "Sai kiyi na jini ma in ga ai" ta hade kanta da gado tana rerawa, har ya mike xai fita sai kuma ya fasa, ya dake ya xauna ya dagota yace "What's the meaning of this Samha, Where is d love?" Bata bari sun hado ido ba, ya dago kanta yace "look at me Samha" a hankali ta dago manyan idonta tana kallonsa, murya can kasa yace "Wahala kike son bani don kin ga ina son ki da yawa ko, me yasa tun da baki min haka ba sai yanxu?" Sauke idonta tayi kasa ya jawota jikinsa yace "Baki sona yanxu koh?" Kamar xata yi kuka tace "A'a" yace "Toh me yasa kike cewa baki son in taba ki" ta fashe da kuka a hankali tace "Ni tsoro nake ji" ya buda ido yace "Tsoro kuma? Tsoron me?" Bata ce komai ba kuma bata daina kukan ba, yace "Talk to me mana Wife, tsoron me?" cikin muryar kuka tace "Kai..." sosai ta basa dariya ya dake yace "Ni kuma, toh me nayi maki kike tsorona" k'in cewa komai tayi yana shafa gashin kanta yace "Ki gaya min mana tsoron me nake baki dear, baki son gani na ne kuma?" Girgixa kai tayi, yace "Then me nake maki da baki so?" A hankali tace "Bana son kana taba ni..." Shiru yyi, sai kuma yace "Why?" Tace "Saboda ni dai bana so" murmushi yayi yace "Amma da a can gida baki ce min baki so ba ai" Kallonsa tayi tace "A'a ka dai manta, duk san da ka taba ni ae bana sake xuwa sai an dade" yace "Hmmm, shknn na daina taba ki tunda baki so" daga haka ya saketa ya koma baya yace "Is that all?" Kai ta gyada masa ya mike yace "Quite alryt...." Sannan ya nufi kofa yana murmushi can underneath his breathe yace "Nasan maganin ki" bin sa ta yi da ido har ya fita kafin tayi kwanciyarta. Washegari da ya kasance monday ko kafin Abuturrab ya fito duk ta gama gyaran gidan gaba daya tayi wanka ta shirya cikin abayarta, Tun takwas mai aiki ta kawo masu breakfast in ji Ummi, Kallo daya yyi mata yayi xamansa parlor yana kkrin bude laptop dinsa, tace "Ina kwana?" Ba tare da ya kalleta ba yace "Lfya baby" tace "In kawo maka breakfast din yanxu?" Ya girgixa kai yace "Nop" kwankwasa kofa aka yi ta mike ta isa kofar ta bude, Fatima ce tsaye sanye cikin abaya da jaka a hannunta ta sa siririn glass a ido Kallon kallo suka dinga yi na kusan second goma, can Samha ta dake tace "Ina kwana" Fatima tace "Alhmdllh, Doctor na ciki?" Kai kawai Samha ta gyada mata, d'aga wayarta dake ring tayi ta bi ta gefenta ta shige parlor Samha ta bi ta da ido, Tsaye tayi d'an nesa da shi tana ci gaba da waya da kawarta da ta kirata, Abuturrab da bai dago ba tun shigowarta, cab ya juya ya kalli bakin kofa suka hada ido da Samha kallon Fatima da ke kkrin mayar da wayar jaka bayan ta gama yyi, ta dago suka hada ido, kirkiran murmushi yyi yace "Morning" sosai tayi mamakin hakan ita ma ta mayar masa da na yake tace "Good morning" yace "Ya boko?" Tace "Alhmdllh" idonsa ya mayar kan laptop yace "Wani course kike?" Tace "MBBS" kallonta yyi daga kasa har sama kafin yace "Lvl?" Tace "300" yayi d'an murmushi yace "Nyc" Tace "Thank you" ya mayar da dubansa laptop yace "Welcome" "Dama Ummi ce tace ka je" ta fadi hakan tare da juyawa tayi hanyar kofa yace "Alryt" Samha na nan tsaye inda take tun shigowar fatima, Abuturrab ya saci kallonta ya dauke kai ya ci gaba da abinda yake, fatima na fita ko rufe kofar Samha bata yi ba ta nufi hanyar daki, ya kalleta da sauri yace "Dear a ban break din yanxu i think am hungry" ko kallonsa bata yi ba ta shige daki, yar dariya yyi ya mike ya fita xuwa kiran Ummi, suna gaisawa tace "Are you still interested with the job or i give someone?" Yace "I am Mami" tace "When re you resuming?" Yace "Probably today" tace "You leave it tomorrow" godiya yyi mata ya mike ya bar parlon, yana komawa part dinsa tea kawai ya hada ya sha ya fita, compound ya tadda khadija ya sa ta dauko masa makullin mota ya fita siyo masu foodstuffs, sai kusan karfe goma ya dawo gidan mai gadi ya taimaka masa fiddo kayan abincin xuwa cikin gida, shi kuma ya karasa da su kitchen, bedroom din da take ya nufa ya ganta kwance idonta rufe, karasawa yyi ya xauna gefenta ya kamo hannunta yace "Baby baki ban breakfast ba fahh" mikewa tayi xaune kmr warce aka tsikara tace "But i told you, i warned u bana son kana taba ni, i don't like it...." Kallon ynda ta hade rai sosai yake yi, can ya mike yace "And that's because i forgot" daga haka ya fice daga dakin. Makullin mota ya kuma dauka ya fice daga gidan, bai dawo ba sai bayan isha ya samesu tare da khadija a parlor, khadija ta gaishesa ya amsa da fara'a ya wuce daki, ba a dau lkci ba khadija ta wuce ita ma ta mike ta shiga daki, kwanciya tayi don tayi wanka, can ta gaji ta mike xaune ta hade kai da gwiwa sai hawayen da bata san dalilinsa ba, ta kusa awa biyu a hakan, can ta mike da kyar tana kallon agogo taga karfe goma, tashi tayi kamar mara lafiya ta fita dakin ta wuce nasa, dai dai fitowarsa wanka yana sanye da bathrobe yana goge gashin kansa yyi mata kallon gefen ido ya xauna bakin gado yace "Baby baki yi bacci ba" bata ce komai ba shi ma bai kalleta ba, yana ci gaba da goge gashin ya jawo wayarsa yana danne danne, still ba tare da ya kalleta ba yace "Hope kin ci abinci?" Nan ma bata ce masa komai ba ya mike ya isa gun kayansa ya fiddo pyjamas dinsa, muryarta ya ji a hankali tace "In kawo maka abinci?" Yace "No baby, na ci abinci a waje..." Daga haka ya nufi gaban mirror ya shafa man da xai shafa a gashin kansa ya sa turare, sai a snn ya juya ya kalleta yace "Hope kema kin ci abincin?" Hawaye ya gani idonta, ya buda ido yace "Toh kuma, did i still touch you?" Juyawa tayi ta fita daga dakin, ya girgixa kai ya ci gaba da shirinsa ya gama saka sleeping wear dinsa snn ya fita dakin ya shiga nata, bai ganta a bedroom din ba sai sautin kukanta da ya dinga ji a bathroom, bathroom din ya shiga da sauri ya ganta durkushe tana rera kuka, da mamaki yace "Are you okay Samha?" Hade kanta tayi da gwiwa, ya dagota ta kuma rushewa da kuka ya ja ta suka fita bayin, xaunar da ita yyi gefen gado yace "What's d meaning of all this Samha, kina da damuwa ne?" Rungumeta yyi ganin ba shiru xata yi ba yace "Samha me yasa kike son ki dinga tada min hankali" dago kanta yyi yana kallonta taki bari su hada ido, hade bakinsa yyi da nata yana kallon idonta, ta rufe idon da sauri, ya kwantar da ita a hankali ya fara sarrafa ta, sun dau lkci me tsayi kafin ta bude ido da kyar xuwa lkcn ko ina na jikinta bari yake, dai dai kunnenta cikin sanyin murya yace "Baby don't tell me no plss, you've punished me enough" ta fashe da kuka tace "Doctor noo" daga haka ta turasa iya karfinta ta ja bargo har kanta, wani irin kallo yake mata na kusan minti biyar kafin ya mike ya fice dakin. Washegari tun bakwai ya bar gidan tana kitchen tana hada breakfast ya gama warming mota ya dau hanyar clinic, Tana jin fitansa dama ta kashe komai ta koma daki tayi kwanciyarta.

*Haske writers asso*

Sorry!!
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
64.....

Kusan a tare suka shigo compound da fatima da yamma, bai je parkn space dinsa yyi parking ba yayi a compound din ita ma haka, Samha da khadija da mai aikinsu na xaune gaba dayansu a balcony dinsu khadijan, Abuturrab ya kulle motarsa ya d'an kalli fatima dake kkrin kulle mota, suka hada ido tace "Ina yini" yace "Lfya lau, ya lectures" tace "Ban yi lectures ba yau, had an attack da safe" yace "Subhanallah, bakya fita da mask ne" Ta girgixa kai tace "I don't" duk hankalin Samha na kansu duk da hiran da mai aiki ke masu, Abuturrab yace "May be you re enjoying d attack" murmushi tayi tace "not really" Mikewa Samha tayi tana kallon su khadija tace xata shiga gida daga haka ta bar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login