Showing 132001 words to 135000 words out of 180592 words

Chapter 45 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1141

ta lafiya" yace "A siyo take away kawai koh?" Ta girgixa kai tace "A'a xan iya girkin"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
80.....

Samha bata iya ta karasa girkin tuwo da miyar ganye, sai jollof din da ta fara ba ta dinga jin jiri da tashin xuciya, bedroom ya wuce da ita ta kwanta, da damuwa yace "Sannu baby shi yasa nace mu siyo take away kika ce xa ki iya" bata ce komai ba sai rufe idonta da tayi, ya langwabar da kai yace "Bari in kira khadija ta karasa maki ko baby..." Bude ido tayi tana kallonsa, yace "Yau Saturday nasan she's at home" bata ce komai ba ya mike ya fita, Ummi kadai ce xaune parlor tana kallon wani program, ya xauna suka gaisa snn yace "Mami khadija na nan don Allah" tace "Ehh tana ciki" yace "Dama Samha ce ta fara girki kuma bata iya ta karasa ba...." Ummi tace "Ayya, toh bari ta fito ta karasa mata" daga haka ta kirawo khadija tace "Dear ki tafi ki taya Samha aiki kin ji" Khadija tace "Toh" daga haka suka fita tare da Abuturrab da yyi ma Ummi gdya, Khadija na shiga kitchen din ta ci gaba daga inda Samha ta tsaya shi kuma ya shiga dakinsa, waya ya dauka ya kira Anty Maryam tana dagawa suka gaisa yace "Kin taso kuwa Anty?" Tace "Eh tun safe na taso Aliyu, mun ma yi nisa" yace "Toh Allah ya kawo ku lfya, ya kiyaye hanya, idan kun iso park sai ki kirani xan xo in dauke ki" Tace "Ameen Aliyu, Alryt xan kira ka" yana ajiye wayar ya fita ya shiga dakin Samha ya sameta tana bacci, ya kalli agogo ya daura hannu fuskarta a hankali yace "Dear baxa ki daure ki shirya ba kafin Aunt din tawa ta xo?" Da kyar ta bude ido tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "Yes, ki daure kin ji babyna, ko in taya ki wankan?" Gyada masa kai tayi, ya dagota xaune ya cire mata yar rigar baccin jikinta ya shiga bayi da ita. Abaya ya fiddo mata bayan sun fito bayin, ya shafa mata lotion ta sa kayan snn ya daure mata gashinta da ribbon ya fesheta da turare yana murmushi yace "Kin yi kyau wife" hararansa tayi ta kwanta, kafin karfe daya Khadija ta gama girkin ta wuce. Yana kwance gefen Samha dake bacci yana kallo a tv wayarsa yyi ring, ganin Anty Maryam ce ya mike xaune ya daga, tace "Aliyu mun iso fa" yace "Toh gani xuwa Anty" daga haka ya tashi yana kallon Samha, bai tasheta ba ya dau mak?????
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
?
 ulli ya fita, uku da yan mintuna ya isa park din, da fara'arsa ya nufi Anty Maryam dake tsaye rike da hannun autarta ya gaisheta, ta amsa da murmushi tace "Mun same ku lfya" ya duka ya dau kyakkyawar yarinyar da baxa ta wuce shekara hudu ba yace "Pretty how are you" yarinyar tace masa "Fyn" ya wara ido yace "Waow, then what's ur name" kallon uwarta tayi, Anty Maryam tace "Have u forgotten ur name?" Yarinyar tayi dariya tace "I am Ihsan" shafa kanta yyi yana murmushi yace "Welcome little Ihsaan" daukar jakarsu yyi yace "Anty ga mota can" Anty Maryam tace "Okay" daga haka suka nufi motar ya bude mata baya ta shiga ya mika mata ihsaan snn ya rufe motar ya xaga ya shiga maxaunin driver, suna isa gida yyi parking ya juya yana kallon Anty Maryam murmushi dauke fuskarsa yace "Anty bata san fa ku ne bakin da xa su xo ba" tayi dariya tace "Au haba" ya bude motar yace "Wllh kuwa Anty" bude motar tayi ta fito da ihsaan ya dau kayansu yace "This our home Anty" Tace "Maa sha Allah, Allahu ya ci gaba da hada kanku" yace "Ameen Anty" tana biye da shi suka wuce balcony ya bude kofar parlorn suka shiga, Xaunawa Anty Maryam tayi da autarta, ya nufi fridge ya dauko masu ruwa da drink da cups ya ajiye ya xuba masu ya mika ma Ihsaan nata yace "Take pretty" Karba tayi tace "Thank you" yana kallon Anty Maryam yace "Anty ga ruwa bari in taso ta, bacci take" daga haka ya wuce daki, har lkcn kuwa baccinta kawai take, ya xauna kusa da ita ya dinga shafa mata fuska a hankali yana jan hancinta, ta bude lumsassun idonta tana kallon sa, yace "Baby har yanxu baccin dai" murya can kasa tace "Am very hungry" Yace "Toh muje ki gaida aunt din tawa sai ki ci abinci" Da sauri ta mike xaune tace "Ta xo?" Yace "Yea naje park na daukota yanxu" kamar xata yi kuka tace "Ae ban ma gama girkin ba doctor" yace "Khadija ta karasa maki dear" Shiru tayi bata ce komai ba ya mike ya dagota ta tashi tsaye ya bata veil din abayar ta yafa a kai, kallonta yake ganin yanda Abayar ya fito mata da cikin jikinta sosai, yaga tayi masa kyau ba kadan ba, kallon kanta tayi ganin irin kallon da yake mata ta daure fuska ta koma ta xauna tace "Ni baxan iya fita da kayan nan ba" Ya wara ido yace "Me yasa baby?" Tace "Bana so" yace "Ya fa maki kyau sosai dear plss mu je haka tana ta jira fa" kmr xata yi kuka tace "Ni baxan iya ba" yace "Toh sbda me" tace "Ni dai Hijab xan sa" murmushi yyi yace "See you, to ance maki bata da ido ne, ko me xa ki sa ai ba boyuwa abinda kike boyewa xai yi ba" kallonsa take kmr xata yi kuka ta wani hade rai, yyi dariya ya dagota ya rungumeta ta baya yana shafa cikin yace "Baby plss mu je tana ta xaune parlor fa ita kadai" daga haka ya kama hannunta suka fita tana nonnokewa ita a dole kunya, suna shigowa parlon ta tsaya cak tana kallon warce ke xaune tana kallonta murmushi dauke fuskarta, wani kara tayi ta nufeta a guje, har cikin ransa yaji uban tsallen da ta daka, ita kanta Anty Maryam sai da tace "Ke kina da kai kuwa Daughter" bata ko saurareta ba ta fada kanta ta kankameta tace "Antynahh dama ke ce" Anty Maryam tace "Xa ki ji ma kan ki ciwo fa, kina da kai ma kuwa" Shi kam sai kallonsu yake, can ta sake Anty ganin Ihsan ta rungumeta ita ma tace "Anty me yasa baki taho da Asiya da Farouq ba" Anty Maryam tace "Suna gun grannynsu" Rasa inda xata sa Auntyn tata Samha tayi da ganinta tayi farin ciki ne ba na wasa ba, duk sai Anty Maryam taji tausayinta barin ynda taga ta rame, ganin ba kyale Antyn xata yi ba Abuturrab yace "Anty ku yi sllh ku ci abinci, kun kwaso hanya fa" Sai a snn Anty Maryam ta yakice ta jikinta ta mike suka wuce daki, har bedroom ya kai masu abincin don bai ga alamar Samha xata yi hakan ba, Anty Maryam tayi dariya tace "Aliyu kai ne da wahala haka" yyi murmushi yace "Toh Anty naga taki kawo maku ne, kuma da ita ke jin yunwa bbu me kwanciyan hankali sai ta ci" Samha dake jikin Anty Maryam ta daure fuska ta turo baki, ya juya ya fita dauko sauran abincin, Anty Maryam tace "Ji shashanci daga yana maki wasa sai ki hade rai ki cunno baki gaba" tace "Bana son wasan" Anty Maryam tace "Toh ina laifinsa, naga dai duk ni yake ma hidimar ko baki ji dadin hakan ba" tace "Toh ai nima nayi masa da nasa yan uwan suka xo" Anty Maryam ta hade rai tace "Toh ya ishe ki bana son fitsara, yaushe kuma kika xama fitinanna" Samha bata ce komai ba ta dauke kai, a haka Abuturrab ya shigo ya samesu ya ajiye abincin yace "Ga shi Anty, ku ci abinci" Anty Maryam tace "Sannu Aliyu nagode" satan kallon Samha yyi ya fita, ba dau lkci ba ya dawo kuma rike da plate din abinci ya ajiye gabanta yace "Kin ce kina jin yunwa ga abinci" kallon abincin tayi tace "Am nt any longer" Ajiye ma Ihsan abincin yyi yace "Pretty ke ki ci" Anty Maryam dai kallonta kawai take ganin har lkcn ita fushi take, murmushi kawai tayi ganin condition dinta ta kuma san ba laifinta bne, tunanin irin abubuwan da uwarta tayi lkcn da take dauke da cikinta take da irin wahalan da ta sha, can tace "Daughter daga magana sai fushi, to yi hakuri" ita dai bata ce komai, har Anty Maryam ta gama cin abinci Samha na xaune ta xuba ma tv ido, Anty Maryam tace "Yauwa daxu kin ce min yan uwansa sun xo?" Sai a snn Samha ta kalleta tace "Ehh" Anty Maryam tace "Amma bnda Mum dinsa koh?" Tace "A'a kanwar mum dinsa ce sai sisters dinsa biyu" Anty Maryam tace "Ayya, did they stay long?" Ta girgixa kai tace "Just 2 days suka yi" tace "But are they okay" Samha ta kwantar da kanta tace "Yes his mum sis is very kind, har da zinari ta ban na dan kunne, sisters dinsa kawai ne basa so na" a hankali ta kare maganar, Anty Maryam tace "Don't worry duk xa su so ki kin ji Daughter, everything is just time" Daga haka suka dinga hira har aka kusan Magrib, shi kuma Abuturrab yana bedroom dinsa da Ihsaan suna kallon cartoon, yana yin alwala yace "Pretty kije Mumy ta sa maki cartoon a can dakin xan je masallaci" tana fita ya wuce masallacin, Anty Maryam na idar da sllh ta kalli Samha tace "Ke ko ki d'an yi kara ki dinga yin sllh bakya yi koh?" Samha ta kalleta tace "Anty ae baya cewa in yi" Anty Maryam tace "Sai yace maki daughter," murmushi tayi tace "Toh xan na yi Anty" Anty Maryam tace "You still don't have interest in joining us koh" tana murmushi tayi maganar, Samha tayi dariya tace "Uhm Anty ae bance haka ba fah" Anty Maryam tace "Ko akwai abinda yake maki that's prohibited in Christianity?" Kmr xata yi kuka tace "Eh mana...." Anty Maryam ta d'an yi shiru tana kallonta, sai kuma a hankali tace "Gaya min me yake maki Samantha?" Ta turo baki bata ce komai ba, Anty
Maryam tace "Noo ki gaya min kar ki ji komai"

*Haske writers asso*
[11/27, 7:18 PM] * +234 703 709 9528, : =ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
81......

Kamar xata yi kuka tace "Toh ba sai yayi ta kula mutane ba...." Anty Maryam tace "Su waye mutanen?" Dauke kai tayi ta ki cewa komai, Anty Maryam tace "But don't forget his profession, kin ga kuwa ae shi na mutane ne Samantha, beside where in d bible aka ce kar a dinga kula mutane?" Tace "Toh Anty fa sai yarinyar ta dinga xuwa nan tana kawo masa assignment yana yi...." Anty Maryam tace "Wace yarinya ce?" Tace "Our neighbor mana" shiru Anty Maryam tayi kafin tace "Da ya san su ne?" Tace "I don't know for him" murmushi Anty Maryam tayi tace "Ke dai dama har da guntun masifar ki" Samha bata kuma cewa komai ba, Anty Maryam tace "Kun yi waya da Abban ki ashe" dawowa kusa da ita tayi da sauri tace "Eh Anty, kuma yace xai xo, yaushe ne xai xo?" Anty Maryam tace "Xai xo amma ba yanxu ba daughter" Samha tace "Sbda me Anty? ina son in gansa" lkci daya hawaye ya cika idonta, Anty Maryam ta dafa shoulder dinta tana yar dariya tace "Xai xo mana, may be to see his grandchild, kinga that's the right time ma koh?" Tuni Samha ta sunkuyar da kai, Anty Maryam tace "Ko ba haka Daughter?" Turo baki tayi ta mike ta kwanta kan gado, Anty Maryam tace "Idan bacci xa ki yi ki tashi ki tafi gun mijin ki" ba tare da ta kalleta ba tace "Ni a nan nake kwana Anty" Washegari Anty Maryam na idar da sllh bata koma bacci ba, tayi wanka snn ta fito parlor, xaune ta tadda Aliyu laptop gabansa, yana ganinta ya katse abinda yake yi ya gaisheta tace "An tashi lfya?" Yace "Alhmdllh Anty" xaunawa parlon tayi yace "Anty amma sati xa kiyi mana koh" tace "Gobe xa mu juya in sha Allah Aliyu, ae an yi xumunci" yace "Anty gobe fa kika ce" tayi murmushi tace "Toh na bar yara gida ai" yace "Kince gun grannies dinsu suke ai" tayi dariya tace "Ehh duk da haka, amma ae tunda mun ga waje xa mu dawo wani lkcn" yace "Toh Allah yasa Anty" tace "Aliyu har ynxu baka ka making effort na ganin ka ja ra'ayin samantha koh" kallonta yake jin abinda tace, can dai yace "Anty bana son taga am forcing her into it" Anty Maryam ta girgixa kai tace "Noo it's nt by forcing her, actions dinka xai dinga jan ra'ayinta mana, infact ba actions kadai ba, time to time yana da kyau ka dinga fada mata do's nd don't's din addinin ka, ka dinga nuna mata islam is nothing but peace, ka nuna mata muhimmancin addinin ka" jin yyi shiru ta ci gaba tace "Misali kana sllh a kan lkci, kana karatun qur'an lkci lkci a inda take, infact u make it ur normal routine, u re educated Aliyu ba sai na gaya maka wa ennan abubuwan ba, a k'ashi dari nasan Samantha ta san meye musulunci k'ashi 40, ai ta xauna da ni, har sllh tana yi idan tana gu na, islamiyya ma kullum tana xuwa sai dai ranan da babu, Idan ka kula ba wai tayo xurfi a Christianity din bane, uwarta ce ke tusa mata ta karfi, yeah Abbanta is a Christian amma sai in ce maka shi church din ma ba xuwa yake ba, xai dai yi karatun littafinsu a gida idan yana ra'ayi...." Abuturrab ya sauke ajiyar xuciya a hankali yace "Haka ne Anty, am nt making any effort into making her fall for islam don kwanki ita da kanta tace tana son in sa ta islamiyya daga baya kuma tace baxa ta je ba, kuma Anty hakan baxai yiwu ba ynxu sbda condition dinta....she's totally changed" Anty Maryam tayi murmushi tace "Sai hakuri, kuma naji ddin da ka fahimci cewar abinda take ynxu ba halinta bane kuma ba yin kanta bane, ban mancewa haka uwarta tayi tana da cikinta don lkcn ina wajensu, ka ci gaba da hakuri har Allah ya raba su lfya" yace "Toh Anty, nagode" tana murmushi tace "Na tambayeta ko akwai abinda kke yi that's contrary to her religion tace eh" xaro ido yayi yace "Me tace ina yi Anty?" Dariya Anty tayi tace "Cewa tayi kana kula mutane" bai san lkcn da yyi dariyar ba shi ma, yace "Anty kinsan kishin Samha yyi yawa, she's making me get frightened with her type of jealousy, kinga just yarinyar neighbor dinmu ce fa wani time din ta kan kawo assignment in duba mata, kuma mum dinta ce ta ban aiki clinic dinsu, so i just can't say No, ban san ynda xan dinga avoiding yin assignment din ba..... Ko me xan ce ma Samha baxa ta taba fahimtata ba, mamakin kishinta nake" Anty Maryam ta girgixa kai tace "Toh Allah ya kyauta ka dai bi ta a hankali har ta sauka lfya, tsabar jaraba ne ke damunta, though ba halinta bane, kishi kuma gado shi tayi gun Uwarta" yayi murmushi yace "Haka ne Anty" sai kusan karfe tara Anty ta shiga kitchen don girka breakfast duk da Abuturrab yyi niyyar fita ya siyo ta hanasa, Hajiya Samha kam tana ta bacci daki da Ihsan, kafin karfe goma Anty Maryam ta gama komai, ta tsaftace kitchen din snn ta fito. Da rana Abuturrab ya fita ya yo masu take away na lunch, Anty Maryam na ba Ihsaan abincin ta kalli Samha dake shan gari tace "Daughter ki bar garin nn haka ki ci shinkafa" ta girgixa kai tace "A'a Anty" Anty Maryam tace "Kina ji na?" Kallonta Samha tayi, tace "Daga yanxu ki dinga sllh ba sai ance kiyi ba" Shiru tayi kafin tace "Toh Anty" Anty Maryam tace "A ko da yaushe fa ba wai idan kinyi zhur baxa ki yi Asr ba" tayi murmushi tace "Toh xan na yi Anty" Anty Maryam tace "Yauwa my daughter, don kinyi addinin kakan ki ae ba laifi bane" Murmushi Samha ta kuma yi bata ce komai ba, Anty Maryam tace "Ko baki sha'awar addinin?" Nan ma murmushi tayi bata ce komai ba, Anty Maryam tace "C'mon talk to me" yar dariya tayi tace "Ina yi mana Anty, kema kinsan i love sallat, kuma akwai time din da doctor ya karanta mani wani verse a bible da yake ce min jesus christ acted like Muslims do, he fall with his face to ground when praying, nd truely Matthew 26:29 said 'Going a little further, jesus fell with his face to the ground and prayed.... And i knw till date d Coptic Christians nd the jews in the holy land still pray d way Jesus did" Anty Maryam tayi murmushi tace "Am happy u kept this at the back of ur mind, amma yaushe ya karanta maki verse din?" Tace "Ya dade fa, ae da yana yawan kawo min verse kawai dainawa yyi" Anty Maryam tace "Do you believe in prophet Muhammad Pbuh?" Samha tayi shiru bata ce komai ba, Anty Maryam tace "You remember this verse 16:5-8.... 'for if i go not away, the comforter will not come unto you, but if i depart, i will send him unto you, and when he comes, he will reprove d world of sin and approve righteousness nd judgement...." Kallonta kawai Samha take, Anty Maryam tace "Who is this comforter?" A hankali tace "The Holy spirit" dariya Anty Maryam tayi tace "Holy spirit ne xai yi reproving world yyi approving righteousness nd judgment? Da can ance maki bbu holy spirit din, Jesus Pbuh was referring to prophet Muhammad S.a.w, an san gaskiyan ake dannewa" ita dai Samha bata ce komai ba, Anty Maryam tace "Doctor din bai taba maki tarihin Prophet Muhammad ba?" Girgixa kai Samha tayi, tace "Toh ki ce ya baki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login