Showing 21001 words to 24000 words out of 180592 words

Chapter 8 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1126

komai ba, ba ruwana" marairaice mata yyi yace "Baki yadda da brothern ki ba knn?" Wani kallo ta jefa masa ta warce hannunta tace "Eh ni ban yrda da kai ba kuma, dama shi yasa this days baka son muna xuwa wajen ka koh?" Hade rai yayi yace "I said she's my patient, are you daft?" Tabe baki tayi ta juya tayi wucewarta, da sauri ya bi ta ya fixgota fuskarsa daure yace "One word about what you just saw will mean you spelling dooomm" saketa yayi ya koma parlonsa, bai dade da shigowa ba peter ya kawo masa breakfast, takwas saura 'yan mintuna ya shiga bedroom bayan ya gama cin abinda xae ci na abincin da aka kawo masa, xaune ya ganta kan gado ta lulluba da bargo, tana ganinsa ta sunkuyar da kai, ya karaso bakin gadon yana kallon gashinta da yyi scatter all over, yace "Good morning" kallonsa tayi tayi murmushi bata ce komai ba, cire bargon jikinta yyi ta jawo da sauri ta rufe, buda ido yayi sai kuma ya d'an yi murmushi yace "ohk.... How's ur health?" Kai ta gyada masa ya juya ya fita, mikewa tayi bayan ta cire bargon ta nufi bathroom, ta tara ruwan xafi ta tsirka sannan ta wanke fuskarta, ta dau Listerine mouth wash/freshner dake bayin ta wanke bakinta snn ta fito, tsaye ta gansa dakin gaban mirror ta juya masa baya da sauri, karasawa yyi bayanta ya dafa shoulders dinta ya juyo da ita, ji tayi kamar ta nutse cikin sarkewar murya tace "Ina kwana...." Kallon kwayar idonta yake sai kuma yayi murmushi bai dai ce komai ba, ta sunkuyar da kanta, saketa yyi yace "xan tafi aiki yanxu....." Da sauri ta dago tana kallonsa tace "Nima xan je sch" kallon agogo yayi da sauri ita ma ta kalla, kamar xata yi kuka tace "Why did you not wake me" ya langwabar da kai yace "Coz you are sick" tace "Ni na samu lafiya.... I can still go" yace "Toh uniform din ki fa?" Xaro ido tayi tunawa da tayi ae fa ta jefar a titi, a hankali tace "Na yadda jakar a hanya doctor" shiru yyi yana kallonta snn yace "Ohk, let me get it for you" daga haka ya juya ya fita, ta koma a hankali ta xauna kamar warce ta tuno abu kuma ta mike ta shiga bathroom ta fara hada ruwan wanka, bayan kusan minti sha biyar ta fito daure da towel dinsa, xaro ido tayi ganinsa ta juya da sauri xata koma bayin ya dakatar da ita ta hanyar cewa "do I look like a monster!" kasa shiga bayin tayi ta kuma kasa juyowa, ya tsura mata ido daga sama har kasa, haka kawae yaji ya kasa tsayuwa, can ta juyo a hankali jin bai kuma cewa komai ba tana kallonsa, dauke kai yayi gabansa ya shiga faduwa, ta karaso a sanyaye tace "Am...am sorry!" Yayi karfin halin kallonta yace "Better, uniform din ki sun jike, kawai ki bari gobe ki tafi schl din" shiru tayi bata ce komai ba, ya dauke idonsa yace "Let me get you something to put on, but before then...." Gaban madubi ya nufa ya nuna mata lotions hadda na gashi yace "You manage this" sunkuyar da kanta tayi ya juya ya fita. Main House ya tafi ya ga Mami ce kadai a parlor tana kallon wani program, kanninsa duk sun tafi boko, ta kalli agogo tace "Baka tafi aikin ba har yanxu Haiydar" yace "Ehh yanxu xan tafi, wasu takaddu da na ba ilham xan karba" daga haka ya wuce sama ta bi sa da kallo, yana shiga ya kulle dakin ya bude closet dinsu, ganin tafi son saka dogayen riguna ya fiddo mata da wani bakin abaya da ya gani gogagge da veil dinsa, har da sabbin inner dinsu ya dauko mata, tunanin yanda xae fita da kayan ya fara yi, can ya leka window sai kuma ya dawo ya dau towel dinsu dake baje a kan gado yayi wrapping din kayan ya koma gun windown ya jefar ya rufe wajen, snn ya dawo ya bude bedside drawer ya fiddo full scap sheet dinsu har uku ya linke yana rike da shi a hannu ya fita, ya sallami Mami da ta bi sa da kallo ya fita, yana xagawa ya dau kayan ya nufi part dinsa, xaune ya sameta gaban madubi har lkcn tana shafa mai, kallo daya yayi mata ya dauke kai ya ajiye mata kayan kan gado ya juya ya fita, cikin few minutes ta ga gama shiryawa ta fito ta samesa xaune a parlor, sosai kayan suka mata kyau kamar balarabiya haka ya dinga kallonta har ta karaso kanta a kasa tace "Thank you Dr!" Yace "Welcome, ga breakfast" girgixa masa kai tayi tace "A'a, gida xan tafi" d'aga kafada yyi yace "As you wish, uniform din suna balcony" tace "Toh" snn ta nufi kofa ya bi ta da ido, sae da ta bude kofar snn ta juya ta kallesa suka hada ido, dauke kai tayi da sauri ta fita, ya lumshe ido na kusan minti bakwai sai kuma ya mike ya dau makullin motarsa ya fita. Ko da ta isa gida bata damu da ta kunna wayarta ba sanin ba lallai ya kawo ba, duk da tasan kila su Mumy na ta kiranta, gabanta ya fadi tunawa da tayi Mumy xata iya kiran gidan su Stella su ce bata je ba, mikewa tayi da sauri ta fita xuwa gun mai gadi tace "Plss ka aran min wayar ka idan kana da flashing power xan kira su Mumy ne" mika mata yayi ta karba, tana flashing ba a jima ba kiran Mumy ya shigo ta daga tace "Mumy!" Daga daya bangaren Mumy tace "Samantha me ya samu phone din ki" kamar xata yi kuka tace "Ya fada ruwa" Mumy tace "How manage, me ya sa baki tafi schl ba" tace "Mumy am coughing, am not feeling fine" Mumy tace "Baki je gidansu Stella din ba kenan?" Tace "Ehh mumy am at home" Mumy tace "You are covered with the blood of Jesus my daughter, don't worry gobe ina hanya, ki dau kudi ki siyo maganin tari" a hankali tace "ohk Mumy" daga haka suka yi sallama, Samantha tayi kwanciyarta, sai can kusan sha daya ta tashi ta fara gyara ko ina na gidan kafin sha biyu ta gama, ta wanke uniform dinta ta shanya snn ta shiga kitchen nan ma ta gyara ko ina, tunanin abinda xata girka ta shiga yi, can tayi deciding tayi jollof rice da sauce din cow meat sai fried plantain anjima, kafin ta fita ta hada tea ta soya kwai ta fito ta ci ta kwanta sai bacci, ba ita ta tashi ba sai hudu, ta kunna TV tayi kallon kusan awa daya, mikewa tayi jin tana jin yunwa ta shiga kitchen don yin girkin, da yake akwai komai a gida kafin karfe shidda da rabi ta gama tayi slicing lettuces, tomatoes, cucumbers, onions, and carrot ta ajiye su gefe, ta debi abincin da xata ci ta fita xuwa parlor, ajiyewa tayi ya huce ta tafi wanka, tana daure da towel ta dawo ta dau abincin ta, tana fara ci Abuturrab ya fado mata haka kawai taji tana son kai masa duk da ba da yawa tayi ba, kallon agogo tayi taga bakwai ya gota, tasan ya dawo aiki yanxu, bata wani ci abincin da yawa ba ta mike ta koma kitchen ta xuba masa shinkafar a warmer, ta debi sauce din a wani cooler, ta dau wani transparent breakable bowl ta xuba masa vegetables din ta rufe, ta sa su gaba daya a basket snn ta dawo parlor ta ajiye, sama ta tafi xuwa saka kaya, ta shirya cikin doguwar riga me tsantsi, ta daura veil a kai ta fita.

*Haske writers asso* =???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

11....
Tsarguwa tayi da irin kallon da mai gadinsu ke mata, ta hade rai tana rike da basket din abincin tayi ficewarta, cikin minti sha biyar ta isa gate din gidan, sai kuma ta tsaya tana tunanin kila ma bai dawo ba, karasawa gate din tayi ta tura a hankali taji a bude, ta leka compound din ta ga motarsa a space din mota biyu dake wajen, shiga tayi kamar mara gaskiya ta rufe gate din snn ta wuce parlor, a bude ta tadda kofar ta shiga da takalmanta tana kalle kalle, ta ajiye basket din hannunta ta xauna jin kamshin sabulu da ya gauraye ko Ina yasa tayi tunanin kila wanka yake, ta kusa minti bakwai xaune ta ji kamar foot step, mikewa tayi tana kallon kofa, sae kuma ta juya da sauri ta nufi bedroom dinsa ta bude kofar ta shiga ta rufe, kasa barin bakin kofar tayi kuma ta kasa juyowa, taji an bude kofar bathroom duk da haka bata juyo ba, ji tayi an juyo da ita ta daga kai tana kallonsa, daure yake da towel a waist dinsa, ta sunkuyar da kai, yayi murmushi yace "No church yau?" Kasa magana tayi, can cikin in ina tace "Dama...dama yanxu xan tafi, I brought you food... Yana parlor" kallonta kawai yake ko kiftawa bai yi, duk ta rikice ta juya da sauri, ya kuma juyo da ita taki dago kanta, murya can kasa yace "You brought me food..." Tana gyada kai kamar munafuka tace "Yess, yes I taught you will like it..." Dago kanta yayi a hankali yace "Thank soo much..." kasa kallonsa tayi, shi ko sai kallon bakinta yake, ta juya a hankali tace "Sae da safe" bata jira cewarsa ba xata bude kofa sai jinta tayi a jikinsa, ta xaro ido tace "Doc...." Bata kai karshe ba ta ji bakinsa cikin nata, a tsorace take kallon kwayar idonsa, ya lumshe ido ya jinginar da ita jikin kofa ya shiga kissing dinta a hankali, rikicewa tayi ko ina na jikinta ya dau rawa ta kuma kasa kwace bakinta, a hankali ta fara silalewa kasa ya rungumeta a bare chest dinsa har lkcn yaki cire bakinsa a nata, sun kusa minti shidda a haka aka bude kofa can parlor, wani karfi ya xo mata ta turasa xata bude kofar dakin ya jawota jikinsa ya kankameta, saukan hawayenta ya ji kirjinsa, ya sa ma kofar key jin muryar Mujaheed, xamewa tayi kasa ta hade kai da gwiwa, bubbuga kofar dakin Mujaheed yayi yana cewa "Are you there Aliyu?" Abuturrab bai tanka sa ba ya bude press ya fiddo jallabiyarsa ya sa ya cire towel din jikinsa ya kai bayi ya fito yana kallonta don har lkcn bata dago kanta ba, bude kofar yyi ya fita ya rufe, Mujaheed da har ya koma parlor yace "Meye na rufe kofa a bedroom kamar mara gaskiya?" Abuturrab na shafa kansa yace "Su Ramla ke damuna" Mujaheed yace "Ohk, Mum ce ta aiko Amira gun Mami.... Shine nayi dropping dinta, and we are leaving yanxu" Abuturrab yace "Ohk xan shigo anjima idan na fito" Mujaheed yace "kamar gaske" daga haka ya nufi gun abincin dake ajiye parlor ya bude yace "Whose food is this" Abuturrab yace "Mine" spoon Mujaheed ya dauka ya debi abincin ya kai baki yana cewa "But tuwo Mami ta xuba mana wai sai mun ci Ashe akwai wnn..." Abuturrab bai tanka sa ba, mujaheed ya xaro ido yace "Kai amma Mami da kanta tayi girkin nan koh..." kara kai wa baki yayi yana lumshe ido yace "Ae sai na koma an xuba min nawa, wnn dadi haka" daga haka ya nufi kofa Abuturrab ya dakatar da shi da sauri yace "look siya nayi ba a gida aka yi ba, kasan ni bna cin tuwo" Mujaheed ya dawo yace "Toh bari in dauko plate..." Kitchen ya tafi ya dauko plate ya dawo ya debi abincin da sauce da vegetables ya xauna ya fara ci yana ta santi, Abuturrab ya xauna ya kunna tv amma duk hankalinsa baya kai, da ya tuna incident din moment din sai gabansa ya fadi, Allah Allah yake Mujaheed ya wuce, ae ko sai bayan kusan minti sha biyar Mujaheed ya bar gidan, Abuturrab ya rakasa ya dawo, kasa shiga bedroom yayi duk jikinsa yayi sanyi, can yayi karfin halin bude kofar a hankali, ganinta yayi durkushe yanda ya fita ya bar ta har lkcn bata dago kanta ba, ya karasa kusa da ita a sanyaye ya durkusa amma ya kasa dagota, lumshe ido yayi ya dafata yace "Am..am sorry I didn't mean...." Mikewa tayi da sauri idonta ya kumbura don kuka ta juya xata fita ya tashi ya rikota kan yace komai ta fashe da kuka sosai har da shessheka, rikicewa yayi yace "Plss kiyi hakuri it's not intentional, I..." Fixge hannunta tayi ta fice da sauri, ya bi bayanta, tana ganin haka ta saka gudu ya bi ta har suka fita gate, hanyar gida ta dauka tana gudu iya karfinta shi ma kuma bai fasa bin ta ba, tana isa dai dai Inda ta saba jin haushin kare ta tsaya cak tana maida numfashi ganin karnuka har biyu, suna ganinta suka fara nufota suna haushi, juyawa tayi a rikice ta fara gudu ta nufi gunsa don tuni ya tsaya ganin karnukan tana isa gabansa ya rungumeta tayi tsit sai dai duk jikinta rawa yake, a hankali ta xame jikinta da kyar tace "Ka raka ni plss" hannunta ya kama ya nufi gate ta ce "No plss gida xan wuce" yace "Not when you are still angry at me" da sauri tace "No am not angry, ni ban yi fushi ba..." Xai yi magana fitilar mota ta dallarosu daga nisa, da sauri ta boye fuskarta a jikinsa don mutane daddaya ne basu san Mumynta anguwar ba, suna a haka har motar ya wuce ta dago da sauri tace "Doctor ka rakani plss" a hankali yace "Ke daya xa ki kwana?" bata bari sun hada ido ba tace "A'a Antyna tana nan" kama hannunta yyi ya fara tafiya xuwa gidan nasu, har suka isa bbu Wanda yace komai, shi dai duk jikinsa a sanyaye yake, bata ko kallesa ba xata shiga gate yace "Frnd..." Shigewa tayi abun ta ba tare da ta juyo ba ta rufe gate din, juyawa yayi ya bar gun ya koma gida.
Yana isa gida ya xauna parlor yana kallon abincin da ta kawo masa, can ya mike ya bude abincin ya kusa minti biyar rike da cover din warmer din yana kallon abincin, can ya dau spoon din da Mujaheed ya ci ya debi abincin ya kai baki, a hankali ya dinga taunawa, sai a snn ya gane ma'anar santin da Mujaheed ya dinga yi, wato the food was just perfect, so sweet, sosai yayi mamakin iya girkinta, plate ya dauka ya xuba abincin da vegetables sae sauce din naman, mancewa yayi da abinda ya faru bai ajiye plate din ba sai da ya cinye abincin, murmushi yayi underneath his breathe yace "Waow, she's a nyc cook" bude kofarsa aka yi ya daga kai da sauri Ilham ta shigo ta karaso kusa da shi tace "Ya Turab towel din mu muke ta nema bamu gani ba....". Kallonta ya tsaya yi kamar bai gane me take cewa ba, tace " Ya Abuu" ya ajiye plate din hannunsa yace "Toh ni ta ina xan san inda towel din ku yake...." Tace "Wa ya kawo ma abinci?" Yace "I bought it" mikewa yayi ya shiga daki ya bar ta wajen a tsaye, tabe baki tayi ta juya ta fita. Kasa sukuni Abuturrab yayi, duk ya tuna abinda ya faru sai ya ji haushin kansa, mikewa yayi daga kwancen da yake misalin tara saura ya fita, ya d'an yi xuke xukensa ya dau motarsa ya fita, gidansu Saudat ya nufa, har ya mance rabonsa da ita, yana parking kofar gidansu ya sa mai gadi yayi masa sallama da ita, bayan kusan minti goma ta fito, ya dinga kallonta har ta karaso babu yabo bbu fallasa ta rungume hannayenta tana kallonsa, yayi murmushi yace "Kin mance ni kwana biyu" wani kallo tayi masa tace "Dole kace haka, tunda kun bata da sabuwar budurwar ka shine ka yo guna yau" yace "Haka kika ce" tace "Eh mana..." Ya tabe baki yace "Toh shknn, will you escort me" wani kallo ta kuma jefa masa tace "Ga mara mafadi ko, dama abinda ya kawo ka knn na sani, in rakaka dabar ku, to baxan je ba" yace "Seems kin fara gajiya da ni Saudat, naga alama you want breakup...." Tace "Toh meye maraban dambe da fada, da wannan sharenin da kake for months ae gwara ma breakup din....". Yace "Alryt..... Good you told me that" daga haka ya shige motarsa ya kara gaba, sosai ya ji ransa ya baci ya koma gida yayi kwanciyarsa. Washegari Tuesday throughout bai ga Samantha ba, duk da xaman da ya dinga yi waje bayan ya dawo aiki, laraba ma ta xo ta wuce bai ganta ba, wasa wasa har Friday, ya rasa dalilin da yasa ya damu haka, ko abinci sai ya tilasta kansa yake ci, he just can't say how much he missed her, misalin hudu na yamma ya kasa daurewa ya dau hanyar gidansu, can gaba da gate dinsu ya tsaya jikin flowern gidansu kamar me jiran wani, bude gate din aka yi Mum dinta ta fito suka yi ido hudu, har ta dauke kai ta kuma juyowa ta kallesa, shi ko ya fara danne dannen waya, Komawa ciki matar tayi ta fito tare da mai gadi tace "Habu wannan fa?" Mai gadin ya kallesa ya karasa Inda yake yace "Malam kana neman wani ne" Abuturrab ya kallesa yace "Ehh abokina nake jira a can gidan" ya fadi hakan yana nuna wani gida, matar tace "Toh ae ba wajen jira bane nn, jikin gidan mutane kake, ka kara gaba kadan malam" Kallonta kawae Abuturrab yake, ta hade rai tace "Ko flawan uban ka ne kke kallo na haka" bude gate aka yi duk suka juya, Samantha ta fito rike da jakar uwar tata, tana sanye da Doguwar riga amma na atamfa ta yafa yellow veil kallan atamfar a kanta, Ido hudu suka yi da shi ta kasa motsi Inda take, Cike da masifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login