Showing 84001 words to 87000 words out of 180592 words

Chapter 29 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1162

dariya, sosai Mumy ta basa dariya, ya rike kai ya dinga yi, Samha ta rikesa a tsorace tace "Noo Doctor xa ta ji plss ka dainaaa" hadiye dariyar yayi ya rike baki, Maryam ta tabe baki tace "Ae ba don Allah bai sonmu bane ya bar mu a haka, sai ki ga mu samu in the world here after" Mumy tace "Inaaa ai kwalelanku ku da arziki, baku yrda da d'an sa ba ku ke zaton xai maku arxiki... Baki ganin ynda ubanku ya mutu ko tinkiya daya ba shi da..." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Da yau xan ga Rebecca gwara in kasheta in yi layyarta" Anty Maryam tace "Sai kuma ki ga kafin ta dawo ta musulunta, kila har ma ya aureta da ciki jikinta" wani kara da ya firgita sarah dake bacci ta fito da gudu Mumy tayi, Ta isa gun Maryam da gudu ta shakota tace "Jehovah ya isa tsakanina dake, Jehovah ya kona bakin ki da ya furta haka, Jehovah ya hanaki farin ciki da shegen talakan musulmin mijin ki...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Sarah dauko min jakar kayana in wuce hotel, Idan na ci gaba da xaman gidan nn nasan xan shiga fushin ubangijina...." Sarah tace "Haba sis Rachael me ya hadaku haka duk makwabta na ji?" Tura Maryam Mumy tayi ta shige daki sai ga ta ta fito da jakarta tace "Idan kin ga dama ki fito da taki jakar in kuma so kike mu kone a gobarar da xa a aiko masu yau ne sai kiyi ta xama" Daga haka ta fice fuuuu daga gidan, Sarah tace "Maryam me ya faru haka ne" Maryam ta koma kujera ta xauna hade da sauke ajiyar xuciya tace "Toh ma ina na sani magana kawai muke sai naga kuma kmr warce aka ma allura" Sarah ta sa takalmi ta bi bayanta da sauri, murmushi Maryam tayi tayi hamdala a xuciyarta, ba a dau lkci ba Sarah ta dawo ta dau dankwalinta ta daura da jakar hannunta tace "Gobe xan xo Maryam, ban san me ke damun Sis Rachael ba" daga haka ta fice daga gidan, Maryam ta mike ta sa sakata a gidan ta dawo.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
49.....

Da sauri Anty Maryam ta karasa dakin da suke, tana bude kofar Samha ta mike da sauri ta karasa da gudu ta rungume ta, Anty Maryam kam kallon Abuturrab kawai take, Wanda hakan yasa ya mike ya gaisheta, bata iya ta amsa ba don duk jikinta yayi sanyi ganin kyansa da kwarjini amma ya gwammace yayi ta garari sbda wacce addininsu ya sha bam bam, can dai tayi karfin halin cewa "Bawan Allah don me xaka gudu da yar mutane, and what are you up to?" Sauke kansa kasa yyi kamar baxai ce komai ba sai kuma a hankali yace "Saboda ina sonta Anty, so kuma na aure snn ina son musuluntar da ita ta dawo hanya madaidaiciya" Kallonsa kawai Anty Maryam take, ya karasa gabanta yace "Ki yarda da ni Anty ina sonta sbda Allah ba don in cuce ta ba...." Anty Maryam ta girgixa kai tace "Amma kana ganin hakan shine dai dai, rayuwa fa kake da warce ba muharramar ka ba, wanda addinin mu bai yarje mana da haka ba, ka sani amma ka bi son xuciya...." Yace "Noo Anty, i tried my best na ganin ban saba ma addinina ba all through our stay together" tace "Toh me ya hanaka auren nata har ynxu yau wataninku kusan biyu da barin gida?" Kallon Samha yayi sai dai bai ce komai ba, Anty Maryam tace "Kayi shiru?" Yace "Bana son watarana tayi tunanin ina using advantage din aurenta Anty...." Juyawa Anty Maryam tayi ta bar bakin kofar, Samha ta kallesa snn ta bi bayanta, Ko minti biyar basu yi da fita ba Anty Maryam ta dawo dakin, karasawa tayi inda yake ta zauna kan darduman dakin tace "Aliyu koh?" Kai ya gyada mata, tace "Kaga mahaifiyar Samantha na gidan nn ynxu haka nasan tana within,l.. ban san ka ba, ban san daga inda kake ba, ban san halin ka ba, amma nasan kai musulmi ne d'an uwana, hakan yasa xan baka yarda ta dari bisa dari, nasan da baka son Samantha tsakani da Allah baxa ka gwammace irin wnn rayuwar ba, don haka Aliyu kafin ku bar nan ina son ya kasance Samantha matar ka ce ta sunna, if you've tried ur best abiding to the laws of ur religion wataran hakan gagararka xai yi.... In har da gaske kake ka bari a daura maku aure komai xai fi xuwa da sauki" a sanyaye yace "Nima nafi son haka Anty, ban sai san ta inda xan fara bane...." Anty Maryam tace "Dawowar Samantha musulunci ba abu bane mai wahala ni xan taimaka maka, yanxu dai it's better ka tafi ka samu hotel, ita kuma xan kai ta gidan kawata, don mahaifiyarta na iya dawowa nn a ko wanni lkci." Yace "Toh nagode" tace "Amma all this while kuna ina da ita?" Babu bata lkci ya bata labarin d'an rayuwar da suka yi a gombe da Ummi, sai dai bai gaya mata ga abinda yasa suka bar gombe ba sai ce mata yyi kawai ziyara suka xo kawo mata" Ta sauke ajiyar xuciya tace "Toh shknn Aliyu Allah ya maku jagora, ni nafi kowa farin ciki da abunda ya faru Allah yasa lkcn fitowar yayana daga 6ata ne ya xo, Allah yasa ta dalilin haka ya gane gaskiya" Abuturrab yace "Ameen" mikewa tayi tace "Bari in xubo maka abinci" daga haka ta fita. Shinkafa da wake da mai da yaji sai kayan vegetables a kai ta kawo masa da ruwa a jug, yayi mata godiya ta fita. Mai gidanta ta kira ta sanar da shi komai ta kuma bukaci ya dawo don su hadu da Abuturrab, bayan yan mintuna ya shigo gidan, a tare suka shiga gun Abutturrab, ya gaida mai gidan nata da ladabi, Duk suka xauna dakin, Mijin Anty Maryam mai suna Aminu da ke ta kallon Abuturrab yace "Sannu da xuwa bawan Allah" Abuturrab yayi murmushi yace "Nagode" tambayoyi kmr yanda Anty Maryam tayi masa ya shiga yi masa shi ma, sosai mijin Anty Maryam ya jinjina karfin hali irin na Abuturrab daga karshe shi ma ya nuna gwara kawai ayi auren komai xai fi xuwa da sauki. A can Gombe kuwa tunda Ummi ta dawo Khadija ta fadi mata ai fa tun safe Abuturrab suka fita da Samha, jikinta yyi sanyi don lkci daya ta fahimci tafiya yyi da ita barin da taji wayarsa kashe tun daxu, amma bata nuna ba ta shige bedroom kawai ta kwanta tana tunanin wani rayuwar kuma xa su yi. Sun yanke akan cewa gobe Abuturrab xa su je gun mai gari da Mijin Anty Maryam daga haka kuma Anty Maryam tace ya wuce hotel kafin Mahaifiyar Samha ta dawo ita kuma xata je kai Samha gun kawarta, Sallama yayi masu ya fita, sai dai bai ji ddin rashin ganinta ba har ya bar gidan ita ko tana parlon aunt din tata bacci ya dauketa. Karfe shidda Anty Maryam ta sa ta shirya bayan tayi wanka ta bata nikab da hijabi snn suka fita a lkcn ma yaranta sun dawo daga islamiyya, bata bari sun lura da Samha ba har suka bar gidan, Addu'a Anty Maryam ta dinga yi Allah yasa Rebecca bata anguwannin don tana da kawaye yan coci kamar ta sosai a wajajen, tana rike da hannun Samha sai sauri take su isa bakin titi ta samu machine su hau, ta layin da ke gefensu taji an kwada mata kira, ta juya da sauri cike da faduwar gaba ta ga Sarah ce tsaye kofar wani gida, Anty Maryam da ke ci gaba da jan hannun Samha da ta tsorata ita ma taki tsayawa tace "nan kika xo ashe" ganin Sarah na tahowa yasa hanjin cikinta yayi mugun kadawa tace "Gani xan xo yanxu, bakuwa xan raka" Sarah da har ta kusa isowa gun su sbda saurin da take tace "Sis Rebecca nake jira tun daxu wllh, haba tun fa daxu fada take...." Tuni Samha ta janye hannunta a na Anty Maryam tayi gaba ko ina na jikinta na rawa, Sarah ta bi ta da ido, Anty Maryam na ganin haka ta tsaya gabanta ta ynda baxa ta dinga ganin Samha ba tace "Toh ko mu je in bata hakuri ni fa ban san me ya faru ba" Sarah tace "Jesus, yarinyar nan yanayin Samantha gareta, wacece ita?" Anty Maryam tayi dariyar yake cike da karfin hali tace "Samantha da Nikab kuma? yar wata uwar daki na ce... Haka take fama da rufe fuska" Sarah dake ta kkrin sake kallon Samha da tayi nisa sosai tace "Har tafiyar fa Maryam, Jesus of Nazareth" Maryam tace "Ohh don dai Samanthar ce a ranki, ynxu mu shiga in ba sister hakuri sai ta iya hada ni da yaya" Daga haka ta ja hannunta suka nufi gidan, Suna shiga Maryam tayi wani salati tace "Amma yarinyar nn Sha sha sha ce kinga kudin motar fa a hannuna bata karba ba" Sarah tace "Ayya to kiyi sauri ki isketa mana" bata rufe baki ba Maryam ta fice da sauri tace "Ina dawowa ynxu" Can bakin titi ta iske Samha ta rakube jikin wani shago, bbu wata wata ta tsayar masu da machine biyu ta fadi inda xa su suka hau suka bar gun tana hamdala a xuciyarta.

*Haske writers asso*

Plss ana min uxuri na rasa ynda xan dinga squeezing time ne, snn kuma there is shortage of power a inda nake ynxu wllh shi yasa yake taking time.
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
50......

Suna isa gidan Anty Maryam ta shiga Samha na biye da ita a baya, Anty Maryam suka gaisa da aminiyar tata mai suna Amina daga haka tace mata xata bar Samha nan gidan xuwa gobe ta xo ta dauketa, bbu bata lkci ta bar gidan ta koma gida. Wani hotel Abuturrab ya samu yyi lodge, da ya tuna abinda ya faru gidan Anty Maryam sai abun ya basa dariya, sai dai hankalinsa ya kasa kwanciya ya rasa dalili, yana yin magrib Coffee kadai ya iya sha ya dawo room dinsa. Karfe takwas da yan mintuna Ummi na xaune daki gaban computer sai dai gaba daya hankalinta bai kai, sosai su Abuturrab suka tsaya mata don bata san halin da xa su je su shiga ba kuma, jawo wayarta tayi for the 5th time within that period ta sake dialing numbersa amma switch off ta dafe kai, bude kofar dakinta aka yi ta dago da sauri Yusuf ya karaso ya xauna kujera yana kallonta yace "Sannu da aiki Ummi" ba tare da ta kallesa ba idonsa a kan screen din computer tace "Yauwa" Ya d'an yi murmushi yace "Ummi kar fa ki sa ma kanki damuwa, dama ni ina ganin Aliyu nasan ba shi da gaskiya, as in the way he does his things ma xaka gane hakan, baka taba gane abinda ke ransa na lura, he can be a silent killer, at the first place na tambayeki hadinsa da Samha kika ki gaya min, daga bincikena tun a jiya na gano Samha ba matarsa bace, though bance xaman banxa suke ba, amma daga duk alamu rabo ta da iyayenta yayi may be for his selfish interest, tun daga lkcn da kika ce min bai ji na fara gano wasu abubuwan.... But Ummi me yasa kika boye min kilan da hakan da ya faru ynxu bai faru ba, i would have kept an eye...." Kallonsa Ummi tayi a karo na farko tace "Bana son xancen Yusuf" mikewa yayi yace "Aiit, buh am gonna fish him out idan Allah ya yarda" daga haka ya fita. Anty Maryam na xaune tsakar gida a ranan tana wanke kwanukan da suka ci abinci amma hankalinta na ga tunanin decision din da suka yanke da mai gidanta na aura ma Aliyu Yar d'an uwanta, bude kofar soro aka yi ta juya da sauri taga Rachael ce da Sarah, Duk da ba wuta tsakar gidan sai hasken wata hakan bai hanata ganin yanda Rachael ta daure fuska ba tana tahowa kamar xata tashi sama, Anty Maryam ta dauke kai tana murmushi ta ci gaba da wanke wankenta, sarah ce kadai tayi mata sannu da gida suka shige parlor, Anty Maryam ta mike ta dau abinci ta kai masu ta fito, ko da ta gama wanke wanken xamanta tayi tsakar gida tana sake saken yanda al'amarin gobe xai kasance, can ta mike ta shiga dakin mai gidanta ta xauna tana kallonsa tace "Abbansu Asiya ya kake ganin xa ayi gobe ne wai" Yace "Gun mai gari xa mu je a daura auren sai su tafi duk inda xa su, matukar xai iya kula da ita, na kuma ga yana sonta sosai don da ganinsa kasan ba karamin mutum bane." Da damuwa tace "To fa bata amshi musulunci ba har ynxu" yayi murmushi yace "Ba yar ki bace kin san yanda xa ki bi da ita ai, sai dai kuma kada a tilastata don in har aka yi haka tana iya komawa gidan jiya tun da ba da son ranta ba.... Ko kin mance yanda muka yi da ke Maryam" ganin dariyar da yyi ta hade rai tace "A'a ni baka aureni a Christian ba ni musulma ce a lkcn ma" yace "Amma a lkcn abubuwan da kike yi meye banbancin ki da Christians din, ba fa gori nake maki ba rabin rai kawae dai magana ce" ta tabe baki tace "Ae don ina gun yayana ne lkcn Kuma mahaifiyar Samantha ce matsayin uwata...." Yace "Toh kar ki ji komai ni nasan da kanta xata yi sha'awar addininmu ba sai an mata dole ba, at the first ma da bata son musulunci baxata yarda da musulmi ba har su gudu tare ta bar iyayenta" Anty Maryam tace "Haka ne, kuma kaga lkcn da take xuwa hutu nan bata kin yi duk abinda na sa ta tun daga kan sllh har xuwa tafiya islamiyya da su Asiya" yace "Toh kin ga" Mikewa tayi tace "Bari in je can parlor" daga haka ta fita. Washegari da ya kasance friday da safe Abuturrab ya fito ya nemi d'an boutique ya siya kaya da kudin dake hannunsa, daga haka ya nufi Atm machine don cire kudi, takaici ne ya ishesa don Atm machine din da ya gani bai fi biyu ba kuma duk ba kudi, kallon agogon hannunsa yayi yaga tara bata yi ba, kawai yayi deciding ya wuce cikin kaduna kawae, sai da ya koma hotel ya shirya snn ya dau hanya, yana isa ya kunna wayarsa tunawa da yyi sun yi exchanging number da mijin Anty Maryam, yana cire kudin ya shiga tunanin me xai siya kuma kafin ya koma wayarsa ya shiga ring Sadeeq ya gani jikin Screen din, har ya fara tunanin waye kuma sadeeq kawai ya tuna gayen da suka hau mota tare tun daga gombe, dagawa yyi, nan suka gaisa da fara'a Abuturrab yace "Kasan jiya fa can maraba muka wuce amma yanxu ina cikin kaduna na xo cire kudi..." Sadeeq yace "Au haba, a ina kake yanxun?" Abuturrab ya kalli gun yace "Ina bypass" Sadeeq yace "Haba to ka karaso nan gidanmu mana kafin ka koma" Abuturrab ya kalli agogo sai dai bai son Sadeeq ya ga kamar yyi shun dinsa, yace "Funny you, ni da nake sauri" Sadeeq yace "Sai in kai ka har maraban da motata" Abuturrab yyi jim don bai son exposing secret dinsa ma kowa kuma, can dai yace "Haba don xan xo gidan ku sai ince sai ka mayar dani, bari in taho sharp sharp in koma ba sai ka yi wahalan kai ni ba" Sadeeq yace "Alryt" address ya tura ma Abuturrab da yake yasan garin xuwa gidan bai yi masa wahala ba sai dai ba dai nisa ba don sai kallon agogo yake, babban anguwa ce ta masu abun hannu, Sadeeq ya fito daga wani kantamemen gida mai dauke da gate biyu kai da ganin gidan kasan naira ya xauna, nan suka gaisa sadeeq na dariya yace "Ashe dai xaka gane..." Abuturrab yace "Haba dai ai ba wani wahala" daga haka suka shiga gidan sadeeq ya kai sa har babban parlon gidan, Abuturrab na xama ya ji gabansa na faduwa ya rasa dalili, Sadeeq na kallon kanwarsa da ta fito yace "Kiyi setting mana breakfast a bedroom dina" tace "Toh" sannan ta gaida Abuturrab ta koma kitchen, Sadeeq yace "This is our home, you feel free frnd" Abuturrab yayi murmushin karfin hali yace "Sure" Ana bude kofar parlor ya waiga da sauri kamar jira yake, bai san lkcn da ya mike tsaye yana kallon mutumin dake kallonsa shi ma a bakin kofar ba, Sadeeq ma ya mike yace "He is my Dad...." Abuturrab ya kallesa ya kirkiri murmushi yace "Ohh alryt" juyawa Mutumin yyi ya fita, nan hankalin Abuturrab yayi mugun tashi, ya dake ya koma ya xauna, Sadeeq dake ta studying dinsa yace "Any problem Aliyu?" Wara ido yayi yace "Ohh nothing Sadeeq" ba a dau lkci ba mutumin ya dawo parlor, sai a snn Abuturrab ya gaida shi kansa a kasa, mutumin ya amsa yayi wucewarsa Sama, mikewa Abuturrab yyi yana kallon Sadeeq yace "Let me answer a call in dawo" daga haka yayi waje da sauri, wani mugun faduwa gabansa yyi ganin mutanen da bai gani ba lkcn da xa su shigo tsaye bakin gate wato dai soldiers in uniform, dakewa yayi ya karasa xuciyarsa na bugawa ganin kallon da soldiers din ke masa kawai ya juya ya koma ciki da sauri yana furta innalillahi a xuciyarsa, Yana shiga parlorn ya isa gun Sadeeq da sauri, Sadeeq ya mike da sauri ganin tashin hankali bayyane fuskarsa yace "Aliyu lafiya" Abuturrab yace "Nooo, help me out now plss!! ur dad.... Abokin Abba na ne" Sadeeq dake kallonsa da mamaki yace "Then?" Abuturrab ya kamo hannunsa yace "Don Allah make a way out for me nayi ma Abbana babban laifi i left home for months, nasan kilan yanxu ya ma kirasa wllh.... Plss" tsit Abuturrab yayi ganin Col Ishaq yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login