Showing 15001 words to 18000 words out of 180592 words

Chapter 6 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1123

tayi nan tsakiyar parlon tana juye juye, sai kuma ta fashe da kuka, ya hade rai yace "Kinga idan baxa ki min magana ba ki tashi kiyi tafiyar ki, leave now" mikewa tayi da kyar xata fita ba tare da ta kallesa ba ya bi bayanta da sauri ya jawota ta fado jikinsa, rufe fuskarta tayi jikinsa tana kuka a hankali, sun kusa minti uku a haka ya dago kanta a hankali yana kallonta yace "You are on ur period?" Sauke idonta tayi bata ce komai ba sai hawaye, komar da ita yayi ya xaunar kan kujera ya shiga bedroom dinsa, da yake baya rasa magunguna da allurori na Dysmenorrhea sbda kanninsa daukowa kawai yayi ya fito parlor, kwance ya ganta kasa, ya fara hada alluran yana gamawa ya dawo kusa da ita yace "Kin ci abinci koh?" Cikin kuka tace "Na sha tea" yace "Ohk, let me inject you, xa ki samu relief kin ji" bai jira cewarta ba ya fara daga doguwar gown din jikinta, ta rike da sauri don dama ita ba gwanar sa dogon wando bace, muryarta na rawa tace "Doctor ban sa komai ba...." shiru yayi yana kallonta sai kuma ya mike ya shiga daki ya dauko towel dinsa ya fito ya bata yace "to tashi ki daura," ta mike ta karba ya dauke kai ta daga gown din ta daura, kujera ta tafi tayi rub da ciki ta runtse ido ya bi bayanta, a hankali ya sauke towel din yayi mata alluran, yana gamawa ta fashe da kuka ya dagota xuwa jikinsa yace "It's okay xae daina maki yanxu" Kai kawai take gyada masa, sai da yaga ta nutsu snn ya saketa, ta xamo k'asa ta kwanta ta rufe ido, durkusawa yyi yana kallonta, ba a wani dau lkci ba bacci ya dauketa, ya mike yayi disposing syringe da kwalban alluran ya dawo parlon ya taimaka mata ta koma kan kujera. Yana bedroom aka danna bell ya fito da sauri ya nufi kofar, ganin Ramla ce yace "What again?" Tace "Ohh ya Abuu Mami ce fa ta aiko ni ka bude kofar plss...." ya hade rai yace "Pls go am busy yanxu, or you say it out there" murguda baki tayi don bata san yana kallonta ba tace "Ni fa....." Yace "Leave immediately idan ba haka ba xan sa ki kuka if I shud open this door" juyawa tayi fuu ta wuce. Sai kusan karfe shidda Samantha ta tashi daga baccin, yana parlor har lkcn yana danna laptop, ta mike xaune da sauri tana kallon agogo tace "Wayyo my mum is at home...." ya kalleta snn ya kalli agogo ta mike da sauri xata sauke gown dinta ta cire towel dinsa taga towel din yyi stain, still tayi tana kallon wajen, ya mike yace "What" girgixa masa kai tayi ta nufi toilet dake parlon da sauri, ya bi ta da kallo, cire towel din tayi xata wanke taji yace "Don't worry xan wanke....." Kasa juyowa tayi ta girgixa kai tace "No, xan wanke" juyo da ita yyi yace "Nace xan wanke" ta sauke idonta kasa bata ce komai ba, murmushi yayi yace "Yess" ajiye masa tayi ta nufi kofa ta fice daga toilet din sannan ta bar gidan gaba daya, tana isa gida gabanta ya fara faduwa, daga taje chemist a bata Magani tun uku saura sai after six take dawowa, mai aikinsu Blessing ce ke ta goge goge parlor, Samantha tayi kasa da murya tace "Mumy fah Blessing?" Blessing tace "Ta fita church tun daxun" Samantha ta sauke ajiyar xuciya tace "Bata tambaye ni ba" Blessing tace "No, tayi tunanin kin sha Magani kin kwanta a daki ne" Samantha bata ce komai ba sai dai tausayin kanta kawai take don kwata kwata Mumynta bata da wani lkcnta sai na church, duk ciwon da xata yi bbu abinda xae sa Mumy tayi fashin church in ma bata tilasta ta a hakan sun je church din tare ba, ga Abbanta ba wani xama yake ba ta dalilin aikinsa. Washegari asabar da safe Mumy ta shirya xa su Kaduna da tawagar pastoci kamar ta, Samantha na bacci ta tada ta tace "Rebecca you take care of ur self plss xan tafi yanxu, idan baxa ki xauna tare da Blessing ba ki tafi gidansu Stella, by the grace of God ran Monday ko Tuesday xa mu dawo, ki tabbatar kina shan maganin ki...." Samantha dake ta murxa ido tace "Toh Mumy Abba yaushe zai dawo?" Mumy tace "I don't know, just take care of ur self and make sure kin je church anjima da yamma da gobe da safe even if you cannot go to lesson" Samantha tace "Ohk, amma ni gidansu Stella xanje, Blessing ta tafi gida kawai" Mumy tace "Ohk better, ki kuma tabbatar kin tafi da wayar ki ni ban ga amfanin wayar nn naki da kike yasarwa a daki ba" Samantha tace "Toh xan je da shi Mumy, ki taho min da abu me ddi kin ji" Mumy ta nufi kofa tace "Ohk, tashi ki yi wanka ki ci abinci ki sha magani" daga haka ta fita, Samantha ta kalli agogo taga karfe takwas yayi, hamma tayi ta mike ta shiga bathroom, wanke baki tayi, tayi wanka snn ta fito ta kimtsa jikinta ta shirya cikin doguwar rigarta 'yar kanti pink colour da flowers din blue, ta fito da plain veil dinta blue colour ta daura a kai, bata wani yi make up ba sai eye pencil da tasa a ido snn ta sauko, tea kawai ta iya sha dan idan tana period bata iya cin abinci, tana xaune parlor tana ta kallo har Blessing ta gama aikinta tace "Blessing xa ki iya tafiya gida sai Monday nima gidansu Stella xan je ynxu" ba a wani dau lkci ba Blessing ta wuce. Samantha ta kashe kayan wutan gidan gaba daya misalin karfe tara ta hada kayanta kala uku ta dau bible dinta da textbooks na karatu da yake saura sati uku su fara Waec, a hannu ta rike wayarta ta fito ta kulle main gidan tayi ma mai gadi sallama ta wuce, tafiya take kamar mai tausayin kasa har ta iso gate din gidansu Abuturrab, har ta wuce ta dawo ganin kamar gate din a bude yake ta leka, ai ko ta gansa xaune yana sanye da singlet da short hannunsa rike da lighted cigarette, ido hudu suka yi ta juya da sauri xata bar wajen ya mike yace "Frnd" bata ko juyo ba, ya wurga taban hannunsa ya fita gate din, Sauri ya ga tana xubawa yace "Uhm not even a good morning frnd?" Tsayawa tayi bata juyo ba, ya rungume hannayensa yace "Hmm ae shikenan...." Juyowa tayi ta masa murmushi tace "Good morning" yafito ta yyi, ta make kafada, yayi shiru yana kallonta, ta langwabar da kai tace "lesson xan je" yace "Ohk" daga haka ya juya ya koma cikin gate, bin sa da kallo tayi a sanyaye can ta bi bayansa, tsaye tayi bakin gate din tana kallonsa tace "Are you angry" ba tare da ya kalleta ba yana tsaye kusa da karensa yace "No!" Shiga gate din tayi ta rufe ta karasa kusa da shi kamar xata yi kuka tace "You are" ya juya yana kallonta yace "Am not" murmushi tayi tace "Am sorry Dr, um naga baka shirya bane" rungume hannayensa yayi yace "Uhm ban shirya ba kamar ya?" Sunkuyar da kai tayi tana murmushi tace "Kila fa baka yi wanka ba...." Murmushin yayi yace "Toh mu je ki min" xaro ido tayi sai kuma ta juya da sauri xata bar wajen ya rikota yace "Ae sai kin min" boye fuskarta tayi a kirjinsa tace "Nooo Doctor lesson xan....." Rufe bakinta yayi ya ja ta suka shiga parlor ya rufe kofar da makulli.

*Haske writers asso* =???
' =ث? *Noorul Huda*=ث?

_Happy Belated born day Asmy B Aliyu, age with grace dear sis, Allah ya karo shekaru masu albarka ya nuna mana auren ki mu xo mu sha biki_=??

8.....

Kwace hannunta tayi kamar xata yi kuka tace "Doctor...." Yace "Toh in ruwan ki da rashin wanka na?" a hankali tace "Toh yi hakuri...." Murmushi yayi ya juya ya nufi daki ta bi sa da kallo, can ta ajiye jakar hannunta ta xauna tana kallon program din da ake a tv, bayan minti kusan ashirin taji an danna bell, mikewa tayi da sauri tana kallon kofar, ji tayi ance "Ohh ya Abuu me yasa kake kulle kofa ne yanxu, ni dai ka bude min Mami ce ta aiko ni wllh...." Da sauri Samantha ta mike ta shige bedroom dinsa ta tura kofar tayi lamo jiki, kwata kwata bata ji fitowarsa ba sai gyaran muryarsa da taji a bayanta ta juyo da sauri, daure yake da towel a waist, bakin gashin kirjinsa ya kwanta luf luf don ko goge jiki bai yi ba, a rikice ta juya xata bude kofar dakin ya riko hannunta kamar xata yi kuka tace "Doctor ur sister is outside.... Shi yasa na shigo" key ta ga yasa ma kofar ta juyo da sauri tana kallonsa a tsorace, ya wara ido yace "Tell me what you are afraid of?" Girgixa kai tayi da sauri tace "Noo... Nothing" yayi 'yar dariya yace "Why is it that girls always have this negative thought?" Juyawa tayi bata ce komai ba, yayi murmushi ya kamo hannunta yace "Am not a bad person, erase that thought off ur mind immediately" a hankali tace "Ohk!" Ya kama hannunta ya nufi gado da ita ya xaunar da ita gefen gadon, snn ya dau kayansa ya shiga bathroom, ba a dau lkci ba ya fito sanye da kananun kaya ya dau turaren gaban mirror ya feshe jikinsa da shi ya karasa kusa da ita ya feshe ta ita ma, boye fuskarta tayi jikin gado tana murmushi, can ta dago a hankali taga bbu shi a dakin, mikewa tayi tana kare ma dakin kallo, ko ina fes except from the bed that's untidy, murmushi tayi ta bude curtains din room din ta fara gyara gadon, cikin yan mintuna ta gama ta fita xuwa parlor, xaune ta gansa cup din coffee a hannunsa, ta wuce kitchen ta dauko sweeper da mop ta dawo ya bi ta da kallo har ta shiga bedroom, tana fitowa yace "Well done, thank you" tayi murmushi ta kai abubuwan hannunta kitchen ta fito, yace "Come and make a tea for ur self" tace "Nayi breakfast" yace "Nasan kin yi ae, karawa xa kiyi" tace "Noo na koshi sosai" kan kujera ta nufa ta dau jakarta yace "Ina xa ki?" Tace "Lesson!" Yace "Lesson da jakar kaya?" Ta kallesa tace "Aa xan ajiye gidan wasu family frnds dinmu ne, Mumy ta tafi Kaduna, Abba baya nan, ni kadai baxan iya zama a gida ba shine xan je gidansu" Abuturrab ya ajiye Mug din hannunsa yace "Sbda kina tsoron abu xai cinye ki?" Dariya tayi tace "A'a ni bana tsoro kawai bana son in xauna ni kadai ne" yace "Ohk...." Xaunawa tayi kan kujera ta dalilin ciwo da taji cikinta ya fara mata, kamar ko ya sani yace "Kin samu lafiya Yanxu?" Kai kawai ta gyada masa ta jinginar da kanta jikin kujera, ya bude warmer din dake dauke da wainar shinkafa ya debi biyu ya kalleta ya ga kallonsa take, yace "Taho mu ci" a hankali tace "Masa?" Ya gyada mata kai, tace "Sa min guda daya" yace "Sauko mu ci dai" ba musu ta sauko ta dawo kusa da shi ya kara masu guda biyu, ya debi rich vegetable soup din dake wani warmer a waje daban ya fara ci da spoon, dauka tayi ita ma ta fara ci, ganin yanda take ci kamar ana tilastata yace "Bai maki dadi ba ne" girgixa masa kai tayi da sauri tace "Yayi dadi...." Yace "Then me yasa kike haka da fuska" kamar xata yi kuka ta ajiye Masan hannunta ta kwanta gefensa tace "My tummy" sai kuma ta mike ta koma kan kujera ta kwanta, bin ta yayi da kallo ya ajiye spoon din hannunsa yace "Ya fara maki ciwo" kai ta gyada masa lkci daya hawaye ya cika idonta, a hankali yace "Sorry" mikewa yayi ya shiga bedroom sai ga shi ya fito da allura da Magani ya dawo kusa da ita ya shiga hada alluran, yana gamawa ya kalleta yace "Toh juyo in maki sai ki sha Magani" ba musu ta juyo har xata daga gown din sai ta tsaya kuma, kallonsa tayi hawayen da ke makale idonta ya silalo ta juya masa baya tace "Bude min zip din pls" bude zip din yyi a hankali, ta cire hannun gown din don akwai ves jikinta, ta sauke gown din kasa yanda xai iya yi mata alluran snn ta juya masa baya ta kwanta, daukar syringe din yayi ya mata alluran ta juyo tana kallonsa hawaye na sauka idonta, yace "Sorry!" Ya mike ya dauko table wata ya bata maganin ta sha snn ta koma ta kwanta, bayan awa daya ya kalleta ya ga idonta biyu, yace "Ya daina" ta gyada masa kai, har bayan azahar tana gidan a kwance, yana dawowa daga masallaci bayan anyi la'asar ya durkusa kusa da ita yace "Baki ci abincin ba har ynxu" ta girgixa kai tace "Baxan ci ba" mikewa yayi ya shiga daki ya shirya ya fito da makullin mota yana kallonta yace "Xan je clinic in dawo yanxun..." Mikewa tayi tace "Gida nima xan je" ya hade rai yace "Noo kiyi kwanciyar ki kina tashi cikin xae fara, don't worry i will lock the door" daga haka ya mike ta bi sa da kallo har ya fita, har shidda bai dawo ba, ta sauko da kyar jin cikin xae fara mata ciwo ta xuba abincin da aka kawo masa daxu ta ci kadan ta dau sauran magungunan da ya bata ta sha ts koma ta kwanta, tana kwanciya bacci ya dauketa..
A hankali ya durkusa kusa da ita yana kallonta ganin tun da ya dawo take bacci, can ya kalli agogo ya dafata yace "Frnd!" Da gani kasan bacci me nauyi take da kyar ta bude idonta, yace "Cikin ya daina" ta gyada masa kai a hankali hade da lumshe ido, dagota yayi yace "Taso ki kwanta a ciki, there might be mosquitoes here" girgixa kai tayi cikin sanyin murya irin ta mai bacci tace "A'a gida xan tafi" bai kulata ba ya dagata ta rike sa ta dalilin jiri da taji, ya ja ta xuwa bedroom dinsa, tace "Noo Doctor I want to go home...." Kwantar da ita yyi kan gadonsa ya dau lallausan duvet ya rufa mata ya kai bakinsa kunnenta yace "Go to sleep" rufe ido tayi ya gyara mata gashin kanta a hankali yace "Sleep tight Sam~ha" mikewa yayi ya kashe mata fitilan dakin ya bar na bed side snn ya dau wani duvet din ya fita parlor don idan yace xai shiga wani dakin ma tare da k'ura xa su kwana, kashe wutan parlon yyi ya kwanta kan 3 seater ya lulluba da duvet hade da lumshe ido, ya dade bacci bai daukesa ba, daga karshe dai baccin yayi awon gaba da shi bai tashi farkawa ba sai ana kiran assalatu, mikewa xaune yyi bayan yyi adduar tashi daga bacci ya kusa minti ashirin a haka kafin ya mike ya shiga toilet ya dauro alwala, raka'atainul fajr yyi yana ta xaune kan darduma har yaji xa a tada sllh a masallaci snn ya mike ya fita ya kullo kofar ta waje, ko da ya dawo durkushe ya ganta kusa da gado idonta lumshe ta hade tafin hannunta alamar addu'a take, ya jingina jikin kofa yana kallonta cike da tausayi har dai ta gama, tana ganinsa tayi murmushi cikin sanyin murya tace "Good morning Doctor" ya mayar mata da murmushin yace "Morning how's ur health?" Ta gyada masa kai tace "Na ji sauki yanxu" mikewa tayi ta fara gyaran gado, ya shiga bathroom sai ga shi ya fito da toothpaste da new toothbrush ya ajiye mata gaban mirror ta kallesa tace "Thank you" murmushi kawai yyi ya fita, main house ya nufa don xuwa gaida Mami, a kitchen ya sameta tana hada ma Abba breakfast ya gaisheta ta amsa tace "How was ur nyt!" Yace "Alhmdllh, mene yasa su Ramla ba su yi girkin ba" tace "Na ma gama, he's travelling ne shi yasa...." Abuturrab yace "To where?" Tace "Shiga ka tambaye shi mana" juyawa yayi ya fita ya wuce part din Abbansa, yana kkrin rufe briefcase dinsa ya shigo, Abba yace "How you?" Xaunawa yyi kasa yace "Alhmdllh tafiya xa kayi Abba?" Abba yace "In shaa Allah, ya maganar da muka yi da kai ranan?" Shiru Abuturrab yyi, lkci daya jikinsa yayi sanyi, Abba yace "This is not a matter of u looking at me that way, Yakumbo tace hada bikin da na Yusuf xa ayi..." Kamar xai yi kuka yace "Abba ni fa bani da kowa" Abba yace "That's not a problem, sai ka fara nema yanxu don ina jin nn da watanni biyar ne bikin Yusuf din, idan kuma ka amince mu yi maka xabi it's okay my Stubborn!" Abuturrab bai ce komai ba, Mami ta shigo da sallama rike da tray din breakfast, mikewa Abuturrab yyi ya sallami Abban nasa ya fice, ji yyi ransa ya baci, bai ko kalli Khaleesat dake gaishesa a parlor ba ya fice ya koma bangaren sa ya kusa minti ashirin xaune a waje kafin ya shiga ciki, shara ya sameta take a parlor, ya xauna kan kujera yace "Wel done" murmushi tayi bata ce komai ba, har ta gama ta shiga kitchen ma ta gyara, ya mike ya shiga bedroom yana fitowa ya kalleta yace "Na hada maki ruwan wanka a bathroom...." Xata yi magana wayarta ya dau ring a jaka, karasawa tayi da sauri ta ciro wayar taga Mumy ce ke kiranta, kallonsa tayi sai kuma ta xauna ta daga ta kai kunnenta, daga daya bangaren Mumy tace "Samantha kin shirya tafiya church kuwa?" Turo baki tayi tace "Mumy baki ko tambaye ni ya ciki na ba..." Mumy tace "Ohk ya cikin" kamar xata yi kuka tace "Yana sauki..." Mumy tace "Ohk

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login