Showing 63001 words to 66000 words out of 180592 words

Chapter 22 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1145

ya kama hannunta a hankali yace "Samha!" Dago kai tayi ta kallesa, ya sakar mata murmushi ya kai lips dinsa kan hannun cikin sanyin murya yace "I will never let you down dear, i will be ur hero, i will be ur everything...." Hawaye ya cika idonta ya dago ta ya rungumeta, ta fara kuka a hankali, jin tayi shiru ya dago kanta a hankali ya ga idonta a lumshe, kwantar da ita yayi ya mike ya nufi window yana tunanin next action din da xae dauka, can ya dau kudi ya fita, wani me taxi ya tsayar bayan tsayuwar kusan minti sha biyar a bakin titi duk yana duba responsible cab man da xae tsayar su yi magana, yana kallon mutumin yace "Pls ina d'an tambaya ne" cab man din yace "Allah yasa na sani" Abuturrab na shafa beard dinsa yace "Kasan inda xan samu agent... I mean their office, anywhere around?" Mutumin yace "Wae na gida?" Abuturrab yace "Yes!" Mutumin yace "Wanda na sani da nisa daga nan, sae dai..." Abuturrab yace "No mu je kawai ka kai ni" daga haka ya shiga mutumin ya ja taxi din. Tafiyar kusan minti ashirin suka yi suka iso office din wasu agent, Abuturrab ya fito yayi masa godiya ya basa dari biyar ya shiga office din, ba shi ya fito ba sae kusan karfe shidda bayan an basa tabbacin nan da xuwa gobe xa a karbar masa gida. Ko da ya dawo lodge dinsu tana bathroom tana wanka, ba a dau lkci ba ta fito daure da towel, tana ganinsa ta tsaya nan bakin kofa, yace "Naga alamar ba kya gajiya da wanka yarinyar nan...." Murmushi tayi bata ce komai ba ya mike xae shiga yayi alwala ta durkusa da sauri tace "Nooo" xaro ido yayi yace "Ina ruwana da ke?" Murmushi yayi ya shiga toilet din, ta mike da sauri. Ko kafin ya fito har ta gama shiryawa, yana kallonta yace "Xan je mosque, will be right back" ta gyada masa kai ya fita, sae bayan Magrib ya dawo dakin, ya ganta xaune shiru da alamar tunani take, ya karasa kusa da ita ya durkusa ya ajiye ledan fruits din hannunsa yace "Sorry Dear, na jira anyi magrib ne" ta d'an yi murmushi bata ce komai ba, ya xauna ya bude mata ledan fruits din yana kallonta, Apple ta dauka ta kai baki a hankali, shi ma ya dauka ya kai daya baki, wayarsa dake kan gado ya fara ring, ya dauka yana kallon screen din yaga Hajiya Mariya ce, ya daga ya kai kunne yace "Hello Mum!" Tace "Aliyu where is she?" Kallon Samantha yayi ya mika mata wayar yace "My mum!" Ta sa hannu ta karba ta kai kunne, Hajiya Mariya tace "Ya kk Samha?" Samantha tace "Lafiya Mumy ina yini?" tace "Lafiya lau, kiyi hakuri kin ji, Allah na tare da ku, kar ki sama kanki damuwa...." Kai kawae Samantha ke gyada mata kamar tana ganinta.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
34.....

Mikewa tayi a hankali ba tare da ta kallesa ba ta dau rigar baccin ta shiga bathroom, ba a dau lkci ba ta fito, kallo daya yyi mata ya dauke kai, ta nufi kan gado a hankali ta kwanta ta juya masa baya, bayan kusan minti goma ya mike ya cire shirt din jikinsa ya shiga bayi, ko da ya fito kashe tvn dake aiki yyi ya kashe wutan dakin ya karasa gado ya kwanta, a hankali ya birgina inda take, cikin sanyin murya tace "Doctor..." Yace "Samha...." Bata ce komai ba ya juyo da ita ya kwantar da ita kan faffadan kirjinsa yace "Sleep tight love, am with you" ta lumshe ido tayi lamo jikinsa, a haka har bacci ya dauketa, a hankali ya kwantar da ita ya mike ya koma kujerar dake dakin yayi kwanciyarsa amma ya kasa bacci sae juye juye yake, can dae ya mike ya shiga bayi ya dauro alwala ya fito ya tada sllh, sae kusan karfe uku da rabi ya samu yayi bacci, da asuba a masallacin dake cikin Hotel din ya fita yyi sllh sae da gari ya waye ya shigo masu dakin da breakfast, har ta shirya ya sameta, yana kallonta da mamaki yace "Ina fita kika tashi amma koh?" Kai kawai ta gyada masa, yayi murmushi yace "Alryt xo kiyi break kafin in shirya" daga haka ya shiga bathroom, ko da ya fito har ta gama cin abinda xata ci, yace "Are you sure kin koshi?" Ta gyada masa kai, shiryawa yayi ya ci chip da egg din kadan ya mike yace "Bacci nake ji Samha, let me sleep small" murmushi tayi ta mike xata gyara masa gadon yace "Noo don't worry dear...." Daga haka yayi kwanciyarsa, ta koma ta xauna ta rufe sauran breakfast din, yana kwanciya bacci ya daukesa, ita dai tana xaune idonta a kan tv, sae dae ko kadan ba sanin kan film din da ake tayi ba, tayi nisa a tunanin da take, Abbanta kawai take tunani wanda hakan yasa hawaye ya cika idonta, why did she accept to leave her family because of Aliyu, hade kanta da kujera tayi hawaye na sakko mata sae a snn take jin bata kyauta ba, tayi kukanta mai isarta daga nan ita ma bacci ya dauketa don yanda bai yi wani bacci ba haka ita ma bata jiya ba daren jiya duk tana kallonsa yana sllh, sai kusan goma da wani abu Abuturrab ya tashi, ganin yanda ta kife kai ya mike da sauri ya isa gabanta ya dafa ta yace "Samha" dagowa tayi da sauri tana kallonsa, kallon idonta ya dinga yi, da damuwa yace "Kuka kika yi?" Ta sunkuyar da kanta ya dago ta yace "Samha you re regretting everything koh?" Ta fashe da kuka tana girgixa masa kai, duk ya rikice yace "No plss samha, kar ki min kuka don Allah, naji xan maida ki gida...." Da sauri ta girgixa kai cikin sanyin murya tace "Am not regretting" yace "Toh me yasa kike kuka" goge hawayenta ta shiga yi cikin sanyin murya tace "Its just.... We re in trouble" ya lumshe ido ya kamo hannunta yace "Allah na tare da mu Samha, kar ki damu kin ji" sunkuyar da kanta tayi, yace "Tashi ki raka ni!" Ba musu ta mike ya kashe kayan kallon yace "Mu je" kofa ta nufa ya bi bayanta, suka fita ya kulle dakin, gun agents din jiya ya tafi, suna isa daya daga agent din yace su je ya ga gidan ko yayi masa, a motar agent din suka tafi, gida ne babba hadadde mai flats biyu, gidan na dauke da dakuna uku manya, Abuturrab ya kalli Samha yace "You like it?" Sunkuyar da kai tayi, yayi murmushi yace "Alryt, yallabai gidan yayi, thanks much" bbu bata lkci Abuturrab ya biya komai na gidan kusan 450k, da yamma bayan sun dawo hotel din yace "Xuwa jibi sae mu koma can koh dear?" Kallonsa tayi bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace "Kin yi shiru?" Murmushi tayi bata ce komai ba. Washegari Abuturrab shi kadae ya fita ya bar ta tana bacci don xuwa can gidan ya ga abubuwan da ya kamata ya xuba, a ranan yayi furnishing gidan gaba daya, har food stuffs sae da ya siya, ya kashe kudi ba na wasa ba, da yamma ya koma hotel, Wanka ya sameta tana yi, yyi kwanciyarsa don ya gaji, washegari da ya kasance alhamis misalin sha daya suka tafi can gidan, nan ya fara tunanin anya xae yi ynda Hajiya Mariya tace masa kuwa, bai jin xae iya xama gida daya da ita bayan ba muharramar sa bace, idan shaidan bai ci galaba kansa yanxu ba yasan ko a jima ko a dade akwai ranan da abinda yake gudu xae iya faruwa, don yanxun ma he's just fighting his self from inside, kwanciyarsa yyi a parlor yana tunanin next step din da xae dauka, ana kiran Azahar ya mike ya shiga toilet dake nn parlor ya daura alwala ya fita xuwa masallaci, ko da ya dawo a kitchen ya sameta ta daura girki, ya rungume hannayensa yana kallonta yace "Weldone dear..." Murmushi kawae tayi ta ci gaba da wanke shinkafar da take yi, ya juya ya fita xuwa balcony yayi xamansa, wata dattijuwa da baxata wuce 50 ba ce ta fito daga daya flat din idonta sanye da medicated ta rike jaka ta nufi parking space dake part din nasa ta bude daya daga motocin dake wajen ta shiga ta tada, horn tayi bayan ta fito compound din, Abuturrab ya kuma kallon motar ya dauke kai don yasan lkcn da yake dawowa daga masallaci lkcn mai gadin ya tafi, tayi horn yayi sau uku, can Abuturrab ya mike ya isa gate din ya bude mata, sauke glass tayi ta karasa gate din da motar tana kallonsa murmushi dauke fuskarta tace "Nagode kwarai..." Ya dukar da kai yace "Ina yini?" Tace "Lafiya lau, kai ne new tenant din Apartment din can kenan?" Kai ya gyada mata yace "Nine..." Tace "Maa sha Allah, you re welcome, tare da mai dakin ka koh?" Ya d'an yi jim sai kuma da sauri yace "Ehhh" tace "To sannun ku da xuwa, ni ce occupant din flat din can with my 3 kidz... Hope xa mu dinga ba makwabtaka hakkin sa" murmushi yayi sosai yace "In shaa Allah" ita ma tayi murmushin tace "Maa sha Allah, it's nyc meeting you, na fita aiki sae na dawo" yace "Toh Allah ya tsare" daga haka ta ja motarta ta fita ya rufe gate din, haka kawai yaji matar ta burgesa sae yake ganinta kamar Maminsa, yana murmushi ya koma balcony yayi xaman sa. Shinkafa da miya Samha ta girka tana gamawa ta fito ta gansa har lkcn yana balcony, ta jingina jikin kofa tace "Na gama" ya kalleta ya wara ido yace "Weldone sweetheart" murmushi tayi ta juya ta koma ciki ya mike ya bi bayanta, a tare yasa ta xuba masu abincin don yana son ta ci da yawa, ai ko haka yayi ta forcing dinta har suka cinye abincin, ya tagumi yace "But wa ya koya mamaki girki haka dear?" Tace "Uhm My mum" ya lumshe ido yace "You are a very good cook" a hankali tace "Thank you..." Yace "No thanks baby, bari in je masallaci it almost time for salat" tace "Toh" ya mike ya shiga toilet ya daura alwala ya fita, ta kwashe plates din don xuwa kitchen ta wanke.Bayan magrib yana dawowa daga masallaci matar daxu na shigowa, tsayawa yyi har tayi parking ta fito kafin tace komai ya gaisheta, da fara'a ta amsa tace "Mai dakin naka na ciki in shiga mu gaisa mu san juna..." Yace "Da ki bari xamu shigo yanxu tun da daga aiki kike ai" tace "Toh shknn ina jira" daga haka ta nufi bangarenta. Abuturrab ya juya ya shiga cikin gida, bedroom ya sameta yace "Samha, taso mu gaisa da new neighbor dinmu" ta kallesa tace "Do we need to?" Yace "Yess dear!" Mikewa tayi yace "Ki sa Hijab..." Ba musu ta dau daya daga sabbin Hijabs din da ya siya mata ta saka snn suka fita yana gaba tana biye da shi a baya, kararrawa ya danna ba a dau lkci ba wata yarinya da baxata wuce Samantha ba ta bude kofar, kallonsu ta shiga yi, Abuturrab yace "Hello, mum dinku na ciki koh?" Ta basu hanya tace "Ehh, welcome" Abuturrab ya shiga parlon Samha ta bi bayansa, sosai parlon ya hadu da gani dai kasan Naira ta xauna, xama yayi kan kujera ya nuna ma Samha gefensa ta xauna, yarinyar ta wuce ciki sae ga ta tafito tare da Mum din tasu, da fara'arta ta karaso parlon tana kallon Samha tace "Sannunku da xuwa" Samha ta sauke kai kasa ta gaisheta, ta amsa mata da murmushi tace "It's nyc meeting you... Ya sunan ki?" Satan kallonsa Samha tayi, yana murmushi yace "Samha!" matar tayi murmushi ita ma tace "toh kai fa?" Yana shafa kai yace "Aliyu...." Ta buda ido tace "Maa sha Allah ashe Abbana ne, amma sabon aure kuka yi koh?" Yar dariya yayi yace "Ehh haka ne" tace "Ae naga alama, Allah ya kawo Zuri'a dayyaba, ni sunana Hajarah...." Wara ido yayi yace "Mum dita knn..." Tace "Kai haba, shknn na samu d'a kuma babana..." Yayi dariya tace "Allah kuwa, muna xaune da kidz dina uku a nan, babban son dina Muhd na Uk, sai kanwarsa Maryam da ke Cairo tana aure, snn Fatima da Khadija da autata Rabi'ah, Ba mu yi shekara a garin Gombe ba don da a Abuja muke, yanxu haka ma Mai gidan na can sae dai yaxo week ends, am running my late dad's clinic dake nan ne shi yasa...." Abuturrab ya kalleta yana murmushi yace "Maa sha Allah Mami, Allah yayi jagora" tace "Ameen, amma a gombe ku ke?" Ya girgixa kai yace "A'a kano muke..." Tace "Ikon Allah, toh Allah dai ya bada zaman lafiya, kaga bata da kowa nn dont make her feel lonely ka dinga kyautata mata a ko da yaushe Abbana" yace "In shaa Allah Mami nagode" Hajiya Hajarah ta kalli Fatima dake xaune tana dannan waya tace "Ko ruwa baxa ki kawo masu ba Teemah" Abuturrab yace "Noo Mami Alhmdllh, xamu koma ne ynxu" Hajiya Hajarah tace "Toh shknn Boy, na gode kwarai" yar dariya yyi ya mike ya kuma yi mata sallama haka ma Samha snn suka fita. Sae da suka koma part dinsu yana kallonta yace "You like her?" Murmushi tayi ta xauna bata ce komai ba, da damuwa yace "Why ba kya son magana Samha, you re just nt ur self" ta wara ido tace "Ba komai fa, is just change of environment" yace "U will like it soon dear, nt when am with you" murmushin dae tayi, ya gyada mata kai snn ya shiga daki. A parlor yyi isha sbda hadarin da ya hadu ga iska ana yi, ita dai tana xaune parlon sae kallonsa take har ya idar, yana kallonta murmushi dauke fuskarsa yace "Ko kema kina son ki iya sllhn ne?" Tace "Uhmm" yace "Yeah dear sae in koya maki it's nothing ae" yar dariya tayi yayi shiru yana kallon fararen hakoranta tace "Wa yace maka ban iya ba?" Yace "A ina kika iya?" Tace "Uhm, na xauna gun kanwar Abbana Anty Aisha a kaduna, during my jss can nake xuwa yin long holiday, idan su Mumy xa su Jerusalem can ake kai ni, tare take hada ni da yaranta mu je islamiyya, in dai xa ayi sllh nima sae nayi a gidan, har na xo na saba idan na dawo gida sai in ta yin irin abubuwan islam shknn Mumy ta hana Abba ya kai ni kaduna kuma, at that time ina jss3, har yau kuma ban sake xuwa ba" Abuturrab dake ta kallonta ko kiftawa bbu yace "Yanxu kin iya alwala knn?" Tace "Uhm har da sllh ma, kasan suran da muke lkcn a islamiyyar da muke xuwa?" Da sauri yace "A'a" tace "Mulk" ya lumshe ido yace "Kuma kin iya?" Dariya tayi tace "May be xan iya yi da qur'an because i know the arabic letters very well" kallonta kawai yake can yyi murmushi yace "Gobe xa ki min in ji" mikewa tayi tace "Xan yi bacci...." Yace "Ohk dear ki rufe windows sbda ruwa" kai ta gyada masa ta nufi daki tana adduar Allah yasa kar ayi ruwan sbda tsoron tsawa da take. Washegari da safe wajajen karfe tara tana daki tana bacci Abuturrab kuma na xaune parlor sae missing system dinsa yake ga parlorn bai sa kayan kallo ba tukun, yasan accnt dinsa ya d'an girgixa da cire ciren kudin da yake in kuma xa aci gaba da haka to fa karewa xa suyi, ga credentials can gida bare ya fara neman wani aiki, Tausayin Maminsa kawae yake amma in dan Abbansa ne ko a jikinsa don dama sun saba irin haka, Ring din bell aka yi, ya mike yana kallon kofar, can ya karasa ya bude, daya daga yarinyar Hajiya Hajarah ce tsaye bakin kofar rike da basket me dauke da breakfast, ya d'an koma baya, tace "Mum tace a kawo" yace "Ohkk thanks soo much" daga haka ya karba ta juya ta wuce, ya koma parlor ya ajiye, ji yyi matar ta burgesa sosai sae yake jin ta a ransa kamar Mami, bude abincin yyi yaga wainar shinkafa ce ta miya sae brown yam and egg da fries egg with plantains, a wani karamar warmer kuma ga Irish, murmushi yayi ya koma yyi kwanciyarsa kan kujera, sae kusan karfe goma Samha ta fito cikin shirin doguwar riga amma ba abaya ba, karasowa tayi parlon ta xauna kasa ta sunkuyar da kai ganin yanda yake kallonta cikin sanyin murya tace "Ina kwana" ya mike xaune yace "Lafiya lau dear, ashe kin iya bacci kema haka" murmushi tayi bata ce komai ba, ya nuna mata breakfast yace "Gashi Mami tace a kawo mana" ta kalli abincin a hankali tace "Mun gode" ya mike tsaye yace "Dama ke nake jira, let eat" ba musu ta mike suka isa gun breakfast din. Da rana mai aiki ne ta kawo masu lunch, Abuturrab ya karba yana kallonta yace "Hajiya na nan ne?" Ta girgixa kai tace "Ta fita aiki tun safe" yace "Alryt" Da yamma bayan la'asar yana zaune bakin gate tare da mai gadin gidan Hajiya Hajarah ta dawo, gaisheta yayi ta amsa da murmushi tace "Ya gidan?" Yace "Alhmdllh Mami ya aiki?" Tace "Alhmdllh, ina Samha?" Yace "Tana ciki" tace "Toh a gaisheta" yace "Mami mun gode for the food" tace "Ohh it's nothing Boy" daga haka ta ja motar ta ta shiga gidan.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?




By khaleesat Haiydar=???
'




35....

Yau kwana goma sha hudu da xuwan su Gombe, yana xaune parlor laptop a gabansa sae dai gaba daya hankalinsa baya kan abinda yake, damuwarsa daya yanda yake cire kudi a account gashi ba shigowa wasu ke yi ba, at all shi bai iya sana'a ba bae ma san yanda ake yi ba, he don't want to run short of money, ya lumshe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login