Showing 123001 words to 126000 words out of 180592 words

Chapter 42 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1157

ta wuce daki ta fada kan gado ta ci gaba da kukanta, a dakinsa ya ajiye jakar snn ya shiga inda take ya kwanta gefenta ya jinginar da kansa da nata yace "So dai kike in lallashe ki ko baby, ohk then" mikewa xaune yayi ya dagota ya fara kissing dinta, tun tana son kwace kanta har ta gaji ta hakura, ae ko ya lallasheta yanda ya kamata, sai kuma ta 6uge da kukan shagwaba daga shagwaban kuma sai bacci, jin xa'a tada sllhn zhur yasa shi mikewa don har ya fara bacci shi ma, ya shiga bathroom yyi wanka ya dauro alwala ya fito, ya gabatar da sllhn a daki don har an idar masallaci, bayan ya idar ya koma yyi kwanciyarsa. Sai kusan karfe uku Samha ta farka ta kalli agogo snn ta kallesa, a hankali ta kai hannu fuskarsa, ya bude ido a hankali tace "You've nt prayed zhur" jawota yyi jikinsa ya lumshe ido yace "Nayi mana baby, amma kinsa nayi missing jam'i" ta buda ido tace "Ni kuma" yace "Ehh mana, u made me left this world" rufa fuskarta tayi a kirjinsa, yyi murmushi yana shafa dogon gashinta, can ta xame jikinta yaki saketa yace "Ina xa ki?" Tace "Wanka" saketa yyi yace "Toh muje in maki" Wani kallo tayi masa ta fice daga dakin da sauri, dariya yyi yace "What is she still hiding?"

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By Khaleesat Haiydar=???
'
75.....

Da daddare suna bedroom ta dauko box din da Hajiya Mariya ta bata ta mika masa tace "Mum ta bani wnn" karba yyi ya bude ya wara ido yace "Ehen, nine knn ba a ba komai ba, a gold for you!" Tayi murmushi tace "Kaga ta fi so na" ya langwabar da kai yace "Gashi nn naga alama" daukan dankunne daya yyi ya cire mata na kunnenta ya sa mata, ya cire dayan ma yasa yace "Uhmm you're glittering" lumshe ido tayi, yyi pecking dinta yace "I love you wife" a hankali ta kwanta jikinsa cikin sanyin murya tace "I love you more"
3wks ltr.
Abuturrab na bedroom misalin karfe tara da rabi, fitowarsa daga wanka knn yana shiryawa da yake saturday ne sai yamma yake fita gun aiki, k'auri ya dinga ji ya juya yana kalle kalle sai kuma ya ajiye hair brush din hannunsa ya fita da sauri, yana shiga kitchen din ya ganta xaune kasa ta jingina da bango tana bacci, ya kalli irish din dake cikin mai har ya fara baki ya kashe gas din, durkusawa yyi gabanta yana kallonta, can ya kamo hannunta ya sauke idanuwansa kansu, a hankali ta bude idonta, ya tsura ma idanunta ido, murya can kasa tace "Doctor.... Am feeling sleepy" Murmushin da ya bayyana fararen hakoransa yyi yace "Koh?" Kmr warce ta tuno abu ta wara ido ta mike tsaye da sauri tana kallon pan din dake kan gas, kallonsa tayi kmr xata yi kuka tace "Doctor ya kone, i don't knw...." Rufe bakinta yyi ya ja ta suka fita daga kitchen din ya kaita daki ya xaunar da ita gefen gado, ya kanne mata ido yace "Ke fa kika hanani bacci daren jiya da shagwaban ki baby, ni ban yi bacci a bathroom ba da naje wanka sai kece xaki je kitchen kina bacci ki kona mana abinci?" Kallonsa take kamar xata yi kuka, yayi dariya ya shafa fuskarta a hankali yace "Toh yi hakuri wife, bari in shirya sai in fita in siyo mana breakfast, go nd take ur bath" turo baki tayi ta mike ta nufi bathroom ya bi ta da kallo yana murmushi, har ya gama shiryawa ya fita nearest fast food ya siyo abinda xae siyo ya dawo bata fito daga wanka ba, mamaki ne ya cika sa, ya ajiye ledojin hannunsa ya bude kofar bathroom din, kwance ya ganta cikin bathtub ta tara ruwa tana ta bacci ciki abunta, xaro ido yyi ya karasa wajen ya durkusa ya kashe ruwan yana kallonta murya can kasa yace "Toh fah" hancinta ya ja ta bude ido da sauri yace "Nan din ma baccin kika xo kina yi baby?" Kalle kalle ta fara yi, ya girgixa kai ya jawo sponge tana nonnokewa har ya gama ya fito da ita daki, gaba yasa ta har ta gama shiryawa kar ta kuma yin baccin, yana kallon lumsassun idonta yace "Har ynxu baccin kike ji koh?" Kai ta gyada masa yace "Toh bari kiyi breakfast sai ki kwanta" ta girgixa kai tace "Bana jin yunwa ynxu" shiru yyi yana kallonta, can yace "Alryt kwanta baby" kwanciya tayi kan gadon yyi murmushi ya mike ya fita don hado coffee, ko kafin ya dawo har tayi bacci, haka ya xauna kusa da ita ya tsura mata ido yana kallo, wani kyau na musamman yaga ta kara da haske, can underneath his breathe yace "Waow!" Juyawa yyi jin ringing din wayarsa ya mike ya isa gaban mirror ya dauka ya ga Ummi ce ke kiransa, ya langwabar da kai yace "Oops" bai yi budgeting fita da safe yau ba, a hankali ya daga wayar ya kai kunnensa ya amsa sallamarta snn ya gaisheta, tace "Kun tashi lfya boy?" Yace "Alhmdllh Mami" tace "To Madallah, hope baxan takura ka ba boy xan sa ka aiki coz m nt around...." Yace "Not at all Mami" tace "Alryt, fatima nake son ka dauko daga makaranta, Asthman ta ne ya tashi, xan baka number kawarta ku dinga communicate har ka je can...." Yace "Subhanallah, suna lectures weekend ne?" Tace "Not at all, ae tafi sati biyu a schl, a hostel take" yace "Alryt mami, buh is she with her inhaler?" Tace "They can't find it, daga can kawai ka wuce clinic da ita ko allura ne ayi mata" yace "Toh Mami bari in tafi ynxu" daga haka ya katse wayar ya mike yana kallon Samha, lullubeta yyi da bargo, ya kashe Acn dakin ya sake mata curtains, ya daura lips dinsa kan forehead dinta yace "I wil be right back wife" daga haka ya dau makullin mota da wayarsa ya fita, yana warming motar message ya shigo wayar yaga Ummi ce ta turo masa number kawar fatima Salima, sai da ya bar compound snn ya kira number, ba a jima yana ringing ba aka dauka yyi sallama, daga daya bangaren aka amsa, yace "Salima ce?" Tace "Yea..." Yace "Ya jikin fatiman?" Tace "To ga ta nan dai" yace "Kuna hostel din ne?" Tace "Ehh wai da clinic xamu wuce ynxu it's getting worst" yace "Noo kar ku je ina hanya ynxu" daga haka ya katse wayar, yana isa makarantar ya kuma kiranta tayi masa kwatancen inda hostel din nasu yake, ya jira su har suka fito su uku da Fatiman, Fitowa yyi ya bude back seat yana kallonta yace "Sorry," sai da ta shiga motar snn ya kalli frnds dinta yace "Thanks much, xa mu tafi hospital da ita ynxu" Salima tace "Toh ba sai mun bi ku ba knn" yace "Noo kawai ku koma ciki nasan kila ma karatu ku ke" daga haka yyi masu sallama ya xaga ya bude driver seat ya shiga duk suka bi sa da ido, ya rufe motar ya tada ya dau hanyar gate, ta madubi yake kallonta jefi jefi, sai yaji tausayinta ganin tana jin jiki, yace "Fatima" da kyar ta dago don dama kife kanta tayi, yace "You sit upright, kar ki sake dukawa" mayar da kanta tayi, bai kuma cewa komai ba ya d'an kara speed, suna isa clinic, yyi parking ya fito ya xaga ya bude mata motar ya dagota, hijab din jikinta ya cire ganin rigar dake jikinta ya d'an kamata, ya kai hannu bayanta ya d'an bude zip din ya mayar mata da hijab dinta ya fito da ita daga motar suka shiga asibitin, dai dai sakkowar Dr Shariff daga sama, yana ganinsu ya nufo su yace "Subhanallah" Nurses biyu dake wajen su ma suka yo kansu suna mata sannu, Abuturrab ya mika masu ita yace ku shiga da ita wancan ward din Shariff ya bi bayansu, Pharmacy Abuturrab ya shiga ya karbi alluran da xai mata snn ya fito ya wuce ward din, har Dr Shariff ya cire mata hijab din jikinta ya xaunar da ita ta jingina da bango kan gadon, shi dai Abuturrab kallonsa kawai yake ganin ynda ya wani daga hankali, kawai ya mika masa alluran yace "Gashi kayi mata" Dr Shariff yace "Inhaler dinta fa wai" Abuturrab ya bude hannu alamar bai sani ba, daga haka ya juya ya fita don basa waje yyi mata alluran, ba a dau lkci ba Shariff ya fito yana kallon Abuturrab yace "Let me get her another a office din Dr" daga haka ya wuce sama xuwa office din Ummi, murmushi Abuturrab yyi, bayan yan mintuna sai ga shi ya sakko da sabon inhaler ya shiga ward din, Abuturrab ya bi sa yace "Tunda kayi mata injection kawai ka bar inhaler din, she will be fine soon" Dr shariff yace "Ohh, exactly" murmushi Abuturrab yyi ya juya ya fita, ba a dau lkci ba bacci ya dauke fatima bayan numfashinta ya fara yin dai dai sai a snn Shariff ya fito, shi dai Abuturrab na xaune duk hankalinsa yyi kan Samha, ya mike yana kallon Shariff yace "In tafi kawai xaka mayar da ita gida Dr?" Shariff yace "Am attending to patient ae, sae dai idan xaka tsaya sai in mayar da ita gida,n" Abuturrab yyi dariya yace "Nima matata na can gida na baro ta ba lfya" Shariff yace "Alryt then, ka jira ka mayar da ita kawai" Sai bayan kusan minti talatin fatima ta dawo dai dai, Abuturrab dai na ta xaune duk hankalinsa na kan wife dinsa, karfe sha daya ta fito daga ward din, Abuturrab ya kalleta ya mike yace "How you feeling now" ba tare da ta kallesa ba murya can ciki tace "Fyn" bai kara minti biyar clinic din ba suka wuce gida tare. Yana gama parking ta bude motar ta fita gabansa ya dinga faduwa kar Samha ta ganta ya shiga uku, sai da yaga tayi nisa ta kusa part dinsu snn ya fito daga motar, sae a snn ya tuna ko godiya bata yi masa ba, ya bi ta da wani irin kallo, dai dai lkcn da ta juyo ta kallesa suka hada ido, murmushi yaga tayi ta yi gaba abun ta, ya d'an yi tsaki ya wuce ciki, ga mamakinsa har lkcn bacci Samha take, ya xauna gefenta ya langwabar da kai yace "Wnn wani irin baby ne xai dinga sa min wife dita bacci haka" ji yyi kmr ya tasheta tunawa da yyi bata karya ba har lkcn, ya dai kyaleta kawai ya mike, ana kiran sllhn zuhr ya tasheta, ya kai ta bathroom ta wanke bakinta ya wanke mata fuska ya fito da ita sai layi take masa, da kansa ya dinga bata tea din da ya hada mata, ta sha me yawa kafin tace ta koshi, xata kwanta yace "Baby baccin ya isa haka plss, mu je in kai ki yawo ki ga gari" kmr xata yi kuka tace "Kawai kwanciya xanyi baxan yi bacci ba" xai yi magana wayarsa ya fara ring yana ganin Ummi ce ta langwabar da kai, can dai ya daga tace "Boy sannu da kkri fa, Allah yyi albarka" yace "Amin Mami" tace "Ka turo min Samha ynxu" ya kalli Samha da ta kwanta ta lumshe ido, yace "Toh Mami" yana katse wayar ya dagota yace "Baxa fa ki kara wani baccin ba" kwace kanta tayi a fusace tace "Did i tell you am sleeping??" sai da ya runtse ido jin tsawan da ta daka masa, can ya bude idon a hankali yace "Ohk am sorry wife, dama Mami ce tace ki je" ta kallesa da sauri tace "In je?" Yace "Yes she just called" a hankali tace "Amma sai anjima koh? I dnt feel like going out" Yace "Noo, ki je ynxu baby kilan jira take" da kansa ya dauko mata hijab ya mika mata ta karba ta sa, ta mike ya rakata har balcony, a hankali tayi sallama ta bude kofar parlon ta shiga, ji tayi kanta na juya mata kamshin miyan da ake a kitchen, ta karasa ta xauna da kyar tana kallon Ummi ta gaisheta, Ummi dake ta kallonta tace "Bacci kike ne daughter" a hankali tace "Na tashi Ummi" Ummi dai sai kallon kwayar idonta take, can tace "Alryt, ki gaya min ko da abinda kike bukata, i mean anything... " Samha ta kalleta, can tace "Ba abinda nake bukata Ummi" Ummi tace "A'a kar fa ki ji komai beside hakkin ki ne, sadakin ki ne...." Ta girgixa kai kawai jin cikinta na hautsinewa, cike da karfin hali tace "Ba komai Ummi" Ummi da ta lura da yanayinta tace "Are you okay?" Mikewa tayi da sauri tana toshe baki, Ummi ta mike ta kamota ta nufi toilet dake parlon da ita da sauri, kafin ta shiga ta fara kwarara aman a wajen, Ummi na tsaye sai sannu take mata, can ta duka ta riketa ganin ta galabaita, sai da aman ya tsaya mata snn ta dagata suka shiga bayin, ta taimaka mata ta wanke bakinta, ta cire hijab din jikinta ta ajiye cikin bucket dake bayin, jin temperature dinta ya d'an yi sama ta xuba mata ruwa kadan a kanta snn ta ja ta suka fita daga bayin, Samha ta toshe bakinta hade da hancinta don ko da wasa bata son ta kara jin aroman miyan, hakan yasa Ummi ta fitar da ita gaba daya daga gidan, tana rike da ita ganin duk tayi weak ta wuce part dinsu da ita.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
76.....

Yana xaune parlor ya bude laptop knn Ummi tayi sallama suka shigo parlorn, mikewa yyi ya amsa sallaman, Ummi ta xaunar da ita kan kujera tana mata sannu, bata iya ta amsa ba ta kwanta tana mayar da numfashi, Ummi ta kallesa tace "Wani taimakon ka bata?" Ya d'an sosa kai ba tare da ya kalleta ba yace "Mami... nothing yet" tace "To sbda me?" Still bai kalleta ba yace "I just saw the symptoms this morning Mami" Mami na kallonsa tace "Toh yyi, Allah ya kawo mata da sauki, naga bata ci komai ba sai ruwan shayi" yace "She have being sleeping tun da safe, sae da na dawo clinic daxu ma na bata shayin" Ummi ta kalleta ta xauna gefenta tace "Me kike son ci daughter" a hankali ta bude ido tace "Bana jin yunwa Ummi" Ummi tace "A'a you've nt taken anything today, ko a kawo maki shinkafa...." Da sauri tace "A'a..." Ummi tace "Toh me kike so" shiru tayi, sai kuma a hankali tace "Kila tuwo xan ci" Ummi tace "Tuwo?" Ta gyada kai, Ummi tace "Da wani miyar?" Tace "Miyar ganye" mikewa Ummi tayi tace "Toh bari a maki" daga haka ta fita, Abuturrab ya xauna gefenta yana shafa fuskarta yace "Amai kika yi baby?" Kmr xata yi kuka tace "Bana son kamshin miyan" ya lumshe ido ya bude a hankali yace "Sorry babyna, in'sha Allah baxa mu yi wahala sosai ba" ta kallesa tace "Na mene?" Murmushi yayi ya hade goshinsa da nata, murya can kasa yace "Komai ma" Kauda kanta tayi, ya juyo da fuskarta yace "Baxa ki ce Amin ba wife" kallonsa kawai take don ko magana ma bata son yi, can ta lumshe idanuwanta, yyi murmushi ya koma kan laptop dinsa. Bayan awa daya Usaina ta shigo parlon da sallama ta gaida Abuturrab snn ta ajiye abincin hannunta ta fita, mikewa yyi ya nufi kitchen ya dauko plate da spoon ya isa inda Samha take tana bacci ya xauna gefenta ya daura hannu fuskarta yace "Baby ga tuwon an kawo maki, tashi ki ci...." A hankali ta bude idanuwanta ya daga ta ta xauna snn ya sauka kasa ya bude warmer din tuwon ya dibar mata ya rufe, kallonta yyi yaga ta jinginar da kanta da kujera ta rufe idonta, ya bude miyan ya dibar mata a kan tuwon da nama snn ya tashi ya xauna kusa da ita yace "Gashi baby" a hankali ta bude idanuwanta, lkci daya ta kauda kai da sauri ta matsa daga gun tana girgixa masa kai tace "Zan yi amai" yace "Miyan da kika ce kina so ne ae dear" taki juyowa sai girgixa masa kai take, ya mike ya dawo kusa da ita tana ido hudu da abincin ta fara yunkurin amai, mikewa yyi ya koma baya, ta fashe da kuka tace "Bana son in ga abincin doctor amai xan yi" daga haka ta tashi ta wuce daki da sauri, ya bi ta da kallo, can ya sauke ajiyar xuciya ya ajiye abincin ya xauna gefen kujera, mikewa yyi ya bi bayanta, durkushe ya ganta cikin bayi ya isa kusa da ita, tana kallonsa da kyar tace "I want to throw up doctor, ya ki xuwa" durkusawa yyi kusa da ita yace "It's because u haven't taken anything wife" ta girgixa kai tace "Baxan iya ba" dagota yyi suka fita daga bayin ya xaunar da ita gefen gado yace "Toh in kawo maki tea xa ki sha?" Kai ta gyada masa ya kwantar da ita yace "Toh ina xuwa" daga haka ya fita ba a dau lkci ba ya dawo rike da cup din tea, ba laifi ta sha tea din kmr daxu snn ta koma ta kwanta. Tun daga wannan rana Samha tayi bankwana da lafiya, laulayi take me tsanin wanda hakan yasa ya dinga tausayinta ba kadan ba ganin shekarunta, d'an ruwan tea'n da ta ke sha da farko farko shi ma yanxu idan ta sha sai ta amayar gaba daya, bbu abinda take iya ci sai gayan shinkafa shi ma sai an ci sa'a, hakan yasa Ummi ke yi mata kunu shi ma bai fi ta sha sau daya a rana ba, duk ta rame ba kadan ba sai haske, shi kansa ya rame sai ka rantse tare suke ciwon, ko kadan bai son wnn laulayin da take, wani lkcn sai yaji xuciyarsa na urging dinsa kan ya rabata da cikin don wahalan yyi yawa, sosai Ummi ta d'aga masa kafa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login