Showing 72001 words to 75000 words out of 180592 words

Chapter 25 - Noorul Huda Book 1 Complete Hausa Novel

03 Oct 2025

1136

na kan maganganun Maminsa da ya tuna sai gabansa ya fadi, shi dai yasan he can't do without Samha, gashi dai duk rashin jin sa baya tsallake maganan Mahaifiyarsa sai dai by mistake, tunanin yanda xai shawo kanta kawai yake amma bai san taya ba, karfe biyar ya bar clinic bayan ya gama abinda yake, hadari ne sosai garin me hade da iska ya shiga mota ya dau hanyar gida, tsaye yyi da motar bakin gate yana jiran motar da ya tarar gate din ya shiga, cije yatsa yyi cike da takaicin clashing din da suke yawan yi da fitsararriyar nn a cewarsa, gani yyi ta ki tafiya bayan gashi ta danna kan motar compound din, mai gadi dai ya koma yyi xamansa, can kuma dai ta ja motar ta shiga, ya yyi tsaki ya bi bayanta yyi part dinsa, yana gama parking ya fito yana satan kallon motarta ganin irin parking din da tayi, har lkcn iska ake yi sosai ga yayyafin da aka fara, har ya nufi part dinsa ya juyo da sauri jin sound din da yyi kama da na faduwa, kallon mamaki ya shiga yi mata ganinta a kasa, ganin she's gasping for breathe ae bai san lkcn da ya nufeta da sauri ba, yana isa gabanta ya durkusa ya dagota, a dai dai lkcn da Samha da Khadija suka fito daga parlor jin tsayuwar mota, daukarta Abuturrab yyi ya nufi cikin parlor da ita da sauri don an fara ruwan sosai, Khadija ta xaro ido tace "Innalillahi, Her inhaler....." Daga haka ta yi part dinsu da sauri ita ma, ita dai Samha bin su da ido tayi, Abuturrab ya kwantar da ita nan tsakiyar parlon yana kallon khadija da ta shigo yace "Me ake bata?" Khadija ta nufi daki da sauri tace "Inhaler dinta..." Yana rike da ita Khadija ta fito kamar xata yi kuka tace "Ni ban san inda ta ajiye shi ba, ina ta dubawa...." Abuturrab na kallonta yace "Ina inhaler din ki?" Bai ga alamar ta ma san yana yi ba don she is fighting seriously to get her breathe, Abuturrab yace "Inhaler kadai take amfani da, ba a mata allura ne?" Khadija ta girgixa kai tace "A'a ba ayi, sai magani da inhaler...." Da gudu ta koma daki dubo maganin sai ga ta ta dawo a rikice tace "Ni ban gani ba wllh" Abuturrab ya ciro waya ya mika mata yace "Kira Mami yanxu" daga haka ya daga ta ya xaunar da ita ya cire mata veil din da tayi roll a kai, Ummi na daukar wayar Khadija tace "Ummi Asthman Sister ne ya tashi ban ga inhaler ba" Ummi tace "Subhanallah, where did she keep d inhaler kin duba motar ta, where is she now?" Khadija tace "Uncle ne ya shigo da ita yace in kira ki, let me check d car" Ummi tace "Alryt yi sauri ki duba ba shi wayar" Mika ma Abuturrab wayar tayi, ta fice da sauri duk da ruwan da ake xuwa gun motar yayar tata, Ummi tace "Hello Doctor, wai ba a ga inhalern ta ba koh?" Abuturrab yace "Eh Mami, ba ayi mata allura ne?" Tace "Ban fiye son alluran bane son, but idan ba a ga inhalern ba bari in kira clinic yanxun nn a kawo mata alluran..." Daga haka ta katse wayar, ya ajiye ya jinginar da ita jikin kujera yana kallonta yace "Where is ur inhaler?" Dawowa khadija ta kuma yi tace "Ni dai bn gani ba ka kara kiran Ummi plss" daukar wayar yyi ya kira mum din tasu kuma, tana dagawa tace "Na sa Dr Usman ya taho da allura ynxu, he is on his way, kafin ya xo you tell khadija to check my room gun da nake ajiye drugs ta kawo maka magungunan sai ka cire wanda xa ka bata..." Abuturrab yace "Alryt" ya kalli khadija ya bata sakon ta nufi dakin, tana fitowa da drugs din ya dudduba ya dau wanda ya kamata, ya karbi ruwan da khadija ke mika masa, maganin ya kai ma fatima baki snn ya bata ruwan yana kallonta, daga haka ya jinginar da ita jikin kujera, yana nn durkushe gabanta Khadija kuma na tsayr kansu Dr Usman ya kwankwasa kofar parlor, khadija ta karasa da sauri ta bude kofar ya shigo yana kallon Abuturrab da ya karbi ledan hannunsa yace "Har ynxu ba a ga inhalern ba?" Abuturrab na kokarin hada alluran yace "Yeah!" Yana gama hadawa ya kalli fatima da har lkcn numfashinta bai dawo dai dai ba, mika ma Usman Alluran hannunsa yayi yace "Ga shi kayi mata" Usman yace "Noo kai mata kawai mana" mikewa tsaye Abuturrab yyi ya kama hannun Usman ya saka alluran a ciki yace "Kayi mata doctor, ina xuwa yanxu" daga haka ya nufi kofa, Usman ya durkusa don yi mata alluran, part dinsa ya nufa cikin ruwan, har lkcn Samha na tsaye balcony, Murmushi ya sakar mata ya isa gabanta yace "What r u doing here baby?" Juyawa tayi bata ce komai ba tayi shigewarta ciki, ya d'an yi jim, sai kuma ya bi bayanta, kwance ya sameta parlor ya xauna daga gefenta yace "Abun yar shariya ce kuma dear" ba tare da ta kallesa ba tace "Welcome" ya d'an yi murmushi ya mike yace "Thank you" daga haka ya shiga bedroom, sauya kayan jikinsa yyi xuwa jallabiya ya fito parlor, tana ganinsa ta rufe ido kamar mai bacci ta juya baya, ya nufi inda laptop dinsa ke ajiye a parlon ya dauka ya xauna kan kujera ya bude, bai yi minti goma parlon ba aka danna bell ya mike ya isa kofar ya bude, Dr Usman ne tsaye yace "Doctor nayi mata alluran, da sauki jikin nata yanxu, i want to leave now" Abuturrab yace "Alryt Doctor, let me check on her again, sai gobe" daga haka suka yi sallama Dr Usman ya wuce, tsaye Abuturrab yyi bakin kofar, can ya juya ya kalli Samha da har lkcn bata juyo ba bare ta bude ido, fita yyi parlon ya ja kofar, Cikin ruwan ya shiga xuwa part din Hajiya, Khadija na xaune gefenta ta lullube ta ita kuma tana kwance kan kujera, karasawa yyi parlon yana kallonta, ba karamin tilasta kansa yyi wajen ganin ya bude baki yace mata "How you feeling?" Sae a snn fatima ta kallesa, sai kuma ta dauke kai ta gyada masa kai kawai alamar fyn, shiru yyi kmr me tunanin abinda xai ce kuma, can dai ya kalleta suka hada ido, kasa cewa komai yyi, yyi saurin dauke nasa idon ya kalli Khadija yace "Yaushe Mami xata dawo?" Khadija tace "Tace tana hanya ynxu" yace "Alryt," daga haka ya kuma satan kallon Fatima nn ma suka hada ido ya juya xai fita daga parlon yaji tace "Thank you..." Ya kalleta bai ce komai ba yyi ficewarsa. Part dinsa ya koma, wnn karan Samha bata parlor, ya shiga daki ya ganta kwance idonta rufe, juyawa yyi ya koma parlor, yyi ta xamansa yana operating laptop har aka kira Magrib, alwala yyi ya fita xuwa masallaci don ruwan ba sosai ake yi ba, ko da ya dawo ci gaba da abinda yake yi yayi, karfe takwas saura aka danna bell ya mike ya bude kofar ya ga Ummi tsaye tace "Son nagode kwarai fah" yace "Mami ae da kin kirani in xo cikin ruwan nn kika fito" tace "It's not heavy ae, ina Samha" yace "Tayi bacci Mami..." Tace "Alryt, Allah bar xumunci, I don't just knw what's wrong with fatima da xata dinga yasar da Inhaler dinta anyhow..." Murmushi yyi yace "Allah ya tsare gaba Mami" tace "Ameen, Allah ya tashe mu lfya" daga haka yyi mata sallama ta juya ta wuce ya koma ciki. Karfe goma ya shiga kitchen bai damu da abincin dake ajiye kitchen din ba kuma yasan na shi ne,ya hada tea kawai ya fito parlor, yana gama sha ya shiga second room, ruwan wanka ya hada a bathroom yyi ya fito yyi shirin bacci yyi kwanciyarsa.

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
Kawayen Asali Maman Shakur and Fiddausi s Dangi Jiddoh na gaisuwa, ku sani ku na raina a ko da yaushe=??

40.....

Kasa bacci yayi ya rasa dalili, har karfe sha biyu da rabi idonsa biyu, mikewa xaune yayi daga karshe ya jima a xaunen kafin ya tashi ya nufi kofa ya fita, dakin da take ya karasa, ya kusa minti uku tsaye kafin ya tura kofar a hankali ya shiga, kwance ya sameta cikin bargo, ya karasa gefen gadon ya xauna yana kallonta, can ya sa hannu a hankali ya cire bargon, bai kai ga gama cirewa ba ta rike, kallonta ya tsaya yi can ya fixge gaba daya yace "Are you okay?" Mikewa tayi xata sauka daga kan gadon ya rikota yace "You re going no where har sai kin gaya min d reason for ur sudden change of behavior today, what's wrong with you?" Wani kallo ta watsa masa da yasa shi buda ido, ta kwace hannunta tace "That's because i want to be left alone...." Sai kuma ta fashe da kuka tace "Look Aliyu, you take me back to my parent immediately, i don't want any of this anymore...." Fixgota yyi yana mata wani irin kallo yace "Amma dai bni nasa ki taho gidana ki same ni ba that very night ryt?" Tsayawa tayi tana kallonsa ko kiftawa bbu, ya sake ta ya mike ya fice daga dakin ta bi sa da ido, har karfe daya tana nn xaune yanda ya bar ta ko motsi ta kasa, da kyar tayi karfin halin mikewa daga karshe, ta dau Hijab ta saka ta nufi kofa ta bude ta fita xuwa parlor, bata yi xaton ganinsa a parlorn ba, kuma suka yi ido hudu don kwance yake kan 3 sitter, ta dauke kai ta nufi kofar parlorn da sauri, mikewa yyi tana ganin haka ta ja kofar taji sa a rufe tana kkrin budewa da makullin jiki ya karaso ya fixgota, wani ihun da ya ji har tsakiyar kan shi ta saki tana son kwace kanta, ya rungumeta ya rufe bakinta da hannunsa yace "Meye hakan kike yi? Are you on ur right senses" Kokuwa ta dinga yi da shi tana son freeing kanta da bakinta a hannunsa amma ta kasa don wani irin rikon da yasa ko motsin kirki bata iya yi yayi mata, gajiya tayi tayi give up, sai a snn wasu hawaye masu xafi suka dinga xubo mata, duk jikinsa yayi sanyi a hankali ya saketa ta sulale nan gabansa ta fashe da wani matsanancin kuka, xubewa yyi gabanta kan gwiwowinsa shi ma, da kyar yayi karfin halin cewa "I didn't mean it Samha, forgive me plss i don't know what came over me...." Mikewa tayi da sauri ta kuma nufar kofar shi ma ya mike tsaye tun kan ta isa ya rikota, duka ta dinga kai masa cikin kuka tana cewa "Ka bude min pls i am going back to my parent, let me out immediately, xan maka ihu idan baka bude min ba" toshe bakinta yayi ganin da gaske ihun xata kuma yi, ya d'aga ta kamar yar shekara biyar yayi bedroom da ita ya direta kan gado yace "Pls you stop all this Samha and listen to me, am vey sorry don Allah kiyi hakuri i mean none of what i said to you....." Bbu irin lallashin da bai yi mata ba amma kamar yana d'a d'a tunxurata, sosai yake jin kukan da take har cikin ransa, wanda hakan yasa bai yi wani tunani ba ya kai bakinsa nata, nan ma dai ba karamin kokuwa tayi da shi ba amma lkci daya yasa ta nutsu, Tun yana yi don lallashi har abun ya fara wuce gona da iri, lkci daya ta fara kokarin kwatar kanta amma ta kasa don Abuturrab yayi nisa, xaro ido tayi da duk karfinta ta kwace bakinta cikin rawan murya tace "Don Allah kayi hakuri doctor ka sake ni, what's all this" doctor kam bai san tana yi ba, lkci daya ta fashe da kuka cikin rawan murya tace "Na shiga uku, Aliyu pls stop this am begging you, pls stop...." Da kyar murya can kasa taji yace "Pls Samha, you know... You know i... i love you..." Gigicewa tayi tace "Wayyo Mumy na shiga uku, don't Aliyu, i followed you because i trust you. Don't betray my trust for you.... Na yarda da kai...." Sama sama ya dinga jin abinda take cewa wanda hakan yasa jikinsa yayi sanyi amma ya kasa hana kansa, ji yake kamar his life depend on this, he just can't let go of her, cikin wata iriyar murya da ba tasa ba yace "Trust me Samha, auren ki fa xan yi..." Tana kuka sosai tace "Baka aure ni ba tukun doctor, don Allah ka tausaya min ka bari, ka daina plsss" Doctor fa yayi nisa bai jin kira, ba din daukewa da numfashinta ke kkrin yi ba tsabar tsoratar da tayi a lkcn da Samha fa an fita daga lane din da ake, ba shiri ya dawo Abuturrab dinsa sai dai duk jikinsa ya mutu, lallashin nata ma ya kasa, yana kallo ta mike ta fada bathroom, bayan kusan minti goma yaji karfi ya xo masa yayi karfin halin mikewa ya nufi bathroom din, murda kofar yyi yaji a rufe, ya jingina jiki ya lumshe ido cikin sanyin murya yace "Open pls Samha, kiyi hakuri don Allah, i never meant that too..." K'in budewa tayi kuma bata ce masa komai ba sai dai yana jin sheshshekar kukanta, ya durkushe wajen ya dafe kansa da yayi masa nauyi da ya sani kawai yake a lkcn, what came over him ma yayi haka duk daurewa da shan pills da yake ga yawan tsayuwar dare, ji yayi ya tsani kansa lkci daya, bai ma san me xai kuma ce mata ba, ya fi awa biyu bakin kofar amma taki budewa daga karshe ya mike gwiwa a sake ya karasa kan gado ya xauna, yanda bai yi bacci ba daren nn haka ita ma bata yi ba, ana kiran sallah ya fita ya koma daya bedroom din, wanka yyi ya dauro alwala ya fito yayi raka'atainul fajr sannan ya fita xuwa masallaci har ya dawo Samha bata bude bayin ba, gashi duk keys din har da spare a gu daya suke, ganin gari ya fara haske ya sake komawa dakin nn ma bbu lallashin da bai yi ba amma ta ki cewa komai kuma ta ki bude masa, xaunawa yyi gefen gado yana tunanin abun yi kuma, bakwai da kusan rabi ya mike da kyar jiki a sanyaye ya fita, part din Hajiya ya tafi, ya danna bell mai aiki ta bude, ya amsa gaisuwarsa yace "Hajiya na ciki?" Tace "Ehh tana nn" yace "Kiyi min sallama da ita" juyawa tayi ta koma, bayan kusan minti biyar ya ji muryar Hajiya na cewa "Boy ka shigo mana" ya shafa kai yace "Ba jimawa xan yi bane Mami..." Mami ta karaso bakin kofar ya gaida ta da ladabi ta amsa yace "Ya mai jiki?" Tace "Alhmdllh ga ta cab tana breakfast ne ma" yace "Toh Allah ya sauwake..." Tace "Ameen boy" ya na ci gaba da shafa kansa yace "Mami dama wata yar magana xa mu yi dake if you re free pls" tace "Toh shigo daga ciki mana" Yace "A'a Mami idan ba takura i wanted mu yi shi a can ne" ya nuna balcony dinsa, Mami tace "Alryt... Mu je" daga haka suka nufi balconyn a tare, ta ja kujera ta xauna tace "Toh ya aka yi son?" Xaunawa yyi, ya d'an yi shiru sai kuma yyi kasa da kai yace "A kan Samha ne Mami" Mami ta tattara hankalinta gaba daya tace "What about her boy, laifi tayi maka ne?" Ya girgixa kai yace "Mami ba dauke ki matsayin mahaifiyata da na baro a kano, don haka baxan boye maki komai ba, amma Mami this is a secret between us...." Mami ta gyada kai tace "Ina jin ka?" Ba karamin karfin hali yyi wajen cewa "Mami Samha fa ba matata bace!" Wani kallo Hajiya ta shiga yi masa daga sama har kasa kamar bata fahimce abinda yace ba, ya dafe kansa yace "Yea Mami sai dai kuma ba xaman fasikanci nake yi da ita ba Allah ma ya shaida..." Ita dai Hajiya har lkcj kasa cewa komai tayi da ganinta kasan ba wai mamaki kadan tayi ba, ya girgixa kai da kyar yace "It's a long story Mami... And Samha ba musulma bace Mami, hasali sunanta Samantha ni ne na mayar Samha..." Buda baki Hajiya tayi tana kallonsa da mugun mamaki, ya gyada kai a hankali yace "Ehh Mami" Hajiya tayi karfin halin cewa "Aliyu???" Bai dago ya kalleta ba ya ci gaba a sanyaye yace "Gidan iyayena is just few houses away from her parent's... That is layi daya muke, My father is a soldier My mum a lecture then, Samantha was born nd brought up in a strong Christian home, mahaifiyarta Pastor ce, her dad a politician...."

*Haske writers asso*
=ث? *Noorul Huda*=ث?

By khaleesat Haiydar=???
'
41......

Cikin sanyin murya yace "Duk da layi daya muke da Samantha ni bn taba lura da ita ba sai watarana da daddare....." Nan Abuturrab ya shiga ba Hajiya Hajarah labarin tun daga farkon haduwarsu da ita har ixuwa ranan da suka bar garin kano tare, Hajiya bata samu bakin cewa komai ba da ganinta kasan kanta ya gama daurewa haka ta tsaya kallonsa baki bude, ya ci gaba kansa a kasa har xuwa abinda ya faru jiya bai boye mata komai ba sai dalilin fushin da Samha tayi, Sai a snn Hajiya tace "Ya salam! Haba Aliyu duk ilimin ka ynxu kake xaune da warce ba muharramar ka ba, why boy, ynxu ba don Allah ya tsare jiya ba me kke tunanin xae faru, me yasa ka ajiye koyarwar addinin ka sbda son xuciya?At d first place ma meye na guduwa da yar mutane ka xabi toxarta iyayen ka, wato kai ba indiye koh?" Da damuwa yace "Mami ko da ma ban gudu da ita ba nasan baxan ji dadi gun Abbana ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login